Showing 102001 words to 105000 words out of 210919 words

Chapter 35 - CIWON SO

10 Oct 2024

4252

ya isa gaban gate din ya danna horn sai police suka taso shi kuma ya sauke glass din motarsa.

%??mannu da zuwa%???

%??mauwa Mai gidan yana ciki?%???

Police dake son tantance fuskar Abiey ya ce.

%??mana da appointment da shi?%???

%??meah ka fada masa Abiey ne Mai Martaba ya turo ni%???

%??mllah sarki ni kam na ce kamar Abiey sannu da zuwa ranka ya dade%???

A take suka bude masa gate din ya kunna kai cikin gidan mai kama da wata masarauta a gurin da aka tanada domin aje motoci ya nufa ya faka motarsa yana tsara yadda zai amsawa Mai gidan idan ya tambaye dalilin zuwansa, mutumen da ya gani a kusa da motarsa ya saka ya sauke gilashin motar.

%??ma aka yi?%???

%??mai ka juyo da motar ranka ya dade masaukin bakin ta can yake%???

Abiey ya bude gurin da yake ajiyar kudi a cikin motar ya dauko bandir din 500 ya mika masa.

%??mhiga cikin gidan nan gurin matansa ka ce Abiey yana sallama da Zahra%???

Mutumen ya saka hannu biyu ya karba jiki na rawa yawu ma magana.

%??mo ranka ya dade%???


ZAHRA POV.


Da hannu Ummiter ta nuna min ??akin Hajiya Jamila sannan ta juya tayi tafiyarta, a lokacin falon babu komai amman gudun yin laifi ya saka ban hau stairs din ba na dawo na zauna a kasa har na tsawon lokaci. Ganin bata fito ba kuma wani wanda zan iya cewa yayi mata magana be fito ba yasa na tashi na fara taka stairs din har na haye sama tsintar kaina na yi a wani guri mai kama da karamin falon sai dai wannan dakunan ne a jere wasu kuma suna kalon juna, daki na biyu na nufa kamar yadda ta fada sannan na kwankwasa ban ji an amsa ba, hakan kuma be saka na kasa kwankwsawa a karo na biyu ba haka na kwankwasa har sau uku jin ba a amsa min ba ya saka na murda kofar dakin na shiga da sallama.

%??ma a shigo min ??aki Zahra sai na bada izini%???

%??ma yi ta kwankwasawa ba amsa min ba%???

%??mun da kika ji ban amsa miki ba ai kin sa ina uzuri%???

Na yi shiru ban ce mata komai ba, a yadda na lura Hajiya Jamila na da wani irin izza da nuna isa da son wulakanta mutane. Haka ta bar ni a tsaye a jikin kofar har sai da na gaji da tsayuwa na juya zan fice sannan ta yi min magana.

%??mna zaki je? Ki zo ki ba shi nono mana%???

Na juyo na dawo kusa da inda take zaune, na karbi yaron na zauna kan kujera na bude nono na saka masa rigar baki tare da Bismillah, wani irin dadi ne ya ziyarce ni sam yau ko ciwon da nake ji idan ina matsa nono ban ji ba, tashi ta yi ta rufe dakin da key sannan ta juyo ta kalleni

%??mdan kin gama bashi nono ki dora shi akan gado, ga blanket nan a kasa ki shimfida ki kwanta%???

Na kalli blanket din dake aje a kasa na kalleta.

%??mo dai baki san inda na fito ba be kamata ki wulakanta ni ba%???

%??mu to da miye nufinki? Ki hau saman gadon miliyan uku ki kwanta? Ni na kwanta ke ki kwanta?%???

%??mudi ba hauka ba ne Hajiya Jamila, kuma ni ba aiki na zo yi miki ba taimako kika nema kuma na yi miki, na fi karfin wulakanci%???

%??mlhamdulillah tun da har kin san ina da kudin, taimako kuma ke ake yi ma alfamar%???

%??mi dai na ke muku alfamar ko ba komai kin ci amfanina tun da na baki abun da kudin da kika takama da su ba su ba ki ba%???

Ina ganin yadda ta bata fuska na san kalamaina ba su yi mata dadi ba.

%??mudi sun biya bukata domin sun siya min abun da baki san kimarsa ba, kin zubar da darajarki ta uwa, kara ni neman haihu ya saka ni aikata abun da na aikata ke kuma fa?%???

Na sauke kaina kasa ina jin rashin kyautawar abun da na aikata.

%??ma a haife ki ba Zahra, ba ayi wata ??iya mace da zata tako har cikin ??akina ta fada min bakar magana ba, aje min yaro karki shayar da shi bakin nononki%???

Ta furta da karfi sannan ta nufi wayarta ta dauka ta kira Dr Hamid tana ta masifa a waya har da su rantsuwar ba zan kwana a gidan ba. Ni ko sai na ji kamar na ce ta yi hakuri saboda na samu kasancewa da ??ana. Tana gama wayar ta jefar da ita kan gadonta ta nufo ni ta karbe yaron da karfi bana son na yi kokuwa da ita ??ana ya ji ciwo hakan yasa na sakar mata ta cire bakinsa daga nono sai ya fashe da kuka.

%??mice daga ??aki.. Wawuyar banza kazama%???

%??mazamar da ta yi miki amfani ba, wawuya kuma bata wuce ki ba wanda ke wulakanta matar da ta taimaki rayuwarta ta rufa mata asiri%???

Na fada a fusace sannan na juyo na nufi kofar na bude na fito, ban san miyasa Hajiya Jamila ta son wulakanta ni ba, daga taimako sai kuma abu ya koma da cin mutunci kamar wata Kishiyarta. Falo na dawo na zauna sai da na zabi kujerar da nake kyautata zaton tafi sauran tsada sannan na zauna zuciyata har bugawa take saboda bacin rai, ba dan kura ta yi lafiya ba karnuka har sun isa su yi mata haushi. Ina zaune akan danna door bell din falon sai na tashi da sauri na isa gurin kofar a zatona Dr Hamid din na da ta kira ya iso, sai dai ina budewa sai na yi arba da wani mutumen da ban sani ba.

%??marka da dare dan Allah ki ce ma Hajiya wai Abiey yana sallama da Zahra%???

Da mamaki na kalli bayan mutumen sai dai ban hango kowa ba.

%??mna yake?%???

%??mana ta can gurin motoci%???

Na kara bude kofar na saka takalmina na fito ina da mamakin waya fada masa ina? Miya zo? Anya ni Zahra? Kuma Abiey dai wanda na sani ko wani. Bayam mutumen na bi sai ya nuna min inda wata bakar mota take fake, tsaye yayi na ki na karasa ina ta kallon motar sai gashi ya bude motar ya fito fuska ba yabo ba fallasa ya doso inda nake, be karaso ba yaja ya tsaya yana kallona.

%??ma gaske ke ce?%???

Na kalli ko'ina na gidan tunawa da na yi da Dr Hamid yace min akwai camera a gida na karasa kusa da shi.

%??me kake yi a nan?%???

%??me zan tambaya? Miya kawo ki nan?%???

%??ma ruwanka, ka fita sabga ta%???

Na juya sai na ji an riko dantsen hannuna an jiyo da ni da karfi.

%??mahra saurareni mana, mi zai saka ki zo aiki a gidan nan? Me kika rasa?%???

%??man sani ba, and for your information karka sake zuwa gidan nan%???

%??mai kuma me?%???

Na kalleshi da kyau sannan na furta.

%??m hate you%???

%??mnd...%???

%??m hate you na tsane ka%???

%??mnd...%???

Na rasa kalmomin da zan hada na fada masa maganar da zata masa zafi domin na lurar wadandan basu jika shi yadda na ke so ba. Muna cikin wannan halin aka haske mu da mota kamin daga bisa aka kashe fitilar motar mai motar wanda Dr Hamid ne ya faka a kusa da inda muke tsaye har lokacin Abiey na rike da cinyar hannuna dake cikin hijabi.

%??mafiya?%???

Shi ne abun da Dr Hamid ya fara tambaya a lokacin da ya fito motar, sai Abiey ya sake ni ya kalleshi.

%??mkay kai ka kawo ta nan kenan?%???

Dr Hamid ya kalleshi irin duba na tsanaki sannan ya kalleni.

%??muce mu je ciki Zahra%???

%??mo ta shiga mu gani%???

Abiey ya fada yana hade fuska kamar ba shi ba, haka nan kuwa na samu kaina da masa juyawa na koma cikin gidan kamar yadda Dr Hamid ya bukata.

%??mhiga mota%???

Dr Hamid ya fada, nan ma ina cira kafa Abiey ya ce.

%??marki shiga motar nan%???

Ni dai kam na yau san Abiey ba a banza ya zo min ba, sai da yayi min asiri domin umarninsa na bi na kasa shiga motar.

%??miye tsakaninki da shi?%???

Dr Hamid ya tambaya.

%??marka sake tambayar abun da yake tsakanina da ita, and karna sake ganin inuwarka a inuwarta, ke kuma tun har kin fi son haka mu zuba zuwa ni da ke i will show you my other side%???

Ya karasa yana kallona babu wasa a maganar shi kamar yadda fuskarsa ma ta nuna.

%??mhiga mota mu je%???

A nan kam Allah ya ba ni ikon karya sihirinsa na ki bin umarninsa amman ban iya furtawa ba sai hade hannu da na yi na juya na nufi gate ina takawa da kafafuwana a lokacin har an fara yayyafi, haka na isa gate din suka bude min na yi tafiyata na bar su can a tsaye sai da na yi nisa na fara jin tsoro ga ruwa ya fara karfi kamar na juya na koma sai ga motar Abiey ta faka gabana, bude motar yayi ya fito ya nufi bayan motar ya bude ya dauko hula da wata jacket ganin haka yasa na ja na tsaya ina kallonsa har ya karaso kusa da ni ya dora min jacket din saman hijab hular sanyin dake kansa hannunsa ya saka min a kai.

%??muce mu tafi Malama%???

%??mi ba zan shiga motar ba%???

%??maya ce ki shiga?%???

Ya nuna min hanya sai na wuce gaba yana bayana, ina ta jiran ya fara rokona na shiga motar ya kai ni gida amman be yi ba har na wuce motar ina jin lokacin da ya rufe ta ya biyo bayana muka fara takawa a kasa ga ruwa sai karfi yake karawa, na san kuma idan na yi tafiyar lafa ni da isa sai Asubahi domin ni ba gwanar tafiya a kafa ba ce ga unguwar babu mutane sai mu kamar mayu.

%??ma fiki zama bad boy ai, idan arziki be miki ba ai tsiya zata miki%???

Na juyo a fusace.

%??mna ruwanka da ni wai? Na tsane ka Abiey ka fita daga rayuwa%???

%??ma zan fita ba%???

Ya amsa min kamar zai doke ni yana matsawo kusa da ni har muna shakar numfashin juna ni da shi...





ABIEY POV.

A hankali ya busar da iskar bakinsa ya gyara zaman hannunsa na hagu dake aljihu, hannunsa na dama kuma na rike da kofin ruwa. Can kuma ya ciro hannun ya duba agogon dake daure a hannunsa.

%???9:13pm%???

Ya furta sannan ya aje daga kai yana kallon harabar gidan tare da kurba ruwan, ajiyar zuciya ya sauke ya sunkuya ya aje ruwan ya dauki keys dinsa dake kan mini center tebur dake gurin ya juyo ya fito daga backyard din ya dawo cikin dakinsa, kai tsaye ya zarce zuwa kofar fita dakin kamar an korashi haka ya sauko stair ba karamin dadi ya ji ba ganin falon ba kowa, balle ya tsaya amsa tambayayiyin Ammy na ina zai je. Yana isa gurin kofar falon ya bude ya fita be san key din wace motar ce a hannunsa ba har sai da ya latsa key din wata kafirar BMW ta yi kara, sai ya zagaya tsakamin motocin ya nufi inda take ya bude ya shiga yana reverse ya kunna kai daman masu kula da shiga da ficen gidan tuni suka wangale masa gate. Driving kawai yake yana tunanin yadda zai wanke Zahra a gurin Ammy da Anty, musamman ma Anty da yake ganin ta fi kowa daukar abun da zafi.
In 35min ya iso kofar gidansu Yasmin horn yayi aka bude masa sai ya samu guri a harabar gidan ya faka, hakan nan kawai yake jin baya bukatar shiga ciki daman ba gurin Momy ya zo ba balle yace zai shiga ya gaishe ta, wannan zuwan na Yasmin ne kawai, wayarsa ya ciro dake aljihu ya kiran number Yasmin kamar ba zata dauka ba sai kuma ta yi picking.

%??mito gani nan waje%???

Jimmm ta yi kamar ba ta ji abun da ya fada mata ba.

%??moh%???

Ta amsa ya yanke sannan ya maida dubansa gurin kofar falon yana jiran fitowar Yasmin. After like ten min aka bude kofar ta fito tana sanye da doguwar rigar atamta sai mayafin da ta rufe jikin, bude motar yayi ya fito yana jiran karasowarta ita kam bata yarda ta kalleshi ba har ta iso inda yake tsaye.

%??marka da dare%???

%??mow are you?%???

Ya bukata kamar an masa dole sai a lokacin da kalleshi hawaye na sauko mata wasu kuma na taruwa a idonta.

%??m'm not fine%???

%??me too%???

Ya furta yana dauke kansa ya kalli sararin samaniya da iskar hadari ke kadawa.

%??ma zo na yi magana da ke ne akan maganar mu shiyasa ban shiga ciki na gaisa da Momy ba%???

Yana maganar tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi.

%??ma yi magana da Abbah Musa na fada masa ina son a fasa zancen baiko...%???

Sai kuma ta yi shiru, Abiey ya tattara dukan hankalinsa da natsuwarsa ya mika mata zuciyarsa na wani bugawar dadi.

%??mhen... Ina jinki%???

%??ma ce ba zan raina musu hankali ba, ban isa na zubar musu da mutunci ba, miyasa ban fadi haka tun kamin su amsawa Mai Martaba ba, sai bayan sun amsa zan taso musu da wata maganar, wai ban isa na maida su kananan mutane ba, ba za su yarda matsala ta taso daga garesu ba, kuma babu fashin aure sai idan kai kace ka fasa....%???

A take annashuwa da farincikin dake tare da Abiey suka gushe.

%??mhat...! What do you mean? Yasmin ya zaki saka ni a matsala... Ya salam.. %???

Ya fada yana juyawa ya daki motar da mugun karfi, kana ya juyo ya rika hade kafadunta yana jijjigata da karfi.

%??masmin ya zaki min haka? Tun abun na sabo da kin yi abun da na fada miki da yanzu haka be faru ba! Miyasa zaki saka mi a matsala?%???

Sai ta amsa masa cikin kuka.

%??mai ka saka kanka a matsala Abiey, miyasa zaka saka zobe a yatsan da ka san idan har za a cire shi sai dai a gutsure shi? Miyasa zaka ambaci sunana a bagirin da zuciyata ta dade tana nema? Na sani ba zaka taba so ba Abiey ni kuma ban isa na bude zuciyata na cire soyayyarka ba....!%???

Sakinta yayi ya matsa baya ya nuna kansa with shock, sai ta daga masa kai ta saka hannayenta biyu ta rufe fuskarta ta fashe da kuka. Baya baya Abiey yayi har sai da ya jingina da motarsa ya dafe kanshi ya duka a gurin yana jin wani zazzabi na taso mashi.

%??ma shiga uku... Yau na ga Idi zigidir%???

Sai kuma ya mike tsaye yana girgiza mata kai.

%??masmin ba zaki iya zama da ni%???

Ta cire hannayenta daga fuskarta tana kuka.

%??man iya%???

%??muciyata babu wanda take so sai Zahra da Zahra ita kadai...%???

%??man roka maka Allah ya sassautawa maka son Zahra Abiey%???

Addu'ar da tace zata yi ta yi farraku tsakaninsa da Zahra sai ya saka a take ya ji ya fara tsanarta.

%??mmadadin kin min addu'a ki raba ni da Zahra, me zai hana ki yi ma kanki addu'a so na ya fita daga zuciyarki?%???

%??mamin yau... Na roka a dare mabanbanta, ka min a kawo yanzu na roka amman ba a amsa min ba sai ma aka kara kawo kusanci a tsakanina da kai ta inda ban zata ba%???

%??masmin indai kina so so na hakika to ba zaki so na shiga matsala ba, kuma zaki so abun da na ke so%???

%??mndai har da gaske kana son Zahra to zaka fi kowa fahimtar halin da nake ciki, Ciwon So masifa ne Abiey da ace ina da iko da ban bari Son ka ya shiga zuciyata ba%???

Ta fadi durkushe kasan guiwoyinta tana kuka, ita kadai ta san abun da take ji, ita kadai ta san halin da take ciki akan Abiey kuma tabbas da zata iya da ta cire soyayyarsa a zuciyarsa, gana daya sai jikin Abiey yayi sanyi, durkusawa yayi kasa ya rika hannunta sannan ya matsa kusa da ita sosai ya rumgume ta a hankali.

%??m'm sorry....%???

Lumshe ido ta yi tana jin kamar ta saka wuka ta tsaka kirjinsa ta shiga cikin jininsa ta kwanta, sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya mike tare da ita tsaye.

%??mi shiga ciki ki huta zamu yi magana daga baya okay%???

Dagowa kai ta yi ta kalleshi sannan ta daga da ga jikinshi tana jin kamar ta rayu a kirjinsa rayuwa ta har abada.

%??ma yi hakuri idan na bata maka rai...%???

Ya hade yawun bakinsa.

%??mo dukanmu ba ma iya sakawa junanmu abu kuma ba ma iya cirewa, ko wace zuciyata tana juyawa bisa ga ikon da Ubangiji ya bata, da ace dan adam zai iya wani abu, na tabbatar da yanzu Zahra ta cire so na a zuciyarta, amman ta kasa saboda bata da iko akan komai, abun da ta yi min dazun yanzu ya kara tabbatar da da har gobe Zahra tana kaunata%???

Yasmin ta yi murmushi irin murmushin nan da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo.

%??mahra ta yi dace Abiey ka rayu da soyayyarta na tsawon lokaci%???

%??masmin.... Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, ni da ita mun kamu da kaunar junanmu ba tare da mun sani ba, sannan Zahra ta cika duk wani sharadi da na ke so a mace, ko kadan bana son na auri mace da ita take so na ni bana son ta, saboda zan iya cutar da ita, Yasmin na shiga a zuciyar Zahra na nuna mata kauna kamin abubuwa su canja mana, ba zan manta lokacin data durkusa har masa tana rokon kar na fasa aurenta ba amman ban iya yin komai ba saboda Deen ya shiryar mana gadar zare, wannan ce damar da nake da ita wanda zan nuna Zahra cewar ina kaunarta irin kaunar da babu wanda ya taba yi mata irinta, ina son na rayu da Zahra fiye da yadda kike jin kina son rayuwa da ni....!%???

Yana kaiwa nan ya bude motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar Yasmin a tsaye ta bishi da kallo.

%??miwon so yana dawainiya da kai Abiey, ni kuma be bar ni ba, %?}io%??? baka kyauta mana ba%???

Yasmin ta fada tana hawaye jikinta sai kamshin turaren masoyinta yake.


*** *** ****

Tuki kawai yake yana jin kamar bata son komawa gida, kuma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login