Showing 201001 words to 204000 words out of 210919 words

Chapter 68 - CIWON SO

10 Oct 2024

4202

yarda son Zahra ya saka ka zalinci Yasmin, kuma karka nuna musu banbanci kyautatawa ce kawai ba zan cilasta ka ka yi ma wata ka hana wata ba, dole wannan wanda ka fi so ko kuma wanda ta fi kyautata maka kai ma ka kyautata mata, kuma ban baka shawarar ka aje su a gida daya ba, domin kazantar da baka gani ba tsabta ce inji hausawa, idan daya bata ganin daya an fi marmarin juna, kuma wata soyayyar da zaka nunawa daya ta banbanta da wata ba lallai ne dayar ta sani ba, sannan karka yarda ka nunawa Zahra ka fi kaunarta akan Yasmin haka ma karka nunawa Yasmin ka fi kaunar Zahra akanta, kuma karka wulakanta ko wace, kar ka daya wata ta zagi wata a gabanka, karka aikata irin kuskuren da mahaifinka ya aikata wanda ya haifar mana da matsala a yanzu%???

Ya jinjina kai cike da gamsuwa da shawarwarin da Ammy ta ba shi.

%??mn'Shaa Allah, Allah ya ba ni ikon yin haka, amman abun nan ba sauki, ni ban ma taba sammanin zan iya zama da mace sama da daya ba%???

%??maman haka rayuwa take, kana nata Allah na nashi, dukam mu ba mu yi tsammanin haka ba, kai dai ka yi ta godiya ga Allah na yadda abubuwa suka zo maka da sauki kuma cikin farinciki da jindadi%???

%??mna ta yi kuma zan kara i love you sweet Mom, Amman ina son na fada miki Zahra ta barwa Allah Mr Bashir Amir%???

Abiey ya karasa yana kallon Dr dake murmushi domin ta san da labarin, Ammy kuma da take jin labarin wani banbaragwai ta zaro ido ta rufe baki.

%??ma sanar yana ra murna, ya fada a yanzu har ya fi jin kaunar Amir fiye da baya, ta yi abu mai kyau domin ta rufa masa asiri kuma shi ma ya cancanci haka, ya kira ni da kansa ya fada har ya nemi na zama mai rike masa sirrinsa%???

%??mmman Zahra ba ta yi tunani ba, anya kuwa da sanin mahaifiyarta ta aikata wannan abun?%???

Abiey ya kalli Ammy dake tambayar.

%??ma saninta ta aikata, ita ma ta bata shawarar yin haka wai suna tunanin haka zai fi saboda tana tsoron kar labarin ya fita ace ita ta aikata, kuma tace min yaron ma kuka yake idan ta rabe shi ya fi sha'awar zama a gurin Mr Bashir din, and Ammy kin san indai yaron nan yana hannun kakaninsa ko gurinmu hankalina ba zai kwanta ba, domin Zahra zata tattara hankalinta gaba daya ta maida gurinsa ne, ba dan abun da ubansa yayi ba da yanzu ??ana ta haifa ba Amir ba%???
12/28/22, 11:23 - Buhainat: %??mai dai Abiey kana ta kishin mutumen da bashi raye, ni fa har yanzu ina ganin Deen ya aikata abun da ya aikata ne saboda yana son Zahra, kamar yadda ka aikata abun da ka aikata a yanzu wanda na tabbatar da ace Mai Martaba da Ammy tsine maka albarka za su yi zaka yarda ka sauki wannan%???

A take ran Abiey ya bace da maganar da Dr ta yi.

%??maman ai kina goyon bayan abun da ya aikata shiyasa ba ki ganin laifinsa, and that's why i hate him so much wannan Amir din ma ba dan Zahra ba da babu abun da zai saka na kula shi, domin jinin makiyina ne%???

Ammy ta ce.

%??manzu ai komai ya wuce tun da shi ya bar duniyar kuma ka mallaki Zahra a yanzu me ya rage, gashi Allah ya kara maka da Yasmin zaka auri budurwa kai ma ayi maka wanka lalle irin yadda ake yi ma kowa%???

Mikewa yayi tsaye ya fice daga dinning.

Mama Lami ce zaune a gaban Mai Martaba yana kallon video da aka turowa Mai Martaba na wasu yan jarida gudu uku sai dai dayan cikin ruwan sanyi ya bada amsar wadanda suka saka shi, sauran kuwa sai da suka sha wahala sannan suka fadi cewar Rilwan ne ya fada musu komai kuma ya bada umarnin su je su dauki rahoton har ya hada musu da tukuicin kudi. Mama Lami dake rike da baki ta girgiza kai jikinta sai tsuma yake idonta sun yi kwayan irin na marasa gaskiya domin tonuwar asirin ??anta kamar nata ne, domin ita ta saka shi yin komai da saninta aka aikata.

%??mannan sheri ne kawai%???

A take Hajiya Kilishi ta karba mata.

%??mauwa ni ma ai na fadi haka, domin mutane babu sherin da ba a iya ba ko dan a haka shi da Mai Martaba%???

Anty Amarya ta tabe ki domin ta san borin kunya suke kuma bakinsu a hade yake.

%??mallahi wannan sheri ne aka yi masa Mai Martaba ka fahimci haka, akwai wanda ke son ya hada ka da shi ne, shi kanshi Abiey ai zai iya haka saboda kar sunansa ya bace shi kadai%???

Mai Martaba ya mika hannu ya karbi wayarsa rai a bace.

%??ma tara ku a nan na nuna muku wannan saboda na gargade ku, ku cire idonku da hannunku akan ??ana, saboda ina fushi da shi, hakan ba yana nufin bana sonsa ba ne, kamin na nuna miki video ne saida na yi magana da Rilwanu kuma ya karbi laifinsa, kuma ya fada min gaskiyar abun da ya faru daman can na saka ran wannan abun a tsakaninku ya fito, domin idan ba nan ba babu ta inda labarin nan zai fita, Abiey ya fada min cewar ba shi ya rusa gidan nan ba, yanzu ma na kara yarda hakan domin Rilwan ya fada min cewar ke kika saka shi, kuma be kara min komai ba sai son Abiey da godiya ga Allah da ya ba ni ??a irin Abiey, ina son na ja kunnenku ne gaba dayanku kar na sake ji ko ganin wani abu makamancin wannan akan kowa balle kuma akan Abiey, inda hakan ta sake faruwa na bincika na gano gaskiya to zan dauki tsastsauran mataki akan haka%???

%??mmman Mai Martaba wannan ba adalci ba ne, daga mutane sun fadi sunan Rilwan sai ka dauka da gaske ne, kuma har ka tara mu kana mana irin wannan gargadi akan wani ??ana kamar su sauran ba haihuwar ka yi ba?%???

Cewar Hajiya Kilishi a kokarinta na tarewa yar'uwarta laifin da dukansu sun san gaskiya ne, har Rilwan dake zaune a can gefe sai gumi yake, ya kasa dago kai ya kalli kowa.

%??mana kwai sai da zakara, ba iya wannan abun suka fada ba, har shaida sai da suka nuna ta kudin da ya tura musu da kuma maganar da yayi da su, shi ma ai be amsa min laifinsa kai tsaye ba sai da ya ga hujojin da ba zai iya wanke kanshi da su ba, saboda haka ina gargadinku dukanku ku cire Idonku akan Abiey, ba shi kadai ba har da sauran yayana, idan wani abu ya sake faruwa ko wacce ku ta shiryawa zaman yayanta, domin zan iya zabar yayana akan matana, idan baku taimaka min na hada kan iyalina ba, be kamata a same hannunku a cikin ruguzasu ba%???

A take Mama Lami ta saka kuka, Hajiya Kilishi na bata hakuri.

%??mi yi hakuri, wannan abun duk sherin makiya ne, shi kansa Rilwan din da wahala idan a hayyacinsa ya amsa cewar ya aikata wannan abun ,domin ba halinsa ba ne kuma babu yadda ba a iya ba, shiga tsakanin uba da ??a ko uwa da uba duk ana yi%???

%??milishi ki yi zaman yayanki, Zuwaira tashi ki koma bangarenki%???

Mai Martaba ya fada cikin bacin ran musun da Hajiya Kilishi ke masa, gaba daya kamar bakar kaza yake ganinta a yau.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Anty Amarya ya rufe baki da sauri, jin Mai Martaba yayi furucin da bata taba sa ran zai iya ba ga matan da take ganin sune yan lelensa kuma yan gaban goshin da sai abun da suka fada ake yi. Wani irin zabura Hajiya Kilishi ta yi ta daki kirjinta.

%??mi kuma? Ni Mai Martaba? Daga bada hakuri sai abu ya dawo kaina, aa ba dai ni ba Wallahi, haba Mai Martaba ni miye nawa a ciki daga ba da hakuri, dan Allah ka yi hakuri, abun da ba ayi da kurciya ba yanzu bayan an yi yaya da jikoki za a ce a rabu ka dubi girman Allah ka yi hakuri%???

Ta kai kasa tana kuka tana rikon kakafuwansa mikewa yayi tsaye yana kokarin shi na janye kafafuwan na sa yayi ma Anty Amarya alama da ta tashi ta tafi domin mamaki abun da ya faru ya saka ta manta da umarninsa.

%??mo Wallahi ba ki isa ba, Lami idan ma wani kullin ne kika shirya min to wutar ba zata ci ni kadai ba, daman ai kishiya ba yar'uwa ba ce, ba ki yin min da kurciya da zan iya aurowa ba sai yanzu da tsufa ya kama, wato ki zauna ki mulke gida yadda kike so?%???

Lami ta fara yi mata alama da ido cewar ta yi shiru, amman ina son a yau Hajiya Kilishi bata sauraren maganar Lami saboda an yi mata abun da ba a taba ba, kuma akan abun da ba ita ta aikata ba.

%??ma zan yi shiru ba, ai babu kalar shirinki da ban sani ba, haka kika yi sai da kika fitar da Umaima a gidan nan, ke da bakinki kika fada min indai kina raye ita da duk zuri'arta ba za su taba samun muhalli a zucutyar Mai Martaba ba, shi ne a yau ni zaki dawo kaina? To Wallahi sai dai niyarki ta biki, kuma Wallahi ke kika saka aka rusa gidansu Zahra, saboda ki kulla masa sheri kika aika ??anki Rilwan ya saka yan Jarida su kitsa wannan abun saboda ki bata tsakanin ??a da uba%???

Lami dake tsaye kamar karan dawa ta girgiza kai cikin kwarewa ta iya makirci na mata.

%??mallai kin hauka a yau Kilishi ni kike kullawa wannan sheri saboda abincinki ya kare a gidan nan? Kamar ni nace Mai Martaba ya sake ki? Ina kika kai hankali ne? Idan ma kishi ne ai an yi can da da kurciya amman yanzu girma ya kama an watsar da komai, kuma idan magana kike ta asiri ai tare muka aikata domin munduwa daya bata amo, har kara ni na yi na iya wanda mijina zai kauna ce ni ne, ke fa ke da bakinki kika fada min cewar Umaima har ta mutu ba zata sake aure ba, kin riga kin jefeta da mugun kullin, wannan haukar da kike ma amanarta ce ta kamaki Wallahi shiyasa kike fadar abun da kika aikata kina dangantasu da ni, amman ni ban san wannan sherin na ki a ina ya zamo asali ba%???

Kilishi ta yi cikinta kamar za su daki juna sai ka rantse da Allah ba manya yaya ne da su ba.

%??marya kika yi, Wallahi ke kika shirya komai ai daman kin fada cewar babu macen da zata yi mulki bayan ke, Zuwaira ma da aka kawo daga bayan nan mallake kika yi kika saka mata tsoronki kin mallake kowa a gida, ni ma ai banza kika bar ni kuma Wallahi Allah ya isa%???
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Mai Martaba ya nade hannayensa baya yana kallon dramar da ake a gidansa, abun da be taba tsammanin faruwarsa ba, kuma be yi zaton da sa hannun matansa a lamarin Ammy ba. Anty Amarya ta mike tsaye idonta cike da kwalla na tausayin Ammy ta fice daga falon ba tare da tace komai ba tun da Mai Martaba ya tarasu har rikicin ya faru. Da gangan Hajiya Kilishi ke fadar abun da Mama Lami ta yi saboda Mai Martaba ya ji komai domin a tunanin Mama Lami ta shirya mata wani abun ne ta fitar da ita a gidan ta wargaza mata yaya, daman can ana zaune ne kawai amman babu aminci da yarda da juna, ko wace tana yi ma yar'uwarta asiri. Uffan Mai Martaba be sake cewa ba ya fara takawa cikin takun kasaita irin na manya sarakuna ba tare da ya san yana yi ba.
Dakinsa na bachi ya shiga sai da ya kai karshen dakin sannan ya daga kansa sama yana jin zuciyarsa babu dadi, be taba jin bakinciki rayuwa da Ammy ba irin yau, ya dade yana tambayar kansa dalilin kauracewa matarsa da yayi wanda hakan ya jefata ga halaka, i duk lokacin da zai waiga ya duba sai ya tarar babu wani laifi da ta yi masa kawai ya kasa zama da ita ne, har abun da ya faru ya saka shi sakinta.

ANTY AMARYA POV.

shiga bangarenta ke da wuya ta dauki wayarta ta kira Ammy, bugu daya ta yi Ammy ta amsa kiran.

%??mssalamu Alaikum%???

Amsa sallamar ma bata Anty bata samu yi ba, ta fara zayyana mata abun da ya faru cikin kuka.

%??mi gode, a yanzu komai ya zo karshe, kara ke an sake ki da kurciya ita kuma yanzu da tsufanta ya haramtawa kansa ita domin yace ta yi zaman yayanta kuma na tabbatar bakin ciki ba zai bari ta iya zama a cikin gidan nan ba%???

%??mani abun a nesa yake na yarda, na sha wahala, na rayu a cikin bakinciki tun bayan fitowa a gidan nan, kuma Allah yayi musu yadda suke so sun raba auren kuma sun yi nasarar yin min aikin kar na auru, tabbas tun bayan fitowa ko kare be sake zuwa yace yana so na ba, amman hakan be dame ni ganin ina da Yaya sai na maida hankali gurin rainon yayana%???

%??mllah ya saka miki Ammy, Allah ya isar miki%???

Ammy ta share hawayen da suke mata zuba mata ta ce.

%??ma isar min ai, sai dai a lahira ayi wannan shari'ar, a cikin yayansu waye na kwarai? Matan ne kawai suka samu gurin zama mai kyau amman mazan daga masu neman bata masa suna sai wadanda ke jiran ya mutu a raba gado a ba su, ni ko ki dubi ni Zuwaira ba fariya ba Allah yayi min komai a cikin yayana babu lalatacce, dukansu suna aiki kuma suna arzikin da za su iya gogawa da masu kudi ko masu mukami, a cikin yayana ina da sojan sama da na kasa ga babbar likita a kuma Aliyu babban dan kwallon da duniya ma tana ji da shi, to me Allah ya rage ni da shi? Alhamdulillah, shiriyar yaya ai ita ce babbar shiriya iya haka ni Allah yayi min komai, balle kuma yanzu da Allah ya bawa ??ana matar da yake so kuma ya shirya tsakaninsa da Mahaifinsa%???

%??maka ne, idan Allah ya hana ka wani abun sai ya baka wani, hanyoyin Allah yawa ne da su, Allah ya karkato da hankalinsa ya dawo dake cikin gidan nan, hankalin Abiey zai kara kwanciya%???

Ammy ta yi murmushi bakinciki still hawaye na kwaranya a idonta.

%??mliyu ai be rasa uwa a gidan ba, ke zaman wa kike ba ??ana ba? Wallahi ko mutuwa na yi a yau na san Aliyu ba zai yi maraici ba saboda ke, ke ma kuma lokacin jindadinki ne ya zo a yanzu a da can sun kame gida babu mai iko sai su, yanzu kuma komai ya wuce, ni kam sai aljanna idan Allah ya ba ni ikon zaben abokin rayuwa, amman zaman aure tsakanina da Mai Martaba ya kare har abada, yanzu aure ba ya burge ni ai sai dai mu yi ta bawa yaya shawara%???

Da tausayin Ammy Anty Amarya ta yi sallama, domin an raba aurensu ne a lokacin da suke matukar kaunar junansu kuma suke da kurciyar zama a tare, a zaton Anty Amarya Mai Martaba yayi ma Ammy saki uku ne da babu gyara shiyasa ba take fadar cewa zamanta da Mai Martaba ya kare a duniya.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: ONE MONTH LATER...


ZAHRA POV.

Abubuwa da yawa sun faru a wata nan, a cikin akwai tarewa ta a gidan mijina kuma masoyina wato Abiey, da kuma tarewa Mama a gidan da Abiey ya gina dake fuskantar na mu na da, wanda ya cilasta mata zaunawa a ciki duk da kasancewar Mr Bashir yayi mana kyautar gida na alfarma. An yi bikin nadin sarautar da ya amsa nadin sarautar da aka dade ba ayi irinsa ba. Domin an kashe naira kuma cikin ya samu halarta manyan mutane daga bangaren Ammy da Mai Martaba sai ka rantse sabon Sarkin Kano aka hada ba dansa a matsayin Galadima ba.

Hakika na ga kauna da soyayya daga gurin Mai Martaba a ranar da aka shiga da ni Masarautar da sunan gaisuwa kamin ya a kawo ni gidan da zan nake da tabbacin shi ne na zamana har aljanna. Mai Martaba ya tara iyalansa ciki har da yayansa da matan biyu wato Hajiya Lami da Anty Amarya jawabin maraba da ni a cikin zuri'ar bayan ya kira da sunan Mahaifiyarsa, kyautar tsadadiyar Alkyaba yayi min a take aka saka min ita a gurin aka cire yan kunena na zinari aka saka min wasu na zinarin da Mai Martaba yayi min kyauta da su na miliyoyin nairori, ranar yayi mana nasiha ni da Abiey sannan aka yi addu'a tare yi mana fatan zaman lafiya, turaren da aka feshe ni da shi sai ka rantse da Allah a gidan aka kafa kamfanin turare. A lokacin da zamu fita gidan Anty Amarya ta bada sabuwar motar da aka kawata da balon balon da fulawoyi da kuma jan kyale. Ni kadai aka dauka a motar wasu motocin suka shiga gaba wasu a baya masu busa na ta aikinsu har muka isa gidan da aka kawata da kusasasun dawankan Abiey guda Hudu. A ranar na ga taron mutane sosai ashe Ammy ma tana da yan'uwa da yawa domin sun yi ta zuwa gidan ganin Amaryar ??anta a cikin har da matan yayun Abiey Wato Yaya Auwal da Sani, ta bangaren Mai Martaba ma na ga yaya da yawa wanda ya kara tabbatar min da lallai na shiga babban gida mai cike da zuri'a da kuma sarauta, kowa a unguwar sai da ya san matan Abiey aka kawo kuma surukar Mai Martaba saboda busa da aka cika kofar gidan da shi da kuma shigowar manyan motoci. Na ga baki kala kala wasu am har na manta rabon da na ga fuskarsu, wasu tsofin abokaina ne wasu kuma makonta mu yan'uwa har da na nesa, suna ta zuwa bawa idonsu abinci.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login