Showing 15001 words to 18000 words out of 210919 words

Chapter 6 - CIWON SO

10 Oct 2024

4232

yayarsa take aiki a asibitin. Da gudu suka iso da gado gurin motar suka dauke shi suka dora saman gadon sannan suka nufi cikin asibitin da shi da gudunsu, kamin a shiga ICU da shi Dr Zainab ta shigo cikin shiga ta manyan likitoci da suke bawa manyan patient kulawa tare da wani Dr Haroon. A take suka hau ba shi kulawa Dr Zainab mace ce Jaruma mai matukar karfin hali hakan ya saka take bawa kanenta kulawa cikin natsuwa da gwarewar aiki. Cikin abun da be fi awa daya ba Allah ya sassauta masa har ya samu bachi.
Ammy ce ta kwana da shi asbiti yayi da Dr Zainab ta koma gida ta kwana, tun a dare Ammy ta sanarwa Anty Amaryar halin da Aliyu yake ciki, sannan ta kira Angon ma ta sanar masa, bikin dinner da ba a kasa da angon ba kenan ya nufo asibitin gurin duba abokinsa, sai ya duba jikinsa ya tabbatar da sauki sannan ya bar asibitin, a daren Sauban ya kwana a gidansa tare da kyakkyawar amaryarsa, Abiey kuma ya kwana asibiti tare da mahaifiyarsa. Karfe bakwai da yan mintuna Anty Amarya ta dira asibitin tare da Narjis da Aisha hankalinsu a tashe. Zaune suka samu Abiey rike da gorar ruwa Ammy kuma tana zaune saman carpet din data gama sallah hannunta rike da carji. Juyowa ta yi a hankali ta kalli Anty Amarya fuskarta dauke da murmushi

%??maraba da Hajiya%???

Narjis ta karasa gurin Abiey da sauri ta zauna, sai ya sakar mata murmushi.

%??marjis%???

%??ma'am Abiey ya jikinka?%???

%??mlhamdulillah%???

%??ma jikin Abiey?%???

Anty Amarya ta tambaya sai ya amsa mata fuska a sake.

%??mlhamdulillah Anty%???

Sannan ta maida hankalinta gurin Ammy.

%??ma jikin nasa%???

%??mashi nan ai kina gani ya samu sauki%???

Sai kuma ta sake juyowa ta kalli Abiey.

%??mbiey haka zaka yi ta saka kanka a cikin matsala kamar kanka farau soyayyah yarinya ta yi aure tana can tana rayuwa da wanda take so cikin farinciki kai kuma kana nan kana fama da tunaninta har yana neman hallaka kanka?%???

%??mnty ba za ku gane ba ne, Zahra is my first love, ko da ace rabuwar rashin mutuncin muka yi ba zan taba iya mantawa da ita ba, kuma wasu dabi'u da halayarta da na saba da su dole za su zauna min arai har a bada, balle na raba da ita ina matukar kaunarta, kuma tana so na, and the most painful part is Zahra ta rabu da ni saboda wani banzan dalili da ya rufe muku ido kuka kasa bari na auri yarinyar nan, musamman Dr Zainab%???

Ammy ta nuna kalli Anty Amarya.

%??min gani ba? Ai matsalar kenan ina ce ko wane bawa da inda Allah yake jarabtarsa kuma yayi hakuri ka ga ya ci riba a gaba, amman kai kamar kana yi ma Allah raki ne wannan abun da kake yi%???

Yayi murmushi yana jin kamar shi kadai yake iya fahimtar halin da zuciyarsa take ciki.

%??manzu ya kuke son na yi?%???

%??makuri Abiey%???

Aisha ta fada tana dawowa dayan gafensa ta zauna.

%??ma maka alkawari zan sama maka wata yarinya wanda ta fi Zahra kyau ta fita komai, kuma zuciyarka zata so ta zata ji dadi zama da ita fiye da Zahra%???

Ya daga hannayensa.

%??mine, sama min wata yarinyar is not a big deal, sai dai rayuwata soyayyata mu'amala ta da komai nawa yana gurin Zahra, so duk wanda zan aura zata zauna da gangar jikina ne kawai, ni kaina ina son aure ai. By the way da ban hakuri na yardar da kaddara ba, Wallahi da abun da zan aikata wata kila da labari be kawo yanzu ba, na rantse da Allah da sai na kashe Deen na cire zuciyarsa na datsa ta in pieces na bawa kare ya cinye, sannan na kone gangan jikinsa, ba shi ba har uwar data kawo shi duniya sai na halakata%???

Yana maganar fuskarsa na nuna tsantsan bakinciki Deen da yake jin da ace be yarda da kaddara ba, kuma shi din ba mai imani ba ne da ko mahaifiyar Deen ba zata kwana da rai ba balle Deen. Gaba daya kallonsa suka yi cike da mamaki kamin su kalli junansu.

%??mo yanzu idan baka yarda da kaddara ba zuciya zata iya turaka ga halaka ka aikata abun da ba zai sama maka mafita ba%???

%??muciyata ba zata zuga ni na aikata komai ba Ammy, domin ko da rana daya bata taba raya min na kashe auren Zahra ba, ko na dauki na kirata ba, ko na bi wata hanyar da sake sakani arba da fuskarta, ko wane dare ko wace safiya da soyayyar Zahra nake rayuwa Ammy, tun da ta yi aure ban sake ganinta ba, i delete all her pictures da duk wani abu da ya shafe ta amman na kasa goge ta a zuciyata, na san be dace na yi tunaninta a zuciyata ba saboda matar wani ce, amman i can't, so i want to you to know, this is my destiny...!%???

Ya amsawa Ammy with full confidence. Anty ta sauke ajiyar zuciya.

%??mu rufe maganar nan, Narjis zubawa Yayanki abinci ya ci%???

%??ma zan iya cin komai a asibitin nan ba, kin san bana son asibiti Anty zan tafi gida na yi breakfast a can%???

Har Anty ta bude baki ta yi magana suka ji an turo kofar dakin an shigo, Sauban ne sanye da shadda sai dai wannan karon babu babbar riga a jikinsa sai hula, sai da ya gaisa da Ammy da Anty sannan Narjis ta tashi ya zauna kusa da abokinsa.

%??marka ce min ka bar amaryarka ne ka zo nan!%???

Abiey ya fada with light smile on his face, Sauban ya kalleshi da mamaki.

%??mana nan asibiti ba lafiya zan tsaya gurin amarya? Haba Abiey%???

%??mllah dai ya bar wannan abota ta ku har Aljanna%???

Ammy na kallonsu cike da burgewa, sai suka amsa da Ameen. Abiey ya fara kokarin sauka saman gadon.

%??muje ma ka sauke ni gida bana son warin asibiti Wallahi%???

%??mnty kina jinsa ko? Jiya da aka kawo shi rangi rangi rai a hannun Allah yau kuma ya samu lafiya ya fara tijara%???

Anty ta kalli Sauban dake maganar tana dariya.

%??mada masa dai sai an zo duba marar lafiya sai a ga gado wayam babu kowa a kai? Likitoci sai su ce ina mai jinyacin ai ko?%???

%??mmmy zata fada musu na tafi gida idan sun zo%???

Ammy ta kalli Abiey.

%??maboda ga Ammyn mahaukata ko? Sai na zauna gadin gadon asibiti har likitocin su zo?%???

Duk suka saka dariya ban da Abiey da yayi murmushi tunawa da haka ta taba faruwa da shi da Zahra. Sauban ma ya mike tsaye ya ce.

%??mmmy za ku iya tafiya ai, sai ki fadawa Dr a waya in ya so kamin taje aiki sai ta je can gida ta duba shi%???

%??man gida gurin Mai Martaba ba, tare zamu wuce%???

Juyowa Abiey yayi ya kalleta kamar yayi magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi, saboda ba ya son ya yi wani furuci da zai saka ran Anty ko Ammy ya bace. A tare suka fito da Anty Amarya Narjis tana rike da hannunsa Aisha kuma tana gefen Narjis, Sauban na baya tare da Ammy da waya ke makalle a kunnenta tana fadawa Momy Uwani abun da ya faru. Mota daya Sauban ya shiga da Ammy sai da ya fara sauke ta gida sannan ya wuce nasa gidan.
Abiey da Anty Amarya da yayanta biyu kuma direba ya sauke su a Masarautar Mai Martaba Sarkin Kano Abubakar Aliyu Jauro Na Uku, ko da wasa Abiey be kalli bangaren su Mama Lami da Hajiya Kilishi ba, daman can gaisuwa ma sai Anty ta yi kamar tana yi sannan ya gaishesu, idan kuwa wata lurar ta saka shi zuwa bangarensu ji yake kamar yana saman kaya da karmami minti biyar ba zai iya yi a falon kowancce a cikinsu ba. Idan ma ka ganshi a bangarensu to cilastawar Anty ce, domin shi har mantawa yake da yana da wasu matan uban ko yan'uwan da suka hada uba daya, bayan yayan Anty Amarya Aisha da Narjis, kusan idan ka tambaye shi ma sai yace wai maka be san sunan wasu ba.
Yana shigowa cikin falon kai tsaye ya nufi upstairs zuwa dakinsa, wanka ne abun da ya fara yi ya jika ko'ina na jikinsa da turare kala kala masu matukar tsada da kamshi na tashin hankali, sannan ya sauko kasa zuwa dinning. A zahiri idan ka kalleshi sai ka yi zaton babu damuwa ko bakinciki a tare da shi, bayan kuma su ne suka hade masa kai suka yi kaura a zuciyarsa da ruhinsa, sai dai imani da yardar da kaddara ya hana fuskarsa bayyanar da hakan sai dan abun da ba a rasa ba, ko kuma idan ta dauro.

Kujera yaja ya zauna, shi kadai a dinning kuma shi kadai a iyalahirin kafon falon da baka jin karar komai sai anye air conditioner dake tsaye, warmers din ya bude sai da ya gama kalle abun da aka shirya a gidan na karyawa sannan ya dauki karamin plate ya zuba soyayen dankali da ya hada ruwan tea, ya soma karyawa daman shi ne favorite food nasa, sai da ya gama karyawa sannan ya saka hannunsa aljihu sai ya ji babu wayarsa, runtse ido yayi ya bude ya tashi a dolenss ya nufi upstairs, yana shiga ya samu wayar tana vibration. Safeena ya gani a rubuce saman screen din wayar, dan murmushi ya yi sannan ya kai hannu ya dauka ya nufi inda iPod's dinsa suke ya dauko expensive one yayi connection sannan ya sake kiranta.

%??mey Safeena%???

%??mi Handsome%???

Jimmm yayi kamar ba zai ce komai ba, he is just breath without saying anything, every act, every word, every move is reminding him Zahra, haka take kiransa idan ya ce Hey Pretty sai ta ce Hello Handsome.

%??ma jikinka?%???

Safeena ta katse masa tunani.

%??mlhamdulillah%???

%??mana asibiti?%???

%??mna gida%???

%??maman na san da wahala ka iya zama asibiti ai kai da baka son jinya%???

Ya shafa kansa ya nufi katon dressing mirror dake tsaye yana kallon kyakkyawar surarsa da kwarzantaka da haifa irin ta zakin namiji.

%??man iya aje wayar%???

Ya furta jin ta yi shiru bata ce komai ba.

%??meah why not get well soon please%???

%??m pray so%???

Ya sauke wayar ya saka ta aljihunsa ya nufi inda keys din motarsa suke ya dauko new one na sabuwar motar da ya siya last couple months. Cike da kuzari yake saukowa stairs din agogon GMT dake falon ya soma bada sanarwar 10am, kallon agogon yayi ya dauke kai ya nufi kofa.

%??mbiey...%???

Ya juyo da sauri ya kalli Anty dake fitowa ta kofar baya.

%??meah%???

%??mna zaka je?%???

Ya dan tabe baki kamar mai tunani, can kuma ya daga kafadunsa.

%??m don't know, maybe somewhere else%???

%??ma shiga ku gaisa da Mai Martaba%???

Ya sake kallonta irin duban nan na da gaske kike.

%??ma san jiya ka min alkawarin zaka gaisa da shi idan ka dawo, yanzu kuma yana falo yana gaisawa da yan'uwanka, be kamata ka ware kan ka ba%???

%??mmman Anty ya san ba ni da lafiya?%???

%??manin baka da Lafiya zai canja komai ne? Na fada masa tun jiya%???

%??mai Martaba ko yayayansa da matansa babu wanda ya kira ni ko ya zo duba lafiyata%???

%??matansa da yayanss ba su sani ba, amman dai shi ya sani, please%???

%??mkay since kin bukata i can't say mo to you Anty%???

%??mood muje%???

Ta nuna masa kofa, sai yayi murmushi ya wuce gaba ta bi bayansa, dogon corridor ne guda hudu wanda ke sada duka matan Sarki guda uku da dangaren Sarkin, ta yadda wance ke da girki zata shiga kai tsaye ba tare da kowa ya sani ba, domin corridor kowa dabam yake sai idan ya kawo daf da kofar shiga falon Mai Martaba ake iya haduwa da mutum. Sai da ya cika bakinsa ya iska sannan ya kai hannunsa ya tura kofar falon ya shiga, as usual daya bayan daya ya bi kowa da kallo sannan ya nufi kusa da inda Anty Amarya ta zauna ya zauna, daman a gidan ita ce uwarsa komai yake so ita ce take masa, ko abu aka raba a gidan na Abiey Anty Amarya ake ba ta aje masa, idan kuma wata maganar za a masa ko bukatar wani abu sai an raba ta gurinsa, Abiey wani murdadden mutum ne mai wuyar sha'ani da baya bin ra'ayin kowa sai na kansa, sai dai Anty Amarya ce kadai take iya tankwara shi yayi abun da be tashi ba. He's not the only son a cikin yayan Mai Martaba amman shi nr da daya tilo da gaba dayan matan sarki guda biyu da yayansu basa kauna, ba kuma shi kadai ne namiji ba balle ace saboda suna da yaya mata ne, no Mama Lami da Hajiya Kilishi duk suna da yaya maza da mata, hasali ma Abiey ne kadai dan da Ammy ta haifa da Mai Martaba kamin su rabu, but he's the only son da Mai Martaba ya tsana kamar mutuwarsa, kuma shi kadai ne dan da Matan Sarkin suka tsana a zuciyarsu ban da Anty Amarya, su ma kuma basa nuna matsa tsanar a fili, musamman idan yana gaban Mai Martaba ko a gaban Anty Amarya sai su nuna kamar ma sun fi kowa damuwa da shi.

Farar Jallabiya ce jikin Mai Martaba irin ta manyan larabawa da yan sarauta suke sakawa, mai matukar tsada da nuna isar mai sakata. Idonsa sanye da gilashi grandchild dinsa Aymana tana zaune kusa da shi tana wasa da yatsunsa, kamin ya shigo hira suke cikin girmamawa da nishadi, sai dai yana shigowa a take fuskar Mai Martaba ta canja murmushin dake fuskarsa ya gushe, sauran yayansa kowa sai ya natsu domin sun san idan Abiey yana kusa da Mai Martaba kamar haduwar wuta da ruwa ne, dole sai rai ya bace ko da kuwa Abiey be masa laifin komai ba, wani lokacin har su ta kan shafe su.

%??mbiey baka gaishe da su Hajiya ba%???

Anty Amarya ta fada tana kallonsa, sai ya daga kai ya sake kallonsa da idonsa irin na stubborn boy ya maida dubansa gurin Mai Martaba domin yana jin kamar shi ne kawai ya zame masa dole ya gaisar.

%??marka da Safiya ranka ya dade%???

Uffan Mai Martaba be ce ba, balle yayi wata alama ta amsa gaisuwar da yayi masa, sai ma daukar wayarsa da yayi yana tabawa cike da kasaita da isa da izza irin ta manyan sarakuna. Mama Lami ta yi murmushi mai sauki,

%??mdan be gaishe mu ba mu ai sai mu gaishe shi ba wani abu ba ne, ance dukawa wada ba gajiyawa ba ne%???

Sai Hajiya Kilishi ta tabe baki ta karba mata.

%??mto indan dai duniya kararriya, Allah dai ya kyauta%???

Anty Amarya ta kallesu tana murmushi domin ta san manufarsu.

%??mu ma dai kuna son abun magana, sai ka ce ba ku san halin ??an naku ba, Abiey ai ba magana ta dame shi ba, idan miskilancin nasa ya tashi ko ni da nake uwarsa ba magana yake min ba%???

Abiey saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa zai fara tabawa, Mai Martaba yayi gyaran murya.

%??mnce faduwa kake, sai a sama maka dogarawa kar kaje ka fadi mugun guri%???

Mai Martaba ya fada cikin furuci na isa da sarauta. Abiey ya kalleshi duk da ba shi kadai ne a falon ba ya san da shi yake. A take Hajiya Kilishi ta kada baki ta ce.

%??mubhanallahi farfadiya ta same shi ne?%???

%??mllah ya tsare Hajiya fata ta gari Lamiri ce%???

Anty ta amsa da sauri domin ko kadan furucin da abokiyar zamanta ta yi be yi mata dadi ba.

%??mdan ina son Bodyguard zan iya dauka i can hire them idan ina so, na gode da kulawarka amman bana bukata%???

Abiey ya fada cikin zafin rai da yake ta kokarin ya danne, taya zai kwanta asibiti ya shigo gaishe da Maihafinsa be masa ya jiki ba ya bishi da wannan furucin, sai dai the way da Abiey ya amsawa Mai Martaba be yi ma Anty dadi ba a ganinta be kamata ya amsa masa ta wannan hanyar ba.

%??ma kulawa ba ce, gudun bacin suna ne, karka je wani gurin inda be kamata ba ka fadi ace dan masarauta ne%???

Mai Martaba ya fada yana kallon Abiey fuska babu annuri. Abiey zai sake magana Anty ta tari numfashinsa.

%??mllah ya kara maka lafiya da imani, mun gode wannan ma yana cikin kulawar duk ka ce ba kulawa ba ce, amman ni a gurina kulawa ce da kuma kauna, Allah ya saka maka da alheri ya sa a gama lafiya%???

A take Abiey ya mike tsaye ya fice daga falon fuuuu kamar walkiya rai a bace, Anty Amarya ta bishi da kallo tana murmushi. Mama Lami da Hajiya Kilishi suka kalli juna sannan suka kalli Anty sam abun be musu dadi ba.






ZAHRA POV.

Duk yadda ya so ya hana kansa zuwa asibiti ban yarda na bashi ba, breakfast ma dan dole na yi saboda ya saka ni a gaba daman kuma dan ciki ko ya sun saka ni a gaba da motsin yunwa. Muna gama karyawa na shiga bandaki wannan karon ban barshi shi kadai yayi dawainiyar yi min wanka ba kamar yadda ya saba saboda sanin cewar ba shi da lafiya, kana kallonsa ma ka san lafiyar bata ishesshe ba, domin yayi rama sosai kamar ba jiya ne kawai ciwon ya motso masa ba, ga jikin ma babu karfi sosai kamar yadda ya saba, sai a yanzu na fahimcin mijina ya dade yana boye min ciwonsa, domin lokaci zuwa lokaci ina ganinsa yana rama da rashin kuzari ko samun bachi sai yace min wai zazzabi yake damunsa, ni kuwa a zatona zazzabi irin na malaria wanda aka yi kwana biyu a warke, kamar yadda idan yayi kwana biyu yana shan magani sai ya samu sauki, sai dai ban taba tsaya na kwankwance wane kalar magani yake ba ko da na kwankwance taya zan gane tun da baya ajewa a inda zan gani.

A tare muka shirya muka fito gidan, sannan da katon hijabina mai ruwan kasa wannan karon facemask na saka ba niqab ba sai jakata dana riko. Sai da muka fara zuwa gidan Hajiya muka fada mata komai sai ta ba ni goyon baya duk kuwa da irin hujojin da yayi ta kafawa saboda kar muje, sai dai ita ma tana son nemawa danta lafiya domin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login