Showing 159001 words to 162000 words out of 210919 words

Chapter 54 - CIWON SO

10 Oct 2024

4213

zance na miki murna domin aure babban al'amari ne musamman ace wanda zaki aura din nan tsakani da Allah yake sonki, sai dai ban jidadin da ya kasance wani ne zai mallake jikinki da zuciyarki a yanzu ba, domin na yi wani tanadi a zuciyata da ban sanarwa kowa ba sai yar'uwata shi ma kuma a lokacin da kuka samu tsabani da ita hakan ya kwantar mata da hankali, ashe dai kuma hauka ce kawai nake ba ni ne da rabonki ba%???

Ya gyara tsayuwarsa, wannan karon a maimakon bacin rai fuskarsa damuwawa take bayyanawa.

%??mahra na san ina daya daga cikin mutanen da suka haifar da damuwa da bacin rai a zuciyarki, wannan dalilin ya saka na dauki alkawarin kuranye wannan damuwar na share hawayenki na mantar da ke duk wani hali na bakinciki da kuka taba shiga, na yi kudirin abubuwa da yawa akanki Zahra a farko a kyautata miki da kyautata mu'amala da ke da son duk wani abu da kike so, sannan na yi kudurin aurenki duk kuwa da na san ba lallai ne ki karbi soyayyata ko ki amince da ni ba, a duk lokacin da zan yi yunkurin nuna miki soyayya sai zuciyata tace be dace na yi haka a yanzu ba, saboda ina ganin kamar mijinki be dade da mutuwa ba, kuma ga halin da kika shiga a yanzu wata kila ba ki shirya karbar soyayya ba, ta dayan bangaren kuma ina tsoron irin kallon da zaki min, wata kila ma zaki yi zaton ko kanwata ce ta saka ni ko kuma ina son na aureki ne ba dan Allah ba sai dan na kara rufe sirrin dake tsakaninmu, wadannan abubuwa suka zame min wata tsarka data daure ni na saka duk wani motsi da ya kamata akanki, ashe dai rashin rabo ne ke ta tare ni amman Allah ya sani Zahra na so ki, domin kina da siffa da kyaun da duk namiji mai hankali da sanin rayuwa zai so ki kasance a matarsa%???

Tare da dogon numfashi ya karashe maganar, ni ma numfashin na ja na sauke a yanzu dai ba zan ce ina tausayinsa ba domin idan har akwai wanda zan ji tausayinsa to kaina ne na fi kowa zama abar tausayi a yanzu, tabbas tunaninsa be bashi karya ba ba dan cilastawar Sauban ba, da ban shirya wani aure ba ko da a nan gaba balle kuma a yanzu.

%??mani lokacin abubuwa suna faruwa ba a yadda muke so ba, sai a yadda Ubangiji ya tsara za su faru, wata kila ni din ba alheri ba ce a gurinka shiyasa Allah be mallaka maka ni ba, domin Allah yana zabawa bayinsa abun da ya fi dacewa da su ne%???

A cikin kalamaina babu na kuka, amman hawaye na ke kamar an sanar da ni awanin da suka rage min a duniyar nan, kuka nake sai na rasa dalilinsa ciwon zuciyar dake neman kaine kasa ne ko kuma auren Sauban da ya zame min dole kuma kaddara.

%??maka ne, ina miki fatan alheri Allah yasa mutumen da zaki aura ya rike ki amana, gaskiya yayi sa'a shi ne Abiey?%???

%??mbokinsa ne%???

Ya kada kai.

%??ma gane shi, daman zuciyata ta raya min son ki yake ashe kuwa haka ne, bari na wuce kar ya tarar da mu a nan ya fara kishi%???

Da murmushi ya karasa maganar, sai na saka hannu na share hawayena.

%??ma gode%???

Na juya ina tafiya cike da nauyin kafa har na shige BQ be tunna motarsa ba balle na yi tunanin ya bar gurin.
The following day Sauban ya kira wayata yana tambayar ko akwai abun da nake bukata kamin a daura auren, na amsa masa da babu, sai ya sanar da ni zai balaguro a gobe kuma ba zai samu dawowa ba sai ranar da za'a daura auren, idan ya furta zancen aure sai na ji kamar ya soke ni da mashi a kahon zuciyata, kalmar tana min daci sosai kuma tana sakawa zuciyata bugawa, Jumma'ar da zata zo ma fargabar zuwanta nake domin kuwa jin ta nake kamar jumma'ar mutuwata, ko wane kallo Abiey da yan'uwansa suke min a yanzu oho, wata kila mayaudariya ko yar cin amana, wata kila ma za su ce na bi kudi ne na auri Sauban, haka dai na wuni da tunanin irin kallon da mutane za su min. Ana gobe za a daura aurena na shiga bawa Amir nono kamar yadda na saba na kan ba shi na safe da rana da kuma dare, ina a dakin Hajiya Jamila a zaune na saka masa nonon a baki yana sha idona na kansa sai ruwan hawaye ta taru a ciki har ya zubo akan fuskarsa.

%??man yi aure Amir amman bana jindadi da farinciki ba, zan yi ne saboda na rufa asirinka kuma na rufa nawa domin ban san da wane bakin zan amsa maka ba idan ka tambaye ni miyasa na aikata haka, wata kila a gurinka da gurin wasu mutanen hujjata bata isa ta zama hujja ba, na san na aikata kuskure mafi girma, amman duk haka zan so na ga girmanka, zan so ka kalleni ko da a matsayin wanda ta shayar da kai ne, sai dai bana da tabbacin zan rayu har zuwa lokacin da zaka yi wannan wayon, amman ina son ka sani cewar ina kaunarka fiye da komai a duniyar nan ina son kasance da kai sai dai babu hali%???

Ina shafa gefen fuskarsa da yatsana sai yayi min murmushi irin na yaran da suka shiga wata na uku da haihuwa.

%??mmarya Amarya%???

Shine abun da Hajiya Jamila ta shigo dakin tana fada, sai na yi saurin saka hannu na tare fuskata har sai da na share hawayena cikin hikima sannan na dago ina murmushin karfin hali.

%??mau kuma tsokana kike ji ke da kanki?%???

%??mi na fi kowa murna da farincikin auren nan da zaki yi ne Zahra, Allah dai ya sa gurin zamanki ne%???

%??mmeen%???

Na amsa sannan na kalli wayarta dake ringing, da sauri ta karasa gurin wayar ta cikin zumudi da far'a ta karba kiran da nake kyautata zaton Mr Bashir ne ya kira.

%??mello Hubby, ahhhh i miss you da gaske? Awww i can't wait wannan jumma'ar ta gobe, Okay Allah ya kawo ku lafiya%???

Ashe kuwa na canka a daidai domin yanayin yadda take amsa masa da kuma sunan da ta kira ya tabbatar da haka har wani tsalle take kamar yar yarinya tana ta zumudi.

Ni dai ban ce komai ba na cire Amir daga nonon na kwantar da shi na mike tsaye na fice daga dakin ina jin wani irin kaunar ??ana yana fizgata. A ranar na wuni da tunani da kuma damuwa marar misaltuwa na dan samu sukuni ne a lokacin da Hajiya Jamila ta kirani na fara tayata aikin da zata shiryawa mijinta abinci gobe ta nan na fahimci zai dawo a gobe kenan bayan doguwar tafiyar da yayi, wani abun tun a ranar muka kallama shi, sannan na fito na dawo bangarenmu ina shigowa na rufe windows din da Mama ta bude saboda hadarin da ya taso iska na kadawa da karfi, ina kokarin kwantawa wayata ta yi kara bakuwar number ce cikin fargaba na amsa kiran.

%??mahra'u kuna lafiya ina Mamanki?%???

Ina jin muryar na fahimci Inna ce kanwar Mama, sai na mikawa Mama wayar suka yi magana, bayan sun gama Mama take fada min cewar wai zata zo gobe ita da wata kanwarta.

%??mllah ya kawo su lafiya%???

Kawai na iya fada na cire tufafin jikina na saka na bachi na yi addu'a na kwanta.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Jumma'atu Babbar Rana, sai dai ni zan iya cewa ta zame min ranar tashin hankali domin na farka da kuka kamar yadda na kwana da shi, ina sallah ma kuka nake a boye saboda bana son Mama ta gani zuciyata ta rike gam kamar an daureta dan motsi kadan sai na ji kamar raina zai fita saboda ciwon da take min, Mama ta shirya abun karyawa amman na kasa cin komai sai ruwa na ke ta sha. Misalin karfe tara na safe Inna ta kira wayar tace tana waje na zo na shiga da ita saboda masu gadin sun hana su shiga. Kamar marar lafiya na fito BQ din na fita gate domin shigowa da su a lokacin ne suka budewa Mai gidan Gate direbansa ya shigo da motarsa ni da su Inna muka rabe gefe har sai da ya wuce sannan na yi magana da masu gadin suka bar su suka shigo.
Bana tunanin yayi awa daya da shigowa gidan Hajiya Jamila da kanta ta shigo BQ din da kanta kirana.

%??mllah yasa ba laifi na yi ba%???

Ta yi dariya.

%??mabu laifin da kika yi kawai dai yayi maganar Amir ne sai na ce masa zan sanar masa da wani albishir daga Nannyn Amir amman waka a bakin mai ita tafi dadi zan kira ki fada masa da kanki, shi kenan fa ya tashi hankali sai na kira ki ko abinci be karasa ci ba%???

Hankalina ya dan kwanta da jin haka, na san da ace ba a aurena za a daura ba da bazata fadi haka ba har tana yakar hakora. Haka na bi bayanta muka shiga bangarensa sai dai na same shi a zaune a falon da Ummiter ta taba yi min iso lokacin da ya aikata ta kira ni. Na shiga kaina a kasa na zauna a makamancin gurin da na zauna a wacan lokacin, ita kuma ta karasa kusa da mijinta ta zauna tana murmushi.

%??mata nan sai ta maka albishir din%???

%??moh Madam ai sai kin bamu guri kin san dai ban saba magana da ita a gabanki ba%???

Kunnuwa suka ji sautin muryarsa zuciya kuma na raya min cewar idonsa yana kaina.

%??mhhh ni ai bana da shan kai ga ta ga ka%???

Ta mike tsaye ta fice tare da jan kofar falon, tsit falon yayi kamar babu kowa baka jin komai sai sanyin ac dake tashi.

%??matata tace akwai wani abun alheri da ya same ki, sai dai bata sanar da ni ko minene ba shiyasa na ce ta kira min ke na ji daga bakinki, abu na biyu kuma kin san ba ki karasa min labarinki ba har yanzu ban gama sanin wacece ke ba, tafiyar da na yi a kwanan baya ban yi zaton zata dauke ni wadannan kwanakin ba, sai dai yanayin aikina ko kuma na ce kasuwancin na ya saka dole na dade a turkiya, a jiyan ma ban saka ran dawowa ba sai gashi kuma mun iso nigeria a jiya din cikin amincin Allah, sai dai ban samu karaso gurin iyalina ba sai a yau, saboda mun dawo late sai na tsaya na kwana a Abuja%???

Na daga kai na kalli yadda yake jero min bayanin tafiyaraa kamar ance masa ina da alaka da hakan.

%??mllah ya huta gajiya, wanne zan fara daga ciki Yallabai, albishir din zan sanar maka ko kuma labarin zan karasa maka%???

%??ma dai zaki daina kiran Yallabai din nan wata kila da sai kin fi kima a idona, amman kamin nan bari na yi katsalandan ba ki da lafiya ne? Sannan na kira Ummiter kwanan baya na ce ta baki wayar ina son na tambayeki kina son a gyara muku gidan da aka rusa ne ko kuma a siya muku wani amman baki amsa kiran ba why%???

Sai a lokacin na gane dalilinsa na neman Ummiter ta kawo wayar da na yi zaton ko zai min maganar abun da na aikata ne da matarsa, a yanzu na gane wautata tabbas da akan haka ne da yanzu hankalin matarsa ya tashi, ni kuma da yake tsoro yayi min yawa sai na yi zaton ko Sauban ne ya fada masa wani abu.

%??mlhamdulillah, lafiyar bata wadace ni ba kamar ba, kuma lokacin da ka kira na aje wayar ne na shiga bandaki shiyasa%???

Kafa daya ya dora akan dayar yayi wani zama mai kama da kishingida yana kallona.

%??mna da zumuncin na karasa jin labarin abun da iyayenki suka yi a lokaci da sojojin suka ce za su shigo, tun ganin farko da na yi miki na kalli idonki na fahimci kina da wauta da kiriniya da kuma kurciya a tare dake, sai dai ban dauka a cikin labarinki kin wahalar da iyayenki har haka ba ban yi zaton labarin zai saka ni nishadin da na kwana biyu ban yi irinsa ba, Wallahi har a gurin aikin da na tafi idan na tuna murmushi nake, yau dai kam so nake ki karkare min komai sannan albishir din da Matata ta ce ya biyo baya%???

Ashe da sauran murmushi a kumatuna da ba san da zamansa ba sai a yanzu da Mr Bashir yake fadar na saka shi nishadi. Na kara natsuwa a zaunen da nake sannan na cigaba da bashi labarin daga inda na dasa aya.

-Ni kadai suka bari tsaye a kofar gidan, da na ga babu sarki sai Allah sai na juya na fada masa cewar Mama ta shige bandaki Baba kuma ya shige daki ya rufe, sai sojan yayi murmushi ya kara matsowa kusa da kofar ya ce.

%??maman fa ba wani abun zan musu ba, ni da nake neman su zama surukaina ina ni ina yi musu wani abu, kawai dai na zo ne saboda na yi magana da su na fada musu cewar ina son yarsu kuma ina son yi min izinin rika zuwa ina magana da ke har mu daidaitu da juna, amman tun da ba su yarda sun fito ba zaki iya musu wannan bayanin albashi idan na dawo kin ga ba sai na sha wahala ba%???

%??moh sai anjima%???

%??man jirani ina zuwa%???

Ya nufi gurin motarsa ya bude ya shiga ya zauna, sannan ya fito ya nufo ni ya miko min sabbin kudin yan dari biyar biyar za su yi dubu goma, na saka hannu na karba daman can ni bana tsandar kudi ko a hannun waye suka fito kuwa.

%??mi bawa Baban kuma ki sanar masa zan sake dawowa Inshallah%???

%??moh%???

Murmushi ya sakar min sannan ya juya ya nufi motarsa ni kuma na gyara rikon tufafin Yaya Maryam dake hannuna da dan kwanon naman da Deen ya ba ni daman shi kullin ledar da na sato a dakinsa tana can cikin zanena na laketa yadda ba zata fado ba, sannan na dawo cikin gidan har lokacin Mama na bandaki Baba kuma yana daki ya rufe kansa, karasawa na yi kofar dakin na kara bakina jikin kofar na ce.

%??maba yace ga dubu goma a baka%???

%??mllah yasa rai yace a kara min Zahra Wallahi ba zan fito dakin nan ba, idan kika ga na fito to safiya ce ta waye a lokacin kam na tabbatar da ya gaji da tsayuwa ya tafi, yaushe kika janyo rigima da mahaukacin nan Fisabilillahi ya zo yayi min tsinannen duka alhalin ban san hawa ba balle sauka, yanzu kuma ki je ki janyo fada da sojoji dungurungun%???

%??maba mahaukacin dazun ma shi ya fara fada ni fa, ni kuma na kwashe msa kafafuwa ya fadi shi ne ya biyo ni fa%???

%??mahaukaciyar banza, ai kin ma fishi haukar, ni ba zan ma sake magana ba, waya sani ko kina nan tare da shi yana jina%???

%??ma tafi fa Baba Wallahi ya tafi%???

Baba be sake magana ba, har na gaji na nufi shimfidar da ya tashi na aje tufafin Yaya Maryam na juyo na nufi bandaki na leka Mama da ta yi tsugune ta rafka tagumi idonta narau narau alamar akadan take jira ta yi kuka bayan wanda ta yi dazu.

%??mama ya tafi fa, kuma ba jansa na yi ba Wallahi ganina yayi ya ce yana Son yace na kawo shi gidanmu, yanzu ma da yace a sallamo masa Baba kawai zai nemi izinin hira da ni ne, kalli ma ya bada kudi yace a bawa Baba%???

Mama ta dan taso ta leko harabar gidan ganin babu kowa sai ta ce.

%??me ki rufe gidan%???

Na nufi gidan na rufe sannan na dawo na mika mata kudin.

%??min tabbatar da haka ne Zahra karki janyo mana wahala%???

%??mallahi gaskiya nake fada miki Mama ai kin san bana miki karya, amman Mama kin san da na tafi gidan Hajiya na tarar tana soya naman kaji da yawa, har tace ba zata sammin ba saboda na ce sai na fada maki Ya Deen ne kawai ya ba ni na shi%???

Daga can cikin dakin da Baba yake rufe muka ji yana fadin.

%??me kam dai Zahra kin shiga uku, yanzu kuma zuwa kika yi ki hada ni da uwarki? Ni Wallahi na san idan na ganki aljanna rahmar Allah ce kawai ta kaiki, amman wannan halin na ki ba zai bari ki shiga aljanna ba, to ba ni na siya mata nama ba ita ta siya da kudinta%???

Mama ta tabe baki ta girgiza kai ta fito bandakin.

%??mo sai ki iya bakinki, kuma ki daina dauko mana magana Zahra na rasa abun da yake cikin kanki kullum magana ake amman kamar ana kara cewa ki yi, wannan lamari na ki Zahra ya isheni ya kai min intaha, dazu fa aka cire miki marin nan saboda rashin jin maganarki, amman har kin sake dauko wata maganar%???

Ma dan matsa baya ina kallonta da damuwa a tare da ni, duk na san da cewa mawuyanci abu ne Mama ta saka min hannu da sunan duka sai idan ranta ya bace sosai.

%??mama na daina daga yau, kuma Wallahi dukansu ba wai na ja su ba ne, kin ga wannan so na yake shiyasa ya biyo ni har gida, kuma yayi ya saka yaransa su yi ma Yaya Deen duka sosai%???

Mama ta fito da ido waje tana mamaki.

%??maboda me?%???

%??mai yayi masa fada ne saboda ya tsaya da ni yana magana%???

Mama bata ji dadi ba ba dan komai ba sai dan ta san da cewar Deen zai ya fitar da dukan da aka yi masa a jikina. A lokacin da ta tambaye ni ina na samo tufafi sai na yi mata karyar cewar Yaya Maryam ce ta bani, abu kamar wasa sai ga Baba ya kwana a dakin sai da safe ya fito, ni da Mama muka kwana a dayan dakin. Saboda na san ni mai laifi ce sai na shirya da wuri na tafi makarantar, a ranar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login