Showing 135001 words to 138000 words out of 210919 words

Chapter 46 - CIWON SO

10 Oct 2024

4244

masa rana inji hausawa, sai kawai na ji sallamar Sauban a bakin kofar dakinmu, da sauri na dauki Hijab na saka domin kokarin shigowa yake tun kamin a masa izninin shiga. Mama ma ta tashi ta sauri ta gyara zamanta daman bata rabo da hijabi tun da muka dawo gidan.

%??ma'alaikassalam%???

Mama ta amsa masa, hakan ya bashi damar matsowa sosai kusa da labulen kofar yana tambayar.

%??mama barka da dare, ko zan iya shigowa%???

Cikin sauri na girgiza mata kai alamar ta ce aa amman ba yi min yadda nake so ba, sai ta bashi umarnin shigowa.

%??mh Bismillah%???

Sallama yayi ya shigo cikin dakin ya zauna kusa da kofa ya gaisa da Mama.

%??mauban ka tafi gani nan zuwa%???

%??mannan zuwan ba naki ba ne ke kadai, na zo ne har saboda Mama, saboda na gaji da yawo da hankali da kike min%???

A kaikace na kalleshi ina mamakin yadda zai buga min wata kwallo a ragar da ban san da zamanta ba. Kamin na yi wani unkuri ya fara shimfidawa Mama karyar da ta daure ni da manyan tsarkoki da ba zan iya kwance kaina ba.

%??mama ina son magana dake ne saboda abun da Zahra ta yi min, kuma ina son ki yanke hukunci tsakani da Allah karki duba kusanci da Zahra ko rashin alakarki da ni%???

Yayi shiru ni kuma na zuba masa ido domin na ga iya gudun ruwansa, Mama kuma ta gyara zama ganin babu wasa a tare da shi sai zallar tausayi da ke fita a muryarsa.

%??mama tun ba yau ba mun yi magana da Zahra, magana kuma ba ta soyayyar ba ce ta aure ce, kuma da farko ta nuna min kamar babu matsalar komai, sai daga bayan nan take nuna min kamar ke ce baki son tarayya ta da ita, ni kuma a ganina ba haramun ba ne idan kin amince kin bar Zahra ta aure ni, saboda Abiey yayi sonta shi yake nuna ni ta haramta a gurina ba, kuma Mama ba mu san inda Rana zata fadi ba, lokuta da yawa abin da ba a so shi ne alheri wanda kuma ake so sai ya zama ba alheri ba, kwana biyun nan gaba daya Zahra ta canja min hakan ya haifar min da damuwa ba yar karama ba, kullum da kalar dabarar da take bullo min da ita, tace na bata dama ta yi shawara na bata daga karshe sai ta nuna min ita yanzu matsala ba daga ita ba ne daga gurinki ne, shiyasa na zo da kaina na roki alfarma a gurinki ki dube ni a matsayin ??anki, ya zaki ji idan aka ce wata mace ta yi min alkawarin aure kuma har na sanar da iyaye akan Zahra har matsala sai da muka samu da Matata, na san zaki dubi kamar kusancina da Abiey be dace na yi haka ba, amman Mama so ya wuce nan, Abiey ya riga da ya kama gabansa a yanzu an saka masa ranar aure da Yasmin, ko wannan kadai be isa ya saka Zahra ta nemi rufawa kanta asiri ba? Shi kansa mai gidan nan da yake saka mata dokiki kamar yarsa da ace tana da miji ai ba zai fara mata haka ba%???

Da dai ace gasa ake ta marubuta tabbas Sauban zai karbi Awards a yadda ya tsaya ya marairaice fuska ya kuma shake murya ya tsarawa Mama zancen da ba ne ba. Kamar wata kyanwa haka na zama na lafe jikin ginin dake kusa da katifa ina tunanin yadda zan warware wannan mugun kullun da Sauban yayi min, muna hada ido da Mama sai ta watsa min harara irin wanda ke nuna ko dukana zata iya yi idan Sauban ya bar dakin.

%??mauban, Zahra ba ita ke aurar da kanta ba, tana da magabata bangaren uwa da uba, kuma ba wai bana son ka aureta ba ne, aa ina duba abun da zai fi zama masahala ne a tsakaninku kai abokin Abiey ne be kamata ace ka auri Zahra ba, amman tun da har ta nuna tana sonka kuma ta fada maka ni bana da matsala, indai kun sasanta kanku kuma kin ji cewar za ku iya jurewa da maganganun jama'a na wa fatan alheri kawai sai Allah%???

Mama na rufe baki sai ga Sauban ya kai goshi a kasa yana sujudar godiya, ya dago yana kara yi ma Allah godiya.

%??muk da haka dai, a kara tunani Sauban bana son ku jefa rayuwarku cikin matsala, domin Zahra bata da wayo da tunani wani lokacin%???

%??mnshallah Mama na gode Allah ya saka da alheri, kin gani ko Zahra daman ina ta fada miki Mama bata da matsala ke ce dai kika gagara tsayawa ki yi mata bayanin yadda zata fahimta ne kawai%???

Cikin wasu ruwan hawaye da ban san lokacin da suke kwararomin ba na ce.

%??mauban kana tunanin yin haka zai saka na aureka da karfi ne? Na fada maka ba zan iya cin amana ba, ba zan abun da zai zame min ciwo daga baya ba, akan me zaka zo ka shimfidawa Mama abun da ni da kai mun san be faru ba? Ya kake abu kamar yaro karami?%???

Sakin baki yayi yana kallona kamar da gaske shi ne mai gaskiyar ni ce mai karyar, Mama ta masa nuna taja dogon numfashi ta sauke ta ce.

%??mauban je ka waje zata zo ta same ka%???

%??mo Mama, amman ina fatar ban haddasawa Zahra matsala ba?%???

Mama ta yi murmushi ta girgiza kai.

%??ma komai shashashanci ne kawai irin na ta%???

Cike da nuna damuwa ka ya tashi daga dakin, kusa da Mama na dawo na zauna sai na rasa kalaman da zan hada na wanke kaina, harara kawai Mama take watsa min irin wanda na manta rabon da na aikata wani abu da ya bakanta ranta kamar wannan, cikin karfi hali irin na marasa madafa na dago na ce


%??mama Wallahi....%???

Tassss na ji sauka tafin hannun Mama a fuskata, marin da da sai da shatin yatsunta ya kwanta a farar fatar kumatuna.

%??mhashashar banza wawuya, idan ma bana son alakarki da shi dole sai kin fada masa? Sannan ke ba zaki iya tunanin abu mai kyau ba? Yadda zuciya ta raya miki haka kike? Ina ganin kamar kin yi hankali kin san abun da kike ashe haukarki ma karuwa take? Akan me zaki masa alkawari cewar zaki aurenshi bayan kin san alakar dake tsakaninsa da Abiey? Oh yanzu na gane shi ne dalilin shiga damuwar da kika yi ko abinci ba ki iya ki ci?%???

Na girgiza kai zan sake magana Mama ta buge min baki.

%??mufe min baki, ba dai kin masa alkawarin aure ba? Kuma kika kawo ni a tsakiya kika manna? Amman a nan idan na nuna miki bana son zuwanshi cewa kike ke ma ya zame miki dole ne, ashe kina can kina tsara masa aurensa za ki yi har kina dora laifin a kaina? Tabbas na isa na hana aurenku, daman abun da nake hango miki matsala ne da yadda mutane za su kalleki, amman tun ke baki san Annabi ya faku ba sai ki je ki yi duk abun da kika tunanin mafita ne a gurinki, tashi ki je ki same shi%???

Na runtse ido na bude ina jin yadda duniya da lamurran cikinta suke yamutsa tunani, kamar tsumma a cikin ruwa haka na mike tsaye jiki ba kauri zuciya babu karfi na fice daga dakin.
A lokacin da na hango Sauban jikin motarsa yana jira na fitowata sai na ji kamar ace da bindiga a hannuna na halbe shi ko na huce wannan cikin da ya saka min a yanzu.

%??m'm sorry, na yi hakan ne saboda na taimaka miki wajen shigar da ni gurin Mama, kuma idan har ba ki son kowa ya san Auren dake zamu iya yinsa a sirrance ba tare da Abiey ko wasu sun sani ba, ni dai ina son kasancewa da ke ne ko da na kwana daya ne%???

Na data kai na kalleshi da idanuwan da hawaye suka ci karfinsu, daman na dade da lura kamar ba so yake min irin na Allah da Annabi ba domin a cikin sakwannin da yake aiko min ya fi yawan jaddada cewar yana son ya kasance da ni ne ko da na kwana daya ne kamar yadda ya fada a yanzu. A iya tunanina Abiey ba mazinaci bane balle na ta kai ga na zargi Sauban, sai dai baka iya shaidar kowa a wannan zamanin sai kanka, wata kila akwai wani abu da yake burge Sauban a jiki da ya kasa hakura har ya kwadaitu da son kasancewa da ni kamar yadda ya fada, ya sani sarai idan ya zo min da maganar banza ba zan amince ba, shiyasa ya bullo ta wannan hanyar.

%??mya barazanar da ka yi min bata wadatar ba? Har sai ka biyo ta wata hanyar da ba zata bulle da kai ba? Da farko na yarda da kai Sauban ban yi zaton zaka zo min da wani wasa ta yara ba, abun da ka aikata a yanzu ba abu ne ya burgewa ba, kuma idan kana tunanin ka yi wayo ne to baka yi, kuma wannan be isa ya saka na amince da mugun kudinka ba%???

Dariya yayi.

%??mahra kenan, wato barazana kika dauki abun da na fada miki ko? To na rantse miki da Allah zan aikata matukar baki amince da kudina ba, ki yi tunanin halin da zaki shiga da kuma wanda ??anki zai shiga, da kuma wanda zaki jefa Dr Hamid, da Jamila balle kuma Mr Bashir da mahaifiyarki, ba fa kudi nake nema a gurinki ba Zahra face amincewarki ki aurene, har na baki dama idan baki son duniya ta sani zamu iya yin abun mu a boye%???

%??ma zan yi ba, ka je ka yi duk abun da zaka yi, saboda kun maida ni ba ni da kowa sai ku rika juya ni yadda kuke so%???

Na karasa cikin kuka, sai ya miko min wayarsa.

%??muba wannan, ina fatar dai baki fadawa Mama komai ba, kuma baki nemi shawarar kowa ba sai zuciyarki%???

Ban karbi wayar ba, hakan kuma be hana ni hango takardun gwajin jinin da aka fadada a cikin wayar ba.

%??ma ki ne da na ??anki, wanda aka saka Dr Zainab ta sauya, sauran na Mr Bashir da matarsa na suna ciki, wadannan original din ne ba fake din da aka bashi ba, ita kanta Dr Zainab bata san na dauki wannan ba domin ita ma zai jefata a matsala idan har Mr Bashir ya san gaskiya%???

Guiyoyina ne da suka yi sanyi suka kai kasa, idaniya na zubda hawaye na daga kai na kalli Sauban.

%??mane irin rashin imani ne wannan Sauban? Me na maka? Miyasa idonka zai rufe ka aikata kwatankwatan zalinci da Deen ya taba aikata min, me na muku? Miyasa ma na sanku?%???

%??mdan har Deen zai kirki komai saboda ya same ki, ya kike tunanin ni da ba kirkira zan yi ba na fashe kwan kawai zan yi? Zahra na boye miki wani abu ne kawai amman tun daga lokacin da na fara saka kafata a cikin gidan nan na saka ran batawa da Abiey domin na san ba zai lamunci min na aureki ba, amman na boye masa har sai da na samu hujojin da zan dogara da su su yi min iso gurin neman aurenki, haka yanzu haka ba ma ga maciji da Abiey saboda ke, yan'uwansa sun dauke ni a matsayin macuci shi kanshi haka yake kallona, amman na zabi na jure komai saboda na same ki, sai a yanzu da kowa ya san da komai har iyayena na sanarwa sai kuma ki ce ba zaki aure ni ba? Ke ki wanke kanki ki fita free ni kuma ki bar ni a kunya da bakinciki da nadama, wai Zahra baki yarda ina sonki ba?%???

%??mai sonka baka ganin ramarka idan har so na kake zaka so farinciki ka so kwanciyar hankalina, ba zaka nemi daga min hankali ba%???

%??ma daga miki hankali nake ba, mafita nake nema miki, ko dan saboda Jamila da Mr Bashir, Zahra ko da wani abu ya faru rigar aure zata kareki, domin bana jin Jamila zata kyale ki a haka idan ??anki ya girma, zata yi ta tsammanin wata rana zaki dawo ki aure mijinta ko kuma ki kwace ??anki amman aurena zai kawai da komai Zahra%???

%??mayan ka fallasa komai sai me zai biyo baya? Karshenta a ce za a rufe ni gidan yari, bayan wannan sai kuma me?%???

%??maki barwa iyayenki da ??an naki da kika saida tabo da ba zai taba goguwa a zuciyarsu ba, Zahra wannan ce dama ta karshe da zan baki, kuma ina kara jadadda miki idan har baki son kowa ya san da zancen aurena da ke, ba za a sani ba, zan aure ki kuma na sallame a lokacin da kike so%???

Na mike tsaye.

%??mawai ka fito fili ka ce jikina kake so%???

Sai yayi saurin kawar da fuska.

%??mubhanallahi, idan na nace haka ai ban yi laifi ba domin ba zina na aikata ba, kuma ba ita na neme ki ba, zaki iya jurewa maganganun mutane akan aurenmu, amman ba zaki iya jurewa na siyar da cikin da kika yi ba, saboda haka idan kin koma cikin gidan nan kawai ki amsawa Mama da cewar eh kima so na, shikenan sai na sanar da iyayen su sami naki iyayen domin bana son a dauki lokaci%???

Ya bude motarsa ya shiga yayi mata key yayi reverse ya bar ni a gurin tsaye. Komai ya zo min ta hanyar da ban yi zato ba, na kasa yardar Sauban ne yayi min haka gani nake kamar a mafarki komai yake zuwa min, duk yadda zan yi Mama????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ta saurari uzurina na yi amman bata yi ba saboda ranta ya bace sosai. Kamar wasu abokan gaba haka muka kwanta muka tashi da safe Mama bata son magana da ni, gaishe ma da na yi bata amsa min ba, cikin damuwa da kufuwa na fito waje na share BQ din na wanke kayan da muka bata, sannan na zauna kusa da wasu fulawoyi na rafka uban tagumi, ina ta tunanin abun da zai fitar da ni.

%??ma Allah idan abun da Sauban yake nufina da shi alheri a gareni, Allah ka saukar min da natsuwar amince, ka kawar min duk wani abu da nake gani, idan kuma ba alheri bane sharine ko cutarwa a garemu Allah ka musanya min ka kawo min mafita, shi kuma ka cire masa ni a zuciyarsa%???

Ashe Mama na jin addu'ar da na yi, bayan na shafa addu'a ta fito ta zauna kusa da ni tana kallona.

%??ma wai bana son aurenku da Sauban din ba ne, ina duba abun da zai zame muku mafita ne, amman na lura kina sonki kuma shi ma yana sonki, saboda ki kwantar da hankalinki zan sami dangin mahaifinki zan sanar musu sai su saka masa ranar da zai je ya same su%???

Na dubeta sai hawaye suka riga kalaman bakina fita, na kasa cewa bana wannan ne kudirina ba, kamar wanda aka yi ma asari haka bakina ya rufe rub na gagara furta komai, har lokacin ban iya labarta wa Mama barazanar da Sauban yayi min ba, domin ban san abun da zai biyo baya ba idan na fada mata.
A daren ranar Ummiter ta shigo BQ rike da waya, bayan mun gaisa ta mika min wayar.

%??ma'a kira ki ku gaisa%???

%??ma zai kira%???

%??maya Bashir shi yace na kawo miki wayar%???

A take na samu kaina na faduwar gaba, hankalina yayi matukar tashi babu abun da zuciyata take raya min sai kalaman Sauban, kamar marar gaskiya haka na karbi wayar na rike ina ta kallon hoton Amir dake gaban screen din wayar, sai tausayin yaron da mutumen da ake ikirarin mahaifinsa ne ya kamani, ba su kadai ba har da yan'uwansa da suke nunawa Amir kauna a zuwan ??an Mr Bashir ne. Ta dayan bangaren kuma na san ban kyautawa Hajiya ba da Baba domin su ma za su so ganin jikansu ko da kuwa ace Deen yana raye balle kuma ba shi da rai.
A lokaci da kiran ya shigo sai na kasa amsawa jikina ya dauki rawa kamar mazari, Mama ma da kanta sai da ta lura da haka.

%??mi dauka mana%???

%??ma zan iya ba Mama%???

Na amsa cikin kuka, kiran biyu Mr Bashir yayi a wayar Ummiter da nake kyautata zaton Hajiya Jamila ba ta san da kiran ba, amman na gagara amsa kiran, sai da Ummiter ta dawo ta karbi wayar tana dubawa sannan na mike tsaye da sauri na fito daga dakin.

%??maki amsa kiran ba?%???

Shi ne abun da ta biyo ni tana tambaya.

%??ma amsa%???

Ban bari ta ga hawayena ba na bata amsa, bayan na tabbatar ta fice daga BQ din na koma cikin dakin na bude gurin tufafina na dauko wayata na fito na kunna sai ga sakwanni kala kala na samu na Sauban wasu kuma na nuna kulawa ne daga Dr Hamid, sai da na kara matsawa sannan na kira wayar Sauban.

%??me ka fadawa Mr Bashir?%???

Shiru na ji yayi kamar ba zai amsa ni ba, can kuma ya yi gyaran murya ya ce.

%??me kika tsammanin zan fada masa? Kin yi zaton wasa nake? Haba Zahra ba zan yarda na yi 2-0 ba%???

%??makan be dace ba Sauban%???

%??miyasa ke ba zaki aikata abun da ua dace ba? Ban fada masa ba, na so ma lasa masa zuma ne kawai a baki, amman zan fada masa matukar baki amince da kudirina ba%???

Wasu hawaye masu zafi sun sauko min.

%??man Allah ka yi hakuri Sauban karka fada masa%???

%??min amince?%???

Na daga kai kamar yana gabana, na runtse ido ina wasu hawayen da ban san ranar tsayarwarsu ba.

%??min amince zaki aure ni?%???

Ya sake nanata.

%??ma amince....%???

Na furta daker, halshewa har wani haldewa yake maganar na rabewa min kamar mai koyon magana...
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Da sauri ta mike gannin Rukayar na yarfe hannayenta ta bude baki muryarta a raunane ta ce" To Mamaj bara na gani ko barci ta yi aunty amaryar?" Ta karashe tana nufar hanyar fita ta nufi dakin Aunty Amarya

Su duka biye suke da ita, dan yannayinta dole zai daga hankalin mai kallo
Jiki ba karfi ta buga dakin aunty Amarya sannan suka ja suka tsaya sunna jira

Jim kadan Auntyn ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login