Showing 192001 words to 195000 words out of 210919 words

Chapter 65 - CIWON SO

10 Oct 2024

4243

ki duba tun daga lokacin da abun nan ya faru har ta kai Baba ya sake ki be sake waiwayarmu ba, daga shi har Hajiya sun dauki abun nan da zafi, idan suka san abun da na aikata za su hukunta ni kuma za su sanar da duniya, wata kila ma hakan ya saka kallon da iyayen Abiey suke min ta kara tsami, har wadanda ba su san ni ba wata kila za su ji sun tsane ni, shi kuma Mr Bashir zai shiga damuwa kuma duniya zata san an siyar masa da ??an wata kila ko da iyayen Deen sun hakura hukuta tace zata hukunta ni, amman idan yaron ya zauna a hannun Mr Bashir duk hakan ba zai faru ba%???
12/28/22, 11:23 - Buhainat: %??mmman ke kina jin zaki iya jure rashinsa Zahra?%???

Na daga mata kai ina kallon Amir din dake ta kuka har da hawaye.

%??man iya, na rayu ba tare da uba ba, na kuma rasa mijina na rayu balle ??an da na san zai kasance a kyakkyawar rayuwa kuma zan iya samun wasu yaya a gaba%???

Na mika hannu na karbi Amir din dake hannun Mama na cire hijabina na saka hannuna na ciro Nono na saka masa a baki, sai ya ki karba sai kara fashewa da kuka yayi kamar ya san abunuwan da suke faruwa. Sai da na dorashi a kafata na fara yawo da shi a dakin ina jijjigashi wai ko zai yi shiru amman a banza kamar ma na kara masa, Mama ta karbeshi ta goya tana rarrashinsa nan ma a banza, kuka yake sosai har wani shakkuwa yake kamar zai tsude, a take hankalina yayi matukar tashi, cikin fargaba na saka hijab dina Mama ta saka nata muka fito daga BQ din muka nufi gate domin kai shi asibiti, gurin masu gadi na nufa daman can asali su suke bude min gate idan zan fita domin ban iya bude kofar ba saboda nauyinta.

%??man Allah ku bude min gate asibiti zan kai Amir%???

%??ma Mai gidan yace kar mu bari a fita da yaron nan daga gidan nan yace ko da matar gidan ce%???

Cike da mamaki nake kallonsu.

%??mhi ya fada muku haka?%???

%??mh%???

%??msibiti zan kai shi ba ku ga yadda yake numfashi ba%???

%??mmarni ne aka ba mu, kuma idan za a kai shi asibiti ai ba ke ya kamata ki kai shi ba iyayensa%???

Kamar ya san cewa zan yi ya kira Mai gidan ya fada masa sai ganin na yi ya kara waya yana karanta masa abun da ya faru.

%??mata nan a bakin gate%???

Wata kila cewa yayi a bani wayar sai ya miko min, ni kuma ba karba na kara a kunne.

%??mello...%???

%??mahra... Miya samu Amir?%???

%??muka yake tun da na karbo shi, na bashi nono ya ki ya karba, ina tunanin kukansa yayi yawa ne shi ne numfashinsa yake yin sama, su kuma sun hana na fita wai ka ce kar a bari kowa ya fita da Amir%???

%??mh ba fada musu haka ne saboda na yi tunanin ko Jamila zata yi kokarin guduwa da shi ne, zan fito yanzu nan%???

Na mikawa mutumen wayarsa sannan na juya na kalli Mama na fada mata yadda muka yi sai muka koma gurin kofar bangarensa muna jiran fitowarsa kamin ya fito har na matsu na dauko da Amir a bayana ina kallonsa gani nake kamar mutuwa zai yi domin abun karuwa yake har wani lumshe ido yake kamar mai bankwana da duniya.

%??mama kalli mutuwa zai yi%???

%??mane irin mutuwa kuma, kawo shi a nan%???

Amaimakon na mika mata shi kamar yadda ta bukata sai na tura kofar shiga falon Mr Bashir na shiga da gudu ina kuka, karo muka kusa yi da shi domin shi ma ya fito da saurinsa ne sanye da sabuwar shadda.

%??mubhanallahi miya same shi ne%???

%??mun da na karbo shi yake kuka har yanzu be daina ba, kalli numfashinsa cirewa yake%???

Ya mika hannu ya karbe shi, Sai Amir ya bude ido ya kalleshi ya sauke ajiyar zuciya a take kukansa ya yanke, har sai da na yi zaton ko an zare numfashinsa ne.

%??mo ya mutu ne%???

%??ma%???

Ya amsa ni yana kallon Amir din da shi ma kallonsa yake.

%??marbe shi zan musu magana, direba zai kai ku asibitin yanzu%???

Ina mika hannu na karbe shi sai ya sake fashewa da kuka da sauri Mr Bashir ya janye shi ya fara jijjigashi.

%??morry sorry%???
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Sai kuma yayi shiru, ba shi Mr Bashir din ba har ni har ni da Mama mamaki muke, domin jariri mai wata uku zuwa hudu be isa zaben uwa ko uba ba, haka kuma be yi wayon da zai ce da Mr Bashir yake son ya zauna ba balle na ce zaba yayi, idan ma shakuwa ce ina tunanin zai fi shakuwa da ni da nake shayar da shi fiye da Mr Bashir da yake a matsayin ubansa a yanzu, akan kafadarsa ya dorashi ya wuce gaba ni da Mama muka bi bayansa kamin mu isa gurin Motar Ummiter ta fito da shirinta idonta a kumbure kana ganinta ka san kukan da ta yi ba kadan ba ne, kamar ita aka yi ma laifin ba Mr Bashir ba.

%??mna zaku je?%???

%??msibiti Amir za a kai%???

%??me ya same shi?%???

%??muka yake yi yaki yayi shiru numfashina har sama yake kamar zai suma%???

Yayanta take tambaya amman ni nake amsa mata, tsaye ta yi a gurin har muka shiga motar da Mr Bashir ya nuna mana direba ya nufo motar da sauri ya shiga, Mama ce ta fara shiga sannan na mika hannu na karbe shi sai ya fashe da kuka, ina kokarin shiga motar Mr Bashir ya dakatar da ni.

%??mahra kawo shi%???

Na mika masa shi, a nan ma yana karbar sai yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, mun dade a tsaye yana rumgume da shi yana shafa kansa, sannan ya sake miko min shi yana fadawa Direban asibitin da zai kai mu, ya juya da sauri ya koma ciki, a take Amir ya sake fashewa da kuka, kukan da be daina ba kenan har muka isa asibitin da take ta kudi ce, wata kila Mr Bashir ya sanar da ma'aikatan gurin tun kamin mu iso, domin mun same su suna jiran isowarmu, a asibitin muka wuni har yamma sun dauki hotonsa an auna jininsa sai dai ba su fada mana komai ba har dare, wata a wannan asbitin ba su sanar da abun da yake damun yaro da wuri ko kuma ba su gama binciken su ba ne, Amir kuma be fasa kuka ba har garin Allah ya waye idan na bashi nono ba zai sha ba sai kukan kawai yake ta yi har sai da likitan safe ya shigo yayi masa allurar bachi sannan muka samu yayi bachi, muna tare da Mama har lokacin domin bata son ta tafi ta bar ni kadai, ni kuma hankali ya kasu gida biyu daya a nan daya kuma a gurin Abiey ina tunanin ko a wane hali yake a yanzu, idan iyayensa suka gane abun da ya aikata ko wane irin hukunci za su yanke masa? Gashi na bar wayata a gida balle na kira shi na tambayi halin da yake ciki.
Dawowar likita ne ya yanke min tunanin da nake sai na gyara zamana na kalli Amir dake bachi.

%??madam ya mai jiki?%???

%??mashi nan yana bachi, amman Dr baka fada mana abun da yake damunsa ba%???

%??m iya bincike da muka ji na jiya be nuna akwai wata matsala ko wani ciwon a tare da shi ba, amman za mu sake yin wasu waje wajen a yau Inshallah%???

%??mo miya yake kukan?%???

%??mhi muke kokarin mu gano, domin be kamata a rubuta masa maganin komai ba har sai mun gano abun da yake saka shi kuka, kar ya zamana mun yi magani dabam cuta dabam to yaro ne karami ba shi da baki balle ya iya fada mana matsalarsa%???

Na juya a hankali na kalleshi.

%??m da can yana ciwon cikin idan ya sha nonon da bawa nawa ba, ban sani ba ko matsalar ce har yanzu, amman shi ma ya daina daga baya domin bayan nono akan hada masa da madara kuma ya sha bata masa komai ba%???

%??mh Alhaji Bashir yayi mana wannan bayanin tun a jiya da na sanar da shi ba mu ga wata matsala ba, to amman kin bashi wani abun ne?%???

%??ma madarar dai ko jiya ya shekaranjiya ya shata ban san ko ita ce ta haifa masa da matsala ba a yanzu%???

%??mole a kawo mana madarar mu gani kuma zamu son gwada ruwan nono na ki so that mu gano idan ta wata matsala, sannan za a sake yi masa wani hoton da wasu manyan gwaje gwaje Inshallah%???

%??moh%???

Na amsa jiki a sanyaye ina jin wani yanayi na rashin jindadi, sai da likitan yayi abun da zai yi ya fita sannan na kalli Mama cikin damuwa na ce.

%??mama ko dai shi ma mutuwa zai yi?%???

%??mo kuma dai Allah mai hikima yana nufin shirya wani abu a tsakanin bayin nan nasa%???

%??man gane ba%???

%??msakanin Alhaji Bashir da Amir din mana, baki lura ba idan ya dauke shi ya kan yi shiru?%???

Na zaro ido sai kuma na juya da sauri na kalli Amir din.

%??mmir be yi wayon da zai kulla wannan makircin ba, saboda haka mu barwa Allah komai Zahra, ni ma na gamsu ki bar yaron nan a inda zai samu rayuwa mai kyau da tsabta, shi ma kansa Alhaji Bashir din yaron ya shiga ransa tun da har ya riga mu samin halin da yake ciki%???
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Yana shigo kitchen din gaban Ammy ya fadi, sai ta rage gas din ta kalli Jummai dake juya miyar hantar sake saman wuta ta ce.

%??me ki bangarenki idan na gama zan miki magana%???

%??moh Hajiya%???

Ta aje cokalin dake hannunta ta gaishe da Amir sannan ta fice daga kitchen din, Ammy ta kalleshi fuskarta dauke da damuwa.

%??mna ka je?%???

%??murin Mai Martaba%???

Ya amsa mata yana kokarin boye farincikinsa.

%??ma yi magana da shi?%???

Ya daga mata kai sai ta yi saurin sauke kai kasa gabanta na kara faduwa.

%??ma ce ka sake ta ko kuma ya sake yin fushi da kai?%???

%??me min ko daya ba%???

Ya tako ya karaso inda take tsaye sai ya fashe da dariyar da ta firgitata ya rumgume.

%??mmmy Mai Martaba ya saka min albarka%???

%??mo dai ya tsine maka ba%???

Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, Abiey ya dago yana kallonta hawayen farinciki na taruwa a idanuwansa.

%??mi ma na yi tsammanin zai yi fushi da ni, wata kila har yace ba zai sake saka hannunsa a lamarina ba, domin na aikata wannan abun ba tare na sanar da shi ba, daman can na yi ma kaina alkawarin idan har ta dake akan sai na rabu da Zahra, to zan rabu da ita sai dai shi na kuma zai rabu da ni, domin bana jin zan sake rayuwa idan muka rabu da Zahra a halin yanzu, duk kuwa da irin raya min da zuciyata take na cewar Mai Martaba ba zai cilasta ni yin haka ba, domin mutum ne da ya san mi yake yi kuma ya san abun da ya kamata da wanda be kamata ba, haka kuma Mai Martaba uba ne ko da ba ni ??ansa na aikata haka ba na san shi mai shiga gaba ne ya magance komai a gurin wasu iyayen balle kuma a cikin gidansa%???

%??mi duk ba gane wannan bayanin zan yi ba, kawai ka fito fili ka fada min abun da ya faru%???

Abiey ya dafa Ammy yana murmushi.

%??mamin na sanar da Mai Martaba laifin da na yi masa, shi ya fara yafe min ya kuma sakawa aurenmu albarka%???

Ammy ta matsa baya.

%??mhat... %???

%??mes ni ma abun ya ba ni mamaki, Ammy yau na zauna kusa da Mai Martaba har jikinsa na taba jikina har hannunsa ya kai ya taba kafadata, a yau Mai Martaba ya kira kansa a wani mutun da ya kasa ba ni lokacinsa da hakkinsa da Allah yace ya ba ni, Mai Martaba da bakinsa yake fada min ni na fi soyuwa a ransa fiye da sauran yayansa, kuma mahaifiyata ta fi ko wace mace tsayawa a ransa%???

Ammy ta dafa kirjinta hawaye na sauko mata, sai ta juya da sauri ta dafa sink.

%??ma da gaske ba ne wannan abun ba gaskiya ba ne%???

Abiey ya karasa kusa da ita ya dafata yana cigaba da murmushin farinciki.

%??mi ma kamar na ce haka, sai kuma daga baya abun ya zame min kamar mafarki, har kuka na yi Ammy ban taba tunani rana zata zo da Mai Martaba zai yi min furuci mai dadi kamar wannan ba%???

%??ma kamata na tabbatar%???

Ta fice daga kitchen din da sauri, dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira Anty Amarya yanayin yadda Anty Amarya ta amsa kira??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n ma kadai ya isa ya bayyana mata cewar Abiey gaskiya ya fada.

%??mani labari na ji yanzu daga bakin Aliyu wai Mai Martaba ya yafe masa abun da ya aikata%???

Anty Amarya ta amsa daga dayan gefen tana dariya.

%??ma wai ba ne gaskiya ne, be fada miki har da tukuicin albarka ya biyo baya ba? Gani a nan ni da yara sai murna muke%???

Ammy ta fadi zaune a kasa gaba daya tana rufe bakinta.

%??mai hakuri mawadaci Ammy, ni kaina ba tsorota a lokacin da Abiey yace zai yi magana da mahaifinsa, Wallahi na yi zaton zai iya cewa ya tsine masa albarka ma, ashe Allah ya tsara wani abun dabam da shi kadai ya bar wa kansa sani, Wallahi ba yarda mai gaskiya baya tabewa, kuma gaskiya komai ta dade sai ta bayyana%???

Ammy ta lumshe ido tana kuka sosai.

%??mhekara fiye da talatin ina fama kiyayyar Mai Martaba akan ??ana, ko da rana daya be taba cewa Umaima Aliyu yana lafiya, ko yana bukatar wani abu, amman ku ce min ya saka masa albarka, a lokacin da nake tunanin albarkar zai cire masa?%???

Ta girgiza kai ta sauke wayar ba tare da saurari abun da Anty Amarya ke fada ba, Abiey ya karaso kusa da ita ya duka ya rumgume sai ta fashe da kuka.

%??ma ace na mutu kamin wannan ranar da na mutu da wannan bakincikin, amman a yau Allah ya wanke min zuciyata da dattin da ya dade ina dauke da shi a zuciyata, hakurin da ka yi na halin da ka samu kanka shiyasa Allah yayi maka sakamako da abubuwan da kake matukar kauna a lokaci daya, Allah ya maka albarka Aliyu%???

%??mmeen Sweet Mom%???

Kuka ta yi sosai kamar ba abun farinciki ne ya faru ba, kamar an tsikareta sai ta zabura ta tashi ta share hawayenta muryarta na rawa ta ce

%??me...je...je... ka dauko min Zahra karka fada komai ni zan mata wannan albishir din%???

Abiey ya sumbanci Mahaifiyarsa ya sake rumgumeta sannan ya sake ta ya fice yana dariya, safa da marwa ta fara yi a dakin tana daga hannunta sama tana yi ma Allah godiya, can kuma ta sake nufar wayarta ta dauka ta lasa number Mai Martaba har zata kira sai kuma ta fasa ta aje wayar, can kuma ta sake dauka ta aika masa kira kamin ya dauka gabanta ya fadi sau ba adadi.

%??mssalamu Alaikum%???

%??ma'alaikassalam%???

Sai kuma ta yi shiru bayan ta amsa sallamar.

%??mmaima%???

Ta amsa wasu hawayen na silalo mata

%??ma'am%???

%??mo dai kamfanin line sun baki kyauta ne, shiyasa kika kira kuma kika kasa magana, na san dai ba zaki kira saboda ki gaishe ni ba, sai idan na taba ??anki zaki kira ki fara min masifa%???

%??mau din ma ??ana ka taba Mai Martaba, irin tabawar da na dade ina jiran ka yi masa, irin tabawar da nake mafarki a kowane dare, na gode Allah ya saka da alheri%???

Ta fashe da kuka, jimmm yayi na dan lokaci kana ya ce.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: %??miye abun godiya ga wanda ya aikata abun da yake wajibi a gurinsa? Abiey ??ana ne, kuma yanzu nake da damar nuna masa soyayyar da ban yi ba a can baya, saboda yayi alfahari da ni kamar yadda nake alfahari da shi a zuciyata, sai dai hakan ba zai hana na nuna masa kuskuren abun da yayi ba a nan gaba, saboda ya kiyaye ko da yake ba laifinshi ba ne laifinki da kika goya masa baya ya aikata haka saboda kina ganin kin zame masa uba ko? Ko kuma dai kin yi hakan ne saboda ki kara lalata alakar dake tsakaninmu%???

%??mo kadan ni ma ban san ya aikata ba, har bayan da komai ya faru, ya hada kai da abokinsa da yayarsa Dr Zainab suka shirya komai, na masa fada sosai kuma har alkawarin na yi masa cewar idan har ka dage sai ya saki Zahra to dole ne ya bi unarninka ko kuma ni ma na cire hannuna a lamarinsa, ya aikata hakan ne saboda yana ganin kamar idan babu yarinyar ba zai rayu ba, ka san halin yara da kuma kurciya%???

Mai Martaba yayi dariyar da Ammy ta dade bata ji irinta daga gareshi ba.

%??mara kenan, ko da yake yana da gaskiya ai, soyayya gaskiya ce domin bata tsufa bata canja muhalli ko da kuwa masoyan sun tsufa matukar akwai wannan soyayyar ta gaskiya t zata zauna a raine har abada, Allah ya musu albarka%???

%??mmeen, Allah ya kara lafiya%???

%??mmeen%???


Ammy ta sauke wayar tana lumshe ido ta ja dogon numfashi ta sauke a hankali. Abiey ya fita gidan da gudunsa kamar wani karamin yaro har shafa kansa yake yana shiga motarsa ya kure volume da wakar Celine Dion da wakarta ta new day has come. _I was waiting for so long for a miracle to come, everyone told me to be strong...._ haka ya rika bin wakar yana rerawa har da su tafi yana juyawa kamar ba driving yake ba, shi kansa ya manta rabonsa da samun farinciki irin wannan, sai dai be yi sa'ar tararda Zahra ba, saboda suna asibiti ma'aikatan gidan kuma ba su fada masa wace asibiti ce ba domin su ma ba su sani ba, ya dade a waje yana ta jira ko zata dawo ko Mama amman be ga kowa ba, ga wayarta yayi kira har ya gaji bata amsa ba, A nan ya kira Sauban ya labarta masa abun farinciki, Sauban ya kasa hakura har sai da ya same shi a unguwar ya taya shi murna,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login