Showing 246001 words to 247770 words out of 247770 words

Chapter 83 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10416

da suka yadda suka zauna wajen wannan wasan kwaikwayn nasu.

Aiko tini scream ɗin tv ɗin yayi raga raga, sia Sambatu taje yi tana ihu, daga ita sai Su Nihal cikin ɗaki, suma hankalin su a tashe suka shiga kiran Layin Dad.

A ci sa'a baiyi nisa ba, sai gashi ya hauro saman nata, mutane sai gaishe shi suke yi.

"Lafiya kuwa Kubra, kina lafiya haka? Me ke samun ki?"

"Alhaji ni za'a raina ma hankali? Ni za'a shirya ma wasan kwaikwayo, da za'a wani ce Suhan da Umman ta ƴan gidan sarauta ne? Ka dubi fa yanda yaron nan yaje yana kashe masu kuɗi har haka..."

Dakata Kubra, labarin da kika samu gaskiya ne, haka ne, ina ce su ƴan rahotn naki sune suka sanar dake komai? To ba wasan kwaikwayo ko ƙanzon kurege a ciki, su ɗin jinin sarauta ne gaba da baya, kuma ina so ki sani idan zaki hankalta sai ki hankalta ki san kuma ne kike yi, idan ba so kike ki bar abun faɗa ba a taron bikin yaron naki, aure kau babu fashi insha Allahu ko da yardar ki kuma ko babu, don haka shawara ta rage taki.. "

Yana gama faɗar haka ya juya cike da ƙaunar zuciya ya fice daga ɗakin, yana mai gangara wa down stair yana zancen zuci. Baiga ranar da Kubra zata hankalta ba.

Ita kuwa kuka ta fashe dashi, tana mai huci kaman kububuwa, lallai wannan rainin wayau da yawa yake, ku ji fa wai Alhaji ne ke sanar da ita cewa abun da laila ta gaya mata gaskiya ne.

Mu kau bayan an gama ci an gama sha, sai aka sakar mana kiɗi har da Hamisu breaker da Umar M shareef saida suka zo suka taya mu chashewa, a hankali muke taka wa lokacin da aka bada fili ga ango da amarya.

Liƙen kuɗi dai mun sha shi, wannan karon harda Sir Salim da yayi matuƙar ƙoƙari waje danne zuciyar tashi.

Haka aka gama hidimar kamu ɗin, inda ya ƙawata kowa, jikkar surviniers ce aka ajiye kowa a gefen shi.

Turare ne mai kyau da ƙamshi da kwalin tissue da hanky, babu photon mu a jiki, saidai sunan mu kawai, wannan kuma aikin Ammi ne, inda ta sanya Sir Salim ɗin yayi mani a matsayin gudunmuwa.

Ko bayan da aka watse ni ɗakin da aka fiddo ni cen aka maida ni, haka aka kwana ana maganar kamun nan, inda ko shi ya Ameen da kyal muka samu muka ɗan yi waya dashi, saboda irin gajiyar da nayi ga bacci ina ji.

Washe gari da suka tashi komawa, masarauta ce tace ba zasu tafin ba, ai su jira kawai ayi ɗaurin aure a basu amarya, haka kuwa akayi ranar Juma'a ɗin aka sanya ni a lalle.

Ɗan bala'i hajiya kubra ko kiran su Hajiya Sa'a bata sake yi ba.

Hakan bai masu daɗi ba, kuma ko sun kira ta bata ɗagawa, ranar kuma ko falo bata sauko ba, tana ɗaki tana ruwan masifa, inda bata bari kowa ya fahimci halin da take ciki ba.

Shi kau malamin nasu, koda Su Hajiya Sa'a Suka kira shi, cewa yayi aikin gama ya gama, saidai Abunda ba'a rasa ba, Amman don tsabar ta fa sai ya tsane ta, kawai dai suyi ƙoƙarin ganin ya kusance ta, muddin suna so abun ya karye.

Haka suka dinga sa ƙawa da warwarewa, wannan karon kuwa suna ji suna gani ba zasu bari Kubra ta rasa damar ta na samun jikoki wanda suka fito daga wannan babban tsatson ba, ba zasu bari ƙiyayyar ta sanya idon ta ya kulle ba, su sun ma yi mamakin da har yanzu bata gazgata abunda taji an faɗa mata ɗin ba.ko da yake ba zata gane bane, tinda ba wai gani tayi da idanun nata ba.

*******

Ranar Asabar ɗin kafin kace me gari ya cika da baƙi, jini ya kaje ji ko ta ina tana tashi, ɗaurin auren fa ya karaɗe lungu da saƙon ƙasar, mutane ko ta ina ɓulɓulwa suke yi, ranar ne fa jikin Hajiya Kubra ya fara sanyi, ganin sanarwar ɗaurin auren da kafafen yaɗa labarin keyi, akan cewa lallai ɗiyar masarautar *Mai martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo ce*

Jiki a mace take aiwatar da komai, har kai lokacin da tawagar iyayen angon ta ɗauki hanyar tafiya, baƙi kuwa ko ta ina ɓulɓulwa suke, matan manya ne cike da sashen Hajiya Kubran da Sashen ƴan kankiyar, abinci kuwa sai shiga da fita dashi ake yi.

Inda hankalin ta ta ɗan kwanta da taji duk wanda ya shigo yi mata murna sai yace yana taya ta murna da haɗa iri da masarautar da tayi, kenan ajin nata da take gudu ya zube bai zube ba? Dayake ƴar duniya ce sai ta saki jiki, ta haɗe cikin wani arnen lace, kai kace dama cen ta yarda da auren ne, sai washe baki take, inda ake ta zuba mata ruwan kuɗin gudunmuwa tana karɓa, domin wasu kuɗin ma cikin farar ledar su ake bata su haka, saidai ta wurga su cikin wata ƙatuwr sip dake ajiye gefen nata.

Ta sha gwala-gwalai, ko su ƴan kankiyar sunyi mamakin yanda ta saki jikin ta, sai shiga da fita takeyi, har sashen nasu yau ba zasu iya ƙilga shigar ta nawa ba, Amman idan ta tuno da Abunda suka ƙulla, har yanzu zuciyar ta ba wai ta amince bane ko bata amince ba, bata kuma sani ba, tayi nadama ko ɓarayi ba, har sai ta tabbatar da zahiri.

Haka masu kirari suka cika ƙofar gidan, maroƙa da mawaƙa, duk da wai ba'anan ma ne za'a ɗaura auren ba.

Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi dubban mutane suka shaida ɗaurin auren *Gimbiya Hauwa'u Muhammad da kuma Angon ta Yarima Al'ameen Almustapha Dambulan* akan sadaki naira dubu ɗari. Inda aka kuma bayar da dukiyar aure naira miliyan ɗaya, wannan kyauta ce daga asusun Alhaji Auwalu Yusuf uban ango, zuwa ga amarya Gimbiyar tasu.

Ɗaurin aure yayi mutane, kowa ka gani sai washe baki yake, a faɗa aka ɗaura auren, inda aka zarce da shagalin cin abinci kai tsaye.

Ba'a so a ɓata lokaci, saboda yanayin hanya, duk da yau dai kam an zuba jami'an tsaro kala da kala a hanyar, saboda kai kawo ɗin ƴan ɗaurin auren da wasu ma daga nesn duniya suka fara isowa tin jiya saboda yarima na matasa ne.

Umma kam uwar amarya ba'a cewa komai, sai walwali take yi, haɗimi na ta faman hidima, su Hajiya Zainab da Ammi ne kan gaba gaba wajen aiwatar da komai. Inda mama Fulani ta sakar masu ragamr komai, duk da ba da Umma za'a tafi ba, Amman daga Hajiya Zainab har Ammi sunce ba za'a tafi kai amaryar ba tare dasu ba, wannan karon dai kam harda Fulani, da kuma matar shugaban ƙasa cikin waɗanda zasu yi ma amarya rakiya zuwa ɗakin ta.

Nasha Kuka yau bansan dalili ba kuma, haka ak fiddo ni, fuskabjabge da hawaye zuwa wajen mai martabar, faɗa sukayi mani sosai da sosai, inda aka maida ji wajen Umma da su Fulani da su Hajiya Zainab da Ammi. Nan ma dasawa suka yi, inda su mai martaba suka tsaya.

Nan fa aka fara hada hadar haɗa motoci na tafiya kai amarya.

Inda Su ya Ameen da wuri suka wuce domin haɗa takar angon da zasu yi ta yamma liƙis, lokacin amary ta iso.

Tin cikin mota kan nashi ke mashi ɗan ciwo haka kaɗan kaɗan, ba suyi mamakin ganin ya kama bacci ba a motar, sanin irin gajiyar da ke jikin shi da sukayi.

Su Yi tafiya mai nisa ne ya farka yana mai tambayar Bilal wai har yanzu basu isa ba?

Bilal ne ke sanar dashi ai sun kusa, suma amarn sun yi waya cewa gasu nan sun taso.

Ɗan tsaki taja yana mai cewa "Bulal hawan da bar na fa bana tunanin zai yuwu gaskiya, ni fa hidimar nan ta ishe ni, ba za'a iya barin ta ba wai?"

Da mamaki Bilal ɗin ke kallon shi, kaman ba shine ya matsa akan su tafi su shirya komai ɗin ba kan lokaci, saboda yana so ya burge amaryar idan an iso da ita, gashi kuma sun haɗa gagarumar dinner ɗin da daddare.

" Me kake nufi ne wai Friend? Naga sia wasu abubuwa kake yi, kaman ya abar hawan?"

"Eah a bar shi kawai fa, ni har dinner ɗin ma bana tunanin zan iya halarta, kai in short ma fa, ni na fara tunanin menene dalilin da ya sanya ni amince ma auren yarinyar fa da nayi"

Burki Bulal ɗin yaci da ƙarfi, har abokan tafiyar nashi suma suna yin larking, Allah Allah suke yi dai ba wani abu ne ya samu motar da angon yake ciki ba. Da matuƙar mamaki Bilal ɗin ke kallon Al'Ameen.

"Ban fa fahimce ka ba fa malam, me kalaman ka ke nufi ne Al'ameen? Kaman ya? Anya kuwa lafiyar ka ƙlau? Kasan me kake faɗa kuwa?"

Da masifa cike yake kallon Bilal, malam me ya hana kai ka aure ta? Me ya hana? Auren nan sai nake ganin kaman tursasa mani akayi nayi shi, ni fa Sam yarinyar ta fita a kaina, gaskiya bana tunanin idan zan iya jure ma zama da ita"

Ganin kaman abokin nashi ya zare be, ya sanya ce ma sauran abokan angon su koma motoci su, ba matsala yanzu zasu gyara

Suma dai basu kai ga fahimtar inda kalaman abokin nasu ya suka dosa ba, suka koma mota jiki ba kwari, inda sukayi ma motoci key suka sake ɗaukar hanya.

Shima Bilal tada motar yayi yana mai girgiza kai yake faɗin "you are not fine gaskiya friend, baka da lafiya ga dukkan alamu, Allah dai yasa ba stress bane ya kama ka."

"Ba wani Stress Bilal, I AM Al'ameen Dambulan, and I am fine is u can see"

"Girgiza kai Bilal yake" Kafin ka ɓata mani rai, zaifi kyau kayi shiru kawai friend, hawa ba fashi kaman yanda dinner ma haka babu fashi insha Allahu, yanzu haka ma nayi waya an gama shirya komai, kawai isar tamu ake jira.

Cikin serious tone Al'ameen ya shiga kallon ya Bilal, sai kuma ya fara magana cikin ɗaga murya *"NACE BA ZANJE BA KUMA KAI BAKA ISABKA SANYA NI INYI ABUNDA BANYI NIYYA BA BILAL, U KNOW WHO I AM, BANA MAGANA BIYI, DON HAKA SAI KUJE KU KUYI TA YI, AURE DAI NE NA FAƊA DA BABBAR MURYA CEWAR NAYI NADAMAR YINSHI SAI KUMA YAYA???"*




~Oum-Deedat ce~

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login