Showing 234001 words to 237000 words out of 247770 words

Chapter 79 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10436

da suka rako su, ganin hakan sai suka sulale suka fice, domin doka ce cewa ba zasu taɓa tsayawa ayi maganar da ta shafi masarautar gaban su ba.

Kaina a ƙasa na shiga gaida ta. Waya Ammi ta ɗauka tana mai kiran Salim, nan ta shiga shaida mashi Abunda ke faruwa, da alaƙar shi da Suhan ɗin, yana cikin raɗaɗin rabuwa da Suhan ɗin, ce mata yayi kawai sai yazo, ya datse wayar yana mai runtse idanu.

Fulani ce ta samu bisa sofar dake ɗakin ƙwaya ɗaya ta zauna, itama mamaki takeyi inda har Khaltum ƙanwar tata ta san mu haka.

Nan Ammi ta shiga shaida ma Addar tata yanda akayi ta santa, da kuma irin abubuwan da suka faru.

Gyaɗa kai ta shiga yi cike da sarauta, "Khaltum ashe kin daɗe da sanin hasken masarauta Gimbiya Merama, Amman dayake ba zumunci yanzu sai ba ku gane juna ba, baku san ku ƴan uwa bane"

"gaskiya ne Adda Fulani, saboda haka ayi haƙuri, Nidai nazo da mai gyaran jiki, wadda zata fara yi mata kuma daga yau, saboda haka sai a shigo da ita, domin muji yanda abubuwan zasu kasance"

"Haka ne Khaltum"


"Gajee" Fulani ta kwala ma wata haɗima kira, ɗaya daga cikin masu kula dani.

"Na'am ranki ya daɗe" ya faɗa tana mai shigowa da gudu ta gurfana gaban ta"

"Aje maza a shigo da mai gyaran amarya"

Fulanin ta faɗa cike da isa.

"an gama rani shi daɗe"

Ta faɗa tana mai miƙewa ta sunkuya mata, muma ta juyo ta sunkuya mana, sannan ta fice.

Nidai zaune nake, na kasa sakin jiki na sosai, ga Ammi ga Fulani, firar su suke yi a hankali irin ta ƴan uwa.

Gaje ce ta shigo da mai gayarn jiki.

Su duka durƙusawa suka yi, suka sake kwasar gaisuwa ga Fulanin, sannan gaje ta miƙe ta fice.


"Muna so ne za'ayi mata na musamman, saboda haka kada ki damu da Abunda za'a baki ko na nawa ne ayi mata" cewr Ammi dake zaune gefe na riƙe da hannuwan nawa har yanzu.

"To Hajiya yanda kika ce haka za'ayi, saidai dole ne gimbiya ta kiyaye shiga rana har sai ranar da aka kammala"

"Ba damuwa, dama babu inda take zuwa" cewar Fulani dake hakimce bisa kujera.


Sake gurfanawa tayi, tana faɗin "An gama Ranki ya daɗe"

Fulani ce ta miƙe tana mai cewa "Hajiya Khaltum idan kin gama, ina mai jiran ki a sashen nawa"

Tana gama faɗar haka ta sanya kai ta fice, fuskar ta cike da fara'a. Na kula mutumci da kirkin Su Ammi a jinin su yake, to ni kam ina mamaki ta ina suka haɗa alaƙa da su Umma? Koma dai minene nan gaba zamu ji.

Kasa sakin jiki nayi, nan mai gyaran jikin aka nuna mata toilet ta shiga ta fara haɗa abubuwan ta, nan fa ɗakin ya ɗauki ƙamshi na musamman, har baka gajiya da shaƙa.

Ammi bata bar gida ba sai kusan dare, har bayan da aka gama man dilka da halawar sana, ɗaki guda aka ba mai gyaran jikin zata zauna nan har a kammala.

Da kanta Ammi ta dinga yaba ƙyauna, har yanzu tana jin babu daɗi rashin samu na da Salim ɗin baiyi ba, kuma gashi lamarin Ma'u maimakon abu yayi baya sai gaba yake ci gaba, yanzu ta kai da ko kwanciya da ita Salim ɗin yazo yayi sai ta barbaɗa ma ƙawayen ta, ga ƴan shige shige da gulmace gulmace da muguwar ƙazanta.

Naji daɗin kasancewa da Ammi, duk da duk yanda naso in saki jiki da ita na gaza, duk da ina mata kallo ne kaman na Umma ta.


*******

Kwanaki na ɗauka ana mulke mani jikin nawa, yanzu ko ni bana gajiya da shaƙar ƙamshin jiki na, duk da ina jin jiki wajen dirzar mani jiki da ake ta yi. Cikin kwanakn su Raihana suka iso, su kansu sunyi matuƙar mamakin ganin gidan namu, dama dai ban taɓa ce masu komai dangane da ko ni ɗin wacece ba, dama haka ake son mutum da kama bakin shi, domin yana iya sakin jiki yayi ta bada labari abubuwa suzo su cenza, daga baya ayi tunanin ƙarya yake yi ba haka bane.

Naji daɗin zuwan nasu, dasu aka haɗa aka cigaba da gyara mana jikin. Ya zuwa yanzu bana da matsalar kaɗaici, matsala ta ɗaya, rashin kasancewa da Yayan da bana samun yi sosai ko a waya, to shima dai ɗin abubuwa sun mashi yawa, ga tarin masoya da abokai da suke ta ɓullowa jin hidimar tashi ta kankama.

Ya zuwa yanzu fata ta tayi wani irin sulɓi da kyau, ga wani sheƙi da walwali da take yi, hatta man da nake shafawa wani haɗi ne na musamman, kowa ya ganni sai ya yaba, akai akai Ammi ke zuwa ta duba ni, tare da tambayar ko bana da wata matsala, su kansu su Raihana sunyi mamakin cewa wai ita ce mahaifiyar Sir Salim, ashe ma duk abun nan muna da alaƙa da su ta sosai. Itama sakin jiki take suyi ta fira, wani lokaci har da Aseeya ƙanwar Sir Salim ɗin sukan taho, wadda ta shige cikin mu mun zama kaman ƙawaye.

Tin ranar da Ammi tace kayan zasu isa, suka isa ɗin, sunyi mamakin kayan ita da Hajiya zainab, masalan da Umman ta sanar da ita wacece Hajiya Khaltum ɗin a wurin ta, domin Ammi ta ce ba zata kira Umma akan alaƙar dake tsakanin su ba, jira take sai tazo kwatsam su haɗu suyi ta mamaki.

Hajiya Zainab ce ta kwashi kayan zuwa sashen nawa, wanda aka haɗa har ya gaji da haɗuwa, shi kanshi Ya Ameen tinda aka gama tsara sashen bai shige shi ba, dayake makullan na hannun Hajiya Zainab ɗin, sai yabar mata, ko da suna so su ƙara zuba wani abu ciki daga baya.

Hafsat da tazo taga sashen ihun murna ta saka, ya zuwa yanzu cikin nata kaman zai faɗo, sai nishi take daƙyar take ɗaga ƙafa, domin ya wuce watan haihuwa tuni, so suke suyi mata aiki, daga ita har sadeeq ɗin sun hana, cewa sukayi a bari idan lokacin haihuwar yazo ba abunda zai hana a haihun.

Tana yawan kira na, akai akai mu kan yi waya, da cewa tayi itama zata zo, sai da akayi da ƙyal aka bata haƙuri akan kada taje cen ta haihu masu, ba don ranta yaso ba, tana ji tana gani Umman tawa ta shiga harhaɗa kayan da zata tafi dasu cen.

Saura sati ɗaya biki ƴan kankiya suka iso, kaf gidan babu wanda bai girgiza ba ganin ɓangaren da aka tanada ma amarya, ya zuwa yanzu dai maganar kamun da za'ayi a ɓangaren amarya ya yaɗu, saidai babu wanda yasan inda za'aje ayi shi ɗin.

Su ma dangin Maman Hajiya Kubran sun iso, sai zuba isa da habaici suke yi, to dayake ba wanda ke ta su, umma dai in dan ita suke yi, saura kwana biyu ma tabar masu gidan, sai suyi ma wanda zasu yi mawa.



Haka kuma isowar ƴan kankiyr ne ya shaida ma sauran ma aikatn ɗin wadda Al'ameen zai aura, ai Maree suma tayi, saida aka yayyafa mata ruwa, koda ta farfaɗo sai ta saki kuka mai haɗe da ihu, tana ta shiga Ukku ta lalace ita Al'ameen zaiyi ma haka? Ganin asirin su zai fallasa ne ya sanya Mama talatun cewa ai aljannu ne suka kama Maree ɗin, ba wai don sun yarda bane, sai dai ya zuwa yanzu kowa ya gane nufin Maree da Mama Talatu da tuni aka daɗe da gano cewa ita ce mahaifiyar ta, na son mallakar gidan, kuma ya zuwa yanzu kowa ya gane cewa Mama Talatu da Mama saude sune munafukai gidan, kuma Al'ameen ya san duk wani abu dake faruwa, domin kuwa ya sanya Mudee yana mashi CID a cikin gidan, kuma duk Abunda ke faruwa yana sanar dashi ɗin.


Aiko gida ya kacame, ko ina ka gani sai hada hada ake yi, dangin Hajiya Kubra suka buƙaci da abasu makullan sashen Al'ameen ɗin zasu duba, Hajiya Zainab ta hana su, tace masu bata san inda ta saka ba, dole haka suka yi ta gaye gayen magana suka haƙura, duk da jin kansu da suke su wasu ne a gidan.



Cikin kwana biyun ne Alhaji ya bada motar da za'a kai Umma Adamawr, Hajiya Zainab ce ta raka ta, kwana ɗaya tayo ta baro Ummar cen ta dawo, tayi mamakin yanda ta tadda ana ta shiri masarauta, kowa ka gani cikin farin ciki, domin tin bayan hawan mai martaba ɗin ba'a ƙara wani shagali ba a masarautar da ya wuce na salla, kasancewr Allah bai bashi haihuwa ba.

Cikin ƴan tarbar Umman harda Ammi, su duka sunyi mamaki, masalan da Ammi ta shaida ma Umma yanda suke, ai sai aka buɗe sabon ba in fira da ƙaunar juna, Aseeya ƙanwar Sir Salim ta dawo nan gidan har sai an gama hidimar bikin, itama kullum mitar ta, cewa take dama Yayan natane zai kwashe ni gabaki ɗaya, su Raihana ne ke ce mata, dan bata ga wanda zan aura bane Shiyasa take cewa haka, har take ganin ƙarkon yayan nata.


Ranar da su Umma suka tafi, ranar Su Afnan suka iso, har kuka tayi jin cewa wai ina cen kuma yau Umma suka tafi.

Shagwaɓa take ta zuba ma yayan nata, wanda daƙyar ya ratso ya shigo gidan shi da Bilal, akan cewa sai ya sanya an kai ta, ba yanda ya iya, haka ya tada mota aka tafi kai ta inda muke ɗin, to itama dai da kallo take bina, ganin a inda nake da kuma yanda na koma.

"Allah yaso ba muyi asara ba" Abunda ta fara furta wa kenan tana mai ruƙunƙume ni.

Tayi mamaki, kuma dama haka lamarin Allah yake, zata so taga yanda Mom ɗinta zata yi, duk ranar da aka shaida mata ni ɗin wacece.


Nan fa hidima ta kaure, kusan kullum sai an yanka shanaye, kai hadda raƙumma aka yanka, kaji kuwa kullum ne, hidima ake sosai, ya zuwa yanzu ko ina labarin auren namu ya bazu, kafafen yaɗa labari sai sanarwa suke yi.

Ko da Hajiya Kubra taga iyayen kayan da Aunt Feena ta haɗo, faɗa ta hau yi, wai akan me za'a banzatar da kuɗi haka? Akan wadda hatta da kayan ɗaki uban ango ne ya sanya mana, saboda tsabar faƙiranci da talauci.

Ƴan uwan nata na zuga ta, to basu da yanda zasu yi, dandai ƴan kankiya sunga kayan, Amman da rage su zata yi, ko gwala gwalai da aka zubo ciki sunfi saiti goma, ita babbar matsalar ta da zai kasance cewa ba wani abu zasu samu ba in return.

Haka suna ji suna gani Alhaji Mustapha ya sanya aka kai kayan lefen sashen amaryar aka kulle. Tinda dai ance ba za'a kai ba sai an kawo ni ɗin.

Yanda tafiya kamun zai kasance ake tsarawa, ƴan uwan Hajiya Kubra cewa sukayi ba zasu je ba, sai dakyal ne suka zaɓi mata Ukku shima dan kar ace abun nasu yayi yawa ne, da Hajiya Laila da Hajiya Sa'a mutum biyar kenan, dama su su Nihal ba'a tsara dasu ba, saboda ansan cewa ba zasu je ɗin bane ba ma, suma daga cikin ƴan kankiya mutum biyar, duka mutum goma kenan.


Hidimar da akeyi gidan da shagali da akeyi, kaman ba kuɗi ake kashewa ba, dan dai Alhaji Mustapha hannun Hajiya Zainab ya hannanta komai, saboda yasan idan ya bar Hajiya Kubra akan hidimar za'a ga ba daidai bane.

Sashen Umma kuwa saidai aka kulle shi.


********


"Laila na fara nadamar amince ma auren nan da nayi fa, kada ina ji ina gani wankin hula ya kai ni dare, yanzu fa kina gani sai in kwana in yini ban sanya Al'ameen a ido na ba fa, tin ma yanzu kenan?"

Hajiya Kubra ta faɗa, tana zaune gefen gado ita da sa'a Hajiya Laila kaɗai ne a ɗakin.

"Kada kice haka Hajiya ta, komai zai tafi yanda aka tsara, ai ki ƙyale su, wannan dariyar da suke yi zata zame masu kuka ne, ba ita Maryamar ta tafi ba? To ki zuba idanu ki gani, ita da gidan nan sai a lahira, kuma itama yarinyar da za'a kawo da ƙafafn ta zata kwashi takalman ta a sukwane ta bar maki gidan ki"

Cewar laila ɗin wadda ta dafo kafaɗar Ƙawar tata cikin wani irin yanayi na jimami da ƙuncin zuciya.

"Laila girma na da aji na ya zube, muddin na bari akayi auren Al'ameen da yarinyar nan, kowa yasan Al'ameen ba ƙaramn mutum bane, duniya ma ta shaida haka, ace babu wadda zai aura sai maƙasƙanciyar ƴar aiki? Beside ma fa ni na tsani yarinyar wallahi, ganin ta nakeyi kaman aljana ma ni, wani lokaci fa idan ina kallon ta sai inji gaba na yana faɗuwa"

"Kada ki bamu kunya mana Hajiya Kubra, ki daure ki cije ayi abun nan lafiya, kada ace kece kike ɓullo da wani tashin hankalin kuma" cewar Sa'a dake gefe, wadda ta taso itama zuwa ga Hajiya Kubra ɗin.

"Sa'a ku tabbatar duk Abunda aka shirya ya kammala, ku tabbatar yarinyar nan bata samu wuri a zuciyar Al'ameen ba, ku ruguza abun ku wargaza komai, gaba na yana ta faɗuwa, masalan kwanan nan, gani nake kaman wani gagarumin abu na shirin faruwa, ku taimaka mani ku san yanda zakuyi"

Hajiya Kubra ɗin ta faɗa cike da zullumi.

"Hajiya Kubra ki kwantar da hankalin ki, ina mai tabbatar maki da cewa da zaran an ɗaura auren Suhan da Al'ameen ba zai kuma kallon ta a matsayin ɗiya mace ba, zata dinga warin jaɓa, zata zama kaman mujiya a cikin tsuntsaye a idanun shi, idan ta doshe shi, zai ga kaman baƙin maciji mai tattare da dafi ne ya fasa kai ya nufo shi, zai ƙuntata mata, zai tsane ta, zata yi nadamar Auren yaron namu da tayi"........











~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'a idan aka ga wani wanda wata masifa ta fada masa:*

الْحَمْدُ للهِ الَّذِي عَافَانِي مِمَّا ابْتَلاَكَ بِهِ، وَفَضَّلَنِي عَلَى كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقَ تَفْضِيلاً
.
Alhamdu lillahil-lazee 'afanee mimmab-talaka bih, wafaddalanee 'ala katheerin mimman khalaqa tafdeela.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda Ya amintar da ni daga abin da Ya jarrabce ka da shi (na masifa), kuma Ya fifita ni a kan da yawa daga cikin wadanda Ya halicce su fifitawa.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*_Bana da bakin da zan iya gode maku, ashe haka ban fi ƙarfin ta yake da masoya da fans? Haƙiƙa ina mai alfahari da ku masoyana na haƙiƙa. To kuna ina? Duk ku fito mu ɗinguma zuwa gidan mai martaba domin gabatar da shagalin wannan gagarumin aure, yau dai Allah yayi. Saboda haka ne duk nake maku fatan alkhairi_*

*Salamatu Abj, and Mrs Daura Kd, aga saƙonƙu kuma na gode wannan ya nuna mani iya wuya kuna tare da ni, to babu Abunda zan iya cewa anan illa Allah ya haɗa mu gabaki ɗaya a aljanna firdausi ya raya mana zuri'ar mu, ya barmu da mazajen mu tare da ƙunrsu gabaki ɗaya. Nagode matuƙa*

*Ina kike Jiddon Dady? Sarkin hanzari, ai kin riga ma kowa isa, Salamatu mai masaukin baƙi, da fatan dai kin shirya tarbar ɗinbin tawagar BANFI ƘARFIN TA BA FANS da ƴan GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION domin yau fa kina ga gaggaruman baƙi*

*Page ~61~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


"Ki kwantar da hankalin ki, ki dai yi masu ta ƴan duniya Hajiya ta, da idanun ki zaki ga Abunda zai wakana, duk ki sanya masu ido". Cewar Hajiya Laila da take zaune gefen Hajiya Kubra ɗin.

Ita dai sai faman ƙutawa take yi, hankalin ta a matuƙar tashe, masalan da take ta amsa waya, ta ƙawayen ta da matan manya akan cewa zasu shigo hidimar insha Allahu. To da wane ido zata kalle su ta faɗa masu surukar tata ɗiyar mai aikin ta ce? Kai wannan abun kunya da zubda girma da yawa yake, ita bata hango wani dalilin da ya sanya Alhaji yace dole sai anyi auren ba, ko kuma shi Al'ameen ɗin mai ya gani jikin yarinyar ba.


****'******


Zuwa yanzu dai ni kaina nasan saidai maƙiyi yace ban yi kyau ba, ko ban haɗu ba, koda yaushe muna tare da Ya Ameen a waya yanzu, saidai suga ina ta sakin murmushi dayake yanzu earpiece nake sanyawa a kunnen nawa, ita kanta mai gyaran jikin nawa kullum faɗa take yi tana so taga angon nawa, dayake ita ce mai gyaran jiki, ƙunshi da kuma kwalliya, Ammi ce ma take faɗa mani wai da ita zamu tafi Abujan har ranar walima duk ita ce zata gyara amaryn.

Hidimar biki ake ta yi fafa, duk yawan mutanen da suke zuwa gidan nan, haɗimai ne ke masu hidima, nan su khadeeja da Raihana aka baje ƙafa, har yanzu mamakin daraja irin ta su Suhan ɗin suke yi, ga tsabar mulki da ake zubawa a masarauta, komai a tsare ake yin shi.

Ana haka ne sai ga Jidda ƙanwar Oum-Deedat ta isa,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login