Showing 6001 words to 9000 words out of 247770 words

Chapter 3 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10396

a kotu nake, da sainafi sake wa, Da ace a gaban mutum nake kaman YaAmeen muna magana dashi one on one.

'Yar guntuwar dariya yayi, "Wow kina fadin har kinyi degree da masters, A hakan nan yanda kike yar mitsitsiya?"

Ya fada yana mai nuna ni da duk kan hannun shi yana sama da ƙasa da su saitin Inda nake tsaye, Da wani yanayi, wanda nidai nakasa ganeshi; don bazance zaulaya ba don nasan ba halinshi bane yin hakan.

Sai a lokacin nagane kuskuren danayi,dan zaro idanu nayi alamar wayyo Allah, Gami da Jan sauran hijab dina, na ruge fuska ta ruf, ina dan mai sakin ɗan k'aramin murmushi;

A hankali nace, "am sorry secondary nake nufi yaya"

"OK good " ya fada a gajarce, Yana mai ƙara nazarinta, ko buƙatar da yake da ita zata samu karb'uwa awajenta?

"Ina so kici gaba da makaranta, domin zaman ki a haka kina wahala ba abune mai dad'i ba; ko babu komai ilimi yanada dadi, zaki taimaki kanki ki taimaki ummanki" Ya tsagaita yana mai zura mata idanu da ke taimakawa wajen ƙara ruɗa ta; Domin yaga yanda zatayi, Nikau bansan lokacin da nabude fuskata ba gabaki daya, ina mai sakin murmushi har siririyar wushiryar dake saman hakora na ta bayyana.

"amman kije ki shawarci ummanki, kuma ina so maganar ta tsaya iyakar ni, da ke, da ita; Don bana so wani ya sani kaf gidan nan, idan ta yarda sai ki kawoman takaddunki, da kuma zabin makarantar dakikeso kiyi da abunda kikeson karantawa, kibar sauran maganar a hannuna. Kome zamu ji, ko zaku gani, Ku kauda idanunku gabaki daya, Babu ruwanku a ciki, Ni nace zan yi, kuma insha Allah zanyi;"

Yana gama fadar haka ya juya, Yana mai barin tanqamemen kitchen din, da kai ka rantse da Allah ba'a Nigeria yake ba.

Dakallo na bishi, a yayin da kwalwa ta ta cunkushe,

"tabbas tabbas mafarkina zai tabbata, tabbas lokaci yayi; Alhmdllh naketa faɗa, a cikin raina, saboda na ma rasa tinanin da zanyi, bayan wannan; Juyawa nayi, gami da ci gaba da aiki na.

A gaggauce na gama na rufe kitchen din, gami da barin part din baki daya zuwa namu, Amman zuciya ta cike da tarabbabi, domin nasan halin umma ta, Sannan ni na san kafin in dosheta da maganar, Sai nayi nazarin abunda zance mata tukunna, Don na san ta da gudun duniya da abunda ke cikinta balle wulaqanci irin na hajiya kubra.

Ko da na isa part din namu, Na tadda umma ta, tasha magani amman takasa yin barci, saboda taga na dade har wajen karfe goma da wani abu, Alla Alla take yi, ya kasance lafiya, Gashi ko abinci na ma ban ciba, ina shiga kuwa na taddata zaune bisa sallaya.

Allah sarki umma ta, Mace kamila mai gudun duniya, Mace mai ibada, da rashin hayaniya, Amman dukda wannan halin nata, hakan baisa Hajiya kubra ta ɗaga mata ba, Ni gani ma nakeyi kaman babu wad'anda ta tsana irin mu acikin masu aikin dake gidan, Wanda munfi mu goma sha wani abu, ummata ce ta katseman saqa da warwarar da nake tayi cikin zuciya;

"lafiya dai ko mama na?" ta faɗa tana mai miƙewa a hanzarce, sannan ta ci gaba da magana cikin dan firgici kaɗan; "Naga dare yayi sosai, ya kamata ace yanzu kin kwanta ki huta hakanan"

Ta faɗa cikin sanyinta, mai sanya ni natsuwa, duk da a ɗan firgice take; Kome nake yi, ko ban fad'a ba, son da ummata keman yafi wanda nakeyi mata, Duk da kau a duniya babu wadda tafi soyuwa a raina kamanta, Tinda ita kadai na sani, ita kadai na tashi na gani , ita ce uwata, itace ubana, ita ce yayata, abokiyar shawara ta kuma, ta fanni daya kuma abokiyar wasa ta;

"Ina hankalinki yake ne ummina? Ina ta magana kinyi shiru" ta faɗa tana kamo hannuna, bansani ba ashe har ta nade abun sallar ta iso inda nake tsaye daga bakin ƙofa a tokare.

"Umma saida najira suka gama sannan na wanke kayayyakin kinga gobe in Allah ya kaimu mun rage aikin;" na faɗa, ina mai kama mata hannu nima, muka zauna gefen katifar tamu dake yade a tsakiyar dakin.

"ga abincin ki tau, maza kici ki kwanta, kinga karmu makara gobe dasafe in Allah ya kaimu banaso kullum muke b'atawa hajiya rai;" ta faɗa tana jawoman kwanon abincin.

Kwanon silver ne amman tsaf yake, kaman sabo sai sheqi da walwali yake yi, kaman yau aka budeshi a leda, Allah sarki ummana akwai tsafta, dakin namu ma sai k'amshi yake yi, an goge tiles dinnan sai daukar ido yake yi, abunka ga fari, dakinmu tsaf yake babu tarkace da karikitai, in ka cire katifarmu, sai labulaye da wani teburi a gefe, inda muke ajiye daddumar sallah tamu, da sauran litattafan addini himili guda, kasancewar ummata tayi karatun addini mai zurfi, sai take k'araman duk bayan sallar subhi, akwai wardrop ta bango a dakin, wannan shi ya tak'aita mana tarkace, tinda ba yaro ke garemu ba, kwata kwata ma babu yaro a gidan, kowa da locar ta inda ni biyuma ke gare ni, kasancewar guda uku ce a dakin, amman ajere suke, sai ummata ta dauki daya, tabar man biyu saboda ni budurwa ce zan fita karikitai.

Abincin naci, naje na daurayo bakina na cenza kaya zuwa kayan bacci, muka kwanta umma tayi mana addua muka shafa kowa ya juya cikeda tinani kala kala.

Nikam ta bangare na banyi bacci ba, amman ummana tayi baccinta saboda maganin da tasha, kuma ko ba hakaba, ita bata kwanciya da damuwa ko haushin wani a ranta, takance ba'asan gawar fari ba hakanan kaje lahira da haushin wani duk abun da gaƙuri bai bayar ba ai rashin shi baya badawa.

Gari na waye wa muka gama komai, kama daga salla, karatu, da wanka; zuwa karfe bakwai, kowa yayi shirin fara aiki kaman yanda yake a al'adar gidan namu. Amman mu bamu kai ga fita ba, sabo da ƴan cikin gidan ma basu kai ga tashi ba, kuma ina so in yima umma ta maganar karatu na; sai dai ina zullumin tunkararta da maganar, sabo da na san halin umma ta sarai, wani d'an qaramin yak'i ne gabana, Amman duk da haka hakanan zan daure in tunkareta da maganar domin ga dama ta samu, kuma ko ba komai hakan ci gaba mu ne ni da ita baki daya, fata na dai da addu'a ta Allah ya ɗora ni akan ta, ta yadda ta amince mani, sabo da wannan karon ina tsoron YaAmeen ya ji haushi ya janye burin taimakon mu a ranshi, saboda ba wannan ne karo na farko ba da umma ta ke daƙile shi akan duk wani burin taimaka mana da yake yi, Wanda shi a ranshi har ga Allah taimakon ummana din ne kan ingiza shi ga hakan saboda rashin hayaniyarta da biyayyar ta ga iyayen nashi.

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)

*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)

*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.



*Page* ~5~


°^^^^^^^^^^^^°


Bayan mun gama karyawa ne, muna zaune a ɗaki ni da umma ta,Tana yanke farcen ta na hannu, Yayin da ni kuma nake zaune gefen katifar tamu da littafin hisnul musleem a hannu ina karantawa.

Rufe littafin nayi tare da maida shi ma'ajiyar shi, na dawo na zauna daf da ita, tsawon second biyar na dauka ban iya cewa ƙala ba, tabbas abinda nazo mata dashi ni kaina na san mai girma ne, to sai dai ba yadda na iya, shahada nayi na bude baki na a hankali nace;

"Umma don Allah ina so muyi magana dake" cike da mamaki ta ɗago idanun ta tare da tsare ni da su, take guntun tunani yazo a ranta, wacce irin magana ce wannan da maman tata bazata iya tunkararta kai tsaye da ita ba? Koma dai menene tana fatan ɗiyar tata ba zata zo mata da wani abu akasin tunani nata ba;

"ina jin ki mama na" ta bani amsa tana mai dakatawa daga yanke farcen gami da sauke hannun kan cinyoyinta.

"Umma don Allah ki saurare ni kuna ki fahimce ni, wannan karon izinin ki nake nema; ki duba halin da mu ke ciki na rashin sanin madafa, dama ce ta zo mana da zamu fita daga cikin wannan ƙangin bautar da mu ke ciki, dama ce da zata sanya mu dogara da kanmu har ƙarshen rayuwarmu."

Tinda na fara magana ta tsira man idanu ba tare da tace kanzil ba, sai dai ni bazan iya karantar abunda ke cikin zjciyar tata ba;

Ganin yanda ta kafe ni da idanu ya sanya ni sauke kwayar idanu na ƙasa ina mai murza yatsu na suna bada sauti ƙas, ƙas.
" Uhm, ina jinki mama na, wannan wacce irin dama ce? Ina fatan dai zaki zo mani da buƙatar da kika san zan iya amincewa da ita, ba wadda kika san za ta iya sanyawa ranki ya ɓaci ba"

Tinda ta fara magana bugun zuciya ta ya ƙaru, fargaba da zullumin yadda zata ɗauki maganar suka baibaye ni, dakyal na bude baki na cigaba da cewa;

"Umma jiya ne Ya Ameen yace ya kamata in koma makaranta domin yana so mu zama masu tallafar rayuwarmu da kanmu, kuma yace in nemi izinin ki na bashi takaddu, da kuma zaɓin makarantar da nake so, tin jiya nake zullumin tunkarar ki da maganar, domin ban san yanda zaki kalli abun ba, wallahi umma ba nice nayi mashi magana ba, shine da kan shi ya same ni kitchen ina wanke wanke ya man maganar;

Idan dai ba idanu na bane suke man ƙarya ba, wannan. Karon kallon da ummar tawa take man ya cenza salo, ya rikiɗa ya koma kallo ne mai cike da gargaɗi da kuma tuhuma; kafin ta bude baki ta cigaba da Cewa

"Masu gadi ma da drebobi ban hanaki magana dasu ba? Balle Al'Ameen ɗanɗan masu gida? Miyasa kike son cenza hali ne Hauwa'u"

A firgice na ɗago ina mai kallon ta cikin tsananin firgici damuwa fal a raina, yau ni ce umma ta ta ke kiran sunana kai tsaye; me ya sanya ni? Me ya kai ni? Me ya ja mani? "tsabar son zuciya da hangen gaba" zuciya ta ta bani amsa, tini kwalla suka soma shatata daga idanu na, wanda tini kalar su ta juye daga farare tas zuwa jajaye;


Hannun ta na kamo gami da runtse su sosai sannan naci gaba da magana ba tare da damuwa da goge kwallar ba, gara na barta ta zuba ko zanji saukin raɗaɗin da zuciya ta keyi mani,

"Don Allah umma kiyi haƙuri, wallahi tallahi bani na mashi magana ba, iskeni yayi har kitchen, kuma daga ni sai shi muka yi maganar, umma kiyi haƙuri in na bata maki rai insha Allah bazan sake ba" Na Faɗa wani tuƙuƙi na taso man daga cen ƙasan rai na,

"Ni baki ɓata man rai ba Mama na, gani nayi kawai kaman baki gudun wulaƙanci daga wurin hajiya Babba ne,
sanin kanki ne da ta ita ne ma da yanzu mun bar gidan, sabo da Alhaji ne kawai muke zaune har yanzu, tau minene yasa ba zamu kiyaye ba? Tabbas kinsan idan hajiya taji zaman mu a gidan nan ya ƙare kenan, zata ce ne mun mallake mata yaro gashi har yana wahala akan mu, kinsan kuwa ni bani son abunda zai haɗa ni da su dukkan su balle rayuwa ta ta ɓaci hakanan"

Kuka na naci gaba da yi duk da na ji ta kai aya, Amman zuciya ta na kwadaito man samu ne gashi umma ta na lasa man ɗanɗanon rashi a baki, ban gama maganar zucin da nake ba naji ta cigaba da cewa "idan ya sake maki maganar kice mashi na hana ki, kuma nace mun gode da halacci da irin ƙoƙarin da yake yi a kanmu Allah ya ƙaro buɗi da arziƙi"

Tana gama faɗar haka ta zare hannun ta ta fice a ɗakin, ita kanta cen ƙasan zuciyar tata bata yi mata ɗaɗi, kukan da suhan ɗin ke yi mata yana taɓa mata rai, sai dai babu yanda ta iya wulaƙanci abu ne da kowa ya kamata ace ya guda ba ma ita kaɗai ba, suhan ɗin yarinya ce dududu bata wuce shekara ishirin ba, bata fata wani abu ya shiga tsakanin ta da Al'Ameen, a matsayin ta na babba ta san abu ne mai sauƙi, domin daga tausayi komai ke chanza wa, dukda ta san Al'Ameen ɗin ya fi ƙarfin ɗiyar tata, sai dai ita ba zata so hakan yayi sanadiyyar ɗan zaman da suke yi a gidan ya zo ya gagare su ba.

Ni kau tinda umma ta fice ta bar ni a gurin zaune, fashe wa na kuma yi da kuka tare da faɗawa na kwanta kan katifar tare da kifa kai na, na saki wani irin kuka mai tsuma rai, maraici bai yi ba, mahaifi daban ne a rayuwa, yanzu da yana da rai ko kusa bazan fuskanci irin wannan rayuwar ba, tabbas ummata akan gaskiyar ta take, Hajiya babba muguwar mace ce, yanzu zata sanya a ɓatar da kai a doron ƙasa indai ka nemi shiga gonar ta.

Dukda yace shi kadai zai yi hidima ba tare da ta sani ba, wannan tunani shi ne, Hajiya mace ce mai cikakke iko, komai akeyi a gidan a tafin hannun ta yake, akwai 'yan gulma masu kai mata rahoton duk abin da yake faruwa a gidan;

Ko ba haka ba ma ni mai ya shiga kaina? Mu da muke a ɗosane, sauran ma'aikatan gidan ma duk sun fimu galihu, me yasa nake hangen gaba ne? ALLAH ne kaɗai yasan yanda zai yi da mu, mu bar mashi komai, karatu na ba dole bane, ni cikakkiyar marainiya ce da ban ma san ya kalar mahaifi na take ba, ban taso na ganshi ba, ban taso naji umma ta na maganar shi ba, kuma bata so ina mata maganar shi, shin mai zai sa in ci gaba da damun kaina?


A hankali na rage sautin kukan nawa, gami da goge hawayen, lokacin da idanu na suka kai kan agogo dake maƙale a bangon ɗakin namu, 09:30am, a hanzarce na tashi na shiga bayin dakin namu na wanke fuska ta, ban damu da in shafa ma fuskan komai ba, wa zan ma kwalliya? Rai na a cunkushe yake;

Ƙofar ɗakin namu na fito na tadda umma ta tana tattara sharar tsakar gidan da su sauran ma'aikatan dama basa yi sai ita ko ni, sun ma bar mana mu kadai, a cewarsu ai dama aikinmu ne mu share tsakar gidan tinda ni ke sharar cikin gida, hakan ma baya damunmu in da sabo mun saba.


Wata daga cikin amintattun Hajiyar ce ta zo wucewa zata shiga ɗakin nasu da ke kallon namu, watsa mana wani irin kallo tayi gami da cewa,

"maman Suhana sannu da aiki, Hajiya babba tana neman ku, ya kamata ku tafi domin sun tashi tun ɗazu"

"To uwani, mun gode,an tashi lafiya ko?" umma ta ta maida mata cikin sakin fuska, domin duk kwakwarka ba zaka iya karanto ɓacin rai a fuskan umma ta ba, ko da kayi don ka ɓata mata rai tana tura maka aniyarka ne a wuce wurin; taɓe baki tayi gami da cewa "lafiya" ta shige ɗaki abun ta, muna iya jiyo tashin sauti tsokin ta a hankali.


Juyowa Ummata tayi ta kalle ni cikin sanyi ta tace "Mama na wuce kije gani nan zuwa, sai dai kada ki manta da maganar mu kinji ko?" "To umma" nace gami da juyawa na shiga ɗakin ɗauko hijab ɗina.


*******************************

Yau dai haka na wuni yin aiki sukuku,duk wata hanya da zata haɗa ni da Ya Ameen na toshe ta, ina gama aiki na na koma sashen mu na kwanta yayin da umma ke can tana aikin abincin ranan su, bata bari in taya ta, sabo da Hajiya magana take yi, cewa take kowa yayi aiki shi, ƙarar ƴar mitsitsiyar waya ta rakani toilet ce ta katse man tunanin da nake ina ta juye juye bisa katifar tamu;

Massage ne ya shigo man aunty saudat naso in raka ta shopping, wannan ne ya sanya na miƙe gami da shiryawa domin dama na saba dukan su biyun nice ke raka su, duk lokacin da muka dawo suna kwashe tsofaffin kayan nasu su bani kasancewar su basu da jiki ni kuma ina da ƴar murjewar jiki, dukda sun girmeni sai size din namu yazo daya, haka kuwa aka yi muna dawowa ta tattara tsofaffin abubuwa da bata so ta bani wanda ni a waje na kaman sababbi suke.


*******************************

A haka sai da na shafe kwana uku ina wasan ɓuya da Ya Ameen, sabo da bana so magana ta ƙara shiga tsakani na dashi balle ya tado da maganar karatun nawa, ni a ganina in yaji shiru yasan umma bata barni bane kawai, Daman abunda na sani shine halin yaya Al'Ameen, ba zai man magana ba indai ba nice nayi mashi ba, wannan tasa na saki jiki na ci gaba da ayyuka na yanda ya kamata, na cire ma raina komai da tsammanin zanyi wani karatu a rayuwa ta, na sani dama sau daya take zuwa a rayuwa, ni tawa damar ta zo kuma nayi sake da ita shikenan kawai duk yanda Allah ya so yayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login