Showing 201001 words to 204000 words out of 247770 words

Chapter 68 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10435

ƙyamar ta yakeyi baisan dalili ba.

A hankali ya maida kallon shi kan Nihal ɗin da ta gyara zaman ta, cikin ɗan shakkun Yayan nata haka ta shiga gaida shi.

Amsawa yayi a daƙile, yana jifan ta da wani irin kallo mai ma'anoni da dama.

"Je ki matso mani Cofee"

Abunda kawai ya faɗa kenan, yana mai ɗan zamewa bisa sofar ya jingina bayan shi jikin kujerar.

Da saurin ta ta miƙe, zuwa ga dispenser ɗin da take ta gefen dining da yake cen area ɗinshi ajiye.

A hankali Maree ta ajiye ƴar farar doster ɗin dake hannun ta, tana mai isowa inda yake zaune, daga ɗan nesa kaɗan ta zuƙunna tana mai cewa "Yaya ina kwana? Me za'a kawo maka?"

Bai ko ɗago idanun shi da suke kulle ba ya kalle ta, sai cewa yayi "Kije kawai ki bar shi"

Ko da ya faɗi haka kasa tashi tayi daga inda take zuƙunne, ganin idanun shi a kulle ne ya bata damar kuma ƙure shi da kallo ko motsi bata yi.

Shi ya ma fita batun ta, saboda haka ya ɗauka tabar wurin ne, saidai yanda yaji idanu na yawo bisa jikin shi, kaman ana kallon shi, ya sanya shi buɗe idanun nashi a hankali, sai kuma ya shiga ɗagowa yana mai wara idanun shi akan Maree ɗin da yaga ta natsu ko numfashi bata sauke wa.

"Ke Meye kike yi haka?" ya faɗa cikin daka mata tsawa.

Cikin firgita da ƴar gigita ta ja baya, sannan ta miƙe tana ƴan kame kame, "Yaya jira nake ka faɗi Abunda za'a kawo maka"

Ɗan zaro mata idanun shi yayi, saboda yasan ƙarya takeyi, cikin sakar mata wata uwar harara yace "Nace ki bar shi ko?"

"To" ta faɗa tana mai wucewa da sauri zuwa inda take goge goge

Da harara ya raka ta, yana mai jan ɗan ƙaramn tsoki, "Village girl" ya faɗa a hankali, daidai lokacin da Nihal ɗin ta iso ɗauke da Mug ɗin Cofee ɗin da yake ta faman tururi.

Amsa yayi yana mai nuna mata gefen inda yake zaune, alamun ta zauna.

Tasan ba zai tanka ba, hakan ne ya sanya ta kai zaune kaɗan cikin ɗan ɗosanawa.

Ajiye Mug ɗin yayi bisa stool, sannan ya jawo wayar shi, yana mai latsa kiran wata number.

Ta ɗaya ɓangaren kuma bugu uku tayi aka ɗaga.

Cikin girmamawa Wancen ɗin ya shiga faɗin "Ranka shi daɗe barka da tashi, ya gida da aiki?"

"Lafiya ƙlau Deen ya naka aiki?" shima Al'ameen ɗin ya faɗa babu yabo ba fallasa.

Zaro idanu Nihal ɗin tayi, cikin kaɗuwa, gaban ta ne ya cigaba da faɗuwa, kadai ace Babyn ta ne Ya Ameen ɗin ya kira?

"Lafiya ƙlau Big Bros"

"Deen bansan me ke faruwa ba, na dai dawo naga Nihal a gida, shine take faɗa mana wai ai kai ne kace ta taho, shine dalilin kiran naka domin in yi comfirming sannan inji dalilin tahowar tata, kada ya kasance ace ba kai ne ka turo ta ɗin ba"

Ya ƙarshe cike da takaici, ta ɓangaren guda yana mai sakar ma Nihal ɗin harara, wadda har tayi narai narau da idanu.

Tasan halin Yayan nasu gabaki ɗaya, wannan shine ƙaramn aikin shi, ita dama bata jin Mom daga shi sai Dad take ji, Tasan ko Mom tayi shiru da maganar su fa ba zasu ƙyale bane.

Gyara zaman shi Deen yayi bisa waiting chair, sannan ya shiga cewa "Eh kwarai kuwa yaya, nine nace ta taho gida, dalili kuwa shine, Nihal babu Abunda ta iya, na dangane da zaman aure, kai ko kaya ta cire anan zata bar su, saidai masu aiki ne zasu yi mata, hatta da ɗaki na sune take sanyawa suna shiga suna gyara mani har toilet, gashi ba wata kyakkyawar alaƙa tsakanin ta dasu, kullum sai zagi da hantara, komi sukayi mata bata godewa, girki wannan ko ruwan zafi ne za'a dafa bata san yanda zata yi shi yayi daɗi ba, saidai ta sanya ƴan aiki, na sallama su, saboda ta samu ta koya, shine take faɗa man ita fa ba zata iya ba, wannan ne dalilin da yasa na ce ta taho gida to, idan ta koya sai ta dawo, saboda Nidai na faɗa mata, ko da nake sonta, ba zan iya haƙurin zama da ita a haka ba, infact ma ace ko hidima ta data kamata ace tayi mani saidai ta sanya ƴan aiki suyi mani, na nema mata makaranta da zata je tayi course na shekara ɗaya, inda duk zata iya waɗannan ayyukan tace mani ita gaskiya ba zata iya zuwa ba, shine ya sanya nace ta thao gida domin asan halin da take ciki, na Ɗauka ma za'a kira ni tin jiya, gashi kuma ni yanzu ina airport, da sai inzo gidan ayi maganar gani gata"

Tin da ya fara magana Ya Ameen & in bai katse shi ba, sai ma sipping cofee ɗin shi da yake tayi a hankali a hankali.

Jin ya kai aya ne, ya sanya shi shima ajiye Mug ɗin, sannan ya maida hankalin shi kan Deen ɗin.

"Is ok Deen kayi tafiyar ka, har zuwa lokacin da ka dawo, ai bamu san Abunda ke faruwa ba, da tun tuni mun ɗauki mataki, kayi haƙuri, Allah kuma ya tsare hanya, kada ka damu, insha Allahu duk waɗannan abubuwan za'ayi ƙoƙarin ganin ta iya ɗin"

Ya faɗa cikin wani irin yanayi na takaicin zuci.

"Shikenan Big Bros, na gode matuƙa Allah ya ƙara girma, don Allah ina gaida su Dad da Mom, a sake basu haƙuri, nasan na ɓata masu"

"ah no non no, ba wata damuwa insha Allahu, Allah ya kiyaye hanya"

Al'ameen ɗin ya faɗa yana cutting kiran.

Duk abunda suke faɗa tana ji, domin a yanda free ya sanya.

Har ta fara matar kwalla, wai yau ita ce Babyn ta yake faɗar haka a kanta, bayan babu ta inda ta gaza dashi, jikin ta da duk Abunda ta mallaka nashi ne, bata yi mashi shamaki duk lokacin da ya buƙata, to ai ita a zaton ta shine kawai zaman auren, in har zata biya mashi buƙatar shi, komai mai sauƙi ne.

"Kinji Abunda ya faɗa ko? NIHAL nasha faɗa maku, wannan sangartakun da Mom keyi maku ba gata bane, kowanne namiji da halin shi, shi ya ma yi haƙurin zama dake kusan shekara har da wani abu, a haka Amman bai taɓa koro ki gida ba, yanzu wa gari ya waya? Mom ita ce zata maki zaman auren? Balle kice ta ɗiba maki masu aiki komi sune zasuyi maki? Deen fa ba yaro bane kaman ki da za'a ce bai mallaki hankalin kanshi ba, saboda haka bana son jin komai a bakin ki, idan zaki gyara ki gyara.

Ya faɗa cike da takaici, kaman baya son maganar, ita kanta muryar tashi a hankali a hankali take fita, duk abun nan da ake Maree na daga cen gefe tana aikin, Amman a zahiri hankalin ta yana kan Ya Ameen ɗin, ta baza kunnuwa tana jin Abunda ake

Miƙewa yayi,hannuwan shi duka zube cikin aljihn shi, ya fara taka wa da niyyar barin sashen.

Sai kuma ya dakata yana mai waiwayowa, ya kalli Nihal ɗin da har ta fara shesshekar kula, ko ba komai tana son mijin ta, Babu bai kyauta mata ba, kuma wallahi ya bayar da ita, ita fa babu wahalar da zata yi saboda zama dashi, idan bai iyawa a haka ya rabu da ita kawai, wasu zasu kawo kansu, tinda Allah ya mallaka masu komai na rayuwa.

Muryar shi ce ta katse mata tunanin da takeyi. "Ke Daga yau bana son sake ganin ki a sashen nan kinzo aiki, ki bari Nihal ce zata dinga yin komai a cikin gidan nan, harda girki ma duka" ya faɗa yana kai juna Maree da hannu.

Ba Nihal ɗin ba da maganar tazo mata kaman saukar aradu, har Maree tasha mamaki.

Aikin gidan nan? Ace Nihal ce zata yi?

Lallai rayuwa mai juyi, wai kwaɗo ma daya faɗa ruwan zafi, cewa yayi "Uhmmm kaima ka cenza hali ne?"

Kuka Nihal ɗin ta fasa, tana mai Miƙewa ta nufi ɗakin ta, take faɗin "Wallahi yaya ba zan iya ba, ni wallahi ba zan iya ba yaya"

Bai jira komai ba ya juya ya idasa ficewa, yana mai cema Maree "Kinji dai na faɗa maki"

Gyaɗa kanta tayi, tana mai ƙyaƙyata dariya, bayan ficewa tashi, ko ba komai zata samu sauƙi, saidai inda abun baiyi mata daɗi ba wuri ɗaya ne, ta yanda ba zata samu damar ganin Ya Ameen ɗin ba a kullum, sannan burin ta na ta samu wani abunda Tasan zai ci ta barbaɗa mashi magani ya ruguje.

A haka itama tabar sashen tana mai ayyana in yasan wata ai bai san wata ba, ko ba komai idan ita an hana ta shiga, ai ga Mama talatun ita ba'a hana ta ba, ko ita zata aiwatar masu da komai.

Cikin matuƙar ɓacin rai ya koma sashen nashi, gara yaje ya dafa ko noodles ce yaci, domin yana jin yunwa, gashi ba zai iya komawa wajen Umman yace ta bashi wani abu ba kuma yaci, kunya yake ji, ko jiya da ya faɗa domin ayi raha ne kawai ya faɗa.

Kafin ya isa ga kitchen ɗin ne, ya latso number ɗinta.

Saida ta kusa katse wa ne yaji ta ɗaga cikin murya mai kama da ta yanzu ta tashi bacci.

Sallama nayi mashi cikin ƴar murya ta, ina mai gaida shi a lokaci ɗaya.

"My Queen bacci ma kike yi kenan? Nine na tada ki?" ya faɗa yana mai idasa shige wa kitchen ɗin.

Ɗan gyaɗa mashi kai nayi a hankali kaman yana gani na, yau bana da lecture ɗin safe, Shiyasa nayi kwanciya ta, ina ji su Khadee suka tattara suka tafi library, duk da suma basa da lecture, Amman cen suke zuwa yin karatu wani lokacin.

"Eh yaya, bana da lecture ɗin safe"

"Naji daɗi, ai hrt beat har na fara tunanin sama maki trnsfer saboda bana so wannan malamin tsohon saurayin ki, yana kalle mani ke"

Ya faɗa cikin ɗan zaulaya, lokaci guda yana mai ɗauraye tukunya cikin sink.

"Uhmm" kawai na iya ce mashi, domin dai ni ya bani mamaki, tin bayan rabuwa ta da Sir Salim ɗin, bai kuma yi mani magana akan shi ba, shima haka Sie Salim ɗin ke nunawa kaman babu wata alaƙa da ta taɓa shiga tsakani na dashi.

"Yes dear kada kiyi mamaki, kinsan ina matuƙar kishin ki gaskiya, idan so samu na mane, ya kasance makarantar nan babu namiji ko ɗaya"

Cikin mamakin shi na ɗan zaro idanu na waje, yanzu shi har ya iya yayi mani irin wannan kishin? Duka ma yaushe ne aka fara soyayyar da har za'a e irin wannan kishin ya fara shiga?

Katse mani tunani yayi da cewa "My Suhan gani zan dafa indomie, kinsan ban iya ba, shine na kira ki ki faɗa mani yanda zanyi tayi daɗi, su Mom basa nan sun tafi kankiya" ya faɗa yana mai ɗan ƙumahe dariya.

Nima dariyar nayi, kaman na taɓa ji fa Afnan tace man ya iya girki, to Amman ya na iya tinda yanzu yace mani bai iya ba?

A hankali na shiga kwatanta mashi yanda zaiyi, sai kuma Naji ya kashe wayar, cen sai ga kiran video ya shigo, ooh ni ƴasu, shi dai ya yarda da video call, ko me yake ji idan yana kallo na? Gashi ni kuma ko fuska ban wanke ba, a hankali na sauka kan gadn ina mai jawi niƙab ɗina na ɗaura sannan na amsa kiran.

Cikin ɗan zaro ido shima yake faɗin "Ne zan gani haka? Wa kike ɓoye ma fuska? Abeg ki cire shi tin muna mu biyu" ya daɗa yana mai ɗan haɗe idanu sama da ƙasa, saboda in gane yaji haushi.

"Yaya dama a haka nayi bacci"

Na faɗa a hankali, saida ya kauda fuskar wayar yayi dariya kaɗan, sannan ya maido fuskar tashi yana faɗin.

"Idan ba zaki cire ba, sai in kashe waya ta, ba kuma zan sake kira ba, har sai na dawo"

A hankali na zare niƙab ɗin, ina mai faɗin "yaya tafiya zaka yi ne?"

"Eh dear, wani ɗan aiki ne ya taso mani, Amman kar ki damu kwana biyu kawai zanyi in dawo, nima bana so ina nisa dake, nafi so har sai an ɗaura mana aure sannan, kinga yanzu da kina kusa ba sai na shiga kitchen ba" ya faɗa yana mai ajiye wayar gefe sai tin inda zan dinga kallon shi, ya shiga juye indomie ɗin, sannan ya ɗauko kwai guda biyu ya shiga kaɗawa.

Nidai kallon shi kawai nakeyi cikin wani yanayi, ya saki jiki dani sosai kaman ba shi ba, kuma duk Abunda yakeyi cikin kwarewa yakeyi, gashi dai komai a nutse aka yin shi, kitchen yake Amman kaman yana cikin ɗaki, saboda tsafta da kyaun kitchen ɗin.

Har ya gama yana ɗan hana da fira haka jefi jefi.

Sai kuma ya kinkimi wayar da abincin ya nufi bisa dining, acen muka cigaba da fira haka a hankali a hankali yana zaulaya ta wai tayi daɗi nazo ya bani a baki..

******


Kaduna suka sauka, don haka driver ya kwashe su sai Katsinan Dikko ɗaki kara, kunya garemu ba dai tsoro ba.

Kowa part ɗinshi ya wuce, tin cikin jirgi tsakanin Hajiya Kubran da Hajiya Zianab ɗin saidai sama sama, KO alhaji Auwalu tin da ta gaida shi bata sake tanka mashi ba, Alhaji Mustapha yana kula da ita, saidai kawai ya girgiza kai.

To itama Hajiya Zainab ɗin wannan karon ɗaurewar tayi, ta kula lallaɓa ta da akeyi ne ya sanya take ganin kaman biyayya gareta dole ne, ko kuma tana ganin zata iya taka su a duk lokacin da taga dama ta wuce, ta shirya nuna mata ba fa haka abun yake ba, kawai wani lokaci Albarkaci mijin nata mutumen kirki take ci, tinda bata neman komai a wurin ta, ai tana ganin ba dole bane ace sai ta mu'amalance ta.

Kafin suje an shirya masu abinci mai rai da lafiya, kowa sashen shi aka kai mashi, duk da Hajiya Kubra har yanzu akwai abubuwa cunkushe a cikin ranta, tin da aka faɗa mata tafiyar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login