Showing 189001 words to 192000 words out of 247770 words
akayi ba kenan? Me hakan yake nufi?
Salla nayi sannan na ɗan ci indomie ɗin da raihana ta dafa mana.
Sake kwanciya nayi, duk jikina ba daɗi, duk da zazzaɓn ya sakeni, sai ɗan ciwon kai dake damuna haka kaɗan.
Ƙarar shigowar text ne a waya ta, ya sanya ni ɗan firgita daga duniyar tunanin da na shiga, magangann Umma ne ke ta kai komo cikin ƙwaƙwalwata, kenan da gaske Ya Ameen yake, Soyayya ni dashi? Aure nan da wata ɗaya?to ta ina ma za'a fara ne?
A hankali na jawo wayar ina mai duba saƙon da ya shigo mani.
Kaman yanda number ɗin take special, haka ta zauna das a cikin ƙwaƙwalwa ta.
Da kallo na shiga bin rubutun.
_"My Moonlight fatan kina lafiya? Yanda zuciya ta ta yini tinanin ki, nasan kema ta ɓangaren ki hakan ne, Dont worry, insha Allahu gobe akwai special outing, kiyi mani kwalliya sosai, see u tumorrow. Bye take care with full of my love"_
Na maimaita karantawa bansan ko sau nawa ba, shi dai ne ya turo mani.
"Hmmmm" na nisa ina mai miƙewa tsaye na fice balcony ɗin ɗakin namu.
Ɗan sanyi sanyin iskar bayan magariba ne ya shiga busowa yana shiga jikina a hankali a hankali.
Wayar na a hannu na, na rungume duka hannuwan, sama nake kallo, taurari har sun soma bayyana, ga haske wata tar dake haske mani fuska.
"My Moon Light"
Sunnan da ya kira ni dashi ne ya shiga amsa kuwwa a kunnen nawa.
Da kallo na sake bin watan dake maƙale a sararin subhanan.
Haske ne mai kyau, mai ban sha'awa, baya kashe ido, sannan zuciya na aminta da kallon shi, ba tare da ta gaza ba.
Kenan hakan yake nufi a kaina?
Kenan ni haskn zuciyar shi ce, kwatankwacin yanda ya faɗa ɗin, kwatankwacin yanda nake kallo a yanzu ɗin.
Bansan lokacin da na saki ƴar siririyar dariya ba, har haƙirana suna bayyana.
Runtse idanu na nayi, Meyasa lokacin da Sir Salim yace mani anje neman auren nawa na dinga jinbfaɗuwar gaba? Amman yanzu Ya Ameen ya shaida mani da ranar shi a kaina, sai kuma bana jin komai sai ma wani feeling da bazan iya kwatanta shi ba?.
A hankali na kai zaune bisa wani ɗan dankali da akayi ma student na zama, ina mai ɗora duka ƙafafu na duka na rungumo su da hannu, ina mai jingina kaina jikin bango na runtse duka idanun nawa.
Fuskar shi ce ta fara kai komo a cikin idanun nawa.
Kyakkyawa ne sosai.
Zuciyata ta shiga raya mani.
Idanun shi masu matuƙar kyau, sune nake gani suna yawo a bisa tawa fuskar.
Kaman fa yana jin bacci, kaman wanda yake ma mutum kallon soyayya, to ai shi dama tinda na sanshi haka idanun nashi suke.
A hankali na buɗe idanun nawa, ina mai tashi jiki a sanyaye na shige Ɗakin namu.
*********
Bansan yanda akayi ba, washegari kuma sai na ganni ina mai tsara wanka, sa'a ta ɗaya bana da lecture a ranar.
Saidai su Khadee suka tafi suka barni ni kaɗai a ɗakin.
Su kansu saida suka tambaye ni wai sunga ina cikin walwala, dariya kawai nayi masu nace "Kaman zanyi baƙi ne yau daga gida"
Khadee na jin haka ta fice, raihanan ce tayi murna, tana mai cewa "agaida shi idan yazo, Allah yasa mu dawo mu tadda shi."
Da "Ameen" na bita ina mai shigwa toilet ɗin.
********
Tin safe ya shirya sosai, Office ya wuce bayan ya shiga sashen Dad ɗin gaida shi, acen ya tada Mom ɗin tashi, Baisan dalilin faɗuwar gaban nashi ba.
Gaidata yake yi, Amman daƙyal ta amsa tana mai jifan shi da wani irin mugun kallo, shima don Alhaji Mustapha ɗin yana wurin ne.
A haka ya fito jiki a sanyaye.
Saida ya shiga sashen Umma, itama a falo ya tadda ta, cikin matuƙar ladabi ya gaishe ta, abun har yaso bata kunya, duk da yanzu yaro yake a wurin ta, Amman dole ta wani fannin yayi mata kallon suruka.
Saida ya shaida mata zai je wajen Suhan idan tanada saƙo.
Cewa kawai tayi ya gaida ta da jiki, saboda jiya tace mata bata jin daɗi, taso ta kira, kuma sai tayi ta neman wayar ta taƙi shiga.
Da mamaki sosai ya fito daga part ɗin Umman, ashe bata lafiya, shine kuma bata iya kiran shi ta sanar mashi.
Yana jin masu aiki na ta faman gaida shi, saidai ya ɗaga masu hannu, haka ya isa office ɗin cikin ƴar damuwa, ga damuwn kallon da yaga Umma nayi mashi, gudun shi ace kada Dad dai yaje mata da zancen ne. Sai kuma da uwar rashin lafiyar Suhan ɗin, duk shirin da yayi kada fa ace ya tashi a banza kenan, to ba lafiya ina Kaga magana.
A office ɗin ya tadda Bilal har ya iso, cikin shirin shi yake na barin ƙasar, suit ce jikin shi baƙa da ƴar ciki Light blue sosai, sai tight dark blue, Bilal ɗin yayi kyau sosai, gashi dama ɗan gayu mai ji da ilimi da wayewa sosai.
A gaggauce Al'ameen ɗin ya fitar da komai ya haɗa mashi cikin brief Case ɗin, sannan ya ɗauke shi zuwa Airport. Bai sanar dashi komai ba, dama kuma shi mutum ne mai matuƙar zurfin ciki.
Bai jira tashin su Bilal ɗin ba ya baro shi cen, kai tsaye hanyar zariyan ya ɗauka cikin matuƙar gudu. Ko ba komai hankalin shi ya karkata kuma wajen ganin ya isa ya duba yanayin jikin nata.
********
A guje motar ta shigo gidan, dama kaman zata ɓalle murfin gate ɗin take ji, yanda take ta danna horn ya sanya mai gadi gane cewa ba lafiya.
A gaggauce ya wangake mata ƙofar gate ɗin, tinda ya ga Nihal ce gaban shi ke dukan tara tara, ko ba komai ya san zai sha zagi yau.
Saidai ga mamakin shi, ko parking daidai bata gama ba, ta ɓalle marfin motar ta shige cikin gidan cikin kuka, ko marfin motar bata tsaya kullewa ba.
Ga gudun ta ta shige sashen Mom ɗin tata.
Mom dake ɗaki tana shafa hoda a kan fuskar tata, ita har gobe fa bata yarda ba, jinta takeyi zam, ko ƴar 30 ba zata nuna mata ƙuruciya ba.
Jin an banko ƙofar ɗakin nata ne, ya sanya ta miƙewa cikin hanzari tana mai fuskantar ƙofar.
"Nihal?"
Ta faɗa cikin matuƙar tashin hankali, yana mai sakin hodar dake hannun ta, ta tarwatse a ƙasa, cikin tashin hankali ya kamo ɗiyar tata ta rungume.
"Nihal Is Ok... Ki faɗa mani me ke faruwa ne? Ya akayi ne? Me ya sa yaki kuka?"
Duk a lokaci guda ta ke tambayar ɗiyar tata.
Wani kukan ta sake rushewa dashi.
A hankali ta shiga janta zuwa bisa gadon.
"Nihal i said is Ok"
Ta sake faɗa cikin wani tashin hankali.
"Faɗa mani mai ke faruwa?"
"Mom ba baby bane...."
"baby what? Faɗa man me babyn yayi maki?"
"Mom cewa fa yayi wai in taho gida sai na koyi girki da wanke wanke da shara da mopping" ta faɗa tana mai sake sakin kuka, da gani dai abun na mata zafi cikin zuciya.
Aiko cikin ƙaunar zuciya Mom ɗin ke faɗin "Shi baby ɗinne yace ki taho gidan ku?"
Girgiza mata kai ta shiga yi.
"To ina house maid ɗinda na kai maki guda biyu?"
"Mom duk fa yace su tafi gidan su, tinda ban gode ma Abunda suke yi mani, kuma fa mom basa da tarbiyya ne, basa jin magana, kuma sun cika ƙazanta, gashi basu iya abinci ba, kullum indai yana ƙasar yaci sai yayi mani complain"
"ya kore su? Shi ya ɗauke su? Ko shi ke biyan su albashi ne? Dama irin zaman da kike yi kenan a gidan? Shine dan ubanki baki taɓa faɗa mani ba saida ya koro man ke?"
Ta faɗa kaman zata doke ta, sai kuma ta jawo wayar ta, tana mai miƙewa tsaye ta shiga tattakawa. Wayar Alhaji Mustapha ɗin ta kira.
Bayan ya ɗauka ne ta shiga zayyana mashi Abunda ya faru, cikin masifa take magana, kaman ita ace an koro mata yarinya daga gidan aure? Wannan abun kunya har ina? Kuma ma wai don wulaƙanci yace tazo wani ta koyi aikin gida? Duk irin gatan da take nuna ma yaran nata? Basu taɓa samun wani abu suka rasa ba? Ga issue ɗin Al'ameen da take ta so taci mai garin su?
"Ai yayi kyau, sai tazo ta zauna ta koya" Abunda Alhaji Mustapha ɗin ya faɗa kenan yana mai kashe wayar.
Da kallo ta shiga bin wayar, kaman ya tazo ta zauna ta koya?
Kaji wani zance, cikin harara take bin Nihal ɗin da kallo.
"Tashi ki tafi ɗakin ki, kafin Dad ɗinku ya dawo"
Ba zaɓi illa miƙewar, a haka ta sauka zuwa falo tana mai sakin wani kukan.
Aunty Feena na zaune, itama cikin tashin hankali ta shig bin ƙanwar tata da kallo.
"Ke Nihal zo nan, me ya faru?"
Ƙarasawa tayi wurin ta, tana mai share kwalla.
"Aunty Feena baby ne yace wai in taho gida, sai na iya wanke wanke da shara da girki sannan in koma"
Da mamaki Feenar ke binta da kallo.
"Shi bby ɗin? To duk ina soyayyar?"
Jin Abunda Aunty Feenar ta faɗa ne ya sanya ta wucewa kai tsaye, tana mai sake sakin wani kukan.
Cikin girgiza kai Aunty Feenar ke cewa "Nasan za'a rina, ai ba kowanne namiji bane zai iya da halin Nihal da saudat ba, Allah shi kyauta" itama tashi tayi ta fice daga part ɗin baki ɗaya ma, ta nufi garden.
Cikin tsabar masifa, ta shiga kiran Al'ameen ɗin.
Saida gabanshi ya faɗi ganin kiran nata.
Da bismilla ɗauke a bakin shi ya amsa kiran, ya san sauran zancen, ya san Abunda ka iya faruwa, tinda yaga kallon da takeyi mashi da safe gaban shi ya dinga faɗuwa, ko ba komai ya san mai raba shi da ita yau a gidan saidai Allah.
Cen ya tsinkayo muryar ta tana faɗin.
"Duk abinda kake yi ka baro shi, kazo yanzu maza maza ina son ganin ka"
Ta faɗa cike da gadara cikin masifa.
"Mom nayi tafiya zuwa Kano, wani abu ya taso mani na gaugawa, Amman insha Allahu dana kammala zan juyo"
Ya faɗa cikin son ɓoye gaskiyar inda yake nufa.
Ba tace mashi komai ba ta datse kiran.
Gabanshi ne ya cigaba da faɗuwa, ko ba komai ya san kwanan zancen.
Abu ɗaya zaiyi ya tsira daga masifar Mom ɗin tashi yau, tunkwa da Abunda zaiyi ne ya sanya shi sakin ajiyar zuciya yana mai maida hankalin shi kan tuƙin da yakeyi.
********
To wai kwalliyar ma me nakeyi?
Na tambayi kaina, ina mai zirara kalli a idanun nawa.
A hankali na ajiye, ina mai tattara kayan shafar na maida su muhalln su.
Kayan dake jikina na shiga bi da kallo.
Material ne mai masifar kyau, Hafsat ce ta siya man shi, tin lokacin bikin su, yana daga cikin kayan data ɗinka mani, sau ɗaya na taɓa gwada kayan na cire, saboda sai nake ganin kaman ya kama ni sosai a lokacin, gara ma yanzu, tinda ƴar wahalar karatu ya sanya na ɗan rame, kai kayan sukayi mani kaf da kaf, kaman an gwada su a jikina.
Gashin kaina a tsefe yake, hakan ya sanya na ɗauke shi da ribom mai faɗi na tuttura shi ciki.
Ɗaurin ɗan kwalin ma ban tsaya mashi kyanare ba, ɗaura wa kawai nayi bisa tulin gashin da yake kumshe a bayan ƙeyar tawa.
Ga mamaki na kuma sai naga yayi masifar kyau, kaman in saka hijabi, kuma sai na jawo gyale da yayi matching da gyalen na yafa.
Ba babban madubi sosai a ɗakin, hakan ya sanya bana ganin kaina sosai, Amman ni kaina nasan nayi kyau, ga wani murmushi da nake yawan saki, don dai ƴar faɗuwar gaba da nake ɗan yi akai akai.
Ƙarar wayar tawa ne ya sanya ni juyawa inda take bisa gado na ɗauko.
YA Ameen ne.
Ga ana ne ya sake faɗuwa.
A hankali na ɗaga ina mai furta mashi sallama.
Amsa mani yayi yana mai faɗin, "Gani a inda muka haɗu shekaranjiya"
"To" kawai na iya furta wa, ina mai katse wayar.
Sai kuma na samu kaina da fesa turaruka har kala uku, tini jikin nawa ya ɗauki sassanyan ƙamshi, ni kaina ina jin kaina adaban ayau, saidai dole ne in daure, ba wanda dama cen ya kamata yake ganin kwalliyar tawa illa mijin da zan aura.
Saida na ɗauki wayata na cusa ta cikin wata ƴar hand force mai kyau, sannan na rufe ɗakin.
A hankali na kulle ɗakin, sannan na shiga taka wa kaman wanda ke jin tausayn ƙasa.
Tin da na sha kwanar gabana ke faɗuwa.
Cem nesa dani sosai na hango shi. Tsaye yake jingine jikin wata ƴar dunƙulalliyar mota, ƙirar royce-royce 2018.
Sanye yake cikin kayan turawa yayi masifar kyau, ƙafar shi Sanye da wasu irin arnan tomps na zallar fatar maciji mai roɗi roɗin ash da baƙi, sai baƙin wando jins dake jikin shi, da ash ɗin riga mai ɗan duhu da baƙin rubutu jikin ta. Haka idanun shi Sanye cikin baƙin glass ba abunda kake hange a cikin su.
A haka na shiga taka wa har jikin motar.
Turaren dake jikin mu, shine ya fara mana sallama a hanci.
A hankali ya zare glass ɗin idanun shi, cikin wani salo ya kuma sakin ɗan murmushi iya keɓo yake cewa "You welcome my Heart beat"
Da ɗan kallo haka nake binshi, duk kunya ta baibayeni, wai ni ba zai iya kirana ne da suna ɗaya ba? Kullum da wanda zai kirani dashi.?
Ban ɗauka mota zamu shiga ba, sai gani nayi ya zagaya ya buɗe mani murfin gaba yana mai faɗin "Gate in dear"
Banyi musu ba, zagaya wa nayi na shiga, saidai kaf hankalina baya jikina, student fa nata kallon mu.
Saidai naga shi kaman ma bai damu ba, shima zagaya wa yayi ya shiga, yana mai yima motar key yayi ribos ya juya yana mai ficewa a makarantar.
Lumshe idanu nayi, sanyin motar da ƙamshin shi na rasa ni a hankali
Samun kaina nayi da cewa "Yaya Ina yini? Ya hanya?"
Mun ɗauki hanya, bai juyo ya kalle ni ba, sai gani nayi ya kawo hannu da niyyar murɗe mani baki.
A hankali na sanya hannu na, ina mai sauke nashi ƙasa "Am sorry" na faɗa cen ƙasn maƙoshi.
Shima ɗan murmushi ta saki, "Kin faye tsoro fa my ƙanwa"
Kaina na sauke ƙasa, ina. Ai sauke ƴar ɓoyayyar ajiyar zuciya, ganin mun doshi hanyar barin garin ma kwata kwata.
Da mamaki nake kallon shi, shima kallon nawa yayi, wanda saida ya jaza man faɗuwar gaba, idanun nashi na rikita ni, aduk lokacin da suka sarƙe da nawa.
"Mamaki kike yi ko? To sai doki zanyi"
Ya faɗa cikin dakewa, kaman ba wasa yake yi ba, hakan ne ya sanya ni sakin ƴar dariya mai sauti.
"Kin ce ma Umma bakya lafiya, sai gashi ni banga haka ba"
Ya faɗa yana mai juyowa ya kalle i sosai.
"Jiya ne nayi zazzaɓi, Amman na warke, nasha magani an mani allura"
Nima na faɗa cikin wata irin dakiya.
Gyaɗa kanshi yayi, yan mai maida hankalin shi kan tuƙin da yake yi.
Mu yo tafiya mai nisa, yayin da shiru ya ziyarci motar, sai ƙira'a da ya sanya tana tashi a hankali, har bansan lokacin da na jingina kaina da makarin kujerar ba ina mai bin karatun a hankali a hankali.
Shima ta gefen ido yake daɗa kallo na, na masifar burge shi, bansan yanda akayi ba, sai gani nayi munyi parking.
"Muje ko?" ya faɗa mani, yana mai sanya hannu ya buɗe man murfin motar ta ciki.
Hakan ya sanya hannun shi shafar jikin nawa, tsikar jikina ce ta tashi, ba Arziƙi nayi saurin ficewa ina rufo ƙofar.
Shima fita yayi yana mai rufe ƙofar.
"Wow masha Allah" Abunda na faɗa kenan a cikin zuciya ta, wurin ya matuƙar ƙawata ni, ciyawa ta fito tayi shar kaman grass carfet, sai korayen flowers da ja, masu matuƙar kyau da ƙamshi, wurin akwai ni'ima sosai, daga gefe wani ɗan rafi ne cike da ruwa, bado da kainuwa sun fito su yi fafut, harda wata farar flower mai adon yellow a jikin ta.
"Here we can go"
Ya faɗa yana mai juna mani cen gefe ƙarƙashin wasu irin flowers masu tsawo, suna zubo da wasu irin ƴan ƙananan flawowi.
Kujeru ne guda biyu, irin na gida wanda akayi da zallar cement da duwatsu.
A baya na shiga binshi har muka isa inda suke.
Shine ya nuna mani inda zan zauna, Nifa kaina ya kulle, na mamaki nake bi shi da kallo.
A zamanin nan da babu tsaro, shine zamu zo wurin nan mu kaɗai mu zauna? Duk da dai wurin yana da matuƙar kyau, kaman wurin shaƙatawa yake.
Saida na zauna sannan shima ya zauna, yana mai faɗin "Huhhh Finaly gani ga Madam ɗita"
Sauke kaina nayi ƙasa, wata irin kunya ce ta kama ni.
"Kinyi matuƙar kyau my Suhan, kaman muyi ta zama a haka nake ji"
Ya faɗa cikin wani yanayi na sauƙi da dakewa.
"Uhmmm" Abunda na iya cewa kenan ina mai wasa da yatsun hannuwan nawa.
"Ki saki jikin ki Suhan, babu Abunda zanyi maki, kawai dai ina so mu saba ne, nan da wata ɗaya ne"
Ya faɗa sosai cikin son haɗa ido dani.
A hankali na ɗago idanun na ina mai kallon shi. Sai kuma yaga ina ɗan waiwayawa alamun a tsorace nake.
Baice komai ba, naga ya jawo wayar shi, bansan me yake yi ba sai naga yana magana, kaman video call yake yi.
Sai kuma ya nuni mani fuskar wayar.
Wasu mutane nagani tsaitsaye riƙe da bindigogi,alamun masu tsaron lafiyar mu ne.
To yaushe suka zo nan?
"kada ki