Showing 186001 words to 189000 words out of 247770 words
bace wadda ta birkice mani jiya, duk da dai naga suna magana da Raihana da safe, saidai bansan abunda suke tattauna wa ba, tinda baus sako ni ba.
Ganin ta da yaye dani ne, ya sanya ni nima share wa, nayi mata ta ƴan duniya.
Karatun namu da ya ɗauko zafi, muna ƙoƙarin cenza aji ne zuwa aji uku, saboda haka komai yake neman dagule mani, ga wannan issue ɗin da ya taso.
Hakan ne ya sanya ni bama kaina shawara, zan ajiye komai in fuskanci karatu na, duk Abunda Allah yayi mai kyau ne, Sir Salim kuma na rungumi ƙaddarar rabuwa dashi, biyayya ga iyaye na dole ce, balle ga Umma wadda tasha matuƙar wahala a kaina.
Duk da ayau ɗinnan, dole ne in kira ta, domin inji haƙiƙanin zance, ti da ita dai har yanzu bata kirani tace mani komai ba.
Shi kuma Ya Ameen zan zuba idanu inga iya gudun ruwan shi, kwana uku rak ya ɗauka ma kanshi wai zai sanya ni in so shi, hmm kaji fa kaman a tatsuniya.
Tattara shi nayi na share shi baki ɗaya, har na fito lecture, nazo nayi wanka na zauna karatu.
A haka ne zuciya ta ta shiga saƙa mani in kira Umman, in ban kira ta ba, tunani ma kawai ba zai barni inyi wani karatun kirki ba.
Duk da duk inda na nufa yau sai inji ana magana ta data Ya Ameen ɗin, ko kuma inga ana nuna ni da hannu, sai abun ya ɗan tsaya mani arai, ni da yabi ta shawara ta ma da bai iske ni makarantar ba, kaman yanda kowa ya san alaƙa ta da Sir Salim.
Bugu uku nayi ta ɗauka cikin sallama mai cike da natsuwa, umman tawa ba dai dattako ba, komai take yin shi cikin natsuwa ne, duk da nima na biyo halin ta, amman sai nake ganin kaman ma ban kai ta ba, tinda nesa ba kusa ba, ta fini kauda kai a al'amurran yau da kullum.
Cikin ladabi na gaida ta, tambaya ta ta shiga yi karatu ina mai bata amsa.
Cen kuma sai nayi shiru, ban kuma katse kiran ba.
Hakan ne ya sanya ta ɗan murmusawa, ita ta haifeni don haka ko gyaran murya nayi tasan abunda nake nufi.
Ɗan gyaran murya tayi tana mai faɗin "Mamana ina fata dai lafiya ko?"
Muskutawa nayi bisa ƴar daddumar ɗana shimfiɗa ƙasa, da yake ɗakin ba kowa sai ni kaɗai, hakan ya bani damar sakin jikin yin wayar.
"Umma maganar Malam Salim ce, yazo ya same ni da maganar wai an dakatar dashi ga nema na, kuma yana faɗa man wai shi ya riga ma ya janye, kun zaɓa mani wani. Sai kuma ga Ya Ameen ya kuma zuwa mani da wata maganar jiya Umma, shine na kira ki inji Abunda yake faruwa" na ƙarshe cikin ƴar jin kunya, duk da bata gabana.
Ɗan jim tayi, sai kuma ta sake murmusawa.
"Hakane Mamana, saidai ina fatan zakiyi mana haƙuri, mun yanke hukunci akan kanmu, ba tare da jin ta bakinki ba, nasan ke ɗin mai biyayya ce, ko da Alhaji yazo mani da maganar ba zan iya musawa ba kaman yanda kema nasan ba zaki ƙi yaron nashi ba"
"Hum" nace sai kuma na cigaba da cewa
"Umma Hajiya Babba fa, ni ina jin tsoro, bata son mu fa Umma ta yaya zan auri ɗanɗanta?" na faɗa cikin wani yanayi, wani miki mai ciwo na taso mani daga ƙasan rai, abubuwan da Hajiya Kubra tayi mana tin tasowa ta ne ya shiga ɗgao mani.
"Ba ruwan ki da Mamana, kedai biyayya ce taki, kiyi mata biyayya, insha Allahu watarana zata soki, bana iya watsa ma Alhaji ƙasa ne a ido Shiyasa kawai na amsa mashi, yaron na ƙaunar ki, tinda shine ma yaje ma Alhaji da maganar, kuma koda ya shigo cin abincin rana ya sake tuntuɓa ta da maganar sun tsaida ranar *Auren naku* nan da wata ɗaya mai kamawa, saboda haka sai kinsan irin shirye shiryen da zakiyi. Mamana ki toshe kunnuwa ki, wannan auren ni nasan zai zo da ƙalubale da yawan gaske, sai mun daure gabaki ɗayanmu, sauƙi ta ma shi Alhajin yace mubar komai a hannun shi, kada mu sanya tunanin komai a ranmu, insha Allahu babu Abunda zai faru. Saboda haka ni dai a kullum addu'a itace tawa a gare ku, ina maku fatan alkhairi, Allah kuma ya kaɗe duk wata fitina da ka iya tasowa a cikin al'amarin"
Cikin wata irin masifar faɗuwar gaba nake sauraren ta, sautin dukan da gaban nawa keyi ma, ya ci ace umman tawa ta jiyo daga cikin wayar, tuni wata irin zufa ta shiga karyo mani, sai kuma wani irin sanyi ya kama ni, bansan lokacin da jikina ya fara kyarma ba.
Sanya biki?
Ni da Ya AAmeen???
Wane irin aure ne haka gagab ya zo mani ni Suhana?
"Hello Mamana, kina jina kuwa?"
Umman tawa ta sake faɗa.
Cikin rawar murya na shiga ce mata
"Eh Umma ina ji, bana lafiya ne Umma, zan sha magani. Amman Umma don Allah ku duba wannan al'amarin, ina jin tsoro, Ya Ameen ya wuce da ajina Umma, ni ba tsarr auren shi bace na sani, kaman yanda Hajiya Babba ke faɗi Umma"
Na ƙarshe cikin wani yanayi.
"subhanallah, to maza kisha magani Mamana, insha Allahu babu wani abu da zai faru, ki kwantar da hankalin ki, Muhammadu yaro ne nutsattse ba zai bari wani abu ya faru dake ba, nasan zai ƙoƙarin fahimtar da mahaifiyar shi, kiyi mana biyayya Mamana, zan kuma kiran ki anjima inji yanda jikin yake"
Ta faɗa cikin son ƙarfafa mani guiwa.
"To Umma sai anjima"
Na faɗa in amai katse wayar, sannan na zame na kwanta a wurin ko fillow babu.
Wani irin sanyi ne ke rasa ni, bansan irin yanayn da nake ciki ba.
Aure ni da Ya Ameen???
Kaman wasa.
Kuma shine ya yarda da kanshi?
Zan iya cewa Ina da sa'a a rayuwa ta wani fannin, nasan samun Ya Ameen a rayuwa ta ba ƙaramin gata ne Allah yayi mani ba, kuma duk wata ɗita mace zata so ace ita ce a matsayin da nake kai, to saidai al'amarin na tafe da abubuwa masu ruɗarwa masu rikitarwa, sannan ina tunanin tashin hankalin da zai iya biyowa baya.
Tin da cen da bai ce yana son a ba ma, munga tasku balle yanzu da zan zama surukar ta?mata ga yaron da tafi so a duk cikin rayuwar ta?
Haka su Raihana suka dawo suka same ni, kwance ringis masassara jikina, siada suka taimaka suka kaini clinic aka bani magunguna da allurai, sana na samu bacci ya ɗaukeni.
********
"Friend kasan kuwa mai kake faɗa? Aure a cikin wata guda? Yaushe ma kuka fuskanci juna kai da ita? Ya zaka yi da Mom?"
Bilal ɗin da yake zaune bisa kujerar falon ya Ameen ɗin ya faɗa.
Tin bayan da abokin nashi yake sanar dashi batun auren nashi mamaki ya cika shi.
Cup ɗin dake hannun shi cike da lemon champaign ya kurɓa sannan ya ajiye bisa stool ɗin dake kusa dashi.
"Kaga Friend, ni ba dalilin da yasa na kira ka ba kenan, shawara zaka bani, yanda hidimar nan zata tafi, kaga dai yanda abubuwan suke, kuma Mom har yanzu da nake maka maganar nan bata sani ba, Amman Dad yace in bar shi da ita, shine zai sanar dani yanda sukayi. So forget about that matter. Ina so ne a tsara mani biki fiye da tunanin kowa, ina jin ƙaunar Suhan har cikin raina, Shiyasa nake so komai nata ya kasance daban ne a rayuwa"
Da mamaki Bilal ɗin ke kallon abokin nashi, lallai soyayya gaskiya ce, watau ita makantar da mutum takeyi gabaki ɗaya, ta sanya ya mance da wani abu wai shi kunya ko?
Dariya ya ƙyalƙyale da ita, yana mai dukan hannun kujerar da hannun shi.
Ko kallon inda yake Ya Ameen ɗin baiyi ba, ya cigaba da katse latsen shi a waya.
Saida yayi mai isar shi, sana ya tsagaita, yana mai ɗan zamiwa daga bisa kujerar yake faɗin.
"Watau Friend Abunda yake bani mamaki shine, ka manta wata ranar bida Ummi muna......"
"Close that chafter guy"
Ya katse Bilal ɗin,lura da yayi iskanci yake so yayi mashi.
"OK, OK" Bilal ɗin ya faɗa yana mai sake yin dariyar.
Ya san halin mutumen nashi da ƴal banzr zuciya, yanzu za'aji kansu, abun arziƙi ya kona na tsiya.
"To friend yanzu ya ake ciki? Me kake so ayi?"
Bilal ɗin ya faɗa yana mai daidaita kanshi ga barin dariyar.
"Sai wani lokaci kuma" Ya Ameen & in ya faɗa yana mai tashi tsaye.
Kai tsaye hanyar fita ya nufa, hakan ya tabbatar ma da Bilal ɗin haushi yaji kenan.
Shima miƙewa yayi, yana mai faɗin "Zakaci ubanka ne friend, indai soyayya ce bakaga komai ba ma," a hankali yake maganar.
Sannan ya shiga bin bayan Ya Ameen ɗin.
Har suka shiga mota bai ko ƙara kallon Bilal ɗin ba.
Saida suk bar gidan ne Bilal ya juyo ya kalle shi yana mai faɗin
"To ina zaka kaini kuma?"
Ɗan ɗaga ka faɗa yayi kaɗan," ina ce kai ka biyo ni? Baka san inda zani ba ka biyo ni?"
Shima ya faɗa cikin dakewa.
"Sorry Friend, am sorry Ameen, ni fa dariya kawai ka bani, gani nake kaman ba kai bane ka zauce akan soyayya, cikin lokaci ƙanƙani, Amman komai ya wuce, yanzu ka faɗa man yanda kake so ayi"
Bai kula shi ba, har suka isa wani katafaren plaza mai matuƙar kyau da tsaruwa.
Da mamaki yake kallon abokin nashi, duk da baisan dalilin su ba na zuwa nan ɗin, hakanan ya shiga bin bayan shi har zuwa ɓangaren da yake na turarurruka masu kyau.
Ɗauka ya fara yi yana duddubawa.
Guda uku ya ɗauka masu masifar tashin ƙamshi da tsada.
Sannan ya nufi ɓangaren gold.
Banguls, zobuna sarƙoƙi masu kyau.
Saida ya gama duddubawa sannan ya zaɓi wadda yake so a bashi.
Set ne na sarƙa da ɗan kunne, sai zobe da awarwaro guda uku manya ƙirar Dubai.
Sunyi masifar kyau sai ɗaukar idanu suke yi.
Haka aka sanya mashi cikin wata farar cover mai kyau da ɗishe ɗishen pink.
Shi dai Bilal sai bin shi takeyi kaman zariya, har yanzu kuma yaƙi ko kallon shi. Saidai yana yin da yake ciki ya nuna mashi abokin nashi yayi nisa baya jin kira, watau irin kyautar nan ce ta masoya za'a fara tin yanzu.
Wuuu, wani abun sai Al'ameen Dambulan, komai nashi cikin aji yake yin shi, hatta da siyayyar komai mai aji yake zaɓa, classic one.
Haka ya nufo mota, Bilal ɗin nata bin shi a baya.
Kai tsaye Office ya nufa, yana buƙatar kiran Abie, ɗazu yaga kiran nashi lokacin yana part ɗin Dad suna tattauna wa.
Saida ya sanya gift ɗin nashi cikin cupboard sannan ya koma bisa kujerar tashi yayi kira, yayin da Bilal ya kwanta bisa sofar Office ɗin.
Abie ɗinne ya ɗaga ta cen ɓangaren yana mai gaida yayan nashi, saida suka gama gaisa wa sannan Abie ɗin ke sanar dashi dalilin kiran.
Shi dai Bilal na kwance yana jin su, idanun shi a lumshe suke. Har saida Al'ameen ɗin ya gama wayar sannan ya tashi zaune yana mai fuskantar shi.
Shima Al'ameen ɗin shi yake fuskanta, fuskar tashi ba yabo ba fallasa yake sauke wata irin ƴar ƙaramar ajiyar zuciya.
"Friend saidai fa ina jin kai ne zaka je, domin Abie ya sanar dani zuwa jibi za'a zauna Meeting akan kamfann nan da suke so mu zuba masu hannun jari, So Kaga ni ina da abubuwan yi sosai, ka shirya ticket, zuwa gobe in Allah ya kaimu sai ka wuce, kaje ka zauna dasu, duk abunda zai yuwu kawai ayi"
Shima Bilal ɗin gyaɗa mashi kai ya shiga yi, ko ba komai ya san Al'ameen ɗin a yadda yake ji shi yanzu, ba zai iya matsawa ko nan da cen ba, muddin ba gani yayi an ɗaura auren ba, hankalin shi ba kwanciya zaiyi ba.
Saida ya ajiye shi gida, sannan ya wuce gidan shima, da zummar goben kafin ya wuce zai fara biyowa ta office ɗin yaga Al'ameen ɗin sana, saboda akwai muhimman abubuwan da yake so ya tattara mashi ya wuce dasu zuwa goben.
Wanka kawai yayi ya zura jallabiyar shi zuwa masallacin da yake mallakn gidan nasu.
Shine ma yana sallar, masallacin na tara mutane, go ba komai idan Har Al'ameen ɗin na ƙasar da wuya Kaga wani yaja manyan mutanen salla in bashi ba, wannan ce ma tasa kaf manyan mutanen dake Layin suna matuƙar ƙaunar shi da martaba shi, a matsayin shi na matashin da yake ji da dukiya, ilmi da asali, gashi yana tsayawa jan Salla, Abunda ba kowanne matashi bane zai iya.
Ɗakin shi ya koma, kai tsaye kallo ya kunna, Amman Sam hankalin shi baya kan film ɗin Expendable 2 ɗin da suke haskawa a tashar MBC Max ɗin.
Wayar shi ya jawo, ya rasa dalilin shi na jin bai kyauta ba, yau ko sau ɗaya bai kira ta ba, baiyi tunanin ita ba zata kira shi ba, saidai Tasan wannan yana ɗaya daga cikin halayyar matan, masalan idan su ne aka nuna ana so, kaf text ɗin da suka shisshigi wayar tashi ya bincike, babu nata ko ɗaya, kai ko na mai kama da number ɗinta babu, wasu daga ƴan matan dake wahala ne a kanshi, wasu kuma daga abokanan shi ne, masalan ma wanda suka san ba lallai ya ɗaga wayar tasu ba.
Ji yake kaman ya kira ta, Amman hakan baya daga cikin tsarin nashi na yau, ko ba komai bai tsara kiran nata ba gabaki ɗaya ayau, wannan yana daga cikin salon tashi soyayyar, yana daga cikin salon dasa tashi soyayyar a zuciyar ta.
Text ya rubuta lafiyayye ya tura mata.
Bai ga reply ba, kaman yanda bai tsammata ba.
Sharewa yayi yana mai ajiye wayar, sai kuma ya tuna da soyayyar shi da ya manta cikin mota.
Ficewa yayi zuwa motar domin ya ɗauko.
Daidai parking lot ɗinne yaci karo da Mom & in tashi ta shigo gidan, cikin haɗaɗɗiyar motar ta take.
Kai tsaye shi ya isa ga motar ya sanya hannu yana mai buɗe mata marfkn motar, bayan tayi parking.
Da murmushi ta fito tana kallon shi, sumar kanshi ta shafi tana mai faɗin "Son are u at home?". Ɗan gyara tsayuwar shi yayi, fuskar shi babu walwala sosai yace mata
"yeah mom, please Mom from where are u at this late hours?"
Ɗan ɗaure fuska tayi tana mai faɗin "To ubana, daga inda ka aikeni nake" ta faɗa tana mai dungura mashi jikkar ta, alamun ya riƙe mata kenan.
Gaba tayi ya shiga bin bayan ta yana mai girgiza kai, ba son kai, ba son zuciya, dole Dad ya nemi wani ƙarin auren, Mom ɗinshi mace ce har mace, Amman bata iya tsayawa tsayin daka ta kula da mahaifin nashi, in ma a ci sa'a tana ƙasar kenan.
A falo suka tada su Aunt Feena da Afan.
Ayan ne ya ruga da gudu ya ɗafe jikin Mom ɗin, ɗan ɗaga shi tayi tana mai bashi peck, sai kuma ta ajiye shi tana mai ce mashi "Oya go and play my boy"
Sannu da zuwa suka shiga yi mata, Afnan ce ta isa ga yayan nata tana mai amsar jikkar daga hannun shi take cewa
"Sweet Bro you Welcome"
Ɗan shafo kumatun ta yayi yana mai faɗin
"thanks Lil, maza ki kai ma Mom jikkata ɗaki.
Gyaɗa mashi kai tayi, tana mai bin bayan Mom ɗin da har ta riga ta yaye ɗan fingilin gyalen dake jikin ta, sannan ta zare fari tas ɗin glass ɗin, tana mai hayewa sama, Afnan na biye da ita.
Kujerar da Aunt Feena ke zaune ya zauna bisa yan mai faɗin
"Big Sis, ya ake ciki? Ina son magan dake fa"
Cike da kulawa take kallon shi, sai kuma ta sanya hannu ta ɗan daki kafaɗar shi.
"Gaske kuwa, naga kaman kana man ladabi yau"
Ƴar dariya ya saki, wacce ba kasafai yake yi ta ba, yace "Please Lovely sis, ki taimaka, muyi ta a ɗakina, secret ne, bana so kowa yaji"
"Amman sai anjima ko?"
"Eh Aunt ko zuwa bayan isha'i haka. Please ko Mom bana so taji"
Ya faɗa yana mai kamo hannuwan ta.
"U Dont have to warry my Bro, zanzo insha Allahu, Allah yasa muji alkhairi"
"Alkhairin ne ma, tinda kunyi suruka"
Ya faɗa yana mai miƙewa, sannan ya shafo kumatun Nasreem da take ta wasan ta da teddy, sannan ya fice.
Kai mashi bugu tayi, saidai bata same shi ba, take faɗin "Bayani zaka yi, kai ɗinne kake wani iya tsayawa kula mace? Aikau da anyi ruwa hadda ƙanƙara"
Yana jin ta bia ko tsayawa kula ta ba, ya sanya kai ya fice.
Da kallo take binshi, har yanzu dai shine Al'ameen ɗin da ta sani, bai cenza ba ko alama, wannan miskilancin yana ɓata mata rai, some times ma ko wani abu akayi mashi, ba'a gane yana yin ɓacin ran shi, yo miskilanci ma ai ba zai bar shi ba ko kallonka yayi.
**********
Na samu sauƙn jikina sosai lokacin d ana tashi, ana daf da fara sallar magariba.
Su Raihana ne ma suka taimaka man da ruwan wanka, aikau na ƙara jin daɗin jikina sosai, nayi matuƙar mamakin yanda khadeen ke kulawa dani sosai, kaman wani abu bai haɗamu ba jiya.
To koma dai minene dama nayi niyyar sharewa.
Abu ɗaya ke damuna, yanda ɗazu Sir Salim ɗin ya shigo yi mana lecture, saidai ya ɗaga mani hannu kawai, kaman yanda yayi ma sauran ɗaliban, ko alama bai bari na fahimci raunin shi ba, ko kuma in fahimci yana cikin damuwa.
Kenan ma bai damu da rabamun da