Showing 195001 words to 198000 words out of 247770 words
abincin, nan fa duk ya biya, gashi sun zama wastage, in banda abun Ya Ameen wannan kayan abincin ai ko mutum goma zasu iya ci su ƙoshi har su rage.
A mota ne yake tambaya ta wai ko akwai Abunda nake buƙata?
Ɗan girgiza mashi kai nayi, ina mai cewa "Babu yaya"
Duk da haka saida ya tsaya wani shopping complex, saidai naga ana jijjibga abubuwa a mota.
Bamu sha wahala ba wajen shiga makarantar, tin dai daya nuna ma masu gadi Id card ɗinshi, sai naga ma har wani sara mashi suke yi.
Hankali na ya ɗan tashi ganin irin kayan da ya jijjibgo mani,to duka ma yaushe ne zamu samun hutun semester? Bai wuce sati uku nan gaba fa.
Godiya yai mashi sosai, har saida ya nuna mani ɓacin rai, sannan yace "Akwai biscuit da Sweet a ciki, harda springles ma, irin waɗanda kike ci da kina kid"
Dariya ya bani har saida na dara.
Jingina yayi jikin motar, yana mai harɗe hanjuwa duka a ƙirji, cikin hasken soler ɗin dake yi hake iya kallon fuskar shi.
"Suhan zan koma masauki na, amman insha Allahu zuwa gobe zan wuce. Kada dai ki manta zuwa jibi ne ƙa'idar lokaci na ta cika"
Ya faɗa yana mai tsattsare ni da idanu.
"Himm" kawai nace ina mai sauke kaina ƙasa.
Sai kuma naga ya sake buɗe motar ya cire wata farar leda ya ya miƙo mani.
Wannan kyauta ce daga hannun Mijin ki, bana so kuna kallo na a wani mutum daban, Suhan ni ne mijinki da izinin Allah, don haka duk Abunda kike buƙata feel free ki tambaye ni. insha Allahu babu Abunda zai gagara, maganar Mom ki ajiye ta gefe, kada ki sake damuwar kanki akan al'amarin, insha Allahu komai mai zuwa ne dasauƙi"
Nidai a ƙasa ƙasa nake kallon shi.
Yau ɗin ta daban ce a tsarin rayuwar tawa.
Godiya na shiga yi mashi a sanyaye cikin jin kunya.
"Ki kira frienss ɗinki su tayaki ɗibar kayan. And Bilal yace in gaida mashi ke, yayi wata ƴar tafiya ne, da tare zamu zo"
"Ina amsawa". Na faɗa cikin sakin murmushi, ko ba komai Bilal ɗin ya kula damu sosai lokacin da babu Ya Ameen ɗin, har ma munyi sabon da ko Ya Ameen ban saki jiki dashi haka ba, bansan kuma dalili ba.
Komawa yayi cikin mota yana mai faɗin "I am going to miss u Wify, zamuyi waya"
Ina ji ina kallo yaja motar yayi ribos ya fice.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi na saki, ina maida kallo na bisa kayan daya jibge mani harda su Lemuna na kwali manya manya, da kayan ƙwalama irin na ƴan makaranta.
Number ɗin Raihana na kira, ai kuwa sai gasu ita da khadee.
Cikin mamakin yawan kayan suka shiga taya ni kwasa, har muka shige dasu duka ɗaki.
Kowa mamakin kayan yakeyi, masalan ɗana faɗa masu Ya Ameen ne ya siya mani, kuma tare muka fita.
Sun tayani murna matuƙa, masalan Raihana, domin khadee na lura har yanzu akwai wani miki dake yawo cikin ranta, duk kuwa da tana ƙoƙarin karewa kada in gani.
Ina kallon raihana na zungurar ta, itakuma sai ta saki yaƙen dole.
To nima kam ta bani tausayi, ko ba komai dai son maso wani ƙoshin wahala ne.
Saida nayi wanka, sannan na rama duk sallolin da ake bina.
Ga mamaki na kwanciya nayi, wai ina mai jiran kiran nashi, domin inji wai yanda ya isa, ni kaina nayi mamakin kaina sosai da sosai.
Ɗana kulle idanu sai in hango shi lokacin da yake ɗaukar mu selfie ko kuma in hango lokacin da ya saka man zobe da sarƙa.
A hankali na ɗago yatsan nawa ina mai ƙare mashi kallo, lokaci guda kuma ina mai shafi sarƙar wuyan tawa da na kasa cire wa, har wanka da ita nayi.
Wani irin yanayi ne yake ziyarta ta, ashe ya Ameen ya daɗe yana dakin soyayya ta. Tun ma kafin in mallaki hankalin kaina, tin ma kafin in san wacece ni, tin ma kafin shima ɗin ya san mecece soyayya.
Allah sarki, Soyayya daban ce, Amman in ba haka ba, ina ni ina Ya Ameen ɗin? To ai ko abokin shi Bilal yafi ƙarfi na, balle shi sunkutukum *yariman Matasan Arewan*
*Ayi manage wlh banda isasshen charge*
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
Addu'ar Wanda Ya Fitinu da Shakka a cikin Imani
- Ya nemi tsari da Allah.
- Ya bar abin da yake sa shi shakka.
Ya ce:
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ.
A'uzu billahi mina shaytanir rajeem.
آمَنْتُ بِاللهِ وَرَسُولِهِ.
Amantu billahi wa rusulhi.
Na yi imani da Allah da Manzanninsa.
Ya karanta fadin madaukaki:
هُوَ اْلأَوَّلُ وَاْلآخِرُ وَالظَّاهِر وَالْبَاطِنُ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ.
Huwallahu wal akhiru waz-zahiru walbatinu wa huwa bikulli shay'in alim.
Shi ne na farko, Shi ne na karshe, Shi ne Bayyananne,
Shi ne Boyayye, kuma Shi Masani ne da komai.
*Page ~54~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Mafarkai na dinga yi a daren iri iri, wasu dai ba zan iya fasalta yanda suke ba, Amman mafi yawan wanda Ya Ameen yake ciki, sun zauna mani daram a cikin zuciyar tawa.
Ni kunya ma nake ji in na tuna wai yau nice da yin mafarkin Ya Ameen ɗin.
Kiran wayar Afnan ne ya shigo tin dasafe a cikin wayar.
Ƙorafi take mani wai na manta da ita, haƙuri na dinga bata, ina mai cewa yanayin karatu ne, saidai duk yanda ta dinga zulaya ta, kasa biye mata nayi, ita kanta Kunyar ta nake ji, in na tuna wai yayan ta zan aura, saidai jin bata yi mani maganar bane ya sanya ni share wa, ina tunanin ƙila basu kai ga jin maganar ba.
Shaida mani tayi yau ne zasu wuce, har ta haɗa ni da Aunty Feena muka gaisa, duk da ba wani sakin jiki tsakani na da ita, Amman ita sai na fahimci kaman ta ɗan san wani abu.
Bini bini na kan saki murmushi, ko a wajen ɗaukar karatu, har malamr saida ta kai ga yi mani magana.
Aiko hankalin kowa ya dawo kaina, hakan ne ya sanya ni natsuwa da ƙoƙarin fidda komai a raina.
A hanya ta ta komawa ɗaki ne muka haɗe da Sir Salim da abokin shi malam Musa.
Yanda naga mun gaisa da malam Musa ɗinne ya sanya ni gane cewa baisan rabuwar mu da Sir Salim ɗin ba, har zaulayata yakeyi yana cewa amaryar mu.
Shi dai Sir Salim saidai ya ɗan kauda kai, ga yadda ma na kula shine kaman baya son kallo na, duk sai naji ya bani tausayi.
A haka na wuce sukuku, wani irin abu yana mani yawo cikin jiki,wanda na Gaza tantance ko na menene.
So nake in kira ya Ameen ɗin, inji ko ya wuce? Saidai ina gudun yace har na fara sonshi ne, ko yayi tunanin wani abu daban.
Sharewa nayi, saidai fa, akai akai na kan kai kallo na kan wayar, ko yaya naga tayi haske sai na ɗauko na duba, ina zaton ko shine ya turo mani saƙo.
Kai daga ƙarshe dai kasa daurewa nayi saida na jawo wayar tawa na rubuta mashi saƙo kamar haka.
_"Aslm Alkm Yaya, Ya hanya ka isa lafiya?"_
Saida naga saƙon ya shiga, sannan na sauke wayar ina mai sakin ajiyar zuciya a hankali a hankali.
Ko tashi banyi ba daga wajen da nake zaune, naga saƙo ya shigo.
Shine ya maido mani da amsa.
_" On my way dear, call u latter"_
Ɗan murmushi na saki, ko me ya tsaida shi har kawo kaman yanzu da ƙarfe huɗu take neman yi?
Sharewa nayi, ina mai miƙewa na shiga tattara kaya na, domin yin wanki.
Gabaki ɗaya Abunda Ya Ameen ya siya mani, a fili na ajiye shi, mu duka zamuyi amfani dashi, saboda abubuwan sun mani yawa, ba zan iya cinye su ba kafin mu samu hutu, nan da sati biyu, tinda na rago mana lokacin jarabawar.
********
Wanka kawai yayi yayi sallah, sannan ya zauna haɗi da jawo wayar shi domin kiran Bilal, sai ga kiran Bilal ɗinma ya shigo.
"Aslm alkm"
Ya Ameen ɗin ya faɗa, yana mai ɗan zamewa kaɗan ya kwanta cikin yanayi na gajiya.
"Wslm Ya dai malam? Kaman kayi wani uban aiki?"
Bilal ɗin ya furta cikin salo na ɗan zaulaya.
"Mtsew, kaidai bari wlh, driving nayi mai nisa, gashi na dawo a gajiye, ko wanka da salla ma daƙyar nayi su, ya hanya?"
Ya sake faɗa a hankali cikin salon maganar shi da gajiya duk ta kama shi.
"Alhmdllh friend, na iso lafiya, harma mun zauna dasu yau, saidai Abunda ke faruwa, ina tunanin fa sai kazo gaskiya, akwai abubuwa da dole sai CEO ne zaiyi signing kuma akwai muhimman abubuwa da zaku tattauna da turawan nan dole"
A hankali ya tashi zaune yana faɗin.
"Friend kadai san halin da ake ciki, ko na taho hankali na zai rabu ne biyu, dole wani abun sai ina kusa..."
"It will not take much time friend, u have to come, kasan yanda suke da tsari sosai gaskiya"
Ɗan ƙaramin tsoki ya sake ja,yana mai idasa zamewa ya kwanta sosai bisa gadon.
"Friend zan duba in gani, zuwa yaushe ne Meeting ɗin?"
"Eah sunce suna jira suji lokacin da zaka basu"
"Nan da kwana uku"
Ya faɗa straight ba tare da ya tsaya wani tunani ba.
"OK Friend zan sanar dasu, kasan duk abunda zan iya yi, na riga na kammala su, ka bari idan na iso kai sai ka taho, zamu taho da Abie ne, yace yana so yazo yaga su Mom, i'll take All the responsible there, idan na dont worry"
"Noo Bilal, kada ku taho da Abie, tell him ni na hana, saboda ko na zo, ni ba zama zanyi ba, ɗana gama Abunda nakeyi zan juyo, idan kun taho dashi wanene zai zauna?"
"Ok Ameen Amman ka bari mu taho tare dashi, idan yaga su Mom ɗin sai ku taho tare dashi, kasan fa ya daɗe ƙasar nan, u have to allow him"
A gajarce yace "OK Friend See u later" ya datse wayar.
Da kallo Bilal ɗin yabi wayar, Ooh Ameen, halin shi na nan ba zai cenza ba, ko ya tsaya ma su idasa maganar da ya kamata suyi.
Shi kam yana matuƙar buƙatar yaga lokacin da aminin nashi zai cenza.
Ɗan sauke kafaɗar shi yayi a hankali, yana mai furta "Allah ya shirya mana kai" a fili.
Sh kau ya Ameen ajiye wayar yayi, yana mai lumshe ido a hankali cikin matuƙar gajiya, sai kuma ya saki murmushi tunowa da text ɗinda tayi mashi ɗazu, kenan ta fara damuwa da lamarin shi? Saidai kuma fa, dama cen ita gwanar yin text ce, bata iya kiran mutum, saidai ta iya yi ma mutum text.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai sake rubuta mata wani text ɗin, sanin da yayi cewa bacci bayan la'asar ɗin ba abu ne mai kyau ba, ya sanya shi miƙewa dole ya koma perlon nashi cikin rashin kuzari, daga shi sai amless da thre queter.
Yana so ya shiga sashen Mom ɗin tashi amman yana gudun Abunda zai iya zuwa ya dawo, duk da ya san rashin zuwa ɗinma wani ƙarin laifin ne.
Dad kawai ya kira, ya sanar dashi ya dawo lafiya, dari kawai Dad ɗin yayi, yana mai yi mashi sannu da zuwa, ya zuwa yanzu baya buƙatar a sanar dashi cewa Suhan ɗin ita ce farin cikin yaron nashi, kula maganar gaskiya yanzu yana matuƙar sonta, yara nawa ne aka kawo mashi talla, ko kuma suka nemi kafa kansu a cikin zuciyar tashi Amman duk yayi biris dasu? Dama ya san lokacin yana zuwa, duk complain ɗin da Hajiya Kubra na mashi saboda rashin kula matan, dama ya kan ce mata ta ƙara haƙuri, lokaci ne bai zo ba, ko kum matar tashi ce bata bayyana ba, ashe acikin rashin sani ma tana a cikin gidan ba tare da sun sani ba.
Bayan sun gama wayar ne ya nemi layin Afnan bai samu ba, so yake ya sanya ta kawo mashi abinci, sai kuma ya jaraba ta Aunt Feena, itama bata shiga, ɗan tsoki yayi yana mai ƙarasawa kusa da telephone ɗin dake ajiye gefe bisa stool, ya kira landline ɗin cikin gidan.
Maree na perlon tana goge goge, kiran ya shigo, matsawa tayi tana mai ɗagawa tare da yin sallama, duk da sallamr bata cika ba.
"Afnan ki kawo mani abinci marar nauyi please" ya faɗa a gaggauce saboda tsaye yake bisa ƙafafun shi.
Har zai ajiye sai kuma ya jiyo ana cewa "Ranka ya daɗe su Afnan basa nan sun koma, Amman bari inzo in kawo maka"
Ɗan dakatawa yayi yana mai sauraren ta, sai bayan data kammala ne cikin shaƙe murya sannan yace mata "ki bar shi kawai" ya faɗa a gajarce yana mai ajiye kan wayar, lokaci guda kuma yana mai sakin ƙaramin tsoki.
Dole dai shiga cikin gidan ya kama shi, baya so su haɗu da Mom ɗin tashi, Amman ya zaiyi? Dole ne ya shiga gidan saboda baya da ra'ayn cin abincin waje kaf a cikin rayuwar shi, saidai in baya da yanda zaiyi ne, wannan ce ta sanya shi koyon girki kala kala, ko domin ya huce ma kanshi takaici, komin ita girkin mace saidai ya cita gyara, Amman ba kaman yanda mafi yawan matan ba jagwalgwalo kawai suke yi.
Ɗakin ya koma yana mai cire amless ɗin, ya zura jallabiya, ƙafafun shi sanye cikin takalman pajamas farare da surmin ruwan omo mai cizawa, ya nufi Sashen Mom ɗin tashi.
A falo ya tadda Maree ɗin da Nihal kuma zaune bisa kujera tana kallo, lokaci guda kuma tana mai latsa wayar dake hannun ta.
Maree ɗin na daga cen ɓangaren dinning tana ta faman gogewa, sai haɗa gumi takeyi, duk da al wai sanyin ac kaɗan kaɗan a sashen.
"Ke me kike yi kuma a gida har yanzu?"
Ya faɗa yana mai ɗauke idanun shi daga kan Maree ɗin da tin da taga shigowar shi, ta saki tsumman tana kallon shi,sannan ya sauke su bisa fuskar Nihal ɗin.
A hankali ta zumɓyra baki, cikin kaffa kaffa kada ya kula ta shiga cewa " Ba Baby ne yace in taho guda ba?"
"Baby kuma? Wanene baby kuma?" ya faɗa cikin ɗan faɗa haka, yana mai gyara tsayuwar shi bisa kanta.
Miƙewa tayi tsaye ta fara diddira ƙafafu.
"yaya cewa yayi in taho gida, wai in koyi cock da wanke dishes, da mopping da shara"
Sai a lokacin ya fahimci me take nufi.
Hmmm
Kowa ya san za'a rina.
"Shine kuma su Mom basu maida ki ba?"
Ya faɗa a ɗan tsawace.
Ba Nihal ɗin ba har Maree da take cen gefe saida ta razana.
Ɗan ja baya tayi, saboda ta san Halin Ya Ameen ɗin, baya shiga sha'anin da ba nashi ba, Amman kuma duk lokacin da ya shiga ɗin basa ji da daɗi.
" ku ba kuna gani cewa mace ta zauna ta latsa waya kaman shine burgewa ba? Ku hau motar da kuke so, kuje inda kuke so kuma a lokacin da kuka ga dama, Mom tana kallon ku ta zura maku idanu, ko hakan aka tsaya ya kamata ku hankalta, masalan ke da kece gaba wajen raina mutane, ai sai kije Suhan ɗin da kuka raina kuke ɗaukar ta ƴar ƙauye bagidajiya ta koya maki"
Ya faɗa yana mai zagaye ta ya wuce.
Aikuwa kuka ta saki, sai kuma ta nufi ɗakin ta tana mai raira wani kukan, Ya Ameen baiyi ba a rayuwa, gashi ya katsa ta a gaban Maree, kuma yana haɗa ta da waɗancen kwaɗayayyun wai har ma yana cewa taje ta koya mata.
Kitchen kawai ya nufa kai tsaye, abinci ake girkawa, saidai sanin da yayi cewa gashi dai Nihal bata iya girki ba, harma miji ya koro ta, to tabbas Maree ce ke girkin, shi kau ko yunwa zata kashe shi, baya jin cewa zai iya cin abincin nata.
Domin da yaci abincin Maree gara ya je eatery yaci, duk kuwa da yanda ya tsane shi.
Ga alama Mom bata gidan ma gabaki ɗaya, ɗan girgiza kanshi yayi yan mai nufar sashen Umma domin ya san ko ba komai ba zai rasa wani abun ci ba.
Saida yayi sallama ta kai Ukku sannan Umman ta fito daga cikin ɗakin, hannun ta ɗauke da counter, da gani dai lazimi take yi.
Cikin sakin fuska ta shiga cewa "A'ah Muhammadu kai ne?"
"Eh Umma nine" ya faɗa yana mai ɗan rissinar da kai alamun girmamawa ya shiga gaida ta.
Amsawa tayi cikin ɗan jin nauyin shi, duk da ta kula boko ta ratsa shi, shi baya ma ko nuna mata sarakuta sosai, to dama ƴan boko haka suke, sun saba da irin wannan rashin Kunyar.
"Mom yanzu na dawo na gaji, nace ko zan samu Abunda zanci anan, cen naje Mom ɗin bata nan"
Ya faɗa kai tsaye a hankali ba tare da ya ko tuna ita ɗinfa surukar shi bace.