Showing 222001 words to 225000 words out of 247770 words
sabon Aure*
بارَكَ اللَّهُ لَكَ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَمَعَ بَيْنَكُمَا فِي خَيْرٍ.
Barakal-lahu lak, wabaraka 'alayk, wajama'a baynakuma fee khayr.
Allah Ya sanya albarka a gareka, yayi maka albarka kum aya hada tsakaninku da alheri.
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~59~*
*Fans Naji daɗin comment ɗinku haƙiƙa, ashe Gimbiya Umma ma tana da masoya har haka?*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Washe gari tin da safe sai ga kira daga masarauta, mai martaba ne da kanshi, yana tambayar lafiyar Umma, da bincikar ko dia za'a kawo mata haɗimai ne masu tsaron lafiyar ta, da yi mata hidindumu?
Dayake Dad suka kira, sai ya miƙa ma Umma wayar, cike da girmamawa take gaida mai martaba Baffan nata. Sannan take sanar dashi cewa babu komai, suna da ma'aikata isassu, koda za'a kawo a bari sai daga baya.
Bayan sun gama magana ne, sai ya buƙaci da taba mai gidan nata.
Sake damƙa amanar Umma yayi ga Dad ɗin, duk da yasan ba za'a samu wata matsala ba, tinda ko da cen lafiya lau suke zaune, saidai haƙƙin fada ne akan tasan halin da gimbiyr tata take ciki a kulli yaum.
Mai martaba ɗinne ya kuma buƙatar da suna so a gaggauta kawo masu amarya, kuma basa buƙatar komai da ya danganci lefe, saboda masarauta ita ke yi ma duk wadda ta fito daga tsatson ta komai.
To sha'ani ne na masarauta, shima Dad ɗin bai ja ba, gudun saɓa ma sarkin, sai ma cewa yayi insha Allahu ba da jimawa ba za'a hannanta masu amaryar.
Cike da girmamawa sukayi sallama, yana mai buƙatar sanar da Al'ameen da Mom ɗin tashi, akan cewa su adana lefen su, har sai yarinyar tazo gidan sannan a bata.
Duk da shi fa har yanzu ba wai ya yarda bane akan cewa har cikin zuciyar hajiya Kubran ta yarda.
Miƙeea yayi yana mai nufar sashen Hajiya Kubran, baya da tabbacin cewa ya zuwa yanzu ma bata fice daga gidan ba.
*********
Wajen ƙarfe tara ya kira ni tare da shaida mani saukar tashi, da yaso ya wuto nan waje na kai tsaye, Amman sai aka kira shi akan cewa order ɗin kayan da za'a sanya a sashen namu sun iso.
Hakan ce ta sanya shi wucewa gidan kai tsaye.
Dayake part ɗin an gyara shi fiye da tunanin mutum, duk da ba'a rushe shi ba, ɗaki ɗayan nan dai har yanzu shine, sai kitchen da babban falo.
Saidai an sake kankare plaster ɗin anyi wata, hatta da fentin da akayi ma part ɗin abun kallo ne.
Shi kanshi daya gani saida abun ya burge shi, haƙiƙa Bilal aboki ne kuma amini ne, shine ya tsaya akan aikin kan jiki kan ƙarfi, dukkan Abunda yasan zai burge Al'ameen da Suhan ɗin shi ya sanya aka zuba.
Umma tana kallon ana aikin, saidai tayi murmushi, zuciyar ta na ayyana mata, yarinyar tata ta kusa samun ƴancin kanta, da yin rayuwa kaman kowa.
********
Duk abunda ke faruwa ma'aikatan gidan basu sani ba, saidai labari ya bazu ko'ina akan auren da Umma tayi ma Alhaji, ko Mama talatin yanzu ba wani samun abun gulmar take ba, Maree dake shiga itama yanzu an hana ta, Nihal ɗince ke jagwalgwala masu komai, kusan ma ince sun koma yin order, domin ko ta girka basa iya ci, haka gyaran sashen da ka shiga zaka dinga ganin ƙura, Amman duk da haka Hajiya Kubran bama wani ganewa takeyi ba, saboda ba wannan ce a gaban ta ba.
Saidai kowa ya kula da sauyn da aka samu cikin gidan, to Umma ce dai, itama ba inda take zuwa, ko fitowa bata cika yi ba, in ba sashen Alhaji zata ba.
Dole ne kuma suka koma girmama ta, yayin da bata nuna masu komai, alheri akai akai takan sanya Alhaji yayi masu, saboda halin girma irin nata, ba kowa ne ma ta riƙe arai ba, masalan Mama talatun da tasan cewa ba ƙaunar ta da ɗiyar ta takeyi ba.
Maree kam tana cen ta haukace, kullum maganar ta Ya Ameen, masalan da taga ana gyaran sashen tana raya ma kanta ko ba daɗe ko ba jima ita ce za'a shigar sashen duk yanda zata yi zata yi, domin ganin ta karkato da hankalin Alhaji ƙarami a kanta.
*******
Kai tsaye gidan Hajiya Zainab ya wuce, to ita ɗin ma bata shaida mashi sunyi tafiyar ba, shaida mata yayi isowar kayan, da kuma buƙatar ko zata samu waɗanda zasu je su shirya part ɗin.
Daga nan ya wuto gida kai tsaye, to a gidan ma ne ya sake yadda Bilal, yana tsaye jingine da mota yana amsa waya da Ummin. Yayin da ma'aikatan kanfanin da zasu haɗa kayan ke ya faman kwasar kayan zuwa cikin sashen.
Tsayiwar shi ya sake daidaitawa, bayan yayi parking ya fito, hannuwan shi duka ya zube cikin aljihun suit ɗin da take jikin shi, da ta kasance kalar ash mai haske.
Yayi matuƙar kyau, ya sake fari, fatar ta sake murjewa, kai da ka kalle shi ba sai an gaya maka hutu ya zauna a jikin shi ba.
Sashen yake kallo, yana raya abubuwa da dama acikin zuciyar shi, shi dai ba wai dan yaso zaman bane, saidai baya so wata fitinar ta kuma ɓullowa ne.
Saida Bilal ɗin ya datse kiran sannan ya juya ta inda yake tsaye yana faɗin "My Man you Welcome, maimakon ka faɗa mani inje in ɗauko ka?"
"ah no, ai wannan aikin da kake yi, yafi ɗaukonin, dama mota ta a airport na ajiye ta Wancen karon, ko da nayi landing kawai sai na Ɗauka" ya faɗa yana mai sake maida kallon shi kan sashen da ake ta faman shigar da kaya.
"Aiki yayi kyau Friend, nagode da samun amini kaman ka" ya faɗa yana mai nuna sashen da hannu haka kaɗan.
Ka faɗar shi Bilal ya dafa.
"Kafi gaban komai my man, ina fatan mission ya kammala?"
"Alhamdullahi, saidai sun ɗan riƙe ni da yawa"
"ai tinda an samu Abunda ake so, ba wani damuwa ina ganin" Bilal ɗin ya faɗa shima yana mai maida kallon shi kan kayan.
"Ina fatan akwai komai cikin kayan, domin ba zasu koma ba, sai sun gama haɗa komai" cewr Bilal ɗin.
"Eh komai akwai cikin package ɗin, Abunda basu kammala ba ma Mama Zainab zata zo da mutane sai su ƙara sa su"
"OK tau shikenan, ya kamata kaje kayi wanka hakanan, sai ka huta"
"Ok Mom na gida kuwa?"
"eh tana ciki ita da Dad"
"OK" kawai ya faɗa, yana mai juyawa ya nufi part ɗin Mom ɗin baki ɗaya.
*******
"Dama ai dole suce kada akai lefe, su san basa da Abunda zasu bada tukuici mana, inma ƴan uwan gaske ɗin ne" Mom ɗin ta raya cikin ranta, a zahiri kuma tayi murmushi tana mai faɗin
"Shikenan ma, sun hutar damu, dama Feena ta kira ni akan cewa end of this Week zata shigo da kayan, shine nayi tunanin ko sunday ne sai aje akai"
"A'a ba sai an kai ko ina ba, ni zan fita sai na dawo" ya faɗa yana mai Miƙewa daga bisa sofar.
Shigoway Ya Ameen ce ta dakatar dashi daga tafiyar d aya yi niyya.
"A'a Son kai ne da safen nan?"
Cewr Dad iɗn, yana mai sakar ma yaron nashi murmushi, ko ba komai ya tabbatar da Yaron nashi zaici aure inda ya dace dashi, babban gida masu dattako, Amman duk da haka mahaifiyar tashi bata sani ba, sai hauka takeyi.
"Dad Good morning, baka fita ba?"
"Yanzu dai nake Da niyya Son, ya aiki ya hanya?"
"Alhmdllh Dad, muna kyautata zaton za'a samu Abunda ake so wajen turawn nan"
"Tau mSha Allah, dama yanzu nake maganar ka da Mom ɗinka"
"To Dad, Mom Good Morning" ya faɗa a hankali yana mai maida kallon shi kan Mom ɗin.
Murmushi ta saki a hankali, tana mai miƙewa itama, "Son You are Welcome"
Ta faɗa itama, tana mai ɗan taka wa kaɗan zuwa wajen yaron nata, fuskar ta ɗauke da murmushi kaɗan.
"Batun lefe ne mukeyi, su ƴan uwan matar taka sunce basa buƙatar komai, shine muka yanke shawara da Dad ɗinka akan a bar shi, alabasshi idan tazo sai a bata daga baya"
Da mamaki kaɗan a saman fuskar tashi, ya juya yana mai kallon Dad ɗin nashi, wane ƴan uwan matar shi kuma? Suhan dai it ace matar tashi, kuma yasan basa da wasu ƴan uwan idan ba su ba.
Gyaɗa mashi kai Dad yayi, yana mashi alama da ya biyo shi waje, da idanu.
"OK Mom hakan yayi, zanje in watsa ruwa"
"OK to a fito lafiya, kayan ka na guest room na sanya aka mayar maka, kafin a gama gyaran"
Itama ta faɗa, tana mai nuna mashi makullin part ɗin da hannu.
Bai ce komai ba, ya shiga taka wa a hankali, yana mai ɗaukar keys ɗin sannan ya fice.
Ko da ya fito har Bilal yabar wurin, hakan ce ta sanya shi bai tsaya sauraran komai ba, ya wuce zuwa guest room ɗin kai tsaye, yana mai ɗan kallon sashen su Suhan ɗin, yana mai raya ma ranshi dama ace tana gidan yanzu ta fito ya ganta.
Daf da zai shiga part ɗinne ya hango fitowar Alhajin, kai tsaye shima wajen kayan y nufa yana masu magana, su kuma suna ta faman gaida shi.
Kai tsaye ya juya zuw aga Dad ɗin nashi.
"Kaje ka huta, zamuyi magana da daddare"
Abunda Dad ɗin ya faɗ a mashi kenan, domin yana iya hango tarin gajiya akan fuskar yaron nashi.
******
"kin tabbata da kammaluwar komai?, domin fa kinsan idan akwai Abunda na tsana a rayuwa ta bai wuce yarinyar da maman ta ba"
"Haba hajiya ta, ai baki da matsala, gani ga laila ma, tare muka sake komawa, kuma malam ɗin ya sake jaddada mana cewa indai aka bi sharuɗɗan da ya gindaya mana, aiki ziyi kyau fiye da yanda muke tsammani, kedai kawai kiyi ƙoƙarin ganin bai kusance ta ba, domin ana ɗaura auren nan fa, zaiji babu wadda ya tsana irin ta, ita dai Uwar ce malam yace muyi haƙurin ganin an gama da lamarin ɗiyar, saboda ita akwai wani al'amari mai girma tattare da ita"
Gyaɗa kia ta shiga yi cikin gamsuwa, "Ba matsala indai dan wannan ne, cin amanar da suka yi mani, ba zan taɓa kyale su su tafi hakanan ba, sai sunyi nadamar shiga rayuwa ta da sukayi"
Ta faɗa cikin kaushin murya, tana mai sauke wayar daga kunnen ta.
" Zasuyi danasani."
********
Kullum ya ganta babu Abunda ke faɗo mashi cikin rai, illa iyaka yaga cewa ya same ta.
Shifa Maree ce kaɗai wadda yake ganin dacewar shi da ita.
Ada kua baya jin hakan a ranshi, ko shi gani yake ya wuce da iyawar ta, Amman dai koma minene zai je ya samu alhaji da maganar akan cewa yana so a aura mashi maree, wallahi idan bai aure ta ba, yana jin za'a samu matsala, ya tabbata ba zata ƙi shi ba, masalan ma idna akayi la'akari da cewa shi ɗan aiki ne itama ƴar aiki ce.
*********
Sai bayan daya kammala komai ne, sannan ya kira ta, duk da bacci da yake ji, Amman yana tunanin idna ba muryar ta yaji ba, baccin ma gagarar shi zaiyi.
Sun daɗe kuwa suna waya, kalami yake zuba mata masu narkar da zuciya, shida baiƙi ma ace gobe a ɗaura auren nan ba , yana ganin wutar shi da cen baya, da ya tsaya ruwan ido, ashe ga wadda ta dace dashi ma tana rayuwa a cikin gidan ba tare da sanin shi ba.
Mun jima sosai a waya, kiran Umma da nagani yana shigowa wayar tawa ne ya sanya ni ce mashi yayi haƙuri zan sake kiran shi.
Shaida mani ta shiga yi, da zaran na kammala Jarabawa ta gobe, in shirya za'a zo a ɗauke ni, dukkan abubuwan da nasan zan buƙata in ɗauka, domin ba lallai in koma makarantar ba saida aure na akai.
Kunya Naji ta kama ni. Nan na kashe ina mai amsa mata, sannan na kira shi, nake faɗa mashi Amman Umman tace driver ne zai zo ya ɗaukeni da kanshi.
Faɗa ya kama yi, wia minene amfanin shi, shine zai zo da kanshi ya ɗaukeni, tinda ai yana gari.
Shifa ba zai lamunci yawan shiga motar driver ba, kai infact ma da munyi auren zai koya mani mota, yana matuƙar kishi na, ace kullum duk inda zani ina tare da wani ƙato, gara ya koya mani in dinga jan kaina.
Ya zuwa yanzu, na sakankance ma soyayyar da Ya Ameen ɗin yake yi mani, ashe dama haka yake, da nayi mashi gurguwar fahimta, sai nake ganin ko Afnan yanzu bata kaishi daɗin zama ba.
Har addu'a nake yi, bayan auren namu, in samu zaman lafiya, da kwatankwacin ƙaunar da yake nuna mani yanzu, domin ni kaina na sani, a yadda nake ba kowa ɗinnan ba, ace na samu miji kaman ya Ameen tabbas nayi ma mata zarra, bana kuma tunanin idan akwai wadda zata iya kamo ni nan kusa.
Haka mukayi sallama dashi, kaman kar mu rabu, kowa na begen juna, duk da har yanzu ina jin kunyar shi, domin wani abu ɗin idan ya faɗa sai na sauke kaina ƙasa tsabar kunya kaman yana gaba na.
Umman na sake kira na shaida mata yanda mukayi da ya Ameen ɗin.
Cewa tayi to ba damuwa, ai sai a gaya mashi inda zai kai ni, domin dai dama shi ɗin ba baƙon wurin bane.
Kai A ya ɗaure, tambayar ta na shiga yi akan cewa ban gane ba, kaman ya inda zai kai ni.
Cewa tayi in bari goben na gani.
Nidai haka na kashe wayar tawa, to me Umman ke nufi? Ni fa wannan hali na Umma na damu na, ita bata taɓa fitowa fili ta sanar da kai komai, tafi so komai ka gani da idon ka, inma ka tambaye ta, ba zata taɓa faɗa maka ba.
Haka na kwana cikin zulumi sosai, koda ya kira da daddare yaji kaman bana lafiya, ba irin tambayar da baiyi mani ba, Amman na shaida mashi cewa babu komai. Haka mukayi firar dai ba wani annashuwa, duk yanda yayi ya shawo kaina kasawa yayi, saidai ya haƙura ya ƙyale ni, shima ran nashi babu daɗi.
Washegari na shiga tattara kaya na, shaida ma su Raihana nayi komai da ake ciki, sunyi alƙawarin halartar biki na ɗin, da cewr idan lokacin yayi in turo masu da katin ko ta waya ne, zasu kira ni.
Cikin wata irin rantsattsar mota ya iso makarantar tamu, misalin ƙarfe sha biyu, shi kaina da kallon mamaki ya shiga bina, jin inda akace ya kai ni, kuma Dad ne ya shaida mashi da kanshi, duk da yace zasuyi magana jiya Dad ɗin bai dawo da wuri ba, yana cen harkoki sun riƙe shi, shirya ɗaurin aure yake yi mai cike da ƙawatarwa, saboda ko ba komai tuwon girma miyar shi nama.
Da kanshi ya dinga kwasar kaya na yana zubawa but, mutane sai mamaki suke yi, wasu na cewa Al'ameen Dambulan ne, wasu kuma na cewa bashi bane, saida Khadeeja ta shaida masu cewa shine, nan fa wasu suka fara ɗaukar shi hoto da waya ba tare da ya kula ma dasu ba.
Nidai da kallo nake binshi, yayi matuƙar kyau cikin manyan kaya, shadda ruwan ƙasa, da hula tangaran da takalma half cover sai kalli suke yi.
Khadeeja kasa tsayawa tayi wurin, haka ta juya zuwa ɗakin namu, zuciyar ta cike da ƙuna da suya, tabbas so daban ne, watau kuma son maso wani ƙoshin wahala ne, ita tana ganin son da Suhan keyi ma Al'ameen ko rabi rabin nata bata yi mashi, da ace ita ce Allah zai mallaka ma Al'ameen ɗin da ta kusa kashe shi da soyayyar ta.
Haka ya zagaya yana mai buɗe mani sit ɗin gaba, ba gaddamanna shiga, har yanzu ba walwala sosai a tare dani, saidai ganin shin da nayi ya mantar dani kusan komai.
Haka muka bar makarantar, tuƙi yake cikin gwanancewa, rabin hankalin shi duk yana kaina.
Hannun shi guda ɗaya ya sanya ya riƙe steary ɗin, yayin da gudan yayi amfani dashi wajen kamo nawa,
"Me ke damun ki ne dear? Ko zullumin auren ne har kin fara?"
Ya faɗa a hankali, cikin salon muryar shi, mai sanyaya mani jiki.
Ban ƙoƙarin ƙwace hannun nawa ba, saidai ina jin taushi da ɗumin hannun nashi har cikin kwalwa ta.
Ba ce dashi komai ba.
Shima bai sake cewa komai ba, sai ma tuƙin shi da yake hankali kwance, har yanzu bai saki hannun nawa ba.
Yatsan da zoben da ya saka mani yake murzawa a hankali.
"Thanks dear"
"For what?" na bashi amsa a hankali.
"Keeping my promise"
"Uhmm"
Na sake faɗa ina mai ɗan ƙoƙarin zare hannu na daga cikin nashi.
Sai kuma na ƙware da miyau ɗin da ya tsinke mani yana ta gudu cikin baki na.
Tari na fara yi, yayin da