Showing 210001 words to 213000 words out of 247770 words

Chapter 71 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10405

su ci abincinku, kuma Allah Ya sa Mala'iku su yi muku addu'a.*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~57~*

*Godiya mai ɗinbin yawa zuwa gareki ƙawata _Salamatu_ haƙiƙa kin nuna mani ƙauna, kin nuna kuna tare dani da kuma ~SuhAmeen~ godiya marar adadi, wannan Page ɗin naki ne, kyauta halak malak, na gode da wannan ƙauna da kike nuna mani, Allah ya barmu tare.*

*Jinjina gareki ƴar uwa ta, Jiddon Dady, kina ƙara ƙarfafa mani guiwa da kuma shawarwarn ki, haƙiƙa nafi kowa dace da samun ƴar uwa kuma ƙanwa a duk faɗin duniyar nan, ba zan iya misalta ƙauna ta gareki ba, har kullum kina cikin zuciyar tilon ƴar uwan ki Oum-Deedat. Fatan zaki dawwama cikin aminci, da ƙauna daga angon ki, mai gidan ki Yusuf Tijjani Baffa (Dady) gaisuwa zuwa gareku baki ɗaya*


_@One lurv marubuciyar ( *Ƙareenaty* ) da Fatima batula marubuciyar ( *Ni da Malama ta*) gaisuwa zuwa gareku. in kuka ɗauke Umar babu wanda ke nuna ma littafi na ƙauna, duk cikin forum ɗinmu kaman ku, ina yinku irin over ɗinnan, a cigaba da zazzaga mana zallah fasaha._

~Hehehe @Batula ina so ki sani, yanzu ne ma na fara karanta *Ni da malama ta* yanda kike zazzaga fasaha ai ba zan taɓa son in dena karantawa ba, kada a shani masilla~


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


A falo ya tada ta zaune, Abie na kwance gefen ta, kanshi bisa dukkanin cinyoyin ta.

Da sallama ya ƙarasa ɗauke a bakin shi, zuwa kujerar da take kusa da su.

Zama yayi, yana mai gaida ta, da dukkanin kulawa da fara'a sosai É—auke a fuskar ta, ta shiga amsawa.

Gama wayar ta kenan da Hajiya Sa'a, ta tabbatar mata da an kammala komai, duk da sharaɗin da boka ya gindaya masu mai matuƙar ƙarfi, cewa an kammala komai da zaran an ɗaura auren zaiji duk duniya ba wadda ya tsana irin matar tashi, to saidai fa, muddin suka yadda ya santa a ɗiya mace, lokacin ne fa komai zai warware. Son da yake mata ma zai daɗa linka na da.

A haka suka amince, masalan Hajiya Kubran da idon ta ya riga ya makance, ƙiyayyar da tsanar ce kawai ke cin ta, ita a ganin ta, tinda kusa da ita zasu zauna, zata yi duk yanda zata yi ta hana shi tarawa da Suhan ɗin, masalan ma gashi ance zai tsane ta, dama dalilin ta kenan na cewa a zauna gidan kenan, saboda ta sanya ma duk wani motsi nasu idanu, ita fa ba zata taɓa sake jiki tana ji tana kallo ta haɗa iri da waɗannan baƙaƙen talakawan ba.

"Son an dawo lafiya? Ya gajiya?"

Ta faɗa, tana mai kallon yaron nata cike da annashuwa, gani takeyi kaman burin ta ya gama kammala, ita har ta ƙagara ma a ɗaura auren, ko zai fara tsanar tata, kuma lokaci ne yanzu da zata sauya salo, zata nuna ma kowa ta amince da auren, kuma tana ƙaunar Suhan ɗin 100%.

Yayi mamakin sakewar ta gareshi, dukda haka dai sai ya basar, yana mai cewa "yes Mom, gajiya akwai ta"

Ya faÉ—a yana É—an zamewa bisa kujerar.

"Ko zaka ci abinci ne? Sai Nihal ta kawo maka"

"wa yayi girkin?" ya faÉ—a yana mai É—agowa ya dubeta.

"Eh to wai Nihal tace ita ce tayi, ai kai ne kace ta dinga yi"

"Uhmm" kawai yace, domin yasan ƙarya Nihal ɗin takeyi, ba zata iya cika sharuɗɗan shi ba.

"No Mom, ta bar shi kawai, kinsan ba iyawa tayi ba, zan samu abun da zan ci a É—aki na"

Ya faÉ—a yana mai É—an gyara zama ya fuskance ta.

ÆŠan É—aure fuska tayi, domin Nihal É—in ta faÉ—a mata komai, to ita ma É—in duk da bata ji daÉ—in hukuncin Al'ameen É—in ba, zata so ace Nihal É—in ta koma gidan mijin nata, kaman ita Hajiya Kubra bai kyautu ace an koro mata É—iyar tata gida ba, Amman yanzu ba ta Nihal É—in takeyi ba, so take ta gama da matsalar Al'ameen É—in tukunna.

"Kai malam sai ka É—aga man Mom ko? Kazo ka wani hahhaye ta"

Ya faÉ—a a hankali, cikin salon maganar shi, mai cike da sanyi.

"A'a ƙyale mani auta na, yaushe rabon da in ganshi?"

"ita Afnan É—in kin bada ta ne? Da kike kiran shi auta, wannan gotai gotai É—in dashi, kalle shi fa, ya kusa tsawo na"

"Mom ƙyale shi, na dawo fa kenan ai, so yake ya takura ni" Abie ɗin ya faɗa cike da shagwaɓa.

Murmushi ya saki, yayin da shi kuma gogan ya É—an lumshe ido yana mai kauda kai gefe.

Saida ya tattaro dukkan natsuwa da dakiya ya É—ora ma kanshi sannan ya fara cewa "Mom daga wajen Dad nake, munyi magana dashi sosai, ya faÉ—a man dukkanin sharuÉ—É—an ki, insha Allahu na amince, kuma zaki sameni mai yi maki biyayya a koda yaushe"

"Dama zaka ce haka mana, Soyayya ta rufe maka ido, to ai ni ba zan zuba maka idanu ba haka kaman baka da gata, ka rasa wadda zaka aura sai takalan masu aiki na" ta faÉ—a cikin zuciyar ta, a zahiri kuma murmushi tayi sannan tace.

"Ba damuwa Son, feel free, nice na amince maka da kaina, da fatan dokokn basuyi maka tsari ba, bana so ne kayi nisa kusa dani, Shiyasa nace a taimaka a zauna kusa dani ɗin, na gane cewa yarinyar tana da natsuwa kuma kan sonta, ni kuma kasan ina ƙaunar dukkanin abubuwan da kake so"

Da matuƙar mamaki yake kallon ta.

Anya kuwa mom ce? What bring this suddent change?

Shima ɗan zura mata idanu yayi, Un blievable, ace kaman mom ce yau ta tausasa murya tana mashi magana haka akan auren nashi, bai ƙara shan mamaki ba, saida tace mashi "ya inlaw ɗin tawa? Fatan dai tana lafiya?"

"Lafiya Lau Mom, tana gaida ku"

Ya faɗa a hankali cen Ƙasan maƙoshin, na farko kenan a tarihn rayuwar shi, tin tasowar shi daya ji tana tambayar lafiyar Suhan ɗin.

Abie ne da yake kwance, Baisan wainar da ake toyawa ba, tashi zaune yayi yana mai cewa "Mom yaya yaƙi faɗa man wacece groom ɗin tashi har yanzu fa"


Kallon ta ta maida kan Abie, "Kada ka damu Son ai ka santa ma, Suhan ce ta gidan nan"

"what? Mom Suhan wadda na sani? Ita yaya zai aura?"

Ya faÉ—a yana mai É—an zaro idanu cikin kaÉ—uwa.

Hankalin shi Al'ameen É—in ya maida kan Abie, kada dai ace shima baya goyon bayan abun kaman saudat da Nihal.

"Yes for Sure Son, kaga tuwon mu manmu"

Ga mamakin Al'ameen wani irin ƙayataccen murmushi ya saki, yana mai tashi ya koma bisa kujerar da Ya Ameen ɗin yake kai, rungumo shi yayi yana mai cewa "Congrat Yaya, Allah ya sanya alkhairi, ai Suhan tayi, tana da kirki da natsuwa, ta cencenci a aure ta"

Su duka da kallon mamaki suke binshi, daga mom É—in har Al'ameen É—in.

Shima murmushi Al'ameen É—in ya saki jin abinda yace, sai kuma ya maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take hakimce, fuskar ba yabo ba fallasa.

Miƙewa yayi yana mai cewa "Thanks Bro, bari in wuce daƙi, ina so ne in huta, gobe insha Allahu da wuri nake so in wuce, alabasshi kai ka tafi daga baya"

"Ina zuwa ne Son?" Mom É—in ta faÉ—a, har yanzu fuskar ta ba yabo ba fallasa.

"Mom New York nake so naje zuwa gobe akwai ayyukan da suka taso mana ne acen, kuma dole sai nine zan yi su, maganar zuba hannun jari ne a cen kamfanonin nasu"

"OK to babu damuwa, inda ka dawo sai muyi maganar yanda abubuwa zasu kasance Son, kada ka damu ni na amince Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa, sannan nima ina so ne muyi maganar ƙara share ɗin da zanyi a nnpc tower, ko zuwa bayan hidimar ne"

"OK Mom see u later"

Ya faɗa yana mai wucewa zuwa sashen nashi, bai san me ke damun mom ɗin tashi ba, da take ta ɗaukar maƙudan kuɗaɗen ta tana zuba hannun jari a kamfanin man fetur da iskar gas ɗin ba, duk dai da cewa lafiya lau tana ganin profit nata, saidai fa shi ba wai ya natsu bane sosai da har kar, kasancewr haka take abun wani lokaci ba lauyoyi, duk da dai shi yana rubuta komai da sanya hannun waɗanda kuɗin nata ke shiga hannun su. yayin da Abie ma ya miƙe ya nufi ɗakin shi, yana mai faɗin "Mom bari inje in watsa ruwa nima"

Da kallo ta bisu dukan su, har suka ɓace ma ganin ta. Zuciyar ta na ayyana mata abubuwa iri iri, watau yanzu aka fara wasan.


********


Umma ce zaune bakin gadon nata.

Tunani ne kala kala cikin ran nata, saidai ita tana ganin wannan ne kawai abun da ya dace tayi, a tsawon shekarn da ta ɗauka, daidai da rana ɗaya bata taɓa tunanin komawa mahaifar tata ba, saidai bata da zaɓi ne, wannan karon ta shirya tsab, koda kuwa cewa daidai yake da rasa rayuwar ta, ba zata taɓa bari yarinyar tata tayi zaman ƙunci a gidan miji ba, ta dalilin rashin sanin asalin ta.

Saidai ta ina zata fara?

Ita É—in da kowa yake tunanin ta mutu, ita É—in da kowa yake ma kallon maragayiya tsawon shekaru masu yawa.

"Hmm" ta faɗa tana mai nisa wa, sannan ta zakuɗa zaman nata, tana mai cewa "komai yazo ƙarshe, Mamana lokaci yayi da kema zaki dara, cikin dangin ki da ƴan uwan ki"

Wayar ta dake gefe ajiye ce ta É—auki tsuwwa, alamun kira ya shigo.

Ganin baƙuwar number sai baisa tayi saurin ɗagawa ba, har ta katse, kiran ya kuma shigowa.

A hankali ta É—aga, cikin manyance da dattako take amsa sallamar da akayi mata.

Muryar mace ce, cike take da annashuwa da fara'a.

A haka suka shiga gaisawa, saidai tin kafin ma Umman ta tambaya matar tayi saurin cewa "nasan baki gane ni ba, nice Hajiya Khaltum, Ammin Salim, malamin su Suhan"

Fara'a umman ta faÉ—aÉ—a, kunya na mai kama ta "Allah sarki Ammi, ya gida ya kwana biyu, nima ina ta so ince Suhan ta bani number É—in in kira wallahi na shafa'a, da fatan dai kowa na lafiya?"

"Lafiya Lau Umma, dama cewa nayi bari in kira mu gaisa, tin bayan da abun nan ya faru bamu sake jin juna ba, Salim ne ke sanar dani an sanya ranar Suhan ɗin, shine nace bari in sanar dake, Suhan har yanzu ɗiya ta ce, saboda haka nake so ki amince ko zuwa sati guda ne kafin bikin in aiko da mai yi mata gyaran jiki irin namu na nan barno, sannan don Allah ki sanya ta, ta lissafo mani dukkanin abubuwan da take buƙata, da suka danganci kayan kitchen, insha Allahu duk na ɗauki nauyi, bana so kice a'a don Allah, alkhairi ne nayi niyyar yi, ko da ace ba Salim zata aura ba, ai shima namiji ne, nasan in nace tayo da kaina ba zata yo ba, kuma nasan idan na sanya Salim yayi mata maganar ba yi zaiyi ba, yace Kunyar yi mata magana yake ji, Shiyasa nace bari in biyo ta ɓangaren ki Umma, don Allah ki taimaka"

Mamaki ma ya hana Umma magana, iko sai Allah, har cikin zuciyar ta, tana jin ciwon rashin suruka da Suhan tayi irin Ammi ɗin, lallai wannan ƙauna daga Allah ne, babu Abunda zata iya cewa saidai godiya, da fatan Allah ya ƙara yalwata masu Arziƙi su.

Ta É—aure ta da dukkanin jijiyoyin jikin ta, don haka ne ta shiga zuba mata godiya, "Ah haba ba wani abun godiya a ciki, ai har yanzu Suhan É—iya ta ce" Ammin ta faÉ—a har yanzu cikin fara'a take.

Kaman Umman tace mata zasu shigo garin nasu, sai kuma ta share, tinda tafiyar ba tata bace ita ɗaya ai bai kamata ta ɓata masu lokaci ba, alabasshi bayan biki zata shirya da kanta zuwa wajen Ammi ɗin, takanas domin godiya da ƙauna da ɗawainiya, ko ba komai duk wanda yaso ɗanka ai kai yake so.

Haka sukayi sallama cikin mutun ta juna, kowa na girmama kowa, lallai Ammi É—in ta cika mace, har ma tafi, duk wadda ya samu Ammi a matsayin Uwa, ko kuma a suruka, ya cencenci jinjina, Ammi É—in irin matan nan ce da za'a iya cewa basu É—auki duniya da zafi ba, kuÉ—i ilimi duk basu isa su sanya ta jin kanta a matsayin ita É—in wata bace.

Number ta Umman ta kira, bayan mun gaisa ne take sanar dani yan da sukayi da Ammi.

Nima kunya ma sai ta kama ni, rabona da Ammin tin ranar rabuwar mu da Sir Salim É—in.

Allah sarki Ammi, kenan ita bata yi fushi ba? Kenan ta fahimce mu? GyaÉ—a kai kawai na shiga yi, ina yi ma Umman godiya, sannan ta gargaÉ—e ni da in lissafa kaÉ—an, domin anan Alhaji ne yace zaiyi komai, kada yaga kaman mun raina abunda yayi mana ne É—in.

Taso tayi mani maganar zama na gidan tare dasu sai ta share, koma miye Hajiya Kubran ke shiryawa, da izinin Allah zai koma alkhairi ne, in ma domin ta ƙuntata mani ne, Allah yana kallon zukatan kowa, bama nufin su da sharri, insha Allahu ba zasu iya cutar damu ɗin ba.


Kiran na Umma na katse wa kiran Ya Ameen ya shigo.

Bansan na saki murmushi ba, har saida ta kusa katse wa sannan na É—aga, wai ni irin jan ajin nan na mata.

Duk da yanzu na yarda ma kaina cewa ashe tsundum na faÉ—a soyayyar Ya Ameen É—in, ashe da cen wauta nakeyi ba soyayya nakeyi da Sir Salim ba? Wasan yara ne nake mashi.

Ashe haka soyayyar take? Akai akai ni kaɗai na kan saki murmushi, wani lokacin har ƴar dariya nakeyi, idan na dinga tunano lokutta mabanbanta, lokacin da na suma a lambu ya ɗauko ni, da lokacin da naji wani abu na bina a bayan gida na faɗa mashi, da lokacin da ya shigo ɗakin ya tadda ni ina neman warin ɗan kunne na. Da lokacin da Umma bata lafiya naje na ruƙunƙume shi.

To dama wai cen ina sonshi ne? Ko kuma yanzu ne na fara, yanda nake ji a kanshi zuwa yanzu kaman na shekaru ina sonshi.

Na saki jiki dashi, dan dai ina jin kunyar shi yanzu sosai, wasu kalmomn da yake faÉ—a lokutta da dama, sai inga kaman ba shine ba, sai inga kaman ba daga bakin shi maganar ke futowa ba.

Sallama yakeyi, yayin da ni kuma na faɗa shauƙin tunanin soyayya.

"My wife kina ji na kuwa?"

Ya faÉ—a a hankali.

Kaman ince ka kira ni video yaya, sai kuma na share, ya zuwa yanzu ba abunda nake marari da muradin gani kaman Fuskar Yayan nawa, kuma mai shirin zama miji na nan gaba, zuwa lokaci ƙanƙani.

"Eh yaya, ina jinka, ina yini ya gida?"

"Lafiya lau ya karatu my sweet?" ya faÉ—a, yana mai mirginawa ya kuma matse filon dake hannun shi rungume.

"Alhamdulillah, gashi zamu fara exam, nan da sati mai zamu iya gamawa" na faÉ—a nima a hankali, cikin muryar da budurwa kan yi ga saurayin ta, ni kaina har mamakin kaina nakeyi, yanda na cenza lokaci guda, nice wai har nake sirara murya ta, ga ya Ameen É—in, harda kashe murya duk domin yaji daÉ—i, lallai ma ni Suhan.

"Wow my hrt, Allah ya bada Sa'a, kiyi karatu sosai kinji dear"

"OK dear insha Allah"

ÆŠan murmushi ya saki, jin har ta fara cenza mashi suna, hmm Suhan ma kenan, nan gaba yana da tabbacin sai ta rasa sunan ma da zata kira shi dashi, domin duk ta riga ta faÉ—e su a gareshi.

"Albishir na kira ki in maki my Janam"

ÆŠan murmushi na saki, ina mai cewa "To Yaya ina sauraren ka"

"Menene tukuici na?". Ya faÉ—a kai tsaye, cikin sake sakin murmushi.

"Me kake so?"

"a'a dear kada ki ce haka, ba zaki iya bani ba"

"ka wuce komai a wuri na yaya" na faÉ—a ina mai kallon zoben da shine ya saka mani da kanshi a É—an yasan nawa.

"OK shikenan tinda kince haka, I want deep Kiss"

ÆŠan zaro ido nayi, ina mai É—auke wayar daga kunne na.

Ƙit naji ya katse, sai gashi kuma ya sake kira ta video.

Duk da ina son ganin nashi, Amman Kunyar shi ta baibaye ni, haka na É—aga a hankali ina mai sanya hannu na na rufe fuskar tawa.

" Look at ne dear, ke kika ce fa zaki iya, oya ina sauraren ki kiyi mani"

Ya faÉ—a yana mai lumshe idon shi da suke É—auke da Zara zaran gashin ido.

Maimakon Kiss

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login