Showing 57001 words to 60000 words out of 247770 words
bisa, gami da juyawa da niyyar komawa cikin ɗakin yana cewa "Ki turo mun Nihal ɗin"
Da kallo ta bishi ta baya har ya shige ɗakin nashi, ajiyar zuciya ta sauke, dama haka Al'ameen ɗin yake? Lallai dole ne ta sake taku, wannan ai kalar nasu ne, ko ba zai aure ta ba, lallai dole ne ta ɗanɗana zumar shi, zata san yanda tayi ta jawo hankalin shi gareta, saidai ita kanta ta san da wuya, da wahala, domin a yanda ta ganshi ba zai yi wasa ba ko ya ɗauki wargi, ƙafafunta ta ja gami da barin sashe tana ta saƙa mugun nufi da mugu nƙuduri akan bawan Allah Al'ameen.
Har ɗaki Nihal ɗin ta tadda shi, kwance yake ba bacci yake ba Amman idanun shi a kulle suke, ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa, sannan ya shiga balbake ta da faɗan, ya sanya tayi mashi abu, ta sanya wata ƙazama cen ta kawo mashi Abunda zai ci, mamakin shi take yi, ai ita a sanin ta yana cin abun hannun ƴan aiki, tinda yana cin na Suhan da mama Maryamar.
Katseta yayi daga tinanin da take yi, "dole ki amshi hukuncin, gobe in Allah ya kai mu ki tabbatas kin gyara mani sashe na tsab, kaman yanda kika ga Suhan nayi mashi, bana son ƙazanta, baƙi zanyi cikin satin nan zaki iya tafiya"
Juyawa tayi tana kumbura baki, har ga Allah in har Yayan nasu na ƙasa yana takura masu, ya sanya sun dawo ƙasar kuma yana neman ya sanya su wahala?
Aikin gyaran wannan sashen ai ba ƙaramar wahala bane, ita da ko toiket ɗinta bata iya wankewa, yanzu saidai ta sanya Maree tayi mata, duk da bawai ta gansu da tsaftar mareen ba kaman suhana, zuciyar ta na raya mata ta sanya Maree ta gyara mashi, wani sashe na zuciyar nan kwabar ta, tabbas zai iya ganewa ba ita tayi ba, inko hakan ta faru ta kaɗe har buzunta, ba zasu rabu ta daɗi ba, ɗan guntun murmushi tayi, mafita da ta samo, ai yace irin yanda Suhan keyi ko? To ba matsala, ai Suhan ɗin ce ma zata yi maka yaya sha kuruminka, tinda aikin nata kake so. Da haka har ta isa sashen nasu, tana labarta ma Saudat ɗin yanda sukayi da yayan nasu, murmushi kawai saudat ɗin tayi gami da cewa "gara ki sanya ta tayi shegiyar, kinga yanzu daga dawowar mu har ta janye Hafsy, ai wannan yarinya wallahi akwai mayya". (😝😝 kunji fa readers ashe sun damu hda hafsat ɗin🤔)
********************
Bacci yake son yi, saidai yunwa ta ishe shi, gashi bai jin zai iya cin abinda yarinya ta kawo mashi, miƙewa yayi a hankali ya isa kitchen ɗin da yake mallakin shi, kaman wata macen, fridge ya buɗe ya ɗauko lemo kwali da ceramic cups ya fito, kai tsaye bedroom ɗin ya koma gefen gado ya zauna, gami da tsiyaya lemon ya sha, kaman wanda aka yi ma dole.
Wayar shi ce tayi tsuwwa, alamar saƙo ya shigo, share ta yayi ya cigaba da shan lemon shi har ya gama, gami da miƙewa ya maida kitchen, ya dawo daƙin gami da saisaita ƙarfin Ac ɗin dake aiki cikin ɗakin.
Gadon nashi ya haye, tare da jan lallausan bargon nashi ya rufe ƙafafun nashi ruf, wayar shi ya jawo gami da maida ta sylent, har zai ajiye sai kuma ya lura da ɗan akwatin saƙo da yake cen sama wayar a maƙale.
Cikin kasala ya buɗe, yayi mamakin ganin sunan ta ɓaro ɓaro a wayar, bai ƙara shan mamaki ba har saida ya karanta Abunda saƙon ya ƙunsa, karantawa yayi ya sake maimaitawa, ita ɗin ce kuwa? Zaune ya miƙe bisa gadon, gami da jan bayan shi ya jingina shi jikin lallausan tissue foam ɗin dake jikin wood ɗin gadon. Sake dai maimaitawa yayi, lallai ita ce ta turo idanun shi ba gizo suke yi mashi ba.
Hannu ya sanya gami da ɗan yin typing a hankali ya maida mata reply, unlight ɗin wayar yayi, gami da tura ta ƙarƙashin fillow.
Zamewa yayi ya kwanta idanun shi a lumshe, zuciyar shi na ta kai komon karanta saƙon nata, su kansu idanun nashi sun gaza dena nuno mashi hoton Rubutun, tiryan tiryan yake karanta shi cikin idanun shi, kaman yana kallon scream ɗin wayar ne, a hankali bacci mai nauyi ya kwashe shi.
Niko da muke cen ɗakin mu mun bararraje muna ta fira da Hafsy, ko ba komai dai Naji sauƙin kaɗai ci yau, na samu aboki yar fira, tana ta bani labarin tafiyar su, ina ji daman nice ace yau na ganni a ƙasashe ƙetare, mu biyu ne cikin ɗaki, domin umma ta ta fice ƙofar ɗaki gami da shimfiɗa tabarma ta zauna tana yanke farce.
Sabuwar waya ta ce ta ɗauki tsuwwa, alamar shigowar saƙo, hannu na sanya gmi da jawo wayar, na buɗa. Cikin ƙwalalo idanu nake kallon wayar, hakan ce ta jawo hankalin hafsat ta tashi zaune tana tambaya ta ko lafiya?
"ina fa lafiya Hafsy?" na faɗa bayan na gama karanta Abunda ta ta tura da shi kuma wanda ya turo.
"To menene a ciki Suhan? Naga ai godiya kawai nayi ba wani abu ba, menene na damuwa, shima ko kinji yace wani abu ne?" ta faɗa bayan ta amshi wayar ta karanta reply ɗin da yayo.
"A'a Amman ni kin sa har na fara jin kunya, waɗannan kalama ai irin naku ne na masoya hafsat, kada fa ki sanya yayi tsammnin wani abu" na faɗa hankali na aɗan tashe, har ga Allah kunya duk tabi ta baibaye ni, kaman ina gaban shi, sai yanzu nayi na damar barin ta ta tura Abunda ta rubuta ba tare da na amsa na karanta ba.
"kinga karki wani damu kanki Suhanan umma, ki kwantar da hankalin ki Yayan namu wayayye ne ba zai kawo ma ranshi komai ba akasin Abunda aka rubuta"
Ta faɗa cikin son ƙarfafa man guiwa, Nidai lafewa nayi jikin bango ina sauke ƴar ƙaramar ajiyar zuciya, gami da ce mata "To Hafsat Allah ya sanya"
~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~21~*
*Ina ma ɗaukacin Al'ummar musulmi barka da shigowa sabuwar shekara a musulunci, Albarka dake ciki Allah ya sada mu da ita, sharri da tsautsayin da yake ciki, Allah yayi mana tsari dashi Albarkacin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
_Assalamu Alaikum, Yaya ina yini, ya gida da aiki? Ya fama da jama'a? Ina fatan komai lafiya, na rubuto in maka godiya da abun arziƙi da alkhairi da kaman, bani da bakin godiya a gareka, irin kyakkyawar kulawa da kake bani, i do appreciate Yaya, Allah ya ƙara arziƙi da wadata_
Ya kai sau biyu kenan ina ƙara maimaita karanta saƙon da Hafsat ɗin ta rubuta ta tura mashi, ina hango rashin dacewar kalaman, idanun a kaman zasu faɗo ƙasa saboda yanda na ƙura ma scream ɗin idanu, kunya tana baibaye dani, gashi dai tini hafsat ɗin ta fice taje ta kwaso kayan ta, Amman duk kina nake yi wani iri, a hankali idanun a suka kai ƙasa kan nashi saƙon da ya maido tin bayan tura saƙon da mintoci kaɗan
_OK ba damuwa, Ameen_
Iya abunda ya rubuta kenan, sai nake ƙara ganin rashin dacewar hakan, fata na dai ace baiyi mani wata fahimta daban da.
Tare da Hafsat ɗin muka kwana a ɗakin mu, wanda saidai umma ta shimfiɗa tabarma gefe cen ƙasa tiles ta kwanta, ta bar mana katifar.
Yau mun hutar da umman tawa, ni da hafsat muka yi komai muka kammala har abun kari, sannan muka yi wanke wanke a cen gefen ƙofar ɗakin namu, kallo ake ta binmu dashi sauran ma'aikatan wasu na zunɗen mu da baki, mu dai bamu damu ba, harkar gabanmu kawai mukeyi.
Hafsat ɗin na kula dasu, shaye da mamaki ta kalle ni lokacin da muka gama wanka muka zauna zaman shafa, "Suhan wai dama haka ma'aikatan gidan nan suke yi maku ke da umma?" ta faɗa mamaki fal a fuskar ta. "Eh nace, ina mai basar da zancen, saboda umma ta bata so ake zancen su. Girgiza kai kawai tayi gami da cewa" Allah shi kyauta" daga haka itama ta ja bakin ta ta kulle lura da tayi Suhan bata son maganar tasu.
Muna cikin shafar ne Naji waya ta tayi ƙara a hankali na jawo gami da dubawa, saƙon nihal ne take sanar dani wai inje in gyara ma yaya ameen ɗakin shi, in turo hafsat ta amsar mani makulli.
Cikin tsantsar mamaki na kai kallo na kan umma ta, aiko ta ƙure ni da idanu alamar tana neman ƙarin bayani.
Sanar da ita nayi saƙon, sannan na ƙara da cewa, umma ina ce an dakatar damu aikin gidan, me zai sanya ba zata sanya maree taje tayi mashi ba?" kuma umma........, shiiiit🤫 ta dakatar dani, gami da cewa" Suhan bana son Abunda zai kawo tashin hankali, Hafsat je ki amso makullin ki kawo mata, kije ki taya ta ku gyara mashi ɗakin, ai ba wani abu bane don kin gyara mashi, yaron da yake mana alkhairi ai ba zamu ji kyashin kyautata mashi ba"
"Haka ne umma" cewar Hafsat da ta miƙe tana ficewa zuwa Amso makullin.
Umman tawa ce ta maida kallon ta gareni, sadda kaina nayi ƙasa, ni fa har ga Allah bana son Abunda zai ke haɗa ni dashi, masalan ma yanzu da afnan ta rubuta mashi wannan text ɗin, umman ce ta katse man tinanin da nake yi gami da cewa
"Suhan ki kula fa, kinga Hafsat ƴar'uwarsu ce ba zata ji daɗi ba idan taga kaman bama son kyautata masu, ita ba lallai ta fahimci komai ba, ki saki ranki, kije ki gyara mashi, yafi gaban nan a wajen mu, shine ya zame mana kaman uba yanzu, ni na san Alfarmar shi ce ko zaman da mukeyi a gidan nan"
Jikina yayi sanyi ƙalau, lallai gaskiyar umma ta kuma, dole zan ajiye kunyar in gyara mashi ɗakin nashi, wannan ne kawai Abunda zanyi in faranta ranshi ko dan in biya kaɗan daga cikin Abunda yake yi mana.
Shigowar Hafsat ce ta katse mana maganar da muke, miƙewa nayi gami da zira hijabina. Tare muka ɗunguma zuwa sashen Ya Ameen ɗin muna tafe muna firar mu gwanin sha'awa kaman wasu ƴan uwa ko ƙawaye.
Santin sashen Hafsat ta shiga yi, lallai ya ameen ɗin daban yake, watau sashen ma ko datti baiyi ba sosai, ba don ma shi ɗin mai tsafta bane, kaman yanda sauran maza suke, ai da ba sai ma an tsaya ɓata lokacin gyaran ɗakin ba, komai tsaf yake a ajiye a muhalli shi, kaman Wancen gyaran da na taɓa yi mashi, da alama dai ya kula da mazaunin komai ne ya sanya yanzu yake kula wajen misplacement ɗinshi.
Hafsat na bari ta gyara falon, yayin da ni kuma na shige bedroom na shiga gyara, hai bathroom duk saida na gyara, na kwal kwale komai tsaf, ko kafin in fito har ta gyaro har kitchen komai tsaf, room freshner na fesa, gami da sakin Ac a hankali a hankali.
Jawo ɗakin muka yi, har yanzu Hafsat bata dena santi ba, ga dukkan alamu Ya ameen ɗin mutumenta ne, sai yaba kirki da halin kwarae nashi take yi, anan ne take faɗa man irin taimakon da yake yi masu cen gidan nasu, dama duka mutanen garin kankiya, duk mai buƙata shi yake nema kai tsaye, kuma baya gazawa wajen taimaka masu bil haƙƙi da gaskiya.
*************
Tsaye yake tsakiyar ɗakin hannuwa shi duka biyu soke a aljihun farin yadin da yake jikin shi an yi mashi ɗinkin osimbanjo, yayi matuƙar kyau, masalan yau da ya kafa hular dara a bisa kanshi, saboda ja ce sai ta ƙara ƙawata fuskar tashi, ko ina na sashen yake bi a hankali, a hankali. Tabbas wannan gyaran ya san ba na Nihal bane.
"Suhan" zuciyar shi ta raya mashi, Amman As How? Ya tambayi kanshi cikin zuciya, "Huh, any way" ya faɗa a fili, yana sauke ajiyar zuciya, gami da kaɗa kai a hankali ya nufi bedroom ɗin.
Mamaki ya kama shi, kanshi ya kulle, a hankali ya isa ga gadon da yaji bedsheet yayi limui, zama yayi gefen gadon yana mai mamakin irin gyaran da yarinyar ta iya, kaman inji, Alwala yake son yi, hakan ce ta sanya shi miƙewa gami da isa toilet ɗin.
Alwala ya ɗaura, ji yake kaman kada ya fita a toilet ɗin, ɗan ƙaramin showel ya ɗauko yana mai tsane fuskar shi hannuwa shi da suke lulluɓe da gashi luf luf dasu. Idanun shi ne suka kai kan wani abu dake cen gefe yade yana ta ɗaukar idanu.
Hannu ya sanya gami da ɗauko wa, ɗan kunne ne mai matuƙar kyau da tsada, tsohon abun kunne ne, da ko wajen siyar dashi yake da daraja, mai ruwan gold, sai sheƙi yake yi, ɗan murmushi yayi na gefen baki, kallo ɗaya yayi mashi ya gane ba gold bane, saboda yana da katafaren shagon siyar da gold da changin kuɗaɗen ƙetare.
"Nata ne" yaji wani ɓari na zuciyar shi yana sanar dashi, saidai tayaya zai bata ɗan kunnen ta? Fitowa yayi dashi a hannun shi riƙe yana mai jujjuya shi, a aljihun wandon shi ya saka shi, da niyyar idan ya fito ya haɗu da ita a harabar gidan ya bata ko ya tura mudi ya kai mata, sallar da yaji an tada ce ta sanya shi hanzari ficewa daga gidan baki ɗaya zuwa masallacin f
Ban tashi gane ɗan kunnen baya kunne na ba, har saida naje cire wa zanyi wankan rana, sake laluba wa nayi, still dai baya kunnen, bayan na fito ne a wankan na dudduba ɗakin baya nan, sai lokacin na tambayi Hafsat da take zaune tana cin abinci, Abunda ke bani mamaki har kawo yanzu babu wanda ya damu da zaman hafsat ɗin sashen namu kaman yanda aka yi ma afnan lokacin da tazo.
"Ban ganshi ba kuwa Suhan gsky, Amman tin lokacin da kika cire hijab ɗinki naga ba ɗan kunnen a kunnen ki, anya kuwa kin sanya shi kafin mu fita?"
Hafsat ɗin ta bani amsa, ta ƙara she da jefo man tambaya,
"Aikuwa tabbas na sanya shi a kunne na, Allah dai ya sanya ba cen sashen na yaddo shi ba, kinsan kuwa wannan ɗan kunnen ya daɗe, umma ta tace tin irin na da ɗin nan ne, itama gadon shi tayi. Shiyasa ma bana fidda shi a kunne na, sai in zanyi bacci kawai" na ƙara she ina mai dafe ƙirji alamar ƙirjina ya faɗi.
Shigowar umma ce ta sanya na wayance tare da yima Hafsat alama da tayi shiru, aiko ta ja bakin ta ta tsuke, saidai da umman tawa ta kula zata gane alamun rashin gaskiya a tare damu.
Tinani na shiga yi ta yanda zan bi in samu ɗan kunnen ya dawo gareni ba tare da umma ta kula ba, gashi an mayar ma Nihal ɗin da makullin, kenan ba damar in koma ba tare da kowa ya kula ba in ɗauka, kuma ko ba haka ba ma ina zullumi zuwa ya kasance yana sashen nashi.
Hafsat ce take sanar dani in shirya zan raka ta siyayya anjima idan anyi sallar la'asar, da to na bita a zahiri, cen kau cikin zuciya ina ta laluben hanyar da zan bi abun kunne na umma ya dawo gareni.
Daga masallaci bai dawo gidan ba wuce wa yayi wajen harkokin shi, ya manta da bai kulle ɗakin ba shaf, abu ne mai muhimmanci ya taso mashi.
Ganin ana ta salla a masallacin gidan namu, ya sanya ni tinanin zuwa ɗakin nashi, da yanzu nake tunanin ma mallakin ɗakin baya ciki in ma har yana gidan to lallai yana masallaci.
Fakaitar idanun kowa nayi, da hafsat muka shirya ko zata kula da umma kada ta gane bana nan, zata ɗauke hankalin ta.
Cikin sa'a kuwa na tadda part ɗin a buɗe ɗan murɗawa nayi a hankali na tura na shiga ina ɗan waige waige.
Fara dubawa nayi ko ina ban gan shi ba, dama na san bani ce nayi aikin falon ba, ya sanya kaɗan kaɗan na duba falon na wuce kai tsaye zuwa bedroom ɗin.
Sai dai me duka ko ina na duba bangani ba, har toilet, bashi ba alamar shi, hankali na in yayi dubu ya tashi, Sam duk na firgice ko ganin kirki bana yi nice leƙa hada ƙarƙashin gado.
Gadon na haye baki ɗaya, gami da yaye zanen gadon🤣🤣 duk cikin nema ne, ina tinanin ko ya faɗa ta bayan gadon, nan ma ban ganshi ba, jawo gadon na shiga yi, da yake gado ne irin mai tayoyin nan, aiko ba wahala na jawo shi, katifar na shiga ɗagawa cikin hanzari, gudu nake mai ɗakin ya dawo ya iske ni.
Al'ameen da yake bakin ƙofa tsaye tin bayan shigar ta ɗakin nata ya shigo, da mamaki sama fuskar shi lokacin da ya jiyo motsi a ta bedroom ɗin nashi, a hankali ya shiga takawa har zuwa buɗe ƙofar.
Da yake bata da ƙara ya sanya Sam bata ji ba, duk ta haɗa zufa sai aikin janyo gado take yi, ɗakin nan fa tayi mashi watsa watsa, hatta da bedsheet ɗin bisa side drower ta ɗora shi, filaluwan kuwa da katifar duk ta jingina su jikin wardroop ɗin tana ta faman leƙawa cen ƙasa gadon ko zata hango shi, da yake da zata gyara har gadon ta ɗaga ta sharo, sai tayi