Showing 78001 words to 81000 words out of 247770 words
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~27~*
*Page ɗinki ne Aishatu Babayo, muna matuƙar yinki, kuma muna jin daɗin comment ɗinki matuƙa, ɗaukacin ƴan golden pen suna gaisheki*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
"Kasha maganin ka ne da kake ƙoƙarin fita?"
Mom ɗin tashi ta faɗa, har yanzu fuskar ta a matuƙar ɗaure take.
Gyaɗa mata kai kawai yayi, ba tare da ya tanka mata ba, kallon ta ta maida kan Bilal da yake tsaye ta bayan Al'ameen kaɗan haka, yana gaida ta.
Amsawa tayi gami da cewa" Bilal ka kula fa da abokin ka sosai, kada ka bari ya wahala Kaga dai Abunda Dr. Yace". Ɗaga mata kai Bilal ɗin ya shiga yi yana cewa "consider it done Mom"
Hafsat na tsinkayi muryar ta tana gaida ta, hakan ce tasa nima na gaishe ta, gaisuwar Hafsat ɗin kawai ta amsa, itama a daƙile, hakan ce ta sanya na ƙara shan jinin jikina gami da ƙara ɗan matsawa baya.
Afnan ce ta ruga kusa da yayan nata, daidai lokacin da Mom ɗin ta juya da niyyar barin wurin, maganar Afnan ɗince ta dakatar da ita da barin wurin da take niyyar yi.
"Yaya me ya same ka? Baka lafiya ne? Yaushe kaje hospital bamu sani ba? Duk ta jero mashi tambayoyi tana mai kamo hannuwan shi gami da dudduba jikin shi da idanu.
Ɗan zare hannun shi yayi yana mai shafo gefen fuskar ta kaɗan," Am OK Dear Love, ba Abunda ke damuna" ya faɗa yana mai juyawa ya nufi jikin motar tashi, domin ya kula sosai da rashin amsa gaisuwar da mahaifiyarshi tayi ma Suhan ɗin.
Bai jira komai ba ya buɗe motar gami da shiga, shima Bilal ɗin shiga yayi, ganin haka ne Hafsat ɗin ta shiga jan hannuna tana cewa "zo muje Suhan, Afnan ɗin zata tadda mu"
Binta na shiga yi, muka shiga tafiya, daidai lokacin da Mom ɗin ta bimu da kallon tsana da jin haushi ƙarara a fuskar ta.
Afnan ce ta bita da kallo daidai lokacin da ta juya da niyyar wucewa sashe kaka zuwaira, girgiza kanta ta shiga yi tana mai ɗaga ma yayan nata hannu har ya fice daga gidan.
Bayan an sauko masallacin ne kiran Alhaji Mustapha ya shiga wayar tashi, umurtar shi yayi da yazo gidan gonarshi yana son ganinshi yanzu shi da Bilal ɗin.
Sai da ya ɗauki hanyar gidan gonar ne, yake sheda ma Bilal ɗin kiran da dad ɗin nashi keyi masu. Har suka isa babu mai tanka ma wani.
Sun tadda falon cike da manyan mutane, sai firar su suke cikin nishaɗi, ga sanyin Ac na ratsa su, wucewa sukayi cen gefe gami da zama ƙasa domin girmamawa ga iyayen nasu.
Miƙa mashi wata kyakkyawar emvelop mai ado da ruwan gold dad ɗin yayi yana mai cewa duba nan ka gani.
Amsa yayi cikin girmamawa ya shiga dubawa, bayan ya gama karantawa ne ya miƙa ma Bilal ɗin, ya maida duban shi kan mahaifin nashi yana mai neman ƙarin bayani.
Dad ya gyara zama gami da duban yaron nashi cikin soyayya, farin ciki fal a kan fuskar shi, sannan ya cigaba da cewa"Daga sarkin Katsina ne, haɗin guiwa da sauran sarakunan yankin namu na arewa, saboda yanda kake taimakon matasa ƴan uwanka da basu ayyukan yi, da taimaka masu da jari, da koya masu sana'oi, suka ga ya dace su girmama ka domin suma sauran matasan masu hannu da shuni suyi koyi da kai, sun yanke shawarar naɗa ka sarautar *yariman matasan arewa* kuma suna buƙatar daga yau zuwa gobe ka shirya komai domin a goben ne zasuyi maka naɗin bayan kammala ɗaurin aure, sannan kuma akwai hawan daba bayan kammala lunching ƙarfe biyar na yamma, da fatan zaku je ku shisshirya komai da ake da buƙata, sannan inaso ka aika manyan motoci guda biyu Katsina da zasu kwaso iyayen matar Aleeyu tin da safe idan Allah ya kai mana ranmu sai su juyo dasu, sannan ina so ka tabbatar da cewa an gama tsara komai na wurin da za'ayi lunching ɗin, akwai manyan mutane da zasu halarta harda shugaban ƙasa da sarkin musulmai, sannan muna da baƙi da zasu fara isowa a yau ɗinnan muna so a kama hotel mai kyau da zasu ji daɗin zama saboda mutanen waje ne"
Ya faɗa yana nazarin yaran nashi guda biyu da suke durƙushe gaban shi.
Fara'ar dake fuskar Bilal zamu iya cewa ma tafi ta kan fuskar Ya Ameen ɗin, wannan ai wata ɗauka ka ce da Allah yayi ma abokin nashi, ko ba komai dai ya san ayyukan Alkhairin da abokin nashi keyi ya zaga dukkan sassan nigeria ba ma arewa kaɗai ba.
Cikin matuƙar jin daɗi suka shiga yin godiya basu fita ba saida dad ɗin nasu ya sallame su, shi fa Al'ameen mamaki kawai yake yi, a ina manyan ƙasar nasu suka san da duk abubuwan da yake yi, bai ƙara sarewa ba saida yaji ana sanarwar naɗin nashi da za'ayi a gobe idan Allah ya kai mu, a hanyar su ta komawa gida.
Sun isa gidan ne, sannan suka kira mudi driver gami da bashi makullin gare jin nasu dake cen gefen gidan gami da umurtar shi da ya fiddo manyan mitocin nan ƙirar homa bomber ya bada a wanke su ɗauki hanyar Katsinan a yanzu nan.
Ficewa suka sake yi daga gidan, saboda gidan ya ƙara ɗinkewa da jama'a ta ko'ina duk mata ne ga wasu manya manyan canofee da ake ta kakkafawa a harabar gidan gefe guda kuma wasu manyan speakers ne aka kakkafa kaman za'a tashi gidan.
"yanzu ina muka dosa ne? Ni fa wallahi duk ma na rasa ta ina zamu fara, kayan da nayi niyyar Sanyawa yanzu dole in cenza su in nemi masu babbar riga, duk yanda kuwa nake gudun ta saboda zafin nan da akeyi"
Al'ameen ya faɗa yana mai kallon Bilal ɗin da hankalin shi yake kan tuƙin da yake yi.
"Ni na san ta ina zamu fara, kai dai kayi kallo kawai" ya faɗa da ƴar Fara'ar shi, mamakin abun har yanzu bai gama sakinsu ba.
Da kallo ya shiga binnhanyar da suke bi har kawo lokacin da sukayi parking daidai wani tanƙamemen shago an rubuta *Your Choice* a jiki.
Je rawa sukayi har cikin shagon da aka ƙawata shi da farin glassai suna ta ɗaukar idanu.
Kaya ne maƙilbiya kallon ka, shaddoji ne ƴan ubansu an masu ɗinku a irin na manya, sun sha aiki matuƙa, kowacce tare da hula tangaras kalar zaren aikin shaddar, gefe guda kuma ƙananan kaya ne iya kallon ka da hange ka, yayin da sashe guda na shagon kuma bugaggun takalma ne kalar na sarakai da manyan masu kuɗi.
Miƙewa mai shagon yayi gami da tarar su cikin farin ciki, domin ya daɗe da sanin Al'ameen ɗin tin ba yanzu ba, hasali ma Al'ameen ɗin shine ya fara bashi jari a rayuwar shi, bayan ya gama makarantar design da Al'ameen ɗin ya buɗe tin yana ƙasar america.
Gaishesu ya shiga yi cikin girmamawa, basu ɓata lokaci ba Bilal ɗin ya faɗa mashi me yake tafe dasu, da taimakon shi suka zaɓi kayan da suke so.
Shaddoji ne farare ƙal suka ɗ auka, duk da cewa ta Al'ameen tafi haɗuwa, sai ƙamshi take yi da walwali, anyi mata aiki da riyal blue ɗin zare, yayin da hular ma take kalar royal blue ɗin, sai takalmin shi irin na sarauta mai half cover da lanƙwasa ya sha adon farare duwatsu sai ɗaukar idanu yake yi.
Shima Bilal ɗin ya zaɓi masu kyau, saidai shi kuma kalar nashi farar shadda ce da aikin Brown, hakan ne ya sanya shi ɗaukar takalmi Brown masu matuƙar kyau da tsari, sai Abie da suka ɗaukar ma kalar sararin samaniya da aikin bula mai ruwan omo.
Sashen masu haɗewa aka miƙa kayan, daidai jikin su aka auna sannan aka haɗe, Al'ameen ɗinne mai cewa a maida mashi babbar rigar fitted yayin da Bilal ɗin ke cewa a ƙyale shi ayi mashi yanda zata yi kyau.
Su sha mamaki matuƙa lokacin da suka zo biyan kuɗin yace ba zai amsa ba, ba yanda ba suyi ba yace Sam Allah ya sauwaƙe ya amshi kuɗin su, ganin ba zasu yarda ba ya sanya shi faɗin bari ya gaya masu dalilin shi na ƙin amsar kuɗin nasu.
Tiryan Tiryan ya basu labarin Alkhairin da Al'ameen ɗin yayi mashi, sannan ya ƙara da faɗin "Haba yallaɓai, ni wane irin butulu ne kuwa da har zan iya amsar kuɗin kaya a hannun ka? Bayan dukkan shagon nan da yanda na zama a rayuwa kai ne sila, yanzu haka ƙanena yana aiki a kamfanin ka na sarrafa hatsi a Lagos, dama ban daɗe da gama sauraren radio ba, Naji irin gagarumin naɗin da za'ayi maka a goben idan Allah ya kai mu, bansan zaka zo ba i da har gida zan kawo maka da kaina, Amman ko yanzu bata ɓaci ba, insha Allah kuwa zan halarta harda iyali na baki ɗaya, Mungode Mungode Allah ya shirya maka zuri'abyasa ka gama da iyayen ka lafiya"
Ko ba komai wannan kaɗai ya isa ya ƙara sanya shi farin ciki, ashe dai shi alkhairi ko ya yake baya da kaɗan kuma daɗi ke gareshi, gashi Alkhairin da yayi ma mata san a lokacin da aka yaye su, har shi ya girbi abinda ya shuka.
Sun mashi godiya matuƙa, yayin da Al'ameen ɗin ya bashi ƙaton shi, gami da cewa bayan hidima ta kwaranye ya neme shi su sake gaisa wa sosai, har bakin motar su ya raka su, yana mai ɗaga masu hannu har suka fice daga plazar, sannan ya juya da maɗaukakin farin ciki, dama tini ya daɗe yana addu' ar Allah ya haɗa shi da Al'ameen ɗin ko a hanya ne ya ƙara mashi godiya, domin ya san ba lallai bane in ya neme shi ya same shi.
Daganan suka zarce kasuwa, inda suka shiga neman kayan kwalliyar doki, da ƙyar suka samu, domin har Al'ameen ya gaji har ya fara faɗin su koma gida hakanan shi fa ya fara gajiya da wannan wahalar sannan suna da sauran ayyukan da zasu aiwatar da yawa kafin zuwan daren.
Kalar kayansu kowa ya ɗauka, sun kwaso kayan kwalliya doki sosai, bayan da Bilal ɗin ya tambayi abokin nashi dokin da zai hau, "Farar Goɗiyar" ya bashi amsa a taƙaice cikin gajiyawa.
Ɗan murmushi yayi shi kuma yana faɗin "sai in hau gwaska ni, shi kuma Abie ya hau kule"
Bai tanka mashi ba har suka iso gidan, Barde mai tsaron barar suka kira gami da bashi kayan dokin suna faɗin ya shirya su goben bayan gama cin abincin ɗaurin auren, sannan suka faɗa mashi dawaman da zasuyi amfani dasu a cikin dawakan dake gidan.
Saida suka ajiye kayan sannan suka watsa ruwa gami da cenza kayan jikin su zuwa ƙananan kaya sannan suka fice daga cikin gidan bayan sun ajiye motar suka cenza wata.
Ganin yau bamu da aikin komai, ya sanya mu kwanciya muka huta bayan mun ware duk Abunda muka san zamuyi amfani dashi gobe, to bamu da yawa dama, mu bakwai ne harda amaryar sai mai kwalliyar mu da suka taho ta ita tinda ga Katsinan yasa muka kama mu takwas, ɗaki ne tanƙameme da toilet, bamu takura ba sosai komai namu tsaf yake, kaka zuwaira kaɗai muka fita muka gaida yau sai hafsat ɗin da taje Sashen mamanta, cen ta tadda ummata har take tambayar ta ina ina? Take ce mata ina ɗaki lafiya ta lau.
Washegari tin da asubar fari aka farka kusan ince dukka gidan, bayan gama sallah ne aka shiga ɗora Abunda za'a karya, tinda dugu-dugu aka yi break fast, sai kuma aka shiga hidima wanka, masu girka abinci nayi masu sake shirya harabar gida inda za'ayi zaman cin abinci nayi.
Mu dai bamu tashi ba sai wajen ƙarfe takwas na safe, mun tadda an kawo mana kayan karin mu, hakan yasa saida muka gama wanka duka sannan muka zauna zaman karyawa, amarya aka fara shirya mawa, mai kwalliya ta hau aikin ta na cakare amaryar, yayi da muku a muka hau gyara ɗakin namu tsaf.
Tin da aka fara hidimar biki banga afnan ɗin taje sashen nasu ba, Sam ta fita harkar su kaman ba ƴan uwanta ba, koda yake hali ya bambanta Shiyasa basa shiri, Amman da yake halin na Saudat da Nihal ɗin ɗaya ne gashi nan kansu a haɗe yake kaman ƴan biyu, saidai wani lokacin aunty Feena kan aiko mata da Nasreem da Ayan masalan ma in tana wata hidimar da yake ita a ɗaki ta ta sauka da yake cikin babban sashen gidan inda aka sauki ƴan uwa Hajiya Kubran.
Dama tini ta maido kayan ta kaf da ta san zata yi amfani dasu cikin hidimar bikin.
Mun gama gyaran kenan muna hutawa wata ƴar matashiya budurwa tayi sallama, yaran dangin hajiya kubran ne, da suke cike da jiji da kai da tinƙahon su ɗin wasu ne, babu wanda ta gaida ta shiga faɗin "wacece suhan wai? To taje Aunty Saudat na kiranta a ɗakin nasu" tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta tsaya jin me za'a faɗa ba.
Tinawa da wulaƙanci da sukayi mani shekaranjiya ne ya sanya ni zamana ba tare da na raya ma raina zuwa ba, har aka gama ma Hafsat ɗin kwalliyarta aka fara ma Afnan da tace lallai sai an fara yi mani ai ina gaba da ita, kuma nice babbar ƙawa, daƙyal dai ta haƙura aka fara mata, ganin yanda nakafe sai an gama mata sannan za'ayi mani.
Ba sallama saidai muka ganta tsulum cikin ɗakin.
Da matuƙar fushi ta maida kallon ta a kaina, bayan tabo kowa dake cikin ɗakin da kallon baku isa ba.
"Dame kike taƙama ne da har zamu sanya a kira ki kiƙi zuwa? Ta jefo man tambaya, Afnan ce riƙe da ƙugu ba'i na cin ta cikin zuciya, ko kallon inda take banyi ba, haka in bangon dake ɗakin ya tanka mata tau nima na tanka mata.
Hakan yayi bala'i ƙona mata rai kuwa, cikin hasala tace
"Aikin mu anan gidan shine aikin ki, kuma a ƙarƙashin Alfarmar Ya Ameen kuke zaune acikin gidan nan, sannan ina so ne in faɗa maki cewa ke baki kai matsayi da har mu zamu ce ga Abunda mukeso kiyi mana ba ki ƙiya, kuma ba zaki taɓa kai matsayi ba, kwaɗayayyun banza da wofi, ke da waccen sululu kasa ɗin uwar taki..... "
*" Aunty Nihal ya isa"*
*"Ya Isa Hakanan, in ba haka ba wallahi zanje na faɗa ma Ya Ameen ɗin"*
Afnan ce take dakatar da ita cikin ƴar tsawa, ranta in ya kai dubu tau ya ɓaci, bata ma san ta ƙwace fuskar taba daga kwalliyar da akeyi mata, ni kau tini fuska ta ta jiƙe da ruwan hawaye, ji nake kaman ƙjrji na zai tsage zuciya ta ta fito.
Wannan cin fuska yayi yawa, gaban ƙawayen Hafsat da basu san ko ni ɗin wacece ba ta biyo ni nan tana ƙasƙantar dani, tini na ruahe da kuka mai sauti, domin ina jin in har banyi ba zuciya ta zata iya bugawa, Hafsat ɗince ta ƙara so wajen da nake zaune bisa gado bansan lokacin da na tashi zaunen ba.
Bubbuga baya na ta shiga yi, ganin haka ne ya sanya ni rungume ta, Allah ma yaso bata kai ga sanya kaya ta ba, da tini zan cukuikuye su, iri. Daƙumar da nayi mata.
Ita kau Nihal jin hakan da tayi ya sanya ta ficewa tana mai saukin maganganu masu zafi a kaina da umma ta, Afnan ɗince ta miƙe gami da ƙarasowa inda nake ta shiga bani haƙuri, gami da cewa "Bari inzo, ai sai na faɗa ma Yayan tinda su dai basa son zaman lafiya"
Nice na riƙo hannun ta ina mai girgiza mata kai cikin kuka, fasawa tayi gami da shiga lallashi na, daƙyar suka samu nayi shiru, babu wanda bai tausaya man ba a cikin ɗakin Allah wadai suka shiga yi ma Nihal ɗin Afnan na jinsu ƙala bata ce ba, to me zata ce ai halinka shi ake faɗi ko bayan ba ranka kuwa.
Manyan kuloli ne aka shiga shigowa dasu cikin gidan, rumfa guda aka ware da aka jejjera abinciccikan, sai ma'aikata masu serving da aka zube saidai Abunda mutum yake da buƙata a kai mashi, babu kalar nau'ikan abincin da babu acikin gidan nan, har ma da na gargajiya ga masu buƙata, kama daga su Alkubua, fankaso, waina, dambun shinkafa lafiyayye da ya sha zkgala da kayan lambu, to dama dai kowa ya san Katsina wa da wannan cimaka kuma bikin nasu ne, wannan ce ta sanya basu yada al'adar tasu ba.
Kaman yanda aka jejjera abinci cika da lemuka kala kala, haka ma acen tanƙameme hall ɗin da yake mallakin Alhaji Mustapha inda za'ayi walimar cin abincin aka har haɗa komai da taimakon su Al'ameen ɗin da Bilal, basu bar wurin ba hr saida suka ga komai ya kammala, kuma an ware ma manya iyayen ƙasa nasu ɓangaren ta inda babu ma mai ganin su, sannan suka wuce gidan domin shiryawa
Ƙarfe ɗaya ƴan Katsinan suk iso iyayen khadeejar Yaya Aleeyun da yake ma harda shi aka je ɗauko suruka nashi, ya sanya shima saidai abokanan shi ne suka taimaka mashi har haɗa komai.
Har zuwa ƙarfe ɗayan ban yadda anyi mani kwalliya ba, yo ni kwalliyar ma me zanyi? Saida Afnan da Hafsat ɗin suka matsa ne gami da tsoratar dani zasu gaya ma Ya Ameen ɗin Abunda ya faru to, sannan na yarda aka yi mani ƴar Light ba mai yawa ba, duk da haka nayi kyau ba laifi kam.
Kowa na ɗakin namu ya haɗe cikin ƴar ubansun ashoben yinin da ta kasance ƴar ubansu atamfa, fara ce tas sai ƴan pattern na dark blue da Orange, atamfar bata da hayaniya, hakan ce ta sanya tayi matuƙar kyau da haskawa gashi zanenta ba mai irin yawan nan bane jefi jefi ne.
Haka muka shirya cikin atamfar, Nidai kasa tashi ma nayi saboda Hafsat ce ta bada mana ɗinkin da aka yi mana, kasancewa ƴar ƙibar dake gareni ya sanya skirt