Showing 219001 words to 222000 words out of 247770 words

Chapter 74 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10438

kanta tako ƙafar tata cikin gidan, sai ya zamana cewa kaman ta rikiɗe ta sake komawa sarauniyr a idanun kowa.

Haka suka gama cin abincin suka miƙe suna mai komawa kan kujeru irin na sarautar suka zauna, jiran wannan haɗimar tazo ta maida su ga faɗar Fulanin.

Ada falon ba wani babba bane sosai, irin ginin nan ne bada, ginin ƙasa da zane zane da yake shimfiɗe da jajayen kilisai da wasu irin barguna an lilliƙa ma bangon, saɓa in yanzu da yake ginin zamani cike da ƙawa da kyau, irin na sarakan yanzu, hatta da ƙofofin gidan abun kalli ne, kai daga gani naira tayi aiki a wurin.

Basu daɗi da zama ba, sai ga haɗimar ta kuma dawowa.

Cike da girmamawa take sanar dasu akan su dawo ta maida su ga Fulanin, kaman yanda ta bata umurni.

Haka suka kuma miƙewa suka bi bayan haɗimar, har zuwa wani ɓangare na gidan inda Fulani take hakimce cen ƙuryar faɗar an ƙawata ta da kumbuna da kwallaye, irin dai faɗar da, sai hakan ya kuma Sanyawa tayi kyau fadar.

Zaune take ta kishingiɗa bisa wani tun tun, ga wasu bayi bayan ta na mata firfita cike da biyayya.

Wasu mata ne zaune suma cikin shiga irin ta manyan mata, gefe da gefen ta, watau dai sun sanya ta tsakiya, da gani dai suma matan sarki ne.

Bayi ne zazzane ana ta fadanci, kowa ya natsu wata zabiya na ta zuba ma Fulanin kirari, ita ko sai faman murmushi takeyi.

Shigarsu ce taja hankalin kowa zuwa kansu, nan fa bayan nan duk suka mimmiƙe suna masu sadda kai ga su Umman cike da girmamawa.

Da hannu Fulani tayi ma Umma nuni da wata shimfiɗe da ta cika da ƙawa, alamun dai nan ne zata zauna.

Hannun Hajiya Zainab taja suka nufi shimfidar suka zauna su biyu. Suna mai tankwashe ƙafafu su kaman yanda sauran matan sarkin sukayi.

Bayin nan ne ɗaiɗaya da ɗaiɗaya suka dinga miƙewa suna zuwa gaban su suna kwasar gaisuwa, daga haka har suka gama, sai kuma suka sanya layi suna mai ficewa daga fadar cike da biyayya.

Bayan fitar su ne, Fulani ta kuma tashi zaune, tana mai gyaran Murya.

Cike da taƙama ta fara magana.

"Waɗannan sune sauran matan mai martaba, kaman yanda yake cewa baki sa su ba, domin sai daga bayan hawan shi ne karaga ya kuma ƙara su, wanna sunan ta Sarauniya Indo, wannan kuma sarauniya Khairiyya" ta faɗa tana mai nuna su da dukkanin hannuwan ta, su kuma sai sakin murmushi suke yi cike da wani irin ya ayi da zaka iya tantance me ke cikin zukatn su.

Sai kuma ta juya ga sauran matan, tana mai nuna Umma. "Wannan ita ce Gimbiya Merama, kaman yanda kuka samu tarihin ta, nasan duk cikin ku tin kafin ma auren ku da mai martaba saida kuka samu tarihin Gimbiya, saboda haka ne nake mai sanar daku cewa Wannan dai ita ce Gimbiya mai cikakken iko a wannan masarauta"

Dukansu da kai suka gaisa, ba wadda ta iya buɗa baki tayi magana. Haka itama Umman, sai sarautar tata ta asali ta motsa.

Fulani ce ta cigaba ta cewa "Yanzu muna jiran iso ne a wurin mai martaba, ya aiko jakadiya a sanar damu cewa duk mu shirya zai aiko mu same su ƙaramar fada"

Jinjina kai suka shiga yi, ita dai Hajiya Zainab iyakar ta kallo, yau Allah ya haɗa ta da inda ake zuba tsabar mulki, watau magana ma basa iya yi ma junan nasu.

Zaman shiru ne ya biyo baya a faɗar, inda kowa da abun da yake saƙawa a cikin zuciyar shi, yayin da duk da ita umma tana cikin wani irin hali na alhinin rashin mahaifin ta, da bayan barin ta gidan Allah yayi mashi wa'adi, Amman hakan bai hana ta sakin murmushi ba, kasancewr ta yau a cikin ahalin nata.

Saidai duk zuba ido da tayi bata ga ta inda matar waziri da ahalin wazirin suka ɓullo ba, haka kuma ko a faɗa bata ganshi ba, indai ba shima ɗin Allah yayi mashi rasuwa ba, batare da ta sani ba, i ko haka ne, duk wata hujjar da ta kama ta rushe kenan.

Suna haka ne, jakadiya ta shigo, sanar dasu tayi ison mai martabar.

Fulani ce ta fara miƙewa, jakadiya ta gyara mata alkyabbar ta, sai kuma ta wuce gaba, yayin da sauran matan suma suka miƙe, hadda su Umma suka mara mata baya.

Sashen mai martaba suka nufa, duk i da suka ratsa bayi ne ke aikace aikace, ta cikin barga suka bi, inda suka ga dawaki masu jini a jika sun cika sunyi ɓulɓul sai harbin iska suke yi.

Sashen mai martaba, kusan mucr yafi ko ina ƙawatuwa, tun daga waje zaka shaida haka, wasu irin ƙofifi ne na zallar glass tar, kana iya hangen abun da ke ciki. Haka suka rinƙa ratsa wasu irin fadoji masu matuƙar kyau, har zuwa isar su ƙaramar faɗar da tafi ko ina kyau da tsaruwa.

A bisa kujeru suka tadda su alhaji Mustapha ɗin, yayin da mai martaba ke zaune gefen su, shima bisa kujerar irin ta sarauta.

Kujerun da suke mallakin matar sarki kowacce ta ja ta zauna, yayin da Umma da Hajiya Zainab ɗin suka zauna ƙasa daga gefe.

"Aa taso ki dawo nan Gimbiya Merama"

Cewr mai martaba yana nuna mata gefen shi daga ƙasa.

Ba musu Umman ta miƙe ta koma inda ya nuna mata.

Jakadiya ce ta russuna cike da girmamawa, sannan ta sanya ƙafa ta bar fadar, tana mai ja masu ƙofar.

Saida mai martaba yayi gyaran murya sannan ya buɗe taro da addu'a.

Bai jira komai ba ya fara jawabi.

"Gimbiya duk da kasancewr yanzu kuke tafe da ke da mai gidan naki da kuma dangin shi, hakan ba zai hana in nuna maki tsantsar ɓacin rai na ba, wanda ke kanki kin sani tafiyar taki ba ƙaramin ruɗu ta saka masarautar nan ba, duk da cewa bamu san babban dalilin ki na tafiyar ba, hakan kuma yanzu ba dalilin nake so inji ba, duk munyi maganganu da mai gidan naki sosai kuma na fahimta, saidai ina so in riƙe shi wata alfarma ne, duk da kasancewar ita mai sunan Fulani shi Alhaji ne ya riƙe ta, har girman nata, kuma ya shaida mana cewa yanzu haka dalilin auren nata ne da yaron wajen nashi Muhammadu ya tafo ku ƙafa da ƙafa, kenan ma da ba zaki dawo ba, da haka ne nake riƙon shi alfarma da ya maido ma masarauta da sarauniyar ta, watau ita Hauwa'un, ayi hidimar bikin nata anan, kuma a ɗauke ta anan zuwa gidan mijin nata, ba ƙwace zamuyi mashi ba, alfarma zaiyi mana, daga yanzu duk wani abu da fannin amarya keyi mune zamuyi mata. Yanzu nasan akwai hidindimu masu ƙarfi dake tafe, Shiyasa ba zamu riƙe ku ba, Amman duk kanku muna so ku sani masarauta tayi matuƙar farin ciki da kasancewar ku waɗanda suka riƙe mata gimbiyar ta har kawo yanzu, ita da abun da ta haifa, zamu samu lokaci mu tattauna dalilin barin naki guda ke Gimbiya Merama, Amman ba yanzu ne lokacin ba, tinda hidimar aure ta taso, ba zamu ce a ɗaga ba, saidai za'a maido mana amarya da mahaifiyar amarya zuwa nan, inda duk wani shagali na fannin amarya zamu gabatar dashi anan, kafin mu baku amarya"

Ya ƙarashe yana mai sakin ɗan murmushi haka kaɗan. Suma su Dad murmushi suke yi.

"Ranka ya daɗe ai wannan ba wani abu bane, ba damuwa ko ɗaya acikin hakan, insha Allahu yarinya daga makaranta ma nan za'a zarto da ita, kafin ta dawo ita mahaifiyar tata zata fara yo gaba, duk Abunda kasan ana gabatarwa na al'ada insha Allahu za'a zo nan a gabatar dashi, godiya mukeyi Allah ya ƙara ɗaukaka" cewr Alhaji Auwalu ya har yanzu fa kallon Umma yakeyi cike da mamaki, lallai ta cencenci yabo da jinjina da ta kasance a matsayin mai aiki a gidan ƙanen nashi na tsawon lokaci.


Sun kuma tattaunawa, sannan mai martaba ya gabatar da matan nashi garesu suka sake sabuwar gaisuwa. Nan fa aka buɗe babin fira kaman ba'a masarauta ake ba, inda shima mai martabar ya kuma sakin jiki yana sake gaya masu halin da ƴan gudun Hijira ke ciki.

Wajen ƙarfe biyar ne sukayi haramar tafiya, ba yanda mai martaba baiyi dasu ba akan su tsaya su kwana suka ƙiya, a ceear su basu shiryo ma kwanan ba, amman yanzu ai ya zama gidan su har sai an gaji dasu.

Shi kanshi mai martaba ya jinjina dattakon su Alhaji Mustapha ɗin, duk da kasancewar su ba baƙin shi ba, hasali ma suna yawan haɗuwa, duk lokacin da wani abu ya taso, dama tin cen yana jinjina Alkhairin mutumen da yaron nashi, hidima suke yi ma ƙasar su da ƙarfin su da dukiyar su kaman basa so, lallai sun cencenci yabawa da kardamawa, ya kuma yi alƙawarn yin bikin tarbar Gimbiya Merama da mijin nata, kafin lokacin tattaunawar yanda za'ayi da sarautar ya taso.



(Uhmmmm to ko me yake nufi da hakan kuma?)

Saida sukayi ma bayin sarki da fadawa alkhairi mai yawa, mai martaba da kanshi ya rako su har zuwa motar tasu yana mai ɗaga masu hannu, da jin Meramar a jikin shi kaman kar ta tafi, ganin ta da yayi ne ya tuno mashi da ɗan uwan nashi har matse kwalla sai da yayi.

Wannan babban abun alkhairi ne ya same shi da ahalin nashi baki ɗaya, kasancewar Allah bai bashi haihuwa ba sai guda ɗaya, itama t a kasance mace ce, kuma ba yanda zata yi ta gaji sarautar tashi tinda dama tin cen asali Meramar ce zata kasance sarauniya ko kuma mijin nata.... Amman ga yanda rayuwa ta juye dasu, saboda haka yayi alƙawarn amsar ɗiyar ɗan uwan nashi da hannu bibbiyu...



Haka suka ɗauki hanya, daga Hajiya Zainab har Umma ba mai ta ƙawa, akai akai Umma ke share kwalla ta, ita bata ma san baffan ta ne a kan karagar mulkin nata ba sai yanzu, koma dai minene lokacin da Suhan zata san ko wacece ita ya ƙarato.

Alhaji Mustapha da Yaya Auwalu ne kawai ke firar ƙaramin su, sai driver daya tattake yana ta zuba uban gudu, gashi dama ya nake cikin shi nak da irin cimar gidan sarauta, da har sai kaji ba wurin zubawa.

Cikin dare sosai suka dawo, saida suka biya suka sauke su Hajiya Zainab ɗin sannan suka juya zuwa nasu gidan. yayin da Hajiya Zainab ɗin tayi alƙawarin shigowa gobe su sake tattauna wa da umman.

Hatta mai gadi yayi mamakin ganin su cikin daren, dama ita Hajiya Kubra koda ta tambaya ina suke aka ce mata sunyi tafiya, taɓe baki tayi, tana mai cewa "zaki ƙaraci abubuwan ki ko guda nawa ne, lokaci na baki, daga ke har talakr ɗiyar ki"

Dama Umma ce keda duty, saida ta sake haɗa masu ruwa sukayi wanka, sannan suka kwanta cike da gajiya, ko Abunda zasu ci basu tsaya nema ba.

Alhaji Mustapha yayi matuƙar murna da sanin asalin Amaryar tashi, yayin da Umma ta kwana tunane tunanen abubuwa, lallai akwai sauran riba a kaba, tinda ko eulgin waziri ita bata gani ba, kuma a duk furar da sukayi da Baffa mai martaba bata ji ya ambaci sunan wazirin ba.

******


Ya Ameen bai kira ni ba tsawon kwana uku kenan, kuma ko na kira bana samu, na rasa dalili, Amman na bar hakan ne a cewar ayyuka ne sukayi mashi yawa.

Gashi har mun kusa gama exam ɗin.

Nayi mamakin da Umma tace mani ko na gama Exam in zauna a makarantar har zuwa lokacin da zata buƙaci tahowar tawa, na rasa dalili, kuma ita bata yi mani wani jawabi ba.

Haka na share na cigaba da zana Jarabawa ta, ranar cikon kwana na huɗun ne, sai ga kiran Ya Ameen ya shigo waya ta.

Cike da ɗoki na Ɗauka, Amman sai na saisaita murya ta kada ya gane cewa ina kewar shi, duk a ƙoƙari na na kare kambu na a matsayi na na mace.

Duk dai da haka saida ya gane nayi kewar tashi, ƙorafi zan fara mashi, ya katse ni da bani haƙuri yana mai sanar dani ayyuka ne sukayi yawa, ashe ba kamfani ɗaya bane ke son ƙulla harkar kasuwanci dashi ba.

"Sai yaushe ne zaka taho?" na faɗa cike da shagwaɓa, ina mai tura baki gaba.

"Kinga my Amarya, kwantar da hankalin ki, yanzu haka ma gani a airport lokacin tashin jirgi kawai nake jira, saidai zuwa nan da wa biyu ne, nayi lattin samun ticket, kinga ba zan ƙara so ba sai goben ku kenan, tinda mu yanzu nan rana ce, kinga kuma ku dare yayi nisa yanzu.

Da kai na shiga amsawa cikin shagwaɓa, ina kallon khady sai mktse moste takeyi, ga dukkan alamu idanun ta biyu, ita da har ga Allah son Ya Ameen ɗin takeyi, ya zuwa yanzu fa ta fara bani haushi, tinda nima na gane cewa tsundum fa na faɗa tarko.

"Zan kama bakin nan naki ne"

Ya faɗa shima yan mai kwaikwayar murya ta.

Maida bakin nayi, ina mai lumshe idanu, jin daɗin muryar shi da nakeyi, har cikin kwalwa ta, ji nakeyi kaman yana busa mani sarewa a kunne, dama ashe haka amon muryar Ya Ameen take da masifar daɗi, ban kuma tantancewa ba, har sai da na fara soyayya dashi sana. Komi yayi burgeni yakeyi, salon shi, kai hatta da wannan miskancin dake bani haushi a da yanzu ya koma burgeni yakeyi.

"Saura kwana nawa?"

Ya tambaye ni, cike da zaulaya, cikin wani irin amon murya da ya sanya na faɗa wani shauƙi.

"Sixten"

Na faɗa a hankali.

"Wow ashe amaryar tawa tana ƙilgawa, kin ƙagara ko baby ta?"

Ya kuma faɗa cikin wata zaulayr.

"Uhmmm Uhmmm ni Allah yaya ba haka bane, ina dai ƙilgawa ne saboda na kusa gama exam"

"Ba wani baby, kina ƙilfa ra ar shigar ki ɗakin Ameen dai ne kawai, Dont worry, dama ina so ne ki faɗa mani abubuwan da kike so a zuba maki a lefe, Aunt Feena ce zata haɗo maki acen, ko kuma zan bata numb ki sai ta tuntuɓe ki"


Da sauri nace "Nooo Yaya, kar ka bata, ba ma sai an tambaye ni ba, ni ai kai nake so, ba kayan ba, don haka duk abunda ta sanya duk ɗaya ne, i only want u"

"Wow dear, are u sure?"

Cike da kunya nace "yes Yaya very much sure ma" na ƙarashe a hankali ina mai noƙe kai cikin fillow, sai yanzu Kunyar abun da na faɗa ta kama ni.

"To ai shikenan, saidai akwai abubuwan da dole sai kin faɗi size ko zaki faɗa mani yanzu, tinda ita kunya kike ji? Ni kau kinsan komai nawa ne"

Kaman in nutse haka na dinga ji.

"Ba zan iya faɗa ba yaya, i'll text u later"

Na kuma faɗa cikin kunya.

"Okay baby, bari in barki ki kwanta, zamuyi waya in na sauka, i kissed u, sleep tight"

Ya faɗa a hankali, yana mai sakin ƙaramin Kiss ya huro mani iskar cikin kunne.

Noƙewa nayi a hankali, kasala na saukar mani, murya cen ciki na shiga cewa "Okay Yaya Safe journey"

Ƙit na katse wayar, ina mai sauke ajiyar zuciya jeri jeri.

Khady ce ta miƙe zaune ta kunna hasken ɗakin, snanna ta maido kallon ta gareni.

"Suhan ina mai maki murna matuƙa, ki riƙe Dambulan da amana, shi ɗin kalar namijin da kowa ke buƙatar samu ne"

Tana gama faɗar haka ta kashe kwan ɗakin ta koma ta kwanta.

Ashe duk firar da muke idanun ta biyu, dama nayi tunanin hakan, wayyo Allah so shegen abu, gashi ta kasa bacci, jin wanda take ƙauna shi kuma ya mutu akan ƙawar ta, har yana faɗa mata daɗaɗan kalaman da idan ya faɗa sai ta rintse idanu wa, ji take kaman ita yake gayamawa, Dambulan da babu wanda zaiyi tunanin zai iya tsayawa ba soyayya muhimmanci haka, sai gashi shine yake faɗar wasu kalaman masu matuƙar sanyaya zuciya.

Ji nayi kaman in mata kuka, Amman in na tuno da Ya Ameen fa take so, sai inji wani haushn ta, ɗan ƙaramin tsaki naja, ina. Ai wulla mata harara daga bayan ta, cikin zuciya ta nake faɗin "wahalla kawai, Ya Ameen na Suhan ne ita ɗaya, ko baki raya ni murna ba, babu Abunda za'a fasa"

(Uhhmmmmm Suhan kenan, lallai kin fara yin nisa)

Shima yana kashe wayar ya rubuta saƙo ma Aunt Feena akan cewa ta siya duk Abunda taga ya dace kawai, saidai ta zaɓi mashi classic kaya, saboda Amaryar tashi daban take.

Shi kanshi mamakin kanshi yakeyi, wai Suhan ce yanzu saura kwana sha shidda auren nashi da ita, shi kanshi ya san yayi dace, aure irin na soyayya, tinda yan da tabbacin cewa, ya zuwa yanzu Suhan ɗin ta dumbula cikin narkon soyayyar shi, tinda gashi har tana faɗin wai *Shi kaɗai take so*



~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



*Addu'a Ga Wanda Yayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login