Showing 21001 words to 24000 words out of 247770 words

Chapter 8 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10401

ta da idanu hawaye na ɗiga ɗis-ɗis saman hijab ɗina.

Juyawa suka yi suka fita har mama Talatu da Ya ameen ya yafito da hannu, kuɗin taci ya bata tare da mata godiya sosai yace ta koma gida sai ya dawo, dawowa yayi ɗakin tare da kira na domin shi wucewa zai yi, a baya na bishi zarai-zarai har muka fita harabar asibitin da har mama Talatu ta samu abun hawa, ina kallon ta tana leƙowa taga shin ina zamu, sai dai ta makaro dan mai motar ma har yaja sunyi gaba, naso nayi mata godiya Amman ba komai ai bana ma fatan mu daɗe asibitin, zan yi mata idan mun koma gida.


"Is OK Suuhaaan" ya faɗa a hankali bayan ya daidaita tsayuwarshi bakin motar sannan ya juya ya jingina da ita sosai, "Comon goge wannan hawayen naki, kukan ya isa hakanan, ki yi mata addu'a sannan ki guji ɓacin ran ta, a mamadin mahaifiya ta ina mai ƙara baku haƙuri, na san ita ce sanadi, Amman insha Allah komai ba zai ƙara faruwa ba" ya faɗa yana mai ƙoƙarin haɗa idanu dani, ni kau sauke kaina nayi ƙasa ina mai bin umarnin nashi na share fuskar tawa gami da jan majina a hankali na shiga faɗin "Mungode Yaya babu komai wallahi, dama umma ta tana da wannan ciwon, nima dashi na taso na ganta, ba Hajiya bace sila, Mungode da karamci Allah ya saka da Alkhairi" na faɗa ina mai ƙosawa da tsayuwar, ba zan iya jure tsayuwa wuri ɗaya dashi ba, kwarjini yake man, gani nake duk ya cika wajen, Al'ameen ɗin daban ne, akwai kamala da haiba tattare dashi, komai nashi da yake yi cikin hankali da natsuwa yake yin shi, daidai da magana kaman baya son yi, muryar shi, ƙamshin turaren shi na ƙara rikitar dani, bana son irin yanayin da nake shiga a duk lokacin da muka kasance mu biyu a wuri ɗaya, kula yayi da irin yanda duk nabi na takura, motsa bakin shi yayi a hankali ya shiga faɗin "ki koma wurin umman, zan je aiki in dawo tin ɗazu ake jira na babu Abunda zaku buƙata, akwai komai a ɗakin kuma akwai drinks a fridge zan sa a kawo maki break fast ki tabbata kunci don na san baki ci komai ba, sai na dawo" Ya faɗa, bai jira cewa ta ba ya faɗa mota gami da yi mata key, janyewa nayi na bashi hanya, ya zo yawuce bai ko kalli inda nake tsaye ba (hoooo Al'ameen miskilanci)


*******************************

Mama Talatu kuwa na isa gidan sashen Hajiya kubran tayi, ta iske bata tashi ba Amman don tsabar san gulma sai da ta jira ta, bayan ta fito ne take tambayar ta ya bata ganni ba? Ban shigo aiki ba,me yake faruwa, "yo Hajiya ina ko zaki ganta? Ai bama su gidan gaba daya" cikin isa take kallon talatun, "ke Talatu bana son munafunci, faɗa man gaskiya me yake faruwa ne a gidan? Ta faɗa cikin gadara lokaci guda tana mai zama kan ɗaya daga cikin sofa na alfarma da sukayi ma falon ƙawanya, sanye take cikin wani ɗanyen lace mai azabar kyau, dama hajiya Kubra ba dai kyau ba, naira ta kwanta mata ta ko ina sai sheƙi take yi da walwali, nan mama Talatu ta kwashe ƙarya da gaskiya har faɗa mata take yi cen ta baro Al'ameen ɗin ai muna tare.

Ranta ko in yayi dubu ya ɓaci, au ta hana taraiya da afnan shine muka koma ma Al'ameen? Al'ameen ɗin nata da take ji dashi tamkar tsoka ɗaya a miya, me hakan ke nufi? Dakatar da mama talatun tayi gami da miƙewa cikin takon isassu ta fita daga sashen zuwa sashen Alhaji da take barowa da sanyi safiya, Afnan ce ta fito tana kallon mama Talatu, ashe ta zo fitowa taji suna magana shine ta koma da baya take jin duk abubuwan da mama talatun ta faɗi ma mom ɗin tasu "mama kiji tsoron Allah fa, ashe ke ke hadda sa fitina tsakanin hajiya da masu aikin gidan nan? Kina shugaba baki so a zauna lafiya, to wallahi kema ba zaki ci gaba da zaman gidan nan ba muddin kika yi sanadiyyar barin su suhan ɗin gidan nan". Tana kaiwa aya bata jira cewar mama talatun ba ta koma ɗakin nata da gudu tana mai rarumar wayar tata gami da kiran Ya Ameen ɗin, tsaf ta kwashe komai ta faɗa ma gayan nata yanda taji mama Talatu na faɗa ma Hajiya, tare da faɗa mashi yanzu zata bar gidan zuwa asibitin ta taya ni zama, koma minene ya faru ai su ne sila; Dakatar da ita yayi gami da cewa ta bari sai ya dawo baya son wata matsala kuma, shi zai jawo hankalin hajiyar ta bar zancen bari ma ya faɗa ma Alhaji komai kafin Hajiyar ta isa.

Da yake da tazara sosai tsakanin sashen nata da na Alhaji, lokacin da ta isa har Al'ameen ɗin ya kira Alhajin ta iske yana waya da Al'ameen ɗin ta nemi waje kusa dashi ta zauna, tana ta cika da batsewa, bayan ya gama wayar ne ya maida hankali shi kan Hajiya Kubran, da murmushi ɗauke kan fuskar shi ya shiga faɗin "uwargida ran gida, lafiya dai ko naga kin dawo, wannan kwalliya ai sai dai ace in biya" ya faɗa cikin zaulaya da murmushi a kan fuskar shi. Fuska a tamke take cewa "Alhaji ba wannan ba, yaron nan Al'ameen...." Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu gami da cewa "Abunda Al'ameen ɗin yayi shine daidai, ai suma mutane ne, ko kuma zai ƙyale ta ta mutu ne cikin gida yana kallo? Mutane su samu abun faɗa a gari? Kada in kuma jin kince komai akan zancen nan kuma anjima ku shirya ku duka muje a dubo ta, Allah ya bata lafiya shine fatan mu. Sannan ina so ki sanya a nemo maki wasu ƴan aikin da zasu zauna mamadin su, abarsu su huta hakanan ita yarinyar ta kula da mahaifiyarta." Yana zuwa nan a zancen ya miƙe gami da gyara zaman babbar rigar shi yana mai kallon ta sannan ya cigaba da cewa" Ni zan fita sai na dawo, kada ku manta ku shirya fa, sannan idan Allah ya kai mu gobe Asabar mu dukkan mu zamu je kankiya mu gaishe da su Alhaji tinda kowa yana ƙasar ki faɗa ma yaran ma su duka su shirya" da kallo ta bishi har ya fice, ita kanta ba tin yanzu ba ta san Alhajin kaifi ɗaya ne, dukkan isar ta da zartar da hukuncin ta, tana yi ne akan ƴaƴan ta kawai da masu aikin gidan sai kuma abokan kasuwancin ta. Amman Alhajin gagarabadau ne a wajen ta, duk abin da take taƙama dashi ya fita shi tsayayye namiji ne a cikin gidan sa, dukkanin hukuncin da ya yanke ya yanku kenan, ba shan ruwa ba ƙetare hanya.

******

Ƙarfe biyu Al'ameen ɗin ya koma gida bayan salla juma'a gami da yin wanka ya shirya, Afnan ya kira a waya ya sheda mata ta fito su tafi, aikau ta saɓo Nasreem ta kamo hannun Ayan, Afnan kenan sarkin ƴaƴa, ko MOM ɗin tasu bata faɗa mawa ba don ta san hana ta zata yi, biyawa suka fara yi, suka yi take away da sauran tarkace, sannan suka wuce asibitin kai tsaye.

A ɗakin suka taddani zaune bisa kujera, na kifa kaina jikin gadon umman tawa da har yanzu bata farfaɗo ba, ban ma ko ji ƙarar buɗe ƙofar tasu ba, na yi zurfi cikin tunani, ƙamshin turaren shi ya sanya ni sauri ɗagowa, ilai kuwa su ne shi da afnan, sanye yake cikin dakakkiyar shadda fara ƙal, yau juma'a tu babbar rana, fuskar nan tashi fayau, idanun shi tarwai cikin farin glass ɗinshi mai kama da medical glass, idanun shi ƙyam a kaina, kallo yake man mai cike da ma'anoni da tuhume tuhume, tabbas na san laifi na, take away ɗin da ya sanya aka kawo man, tin bayan fitar shi da safe, yana ajiye bisa stool ɗin ɗakin ko taɓa shi ma banyi ba har gashi yanzu Ƙarfe uku saura; ba'a magana da ƙarfi ya sanya bai ce an komai ba, sai ma ɗan ƙutawa da yayi ya ajiye sauran ledojin da suke hannun shi ya fice gaba ɗaya a ɗakin.

Gaisawa muka yi da afnan sosai kaman babu abin da ya faru, na shiga tambayarta sauran mutanen gidan, "suna gaida ki da mai jiki" ta furta ba dan taji daɗin ƙaryar da ta furta ba. Hannun Ayan na kamo ina cewa "zo mana Ayan in ba faɗa mi ya kawo gaba?" cikin ƙarfin hali har da ɗan murmushi na na yaƙe. Text ne ya shigo wayar afnan, Ya Ameen ne yake cewa lallai ta sanya ni inci abinci, shi ya wuce sai anjima zai dawo kuma lallai kar suyi hayaniya a ɗakin nan su tada umman tawa.


_Kuyi manage da wannan please bana ɗan jin daɗi ne ku taya ni da addu'a fans_

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:23 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƙARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u nopain✍🏽~*

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


🤸🏻‍♀💃🏻💃🏻 Kuzo ku taya ɗan ku Deedat murnar cika shekara uku cif a duniya, ina fatan Allah ya Albarkaci Rayuwar shi, ya shirya shi shirin addinin islam, ya bashi rayuwa mai Albarka, ya bashi ilimi mai yawa mai amfani, ya cika mashi burin shi na zama Soja😄😆 ya bamu ikon tarbiyyantar dashi. AMEEN ya Rab, Deedat yana gaida dukkan fans na *BAN FI ƘARFIN TA BA*


_*Page ~9~*_


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Mu kau cikin ni da umma ta, babu wanda yayi runtsawar kirki, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai, har gara ma umman tawa, tana ƙoƙarin ganin ta kau da komai, sabo da shawarwarin likita da ya bata na tayi ƙoƙarin ganin bata riƙe abun ɓacin rai a zuciyar ta ba.

Ni kuwa Allah Allah nake gari ya waye, domin na yanke shawarar ƙundunbalan tambayan umman tawa ainihin labarin mu, da asalin mu, lokaci yayi da zata dena ɓoye mani komai, na mallaki hankalin kaina, yaci ace ta fito ta fayyace mana komai kowa ya sani, ko zata fita a zargin da mafi yawancin ƴan gidan ke mana, a kan kunnen mu mun sha jin ma wasu ƴan ƙanana maganganu akan umman tawa da ni kaina ma, kai wasu ma cewa suke yi ni shegiya ce bana da uba, tinda haka suka ganta tazo gidan a wahale ga ɗiya duƙu-duƙu kuma taƙi faɗin wacece ita da kuma ainahin daga ina take.

Alhaji Mustapha kuma ya kafa dokar kada wanda ya tambaye ta, har sai ta gaji dan kanta ta faɗa, a cewarshi babu kyau shiga rayuwar wani, kuma hakan zai tada mata tsohon mikin dake ranta, gida dai nashi ne, tau tinda haka ne ya bata izinin zama har iya lokacin da take so, kuma tinda aiki tazo nema a zaɓa mata marar wahala a bata har sai ta murmure.

Ciwon umman tawa ya so ya tashi cikin dare, amman cikin ikon Allah abun ya taƙaita, ban so ace zan tada mata maganar da safe ba, gudun sake faruwar tashin ciwon nata, tau sai dai babu yanda na iya, wannan karon haƙuri na da kawaici na yazo ƙarshe, ba zan iya jurar ganin irin wannan rashin mutuncin ba daga wajen Hajiya kubran; da haka na samu bacci ya ɗan figeni har zuwa asubar farko da kiran sallah ya tashe ni.


*******************************

Ya Ameen yana shiga ɗaki waya yasa ya kira Afnan ɗin domin sheda mata yanda sukayi da Dad ɗin nasu, "Hello yaya" ta furta daga cen ɓangaren cikin muryar bacci "My Lil bacci kike yi ne?" ya tambaye ta cikin muryarshi mai daɗin sauraro a hankali, "eh Yaya na kwanta, lafiya dai ko? Ko wani abu kake buƙata? Ta tambaye shi tana mai tashi zaune da ƙara gyara ma Ayan dake gefen ta kwance bisa gadon nata lulluɓinshi," No Lil, ina dai son faɗa maki ne munyi magana da dad ne akan maganar waccen yarinyar, Amman tinda kin fara barci mu bari zuwa safe ki same ni part ɗina kinji, Good night dear" ya faɗa yana mai datse kiran ƙit, domin ya san halin zumuɗinta yanzu tana iya cewa ta taso ta taho, shi kuma baya jin ma zai iya doguwar magana yanzu ya gaji so yake ya kwanta, yana da muhimman ayyukan da zai aiwatar gobe, murmushi ya saki na gefen baki, wanda yayi sanadiyyar ƙara ƙawata fuskar tashi cikin hasken ƙwai mai launin dark blue na dare dake falon.

Miƙewa yayi cikin salon tafiyar shi mai cike da aji, ya shiga bedroom ɗin nashi domin yin shirin bacci, kayanshi kawai ya cire ya faɗa toilet ɗin da baya gajiya da shaƙar daddaɗan ƙamshin da suhan ɗin ta sanya mashi har kawo yanzu.


-------------------

Bayan mun kammala komai na Al'adar mu, kama daga sallah, wanka, sai muka zauna karatu ni da umman tawa, muna gamawa ne naga umman na ƙoƙarin tashi na dakatar da ita ina faɗin

"Umma ina so zamuyi wata magana dake don Allah" na faɗa ina mai rufe littafin umdatul-Ahkam ɗin gami da maida shi ma'ajiyar shi, na sake muskutawa domin girman maganar, ba zan ɓoye ba zuciya ta kaman tayo tsalle ta fito nake ji ta ƙirjina, masalan ma da naga irin kallon da umman tawa ke bina dashi, mai cike da ma'anoni daban daban,

komawa tayi ta zauna domin saurarar ɗiyar tata, da kanta yake duƙe kaman tayi ma sarki ƙarya, "Ehn ina jinki mamana, sauri nake yi domin kinga lokaci ya fara ja.


Sake sunkuyar da kai nayi ina mai komawa kalar tausayi maganar tayi ma baki na nauyi, shahada nayi lokaci guda na shiga faɗin

"Umma ki duba girman Allah ki faɗa mani asalin mu, wanene mahaifina? ina ne asalin garin mu, umma ke kanki su wanene mahaifan ki? Umma kin fi so mu zauna a gidan da ba'a san darajar mu ba? Kin fi so mu zauna ana wulaƙanta mu, ana zargin ki, ni kuma ana sheganta ni? Kada zuciya ta tafara yadda da maganar su fa!, na bani da asali, bani da mahaifi umma! Umma su nan ɗin ba dangin mu bane, basu san zafin mu ba, ƴaƴan su ma basa so su raɓe mu, suna kyamatar mu, suna ganin sun fimu umma, bazan iya jurar aci maki fuska a gabana ba, saboda kina ɓoye mana wani abu, kinƙi ki fito ki faɗa ma kowa mu ɗin su wanene ciki kuwa harda ni...... "

marin da ta sauke man a kan fuska ta har guda biyu, su sukayi sanadiyyar datsewar maganar tawa, ɗif nayi dafe da kunci, kaman ruwa ya ci ni, yau ni ce umma ta ta buga, yau ni ce durƙushe gaban mahaifiyar tawa ina faɗa mata malaman da suke barazana ga lafiyar ta, ba zan iya tuna lokacin da umma ta ta ɗauki hannu ta bigeni ba, saboda ita mace ce mai san yin hali, Sam bata da zafi;

kuka na fashe dashi lokaci guda ina mai ƙanƙame jikina, yanda naga ta hassala kaman zata rufe ni da suka.

"Ashe ke shashasha ce hauwau ban sani ba?, ina tarbiyyar da na baki? Ina kika kaita, nan ɗin da kike ganin ana wulaƙanta mu, ya fiye mana cen, in kika koma kashe ki zasu yi, nace kashe ki zasu yi! Ni ma ba zasu barni ba, saboda ke nake zaune nan, dan ki tsira da mutuncin ki, ki tsira da rayuwarki yasa nake zaune nan, nima abun yana man zafi, Amman ko me zasu yi mana ba zasu iya kashe mu ba, zaki mutu ne muddin kika yarda kika koma cen" kwalla ce ke shata ta a idanun umman tawa, abun da ya ƙara matuƙar firgita ni kenan, rarrafawa na shiga yi ina mai zuwa inda take na rungume ta, ture ni ta shiga yi, jeki, je ki nemi mahaifin ki, ƙila zakiyi sa'ar ganin kabarin nashi, ƙila zai iya tashi ya faɗa maki komai, Hauwa'u ban tsammanin akwai ranar da har ke zaki iya zuwa ki sanya ni a gaba ba, ki titsiye ni sai na faɗa maki wacece ke ba, na ɗauka na gama maki komai, na ɗauka na ishe ki komai, ban tsammanin zaki gaji da zama a inda na zaɓa mana rayuwa ba, nace kashe ki zasu yi, muddin kika yarda suka san kina nan da ranki, jeki jeki ki nemo dangin mahaifin ki, ki nemo dangi na, Amman ni kar ki ƙara tambaya ta game da su, kar kuma ki sake ki dawo inda nake, kuma duk Abunda ya same ku ke ce kika siya da kuɗin ki, kar ki ƙara tambaya ta abunda ya shafe su; Ta shiga ƙara ture ni daga jikin ta tana mai share kwallar da take ta ambaliya a fuskar ta.

Ƙara ƙwaƙume ta nayi, ina mai sakin gunjin kuka lokaci guda ina mai faɗin "Umma kiyi haƙuri ki yafe man, ki gafarce ni umma, nayi maki laifi, na aikata maki ba daidai ba umma, na cutar da zuciyoyinmu umma, bansan haka ba, bansan komai ba umma ki yafe man" shiru naji lokaci daƴa kaman ma bata numfashi, A firgice na ɗago, domin in ga me ke faruwa, abunda idanunwa na suka gani ne ya sani sakin razananiyar ƙara da sai da ta cika ilahirin sashen namu. Jikin ta gaba ɗaya ya saki, kaman wadda ta mutu bata numfashi Sam, "umma ki tashi" na shiga faɗi lokaci ɗaya ina mai jijjiga ta "umma ki tashi don Allah na bari, umma ki yafe man, umma kar ki mutu ki barni don Allah, umma ban da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login