Showing 237001 words to 240000 words out of 247770 words
ai tsalle Afnan tayi ta rungume ta, murna take ta yi sosai, Ƙawar ta ce sosai a instagram haka ma Ƙawar Asiya ce ƙanwar Sir Salim a school, ai sai suka haɗe, hidimar biki ake ta yi sosai, domin shi Dady ɗin ne ma dakanta ya kawo ta, tare da damƙa mata dukkanin abubuwan da yasan zata buƙata yana mai sanar da ita cewa sai ranar ɗaurin aure zai dawo tare da su Ya Ameen dayake abokai ne, don dai sunyi nisa ne, kuma kowa na cen hidimar shi tayi mashi yawa ne ya sanya basu cika samun haɗuwa ba.
Ƙawayen amarya su biyar hadda amarya su shidda kenan, tin zuwan Umman aka cenza masu ɗaki, wani sashe ne aka buɗe masu su duka babban falo ne da manyan ɗakuna guda biyu a ciki, Shiyasa suke gabatar da komai nasu a cikin tsari.
Ranar Laraba ne aka yi ma amarya ƙunshi, wohoho, ai ko ni da nake mai ɗaukar rahoto saidai nayi kasaƙe da alƙali na da tawada da ɗan littafi na a hannu.
Amarya ta haɗe ita haɗuwa, duk inda ta juya walwali da sheƙi takeyi, ga wani ƙamshi na musamman dake tashi, ga ƙunshi da tasha na zallar Ja, abun ka da fara ai nan da nan sai ta fara haskawa, kowa sai Sam barka yakeyi.
Yanzu ba'a cika barin ma a ganta ba, indai ba ƙawayen nata ba, ɓoyon amarua akeyi, ba za'a fiddo ta ba har sai ranar kamu, Abunda ke ƙara ɗaure mani kai kenan, idan na tuna ni Suhan wadda ada bata a kowa yau nice na zama haka.
Umma da Ammi kuwa sun ɗinke, komai a tare suke yi, shawara da komai, yayin da Fulani take taya su aiwatar da dukkanin tsare tsaren da za'ayi, mai martaba ne ya bata umurni hakan.
**************
Ta ɓangaren dangin ango kuwa, suma ba'a bar su a baya ba, komai na tafiya yadda ake so, bisa jagorancin Hajiya Zainab, domin ita Hajiya Kubra da dangin ta, sun ware kansu, sai yanzu ne ƴan kankiya ɗin suka shaida cewa lallai fa Hajiya Kubran har yanzu tana kan bakan ta, koda tace ta amince kawai magana ce take yi. To saidai babu wanda yabi ta kanta, wannan kau umurni ne daga Alhaji Isuhu ɗan tsohon, wanda tin kafin su taho dama saida ya ja masu kunne sosai, shi dai yana so ne a yi komai lafiya a gama lafiya.
Yanzu har abinci da eatery ɗin da Hajiya Kubran ta bada Order ɗin a dinga kawo masu kullum har zuwa a fara hidimar bikin. Ba wanda ya kula da hakan, domin kowa ya sani cewa sonsomin tashin hankali ne take nema, kuma a matsayin ta na uwar miji ba za'a biye mata ba azo aji kunya.
A ranar Laraba ɗinne kuma motar laxirious mai ɗauke da tambarn Dambulan ta ɗaga zuwa Adamawa ɗin, mutane goma sha biyu ne a cikin ta.
Hajiya Sa'a, Hajiya Laila, Aunt Feena, sai wasu da suke ƙannen Hajiya Kubra ɗin guda biyu da ɗiyar su mai suna Rauda. Ta ɓangaren Alhaji Mustapha kuwa Goggo Fatima, sai Ƴan biyu Aunt Hassana da Hussaina, da kuma yaran nasu ƴan mata guda biyu suma sai Mama Talatu. Itama ance aje da ita ne saboda ta samu ta kakkama masu wasu aikace aikacen. Dayake fa har yanzu basu san kan dawon garin ba, su Hajiya Sa'a kuwa harda guzuri Hajiya Kubra ta basu, wai bata so suje susha wahala, ita wlh da sun biye mata ma fa, ba zasu wani je ba, yanzu haka ma ko inda za'a ajiye su su kwanta basu, ƙila saidai a kaisu sansann ƴan gudun Hijira wai su kwana, saboda tsabar talauci.
Cikin motar ma da ake tafiya, haka kowa ya kama kanshi, masalan ƴan kankiyr da suka lura dangin Hajiya Kubran kowa na jin kanshi, sai basu biye masu ba aka cigaba da tafiya haka, Hajiya Zainab zata je, Amman sai zuwa gobe ɗin in sha Allahu zata bi tawagar anguna.
Makilli part ɗin nasu ya amsa daga hannun Hajiya Zainab, a hankali yake taka wa yana mai bin ko ina da kallo na sashen, lallai aure na rahama ne, sashen nashi da ɗaya duniya kaman bai taɓa zama ciki ba, kaman ba part ɗin nashi ba, gashi dai har yanzu ba'a cenza tsarin ginin ba, parlour ɗaya ne babba da single bedroom da kitchen, sai toilet a cikin ɗakin, Amman ko ina an ƙawata shi, hatta da plaster ɗin saida aka kankare ta aka yi wata mai kama da ta duwatsu, shi kanshi sashen ya matuƙar ƙayatar dashi.
Kitchen ya nufa a hankali, yana tafe yana sakin dariya shi kaɗai, a tsakiyar kitchen ɗin yaja ya tsaya, hannayen shi duka rungume a ƙirjin shi, komai n a kitchen ɗin ya tsaru, gashi ba wasu tarkace, Amman kai kace a ƙasar Turai ne, juyowa yayi ya fito a hankali yana mai shafa dining table ɗin dake ajiye ta gefen kitching ɗin da glass kawai ya raba su da kitchen ɗin, komai dake falon kana iya hange daga kitchen ɗin saboda zallar glass ne kawai abunda ya katange kitchen da falon, hakan ya sanya indai ba cottons aka saki ba daga cikin kitchen ɗin kana hangen falo, sai ya ƙara ƙawata falon, ga wasu irin kujeru da aka sanya set ɗya ane, Amman kayan set biyu ne a cikin shi, kaman na gidan sarauta, lallai baiga laifin Dad ba, da irin waɗannan kayan da ya sanya aka zuba masu, ai tuwon girma miyar shi nama.
Bedroom ya nufa kai tsaye, a hankali ya murza handle ɗin, yana mai tura ƙofar cikin sanɗa, kaman wanda wani abu zai kama.
Makunnin ƙwan ɗakin ya kunna, ai sai ɗakin ya ɗauki walwali cikin wasu irin launika shi ba shuɗi ba, shi ba fari ba, haka shi ba bula ba, shi ba ja ba, kaman dai raimbow haka hasken kwan ɗakin yake, kayan dake ɗakin ƴan uban su, kalar upwhite hadda gadon shi ya ƙara jan hankalin shi, kuma ya ƙara ƙawata ɗakin.
A hankali ya doshi gadon da aka lailaye shi da zanen gado mai kalar purple da sirkin baƙi baƙi da fari fari haka a jiki, kai kace wani ne zai kwanta saman shi a lokacin.
Ɗosanawa yayi gefe, yana mai miƙa hannuwan shi duka da suke farare samɓal cike da garvasa ya fara shago saman gadon, fuskar nan tashi cike take da murmushi, wai nan da kwana huɗu fa matar tashi na a bisa gadon ko? Kwance ko zaune wama ya sani? Kuka take ko dariya, wama ya sani? Kawai dai Abunda zuciyar shi ke hararo mashi irin zallar ƙaunar da zai nuna mata a ranar.
Hakan ce ta sanya shi sakin dariya mai sauti shi kaɗai, yana yi yana ɗan girgiza kai, alamar abun ya mashi daɗi kenan, toilet ya nufa, nan ma an cenza komai, an jera komai kaman yanda ya buƙata.
Ɗakin ya dawo, yana mai jawo akwatunan da aka jera su reras kusa da gadon da suke kalar purple mai kyau, da upwhite jikin su, kaman dai kalar fentin dake ɗakin.
A hankali ya shiga buɗewa yana dudduba kayan, kaya sunyi ba ƙarya fa, komai classic one ne aka sanya, kayan baccin ya ɗago yana mai imagining kayan a jikin mamallakiyar su, shi kaɗai yake sakin murmushi, haka ya rufe ya maida su kaman yanda ya tada su.
Ji yake kaman kar ya bar sashen, Suhan ta daban ce shi yayi imani, komai da take burge shi yake yi, yanzu ne ya tabbatar da cewa ai ko Bilal ma ba wata soyayya ya iya ba, ko yake yi ba, tinda har zai iya rabuwa da matar tashi yayi nisa da ita, na tsawon wani lokaci, abunda shi zuciyar shi ke raya mashi ba zai taɓa iya yi ba kenan.
Haka ya kullo sashen ya nufi part ɗin ƴan kankiyr, inda acen ne ya tada Hajiya Zainab ɗin ɗakin Kaka Zuwaira tana mata wasu aikace aikacen.
Aiko da wa Allah ya haɗ alaka Zuwairn ba dashi ba, nan fa ta shiga caccakar shi, wai ango har ya fara kyallin goshi, ita fa gaskiya ba zata yarda ba, domin ta lura wannan amaryar ita aka yi wa.
Murmushi kawai yake yi, kaɗan ya biye mata ya fice saboda Hajiya Zainab tana wurin, kuma ko ba komai yana matuƙar ganin girma da ƙimar matar. Saboda shi kanshi ya sani ita da mijin nata ba ƙaramin taimaka mashi tayi ba wajen auren nashi.
Kafin ya fita saida ya sake jaddada mata cewa ta shirya da wuri zasu wuce a goben, saboda yanayi na hanya, da to ta bishi rana mai ƙara yi mashi fatan alkhairi.
Ta ɓangaren Maree kuwa kaman zata yi hauka, komai ta kwance mata, wai yanzu ace yarinyar da ta tsana ita ce zata hau shinfiɗar ya Ameen ɗin a matsayin matar tashi, to ko bai ci abincin da tabbarbaɗa mashi magani bane ba kwanaki? Ga Iro da yake matsa ma rayuwar tata, ba daman ya ganta sai yayi kaman zai rungume ta, kuma ko gaban wanene, ya zauce akan soyayyar ta, iako sauran ma'aikata me zasuyi masu in ba dariya b? Ga mama Talatun tabi ƴan zuwa gidan su amarya balle ta samu wadda zata rage damuwar ta wurin ta, su kuma sauran ƴan aikin sanin rashin Kunyar tata ne ya sanya su duka babu wani mai sake mata jiki, ko kuma ya jawo ta jiki, sanin mugun baƙin halin ta, da na uwar ta.
***********
Su dukansu babu wanda baiyi mamakin ganin sun doshi babbar masarutar garin ba, masalan dangin Hajiya Kubra ɗin da su Hajiya Sa'a, to ko dama cen ita Maryama baiwa ce a gidan Sarauta? Kafin ta gudu daga nan ta koma cen gidan Alhaji Mustapha ɗin?
Kowa Al'ajabi takeyi, suna mai bin fadawa da suke ta wucewa da haɗimai a mota, ga dawakai ko ta ina sai harbin iska suke yi.
A harabar gidan suka yi parking, dama tin da suka shaida tahowar tasu, aka fara sanarwa a masarutar akan cewa ga dangin ango nan sun taho, har kawo isowar tasu, haka suka tadda haɗimai da jakadiya na jiran su, ai tin fitowar su a mota ake masu busa da kirari, hajiya sa'a da hajiya Laila har gama hanya suke yi, ga wasu furanni masu kyau da ƙamshin da ake watsa masu, an shimfiɗa masu jan kilishi suna tattakawa a bisa shi, sai kirara su akeyi ana masu barka da isowa.
Su dai sai zare idanu suke yi, da kallon mamaki suke kallon ko ina, abun fa da mamaki, kaman a mafarki suke jin shi. Suke kuma ganin shi, har zuwa lokacin da akayi masu masauki a wani tanƙamemen sashe dake cen ɓangaren guda na masarutar.
Dayake Umma ta san komai, sai aka bambanta masu ɗaki, ƴan kankiya ɗakin su daban, haka ƴan uwan Hajiya Kubran ma, saidai duk part ɗaya, ne ma'ana falon guda ɗaya ne, cike da kayan alatu na more rayuwa.
Suna shiga Hajiya Laa taja ta tsaya, tin bayan da haɗiman da suka yi masu rakiya suka fice domin kawo masu kayan abinci, kafin su gama a masu rakiya zuwa wajen fulani.
"ke Sa'a wai ko dai mafarki nake yi ne? Nan ina ne mudi ya kawo mu? Anya kuwa nan ne inda amaryar da Maryama suke? Ni dai banga alama ba gaskiya"
Hajiya Sa'a ɗince ta amshe zancen da cewa "To nima dai wallahi Laila Abunda zance kenan, tun da naga mun doso wurin nan gabana ke faɗuwa, ya kamata mu kira Kubra mu snaar mata fa, anya ba wasan kwaikwayo ne aka shirya mana ba? Kinsan fa yaron nan babu Abunda ba zai iya yi ba" Cewar Sa'a ɗin da ta nemi gefen sofa ta zauna.
Aunt Feena ce ta shiga girgiza kai, Sauke Nasreem tayi tana mai cewa "a'a Aunty, gaskiya kada a kira Mom yanzu, a bari dai sai mu ga kamun ludayin abun, ni fitsari ma ya cika mani mara, bari in rage shi.
Ta faɗa tana mai nufar toilet ɗin da yake ta gefen ta.
Rauda ce ta faɗa saman makeken gadon tana mai faɗin" wash ni na ma gaji wallahi, ga yunwa ina ji, wai ba'a fito mana da kayan mu bane daga boot? "
Mahaifiyar ta, wadda ta kasance dangin maman Hajiya kubran ce ta ɓalla mata harara," Ke baki ga inda muka zo bane? Kina nufin zaki rasa abin ci a irin wannan gidan?" ta faɗa tana mai bin sashen da kallo, su kau su Hajiya Sa'a sun kasa ma ko zama, balle su ji daɗi.
Aunt Feena na shigewa toilet ɗin ta zaro wayar ta, gami da danna ma Ya Ameen kira, lokacin yana cikin abokan shi, su Bilal suna gaba gaba wajen tsara yanda hidindimun zasu kasance, masalan dinner da take tasu, bayan an kawo amarya.
Zare jiki yayi yana mai shigewa ɗakin da yake mallakin Bilal ɗin.
"Big sis ya hanya, kun isa lafiya ko?"
"Kai ba wannan ba, nan ina ne mudi ya kawo mu? Anya kuwa gidan su Suhan ne?" ta katse mashi maganar da yake yi.
Dariya ya saki a hankali yana mai cewa "to your suprise big sis, to ina ne haka mudi ya kai ku?" ya faɗa shima cikin murmushi.
"Nan fa wata masarauta babba ce aka kawo mu, kuma kowa da ɗakin su aka bashi Al'ameen, gaskiya ina ji Mudi fa bai san inda ya kamata ya kawo mu ba, kuma shima nan da gani wata hidimar suke yi, ƙila Shiyasa sukayi tunanin mu ma baƙin su ne"
Shima datsar numfashn ta yayi yana mai sakin dariya mai sauti, "Aunty Feena cool your mind, nan dai da kika gani shine gidan su Mahaifiyar Suhan, kuma gidan kakannin Suhan in fact, kawai ki yi kallo, kuma please kada ki yarda su kira Umma for now"
Jinjina kai ta shiga yi, kaman yana gaban ta, sai kuma tace "zan sake kira dai angon Suhana"
Shima to yace yana mai datse kiran, ya kuma sakin murmushi yana mai runtse wayar ta shi cikin tafukan hannayen shi yake faɗin "yyeeess"
Tana fitowa ta sake tadda su dai yanda ta bar su, Amman yanzu an cika masu gaban nasu da kayan ciye ciye, babu Abunda babu a wurin, Amman sun kasa taɓawa , mamaki kawai suke yi, har yanzu a tsorace suke, basu san wa zasu kira tayi masu bayani ba, Hajiya Kubra ce, kuma itama in sun kira ta, ba lallai ne ta san meke faruwa ba, tinda basu ga alamun ta sani ɗin ba, da ko da guzuri ma ba zata haɗo su ba.
Ta ɓangaren ƴan kankiya ɗin ma hakan ce, saidai su sun kira Hajiya Zainab, ta jaddada masu komai, aiko nan suka hau murna, yaron nasu yayi da en mata, ta ɓangare guda kuma jinjina abun suke yi, yanzu ace har Alhaji Mustapha ya san da hakan Amman bai faɗa masu ba, ai da ko wani abu ne sun riƙo saboda dai ayi abu duk a mutunce. Mama Talatu kuwa kaman zata yi bindiga, duk ta ruɗe, har saida suka kula suka yi mata magana, suna mai cewa ta saki jikin ta, nan duk ɗaya suke kaman cen, basa da maraba, su kansu mamaki suke yi, har yanzu ba wai dan a bakin Zainab suka ji ba da ba zasu taɓa yarda ba, saboda har yanzu basu ga wasu masu kama da su Umman Suhanan ba.
Shaida masu akayi akan su ci abinci su huta, za'a masu iso wajen Fulani, amarya dai ce ba zasu samu ganin ta ba, sai zuwa goben wajen kamu, domin ya zuwa yanzu ma an ɗauke ta an maida ta sahen Mai martaba ita kaɗai, ko su Afnan da Jiddan saidai su kira ta ta waya.
Komai suke yi jiki a matuƙar sanyaye suke yin shi, masalan su Hajiya Sa'a, Aunt Feena tana kiran Afnan a waya sai gata da gudun ta, ɗakin ƴan kankiya ta fara shiga, su dayake iyayen ta ne, ta shaida masu gaskiyar komai, inda tsabar mamaki ta sake cika su, mama Talatu har ƙwarewa take yi da abinci, Amman duk da haka babu wanda ya