Showing 9001 words to 12000 words out of 247770 words
dai-dai ne.
Tafe yake cikin salon tafiyar shi ta ingarman namiji, dan ƙwalisa, ga natsuwa, kamala cike da kwarjini; tabbas Al'Ameen ya kai namijin da za'a kalla a sake kallon shi, fuskar shi cike take da annuri dukda kasancewar shi ba ma'abocin murmushi ba, hakan bai hana tsantsar kyawonshi fitowa ba. Fari ne tas yana da tsawo daidai misali jikin shi ya dace da murzazzar fatar shi da take cike da gargasa kwance luf kai ka rantse bata taba shan zafin rana ba, yana da dogon hanci sosai domin ya dauko kyaun mahaifin shi da mahaifiyarshi duk a cikin su shiddan ya kere su a kyau da haske dukda suma suna da nasu kyaun, bakin nan nashi kuwa kaman gidan tsutsa gashi kalar maroon mai haske, kai kace jambaki ya shafa sannan ya goge, sam baya da girma sai dai sajen da ke gewaye da fuskar ya ƙara ƙawata fuskar, sam baya da sanƙo wannan ne yasa gyaran fuskar ya fitar da ainahin kyawon fuskar dimpul din shi na dashe das a gefen fuskar shi na hagu wanda tasa ko bai motsa fuskan ba kana iya hango kwarin shi kwance a kan fuskar shi, Ya Ameen ba dai miskilanci ba.
Sanye yake da farar riga T-shirt ta polo da farin wando na lallausan jins ɗan kamfani gucci watau kayan botique, ƙafar shi Sanye da farin takalmi samfurin adidas, ni kaina mai Rubutun takalmin ya tafi da imani na, hannun shi riƙe da wayar shi samfurin Apple Phone, tare da sun glass ɗinshi sai makkulin motar shi ƙirar Benz, yana ɗan kaɗa shi a hankali.
Waya yake amsawa cike da natsuwa yake taka wa a hankali, kai da ganin shi kai kasan ba RAGGON NAMIJI bane. (littafin Maman mamy)
Falon ya shiga da sallama ɗauke a bakin shi Amman in ba kai da kake kusa dashi ba ba zaka san yayi magana ba, kai tsaye wajen da hajiya kubra take hakimce ya dosa, a hankali yake taka wa sai dai cikin zafin nama, irin na cikakke namiji, katse wayar yayi daidai lokacin da ya isa daf da inda take zaune saman sofa.
"MOM" Ya faɗa daidai lokacin da yake zama kusa da ita, "Good morning Son" ta faɗa cikin murmushi mai nuna isa a duk lokacin da tayi shi, sam ba zata iya ɓoye son da take yi ma yaron nata ba,
"Morning Mom, How Was Your Night" ya faɗa yana mai ɗan zamewa ya kishingiɗa a saman sofar, "Great dear, Hop there is nothing wrong?" ta maida mashi da tambaya.
"Nothing Mom But i want to enrout to china today" ya faɗa da ƴar damuwa a fuskar shi,
"Wat? Hop dai lafiya son"
"Lafiya Ƙalau Mom, kayan da nayi order ne an samu matsala ne wajen shipping nasu so i need to go there, domin in san matsalar da aka fuskanta sabo da kaya ne na manyan kudi, gashi costomers sai magana suke yi sun ƙagara a basu kaya"
"Well Allah ya kiyaye hanya, fatan dae kayi report wajen aiki?" ta faɗa tana dafa kan shi kaman ƙaramin yaro; "Yes Mom ba wani matsala bari naje sai munyi waya, yanzu muka gama magana da Dad ma shima yana hanya Amman ba zamu hadu ba sai dai na dawo, ban san tsawon lokacin da zan dauka ba acen" ya faɗa a gaggauce yana mai miƙewa gami da gyara zaman rigar shi a jikin shi, bai jira cewarta ba ya fice daga falon, yayin da ita kuma take bin shi da kallon ƙauna irin na uwa ga ɗanɗa mafi soyuwa a rayuwar ta, tana mashi addu'a da fatan nasara domin dai ita idan akwai abunda ta tsana a rayuwar ta tau bai fi ganin ɓacin ran Al'Ameen din ba.
*****
A bakin dry centre na gidan muka haɗu ina shanya cottons na goge goge, aikina nake don ni har ga Allah ma ban kula da tahowar shi ba, tinani na ya tafi ga tinanin da ya zame man abun ci, abun sha, a kullum watau tinanin mahaifi na.
Ƙamshin turarenshi ne ya man sallama, yayin da idanunu na suka gaza juyawa su kalleshi, gaba daya naji an zare man lakkar dake jikina, jinin jikina ya katse ya ci gaba da gudu cikin jiniyoyin jikina, domin dai in ban manta ba kwana uku kenan rabon da in sanya shi a idanu na, ni na ma dauka ko baya ƙasar ne kwata kwata ma;
Tinani na ne ya katse daidai lokacin da ya matso daf da inda nake tsaye
"Hey what are u doing here?"
Haka naji kunnena ya faɗa man, ɗan rusunawa nayi a hankali nace "Ya Ameen ina kwana?" "Lafiya" ya bani amsa a taƙaice cikin salon maganar shi da ke ƙara mashi kwarjini a idona,
"ya maganar mu ne ta rannan banji kince komai ba" ya faɗa yana mai tsare ni da idanun shi masu ƙara ruɗa ni,
ɗan kauda fuska ta nayi, sabo da bana so mu haɗa ido dashi.
"umma ta ta hana ni tace kuma nayi maka godiya ga irin ƙoƙarin da kake yi a kanmu Allah ya saka da alkhairi"
na faɗa ina mai sadda kai ƙasa domin nima na san abun ba zai yi mashi daɗi ba;
"its ok"
Ya faɗa yana mai wucewa ba tare da ya tsaya ƙara jin wani abu da zai fito daga bakina ba,
Ni din ma banyi niyyar ƙara tankawa ba, sabo da na san bani da kuma abun cewa.
Kwalla ce ta taru a idanuna, nayi saurin goge ta ina mai fiƙi fiƙi da idanu,amman wata ke ƙara zubowa, shikenan na rasa dama ta, na rasa buri na, umma tafi so muyi ta zama cikin wannan ƙangin na bauta,
Mu fa ba bayi bane da aka siyo a kasuwa, muma mutane ne kaman kowa, Ya Ameen yayi iya ƙoƙarinshi akan mu, sai dai duk yanda naso in karanci halin da zuciyar shi ke ciki akan fuskar shi, bai bani damar hakan ba, kallo na na maida ta saitin da yabi ya wuce, ko burbushin shi ban hango ba, sai dai Ƙamshin turarenshi irin na maza da suka amsa sunansu ya bar mani,
"Nagode ya Ameen ko a haka ka bar mu mun san kaso taimaka mana na faɗa a fili ina mai durƙushewa, gami da sakin wani maraya kuka.
Ba mu ba kawai, duk wani mai aiki dake cikin gidan yana ƙoƙarin taimaka mana, sam baya so duk wani dake ƙarƙashin shi yayi kukan baya kyautata mashi,
Tabbas da duka masu arziki na duniya irin halin shi garesu da abubuwa sunyi ma mabuƙata sauƙi a rayuwa, duk da cewa halin mahaifin shi ya dauko, sai nake ganin ya ma fi mahaifin nashi kula da al'amurran mu a cikin gidan
*Dukka buri na ya wargaje*
*Mafarki na ya tafi*
*Allah kai ne gata na*
*Ka duba lamurra na*
******************************
~Oum-deedat ce~
[8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*
*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)
*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)
*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.
*Fage ~6~*
°^^^^^^^^^^^^^°
Tsawon kwana uku na shafe ban sake jin ɗuriyar Ya Ameen ba, hidimomi na nake yi hankali kwance.
Yau gidan mun tashi da hidimomin aikin abinci, Alhaji Mustapha ne zai yi baƙi, abokan kasuwancin shi daga waje ne zasu zo.
Abinci kala goma Hajiya Babba ta bamu umarnin muyi, mu duka ma'aikatan an rarraba ma kowa nashi aikin, masu gyara gida na yi, masu gogewa nayi, mu da mu ke aikin abincin mun hallara mu duka a babban kitchen ɗin gidan.
Wannan karon harda su Aunty Saudat da Aunty Nihal ne a kitchen ɗin, sai dai banga amfanin su ba, yo eh mana basu da amfani domin kowaccen su kujera ta ja ta zauna suna latse latsen su,sai dai su bada command ɗin yanda zamuyi, wanda a zahiri ma mun fisu iyawa, salon iya yi ne kawai.
Haka muka kammala abincinciccikan duk mun jigata; wannan ce tasa bayan mun gama jejjera abincicikan bisa tangamemen dining table ɗin da yake gefe guda a cikin falon sashen baƙin, na wuce sashen mu domin yin wanka da gyara jikina.
Zuwan su yayi daidai da gama shiryawa ta, kiran Hajiya Kubra ne ya shigo waya ta, tare da bani umarnin zuwa sashen na baƙin domin taya su zuba abincin.
A falon muka haɗu da Alhaji Mustapha ɗin da na kwashe watanni ban sanya shi a idanuna ba domin baya yawan zama; Durƙusawa nayi har ƙasa na gaida shi, yayin da ya amsa man cikin fara'a da sakin fuska, tare da tambayar umma na ko muna cikin ƙoshin lafiya.
A ɗarare nake zuba masu abincin domin harda Hajiya Kubra zaune a wajen saboda baƙi ne abokan hulɗarsu na kasuwanci kuma ita ma tanada share a ciki, wannan ce tasa nake yi a hankali domin kada inyi laifi wajen Hajiyan.
Gama zuba masu abincin yayi daidai da wanzuwar daɗaɗɗen ƙamshi, lokaci guda mamallakin ƙamshin ya bayyana fuskar shi ɗauke da maɗaukakin murmushin da ban taɓa ganin yayi irin shi ba; Sanye yake da lallausan farin tissue yard har kana iya hangen fara ƙal ɗin singlet dake jikin shi, kanshi babu hula hakan ya bayyana kwantaccen sumarshi luf da ita bisa kanshi har sheƙi take yi, hakan ya ba gyaran fuskar shi damar ƙawata fuskar shi da take ɗauke da madaidaici saje, ƙafar shi na Sanye cikin wani cover ɗin takalmi ɗan ƙasar italy sai sheƙi da walwali yake yi.
Cikin hanzari yake takowa cike da kwarjinin shi, lokaci guda yana fadin "am so sorry wallahi na samu tsaikon jirgi ne" ya faɗa daidai lokacin da ya isa gare su yana mai jan daya daga cikin kujerun ya zauna.
Da hannu Hajiya tayi man nuni da in serving ɗinshi, aiko ba ɓata lokaci na duƙa daidai saitin inda zai iya jin me make faɗa, saboda bana so in damesu saboda har wasu sun fara cin abincin;
"Me za'a zuba maka Yaya?"
Na faɗa ba tare da na bari mun haɗa idanu ba, "fried chicken with mixed fruit" ya faɗa shima yana kauda kai gefe cikin salon shi na miskilanci wanda ni na kula ma kwata-kwata shi haka halinshi yake;
Ban ƙasa a guiwa ba kuwa nayi maza na zuba mashi, nuni yayi mani da ido da na bar wajen daidai lokacin da nake miƙa plate ɗin gaba shi, na daga ƙafa cikin sauri na bar falon domin wasu daga cikin baƙin sun fara tsare ni da idanu, ina tunanin shima abunda ya kula dashi kenan.
*******************************
Bansan ya suka ƙare da baƙi ba, domin ni na fita batun su tinda dai na gama masu abin da zan masu, hutu aka bamu cikin gidan na kwana biyu domin family ɗin zasu yi wata tafiya da mu kanmu yan cikin gidan bamu san ina zasu ba, saƙon Alhaji Mustapha ne ya iso mana, dama duk in zasu yi tafiya koda ta yini ɗaya ce ya kan mamu alkhairi irin nashi da ya saba. Kudi ne masu yawa ya bayar a rarraba mana koda zamu buƙaci wani abu baya nan.
"Allah sarki, Allah ya saka ma Alhaji da alkhairi ya ƙara buɗi na Alkhairi" umma ta ta faɗa lokacin da saƙon namu ya iso gare mu, su kau sauran ma'aikatan ƙananan maganganu suka hau yi, wai sun fi so Ya Ameen ya basu kyauta saboda shi bai Iya kyauta ba da yawa yake bayarwa. Kaji butulci irin na ɗan adam, mu dai bamu damu ba ai ance ma raina kaɗan ɓarawo ne, kuma ko ba haka ba umma ta tana da wadatar zuci abu kaɗan ke isar ta a rayuwa hakan ce tasa nima na tashi da irin wannan tarbiyyar.
*******************************
Sun shafe kwana biyar babu su a cikin gidan hakan ce tasa muka samu sauƙin tsangwama da walwala acikin gidan, dama ba mu ke aikin abincin ma'aikata ba iyaka ayi mukai kwano in mun gama ci mu dauraye, iyakarmu gyaran dakinmu sai ko umma ta da take share tsakar gida, domin ita bata son ƙazanta Sam bata iya zama cikin ta, yayin da su kau sauran basu damu ba kitchen ɗin girki kawai suke share wa.
Wani lokaci nakan shiga lambun gidan insha iska ko in katso gwaba ko Apple in ci idan nayi marmarin hakan, umma ta bata hanani domin ta san ko babu komai ba kullum muke samun irin wannan damar ba, hanani sake wa da sauran ma'aikatan kawai ta hanani shima mafi yawancin mazan ne, nima ban damu ba saboda da irin wannan tarbiyyar na taso ta rashin sake wa da maza.
Shugabar ma'aikata mata ce ta leqo ɗakin namu, lokacin ina toilet wankan ƙa'ida na idan na tashi baccin rana ƙarfe uku wanda sake wa yanzu ya zame man kaman nafila cikin ƴan kwanakin nan da sukayi basa nan.
" Maman Suhana Hajiya ce tayo waya, tace a faɗa maku ku gyara masu sashen su duka, Suhana ta gyara na Alhaji ƙarami da na Abie domin dukkan su gobe suna hanya idan Allah ya kai mu"
Dam!! Naji gaba na ya ruguje ya faɗi, daidai lokacin da na fito ina goge kai da towel ɗina na wanka, shi kenan zasu dawo, shi kenan walwala zata ragu, Abunda zuciya ta ke ƙissima man.
"To Talatu, insha Allah yanzu zamuje mu gyara, Amman gyaran zai kai goben tun da kinga yanzu marece ya riga ya kawo jiki" Ummata ta faɗa tana mai kallon Talatun, Talatun ta amsa mata da cewa "To shi kenan Maman Suhana ai ba damuwa gaskiya aikin da yawa, ku fara ɗin zuwa da safen kwa idasa" ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin, da kallo na bita, matar kam kaman ta Allah to sai dai fa fuska biyu gareta, domin ita ce ta gaban goshin Hajiya babba a gidan Amman bata bari a sani,; nima na san hakan ne ta dalilin a cikin gidan nake nawa aikin kuma harda ɗakin Hajiyar nice ke gyarawa.
Haka kau aka yi tuƙuru muka hau gyaran cikin gidan, ko ina yayi ƙal, ya rage gyaran ɗakin Abie ne da ya Al'Ameen ya rage, shima idan aka yi Magriba zanje na gyara na Abie, na Ya Ameen ne sai goben Saboda na san halin wannan sarkin ƴan tsaftan, tsaf zan gyara Amman yana zuwa zai ce baiyi ba.
::::::::::
Washe gari tin da duƙu-duƙu na tashi gami da shiryawa na leƙa ɗakin Shugabar ma'aikata na amso makulli, an ma ci sa'a domin bai barin makullin ɗakin shi a hannun kowa wannan sarkin ƴan tsarin.
Yanda yake na daban, haka ma part din nashi yake, komai dake shashen daban yake da sauran abunda ke cikin gidan, ba wasu tarkace amman an narka dukiya wajen;saitin kujeru ne a falon farare ƙal masu kwalliyar golden haka jefi jefi a jikin su, golden tiles ne malale a falon da ya ƙawatu da wani makeken chinese carpet da ya lashe fin rabin falon bayan su babu komai sai center table na zallan glass fari tar dashi mai haɗe da tumtum irin na gidan sarauta guda biyu tsakiyar falon, akwai stools suma kwara biyu tsakanin kujerun, sai saitin kayan kallo ƴan kamfani Samsung haɗe da Italian Tv stand, up White ne fentin falon yayin da ya dace da cottons masu matuƙar kauri suma kalar golden, sai na'urar sanyaya ɗaki da water dispenser dake maƙale a saƙo guda na falon. Kai kanka in ka kalla sai ka sake kallo, iya tafiya da imani falon ya tafi da nawa.
Corridor ne gefe guda daga bangon hagu da ke falon, idan ka bishi shi zai sadaka da ɗaki ɗaya tal acikin shashen da yake mamallakin shashen, sai ƙofar ɗan ƙaramin kitchen da yake ta cen ƙuryar Corridor ɗin da yake ɗauke da madaidaicin dining area a ciki, kitchen din ya tsaru kaman na wata macen komai na aikin gida akwai shi ciki, sabo da Ya Ameen ya iya girki, in ƴan miskilancin nashi suka taso shi ke girkawa da kanshi yaci abun shi ko kuma in yayi baƙin shi yakan dafa masu abinci simple kuma ya wanke dishes ɗin da kanshi.
Yanda falon ya tsaru sai naga ma kaman bedroom ɗin yafi ƙayatuwa, shima komai upwhite ne da kwalliyar golden, saɓanin toilet ɗin da yake kalar sararin samaniya da fitilu farare, sai ya zamana abun burgewa da ban sha'awa.
Zagewa nayi na gyara ko ina na ƙalƙale, shi tas na kunna boner ta ruwan ƙamshi, take part ɗin ya ɗauki ƙamshi mai sanyaya rai, sannan na kunna na'urar sanya ɗaki domin ƙamshin ya kama ko'ina,bayan na gama na kashe komai na janyo part din na kulle gami da mayar ma da Mama Talatu makullin.
*******************************
Ƙarfe biyar sakaliyya suka iso gidan, yayin da dukka mu ma'aikata muka fita taro su da yi masu barka da zuwa, harda umma ta baiwar Allah da take sanye cikin zurmemen hijab ɗinta, wanda bata ma lafiya kwance take zazzaɓi ne rau a jikin ta, Amman hakan bai hana ta fitowa ba, tinda haka aka saba kafin su shiga part ɗin nasu sai an gaggaisa da kowa tare da jin lafiyar kowa, wannan doka ce daga Alhaji mustaphan wanda a haka dole suke tsayawa suna zuzzunɓura baki suna aika mana da harara su sun dawo a gajiye amman baza'a bar su su shiga ciki su huta ba. Hakan baya damun Alhajin domin ya saba da halinsu tsaf halin mahaifiyarsu ne hakan ta saba masu dashi, halinta ne tin kafin ya aure ta kyamar talaka, masu aiki, sai dai yana tausaya masu har faɗa yana masu a lokutta da dama yakan ce "ku