Showing 15001 words to 18000 words out of 247770 words

Chapter 6 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10397

ganni kaman ba yar aiki ba😅)


Afnan ce ta shigo cikin saurin ta tana cewa "Aunty Suhan maza ki fito, ga yaya cen yana jiran mu na lallaɓo shi, zai kai mu kinsan halin nashi baya son jira, ɗan oya oya ne." Turus ta ja ta tsaya lokaci guda mamaki fal bisa fuskar ta, lokaci guda ta shiga taɓa hannuwa, 👋🏻 sannan ta shiga faɗin "Aunty Suhan wannan kyau haka? Dubeki dan Allah kaman wadda zata je gasar kyau, kina da irin wannan kyaun haka kike boye wa?" jan hannuna ta shiga yi tana faɗin masha Allah wannan ai ni sai ma inji kunyar jerawa dake wlh abu kaman ƙyanƙyasar inji? " ta ƙarashe da zaulaya

Ja nayi na tsaya ina cewa "Afnan Allah in kwalliyar tayi yawa bari in rage, yo ni wa zan ma kwalliya har haka?" murmushi ta sake yi, da ya riga ya zama ɗabi'arta, "ke wasa fa nake maki, Ya Ameen ɗin ne zai tsaya wani jiranki? Har ma fa ya shiga mota mu kaɗai yake jira, kuma yace in na ɗaɗe zan ga wayam, saidai idi dreba ya kai mu" ta shiga faɗi tana mai sake jan hannu na, ni kuma na shiga binta kaman raƙumi da akala.

A tsakar gida muka haɗu da umman tawa, tana shigowa dan shirya zuwa girkin dare cikin gida, da addu'a da fatan dawowa lafiya ta bimu, sannan ta mana gargaɗi da mu kula da kanmu ƴaƴa mata muke, to muka amsa mata gami da jerawa da Afnan ɗin kai ka rantse ƙawaye ne, domin Afnan ɗin ta taddoni a jiki, saidai ɗan tsawo ne kawai zan nuna mata, ba kowa ne ma za'a gaya ma na girme ta ba ya yarda.


Bayan motar ta buɗe mani na shiga, wani sanyi ne mai ratsa zuciya ya mani sallama, ban san lokacin da na ja mun fashi ba, gami da runtse idanu na ba sannan na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya, mota ce mai suna mota, na tabbata ban taɓa shiga mota makaman ciyar wannan ba, duk kuwa da tarin motoci na alfarma da suke gidan.

Tada motar da yayi, shi yayi sanadiyyar dawowa ta cikin hayyaci na, daidaita kaina nayi cikin sanyin magana nace mashi "ina yini Yaya" duk da bana iya hangen shi sosai bayan shi kawai nake iya gani don ta saitinshi nake zaune sai ayan da ya kwanta bisa cinya ta, ina iya hango motsawar shi da motsawar bakin shi ta cikin mirror dake maƙale na driver, "lafiya" ya bani amsa a taƙaice, ban kuma cewa komai ba, sai wasa da na shiga yi da ayan, yana bani labarin school ɗin su a hankali, ina jiyo Afnan ta cika shi da surutu da take zaune gidan gaba wani abun ya amsa mata, wani kuma yayi murmushi kawai ya share ta.

A haka muka isa tanƙamemen super market ɗin da ya haɗa komai, komai na kayan more rayuwa ana saida shi a ciki; ɓalle murfin motar nayi naja hannun ayan muka fita, yayi daidai da fitowar Afnan ɗin tana cewa "Yaya kai ba zaka shiga ba?" girgiza mata kai kawai yayi yana miƙa mata ATM ɗin nashi gami da cewa "30mnt na baku kuma, kuyi maza ku fito ina jiran ku, ina da nawa uzirin rigimar ki ce kawai bana so Lil" (da yake ya kan ce mata Lil wani lokacin)

"OK Bigboo, insha Allah, ta faɗa tana mai ƙamewa cikin zaulaya, zagayowa tayi gami da kama hannun Ayan tayi gaba ni kuma na bita a baya kaman wadda kwai ya fashe mawa, tinda sanyin ac da ƙamshin motar Yaya suka bugeni naji komai nawa ya kwance, kaman an zare man lakka, lallai Ya Ameen daban ne, komai nashi ma daban yake; Ban san mun isa ba saida naji Afnan ta girgiza ni tana cewa "Aunty suhan lafiya dai kuwa? Ko baki lafiya ne?" ɗan murmushi nayi na shiga girgiza mata kai, ina mai cewa "a'a Afnan babu komai kawai dai wajen ne ya burge ni, mu shiga kada mu cinye lokacin mu anan"


Nacewa Afnan ɗin tayi saidai in taya ta zaɓe, haka kau aka yi, duk Abunda na zaɓa sai ta ɗauki biyu, kama daga kayan shafa, kayan maƙulashe, kayan sawa da su eaner wears, Ayan ma da Nasreem ta ɗaukar masu kayan ciye ciye sabo da su basa buƙatar komai.

Haka muka fito masha Allah gaskiya wurin yayi kyau ya ƙayatar dani, haka nake faɗa ma afnan ɗin a hanyar mu ta komawa motar Yayan.

"Ta bangaren shi baya so tinanin yarinyar kan nushe shi a lokutta da dama, sai dai yakan danganta hakan da tausaya masu da yake yi, dubeta don Allah gwanin burgewa yanzu, kaman tayi ta dauwama a haka, ya kula tin shigar ta motar tashi, kashin turarenta ya bayyana kanshi, ƙamshi mai cike da kwantar da hankali, yana so tayi karatu, yana so ta tallafi rayuwar umman tata, yana so su samu ƴanci, sai dai me yasa?, me yasa umman tata take da wani irin tinani, me yasa ta nace ga rashin son tallafa masu da yake yi? Ya haƙura, ya haƙura tin ma kafin ta fara zargin ko yana da wata manufa tashi ta daban akan su, Suhan yarinya ce mai cike da natsuwa, mai cike da kamewa, tana da gudun abun duniya, wannan kaɗai ya isa ya yaba ma mahaifiyar tata, ta nan fannin kuma ta ciri tuta, ta kai a yaba mata gaskiya, kuma yana ganin ƙoƙarin ta, tayi aikin ta na uwa ta haɗa harda na uban ma; "Huh" ya guntsi iska ya fesar, yana saisaita kanshi ga barin kallon ta tin ma kafin ta ankara don baya son raini ya shiga tsakanin shi da ita. 😂

*********

A haka muka isa gidan Afnan ta kama man kayan muka shiga dasu ɓangaren mu, don ta nace cen zamu ajiye kayan ta fitar ma da kowa nashi, a cewarta rabon mu yau ya rantse don duk siyayyar nan da aka yi, cikin kudin Yaya ne, shi yasa ta zage ta ɗibar mana son ranta tinda ba nata aljihun bane yayi kuka, ina jiyo ta tana cewa "Yaya ina so muyi magana, fa wallahi" amsa mata yayi yana cewa "To my Lil, mu bari zuwa dare in na dawo sai mu tattauna, yanzu dai ina da muhimmin uziri kinji auta" ya faɗa yana mai murmusa mata, "OK yaya, as u said bye-Bye, sai ka dawo, a dawo lafiya" ta faɗa tana mai manna mashi ɗan ƙarami peck a kumatu sannan ta sake ɓalle murfin ta fito, na kula ɗabi'ar turawa ta kama su, har basa jin komai su rungumi juna, ko sumbatar juna a goshi, ko kumatu a gaban bainar jama'a, Ni kau tini nayi nisa da ragowar kayan da Ayan saɓe a kafaɗa ta.

Haka ta wawware ma kowa kayanshi, harta umma ta, ta ɗauko mata atamfofi masu shegen kyau ƙwara uku, da less guda biyu, sai hijabai masu ruwan kayan guda uku, da takalma ƙwara biyu, masu kyau zubin na manya, Godiya umma ta ta shiga yi da faɗan na biye mata ta kaso kuɗi da yawa, wannan ai ɓarna ce, "ba komai umma wallahi Albarkarku kawai muke nema" Abunda tace kenan sannan tayi ma umman Alƙawarin za mu kwashi kayan namu da nata masu buƙatar ɗinki, mu kai ma telan dake ma gidan ɗinki, umman taso ta hana ta a cewarta hakan ma ya isa zamu bada nan cikin unguwa ayi mana, ba sai ta ƙara yin wata hidima ba, Amman Afnan ɗin ta nace ai babu komai wallahi duk yi wa kai ne.

Nima ta ware man nawa kayan, wanda sai da tsoro da firgici suka kama ni, rabi da kwantan siyayyar ma ni tayo ma wa, kai ni afnan wacce irin ƙauna take yi mani har haka?, "Godiya na shiga yi mata tare da faɗin sunyi yawa ta rage" ɓata fuska tayi tana cewa"ga duk kan alamu watan ɓatawarmu yayi, ai in tazo Nija bata da ƙawar da ta fini, don me zan maida hannun kyauta baya, banga yanda nake yin kyau ba idan nayi kwalliya? dama maƙasudin siyayyar nice, sabo da bata yo man tsaraba ba da zata taho" godiya muka shiga yi mata ni da umma ta, lokacin da take kwasar nata kayan da basa da wani yawa sai kayan ciye ciye kawai.

Sallama muka yi da ita, tare da mani Alƙawarin gobe zata shigo musha fira in na gama ayyuka na na cikin gida, har bakin sashen namu na raka ta, ina mai walwala da annuri a fuska ta, domin duk wanda yace yana son ka ai ya gama maka komai a rayuwa, ina ganin sauran ma'aikata ana ta zunɗe na, to suma dai da zata wuce sai da ta gaida su, ta masu ɗan Alkahiri a cikin kuɗin da ke pos ɗinta, Amman duk da haka baiyi masu ba, masu mugun abun ganin wannan tarayya tamu ta watse suka ƙudura, masu gulma suka naɗa, domin a gaban su muka shiga da leda niƙi niƙi, Amman sunga ta fito da guda ɗaya tal a hannu, ita ma ba'a cike ba, ashe yau Hajiya Babba da labari kenan, wai don ma basu san Yaya Al'ameen ne ya kai mu ba, wai ni Allah ai da kashin mu ya bushe daga ni, har mahaifiya ta, a haka dai na tura masu aniyarsu, na juyo salin alin na shige namu ɗakin tare da turo ƙofa, domin ɓoye kayan namu, sabo da wasu daga cikin su ƴan ganin kwam ne, zasu iya leƙo wa ko don ganin wainar da ake toyawa a cikin ɗakin.

***************************

Ƙarfe tara da rabi daidai, Afnan tayi sallama sashen Yayan nata, izini ya bata ta shiga daga ciki, kai tsaye kujerar da yake zaune kai yana latsa laptop ɗin shi ta nufa, sanye yake da 3quater ruwan kunun kanwa, watau army green, da fara ƙal ɗin singleti, sanyin falon madaidaici ne, har yanzu gyaran da Suhan ɗin ta yi ma ɓangaren nashi yana nan, tinda ba yara ke akwai ba a sashen, ba yawan abokai ya cika ba, (yo wannan miskilancin nashi zai bar shi yayi abokai ne?) fuskar shi tar cikin haske da yake fitowa ta laptop ɗin, lallai Yaya Al'ameen ƙaƙƙarfan namiji ne, hakan ko ya samo asali ne da jim ɗin da yake zuwa akai akai, a sashen motsa jiki na gidan, kyakkyawa ne na gaske, cikin kalar fatar shi fara tas tas da ita.


Murmushi yake bin ƙanwar tashi da shi, har zuwa lokacin da ta iso wajen nashi, hannu ya miƙa mata tare da zaunar da ita dab da shi yana mai faɗin "Lil wannan magana dai wace iri ce, da har aka bata muhimmanci haka?"

Kallo ta bishi dashi, tana mai ƙara jin ƙaunar yayan nata cikin ranta, shi kaɗai ne zai zauna da ita ya fahimci damuwarta, har yayi mata maganin ta, in ka ɗauke aunty feena da dama ita wannan kaman uwa ta ɗauke ta, tinda a hannun ta ta taso.


" yaya so nake muyi wata magana mai muhimmanci, dafatan zaka saurare ni, kuma ka fahimce ni, kayi ma maganar tawa kyakkyawa duba na tsanaki, don Allah"


Na ɗaya daga cikin dalilan da yake sanyawa yana ƙara jin ƙaunar ƙanwar tashi fiye da kowa a cikin ƴan uwan nashi kenan, manyance da natsuwa tsara zance ga kuma girmama na gaba da ita, "Yaya wata Alfarma nazo da ita, dafatan zaka taimaka ka biya man wannan buƙatar, na sani duk gidan nan babu wanda zan tun kara ya saurare ni, kaman kai, kuma na san zaka iya shi yasa na zo wurin ka Yaya" ta katse mashi tinanin shi, cikin marairaicewa.

Murmushi yayi yana mai tattara dukkannin natsuwarshi zuwa gareta, "ina jin ki Lil wannan wace ALFARMA ce kike buƙata gare ni haka da kike ta kwana - kwana haka?" ya faɗa cike da murmushin da ke ƙara ƙawata mashi fuskar shi, tare da fiddo zallar kyawon fuskar tashi, dimfull ɗin shi yana mai ƙara nutsewa cikin kuma tun nashi.

" Yaya Maganar SUHAN ce" ta faɗa cikin tarabbabin yanda zai amshi maganar tata....... "Ehem!, ina jin ki Afnan me Suhan ɗin tayi ne?" ya amsa mata fara'ar fuskar shi na raguwa, abun da ya ƙara tsorata Afnan ɗin kenan cikin in ina tace

"maaaganaaar... Kara.. Tun,,, ta Yaaaya"....





~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


_*Jinjinar ban girma ga mai gida na, Abbu-Deedat. Nagode da irin goyon bayan da kake bani da irin yadda kake ƙarfafa mani guiwa, a duk al'amurran da na sanya gaba. Godiya marar adadi Allahu ya bar ƙauna ya raya mana Ahmad Deedat🥰*_



_*Page ~8~*_


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


"Look afnan✋🏻" ya katse ta daga inda indar da take yi, sannan ya ɗora da faɗin "Na riga nayi duk iyakar ƙoƙarin da zan iya yi akan issue ɗin karatun yarinyar nan, tin ma kafin ke kizo, saboda haka bana jin zan iya maida kaina acikin al'amurran su, tinda har mahaifiyar ta bata son al'amarin karatun nata, zai fi kyau muma mu dakata hakanan, mu barta tayi ma mahaifiyar ta biyayya Allah ya sani mun riga mun yi iyakar iyawarmu" ya ƙarashe maganar cikin wani yanayi na ƙunar rai lokaci guda yana ɗan ƙutawa gami da janyo laptop ɗin tashi ya buɗe, ga duk kan alamu yana nufin ya gama magana kenan.

Shiru falon yayi, in baya ga ƙarar Ac da take bada sanyi ƙaɗan-kaɗan baka jin komai, ita kanta Afnan ɗin shiru tayi kaman ruwa ya cinye ta, ta rasa minene tinanin umman suhan ɗin akan ɗiyar tata, amman dai koma minene ita bazata bar lamarin haka nan ba, za tayi iya yi ta tinda ta kula babban burin suhan ɗin kenan, don dai Allah yayi ta da kawaici da biyayya ga na gaba da ita.

Muskutawa ta sake yi ba don ta gaji ba, sannan ta marairaice dama abunka da auta an saba shagwaba "Na sani wlh yaya na, sai dai ba zamu bi ta kan umman ba, ita ba sanin daɗin abun tayi ba, Yaya Pls, don Allah ba don ni ba, ka taimaka mani, bana so ma ta gane da sa hannuna" shiru yayi mata na wasu daƙiƙai, sannan ya nisa tare da faɗin "Toh Naji, yanzu ya kike so ayi?" tini fara'ar fuskar ta ta dawo, afnan kenan baiwar Allah, yarinya da kyakkyawa zuciya.

"Yauwa Big boo" ta fada cike da jin daɗi sannan ta kamo hannuwa shi ta riƙe su gam, sana ta ɗora da faɗin " Dady, Dady zaka yi ma magana, shine kaɗai zai iya sawa umman suhan ta yarda, ba tare da samun wata matsala ba, Pls my Lovely yaya" shiru yayi sai daga bisani ya nisa gami da faɗin "Is OK dear, Consider it done, kar ki damu ina so ki bar maganar nan a hannuna zamu san yanda zamuyi, ni kaina ina tausayin Rayuwar su, mutane ne da suka cancanci a tausaya masu don ga duk kan alamu sun fi sauran ma'aikatan shiga halin damuwa, masalan ita umman suhan ɗin" ya faɗa cike da basarwa kai kace ma bashi ne yayi maganar ba, saboda bazaka taɓa kawo ma ranka cewa miskilancinshi ma zai bar shi fahimtar wani abu ba.

Miƙewa tayi tsaye, gami da yin wani ɗan tsale cike da annashuwa, "Nagode Yaya, na gode Allah ya saka da Alkhairi ya bar ƙauna, I love u sooo much, Good night Swt Yaya" ta faɗa tana mai nufar ƙofa domin fita, saboda dare yayi, da murmushi ya bita, wannan zuciya ta Afnan da kyau take, tabbas shi ya san ko ba daɗe ko ba jima sai sun yi alfahari da yarinyar

"Ameen" ya furta a hankali cikin salon san kauda tinanin abun a ranshi, domin aikin da yake yi Afnan ɗin ta shigo, mai muhimmanci ne.

×××××××××××××××××××××××


Washegari bayan mun kammala aikin mu, mun dawo sashen mu munyi wanka wajen ƙarfe biyu na rana, aiken Hajiya Kubra ya iske mu, ni da umma ta wai tana neman mu, har ga Allah gaba na sai da ya faɗi, domin har jin daɗi nake inje in kammala aiki na tana sashen Alhajin ta yanda ma babu abin da zai haɗa ni da ita, sai dai wajen zuba abinci. Ummana ce ta amsa da cewa gamunan zuwa, lokacin da ƴar saƙon ta fita ne ta juyo da kallon ta gare ni da nayi fiƙi fiƙi da idanu, ina ta tinanin laifin me kuma muka aikata yau, saboda duk idan aka yi mana irin wannan kiran to fa ba lafiya ba.

"ki kwantar da hankalin ki mama na, insha Allah lafiya lau, babu abin da zai faru sai alkhairi" da to na bita domin in kwantar mata da hankali saboda yanzu umman tawa sai a hankali ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, don ko jiya dakyar muka yi bacci, ciwon zuciyar ta ne ya kusan tashi. Hijabi na na ɗauko na sanya gami da wucewa gaba umman tawa na biye a baya na, babu mai cewa ƙala har muka isa babban sashen gidan, ta bangare guda kuma zuciya ta na luguden duka, domin na san rashin mutucin Hajiya Kubra sosai, fata na dai kada al'amarin ya shafi umma ta, ko minene dai ya tsaya iya kaina.


Sallama muka yi daga bakin ƙofa, Mama Talatu ce ta amsa mana daga ciki tare da faɗin "ku shigo mana, kuka tokare daga bakin ƙofa kaman wasu baƙi" shiga muka yi, ina gaba Ummana na baya; zaune muka iske ta bisa ɗaya daga cikin sofar da suka yi ma falon ƙawanya, gefe na samu da niyyar zama ƙasa ta dakatar dani, "a'a Suhana, ku shiga dai daga cikin falon Hajiyan, tana daga ciki tana jiran

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login