Showing 66001 words to 69000 words out of 247770 words

Chapter 23 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10418

dire da ƴan tsale tsale.

Bai aune ba yaji an kai mashi cakuma, zuwan shi kenan ta wurin yaji ihun mace, ni kau da dai Naji na samu wanda zan kama sai na kuma ƙwaƙume shi ina ta kurma ihu da tsalle tsalle, duk na cukuikuye hijabi na da fuska ta, wayata datayi tsallen baɗake gefe ta faɗi har headphone ɗin ya zare, karatun ta take ci gaba da rerawa a hankali a hankali.

Ƙoƙarin raba ni yake da jikinshi, ni kau sai ƙara ƙwaƙumeshi nake yi cikin murya ta mai cike da tsoro nake faɗin "wani abu na bina, ƙila kunama ce, a taimakeni"

"Ke ke wai meye haka ne, ya isa babu abinda ke binki, ba kunama bace, gidan nan babu kunama, ana yin feshi ki natsu"

Ban ko saurare shi ba, har saida na cire hijabi na wurgar da ita ta gefe, kama zanin nayi da niyyar kwance wa ya daka man wata irin tsawa, ba azziƙi na dawo cikin hankali na.

Sai sannan ne wata irin kunya ta kama ni, ganin Abunda nake shirin aikatawa, gani tsaye ko hula babu a kaina balle ɗan kwali, duk nayi wurgi dasu harda hijab ɗin.

Kaina kuwa kaman wata sabuwar mahaukaciya, dama ɗazu muka je akayo mana saloon, babu wanda baiyi santin kyawon da kaina yayi ba da tsawon da yayi har kusan tsakiyar baya, dama ban taɓa yi ba wannan ne yina na farko, duk da cika da yawan da gashin nawa yake dashi haɗi da tsawo.

Tattara gashin nawa na fara yi, na maida baya, sannan na wawuro hijab ɗita na sanya gami da ɗaukar wayar tawa da har yanzu sautin ƙira'ar malamin ke tashi.

Juyawa nayi da niyyar barin gurin ina mai cewa "Yi haƙuri yaya" dakatar dani yayi fuskar na tashi murtuk

"Ko kin koma cikin gidan basu gama kaɗe kaɗen nasu ba, zo muje"

Yana gama faɗar haka ya juya ya cigaba da tafiya, zuwa ga ƙofar da zata sadaka da bayan gidan, wanda sai kayi doguwar tafiya kafin ka shawo kwana zuwa bakin Gates.

Mamaki ne cike da raina, in bishi muje ina cikin wannan daren, ko ba ma haka ba, in ummata ta ganni ince mata me? Ko idan wani ya ganni yaje ya faɗa mata fa?

Ganin yaja ya tsaya ne gami da ɗan waigowa ya sanya ni ɗaga ƙafa cikin sauri na shiga binshi, juyawa yayi gami da cigaba da tafiya, duk da ɗan hasken farin wata da fitilu jefi jefi dake bayan gidan, da naga zai yi man nisa na kan ɗaga ƙafa a sukwane in bishi, har muka ɓulla ta fuskar gidan.

Hamdala nayi ganin mutane jefi jefi a ƙofar gidan da alama ma wasu zance sukeyi, bugun zuciya ta ne ya ƙaru, ganin ya nufi motar shi dake fake gefe guda ya kunna ya shiga, alama yayi man da in zagaya in shiga nima.

Ba musu, dole na buɗe gidan gaba na shiga shiga na zauna, ɗan kwali na a hannu, sai raba idanu nake yi.

Tada motar yayi gami da ficewa daga Layin, bai tanka mani ba haka nima ban ce mashi ƙala ba, kowa na fama da ƴan miskilancin shi a kai, ni gani ma nake yi ya cika ƙarfin hali, haka kawai sai yasa ni in shiga motar shi ya ɗauki hanya dani alhali bansan inda zai kai ni ba?

"Sai daki zanyi" Abunda yace kenan ya ja bakinshi yayi shiru, ɗan zaro idanu nayi, bansan zancen zuci ya fito fili ba, ɗan waiwaya wa nayi na kalle shi, ina mai sadda kaina ƙasa, "kayi haƙuri, ummata bata san na fito ba Kaga dare yayi, Shiyasa nake jin tsoro"

Maimakon ya bani amsa, sai shiru da yayi yana mai maida hankali shi kan tuƙin da yake yi, shiru ne ya biyo baya acikin motar kaman ma ba zai tanka ba, sai kuma cen Naji yace

*"Kallon me kike yi mani rannan??? "*




~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~24~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Shiru nayi mashi ban tanka mashi ba, har yanzu fa ni a tsorace nake, yo naga muna ta sharara uban gudu hanyar ba kowa, bansan ina muka nufa ba, sai aikin murza yatsu nake, ganin ban bashi amsa ba na ɗauka ya bar zancen kenan.

*"Kallon me kike man rannan?*

Tambayar ta ƙara zo man a bazata, bayan duk tsawon lokacin da muka ɗauka ban tanka ba.

Shahada nayi wajen cewa" kayi haƙuri"

"Ba haƙuri na tambaye ki ba, so nak insan dalilin kallon, ko nayi maki kama da wanda kika sani?"

Ya jefo man maganar da banyi tinanin zata iya fitowa a bakin shi ba.

Shiru na sake yi mashi ina sun ne kaina, ni sai ma ya bani ƴar dariya, bansan sautin dariyar tawa ya fito ba sai ji nai yana cewa" Dariya ma na baki ko?"

Ɗan juyawa nayi ina mai sake kallon shi, shi ɗin dai ne, Ya Ameen ne yake ta tuƙin shi hankali kwance yake zaroman magana kaman ba shi ba, ashe dama yana magana haka?

Tinani nake ta faman yi, yayin da shi kuma ya sake maida hankalinshi a kan tuƙin shi, ban tashi farfaɗowa daga kogin tinanin da na shiga ba saida naji tsayawar mota alamar dai mun iso inda zamu.

Ɗaga idanuna nayi ina mai ƙare ma wajen kallo, yayin da shi kuma har ya fita gami da kullo ƙofar.

Airport ne muka zo, lallai wajen ya ƙayatar dani, ba ƙaramin ƙaramin kyau wajen yayi mani ba, na saki jiki ina ta more kalle kalle na, tinda na san baya cikin motar, Naji maganan shi kaman daga sama.

"Malama sai ki fito"

Ɗan zabura nayi, kunya duk ta dabaibayeni, domin Sam bansan yana tsaye yana kallo na ba, ashe glass ɗin motar ƙasa yake kaɗan.

Fitowa nayi, zullumi da fargaba duk sun cika man zuciya, na san yanzu umma ta suna cen suna nemana, wayyo Allah na, na san kuma Hafsat zata ce mata bata san inda na tafi ba.

Gaba yayi ina bin shi a baya, sai harɗewa nake ta cikin hijab, yana kallo na kuma bai ce man komai ba, sai nayi kaman zan faɗi, sai ya juyo ya ɗan kalle ni Amman ba zai ce an komai ba.

Mutane ne ke ta hada hadarsu, ga wajen tar da hasken ƙwan fitilu mashi masifar haske kaman rana.

Wasu da ƴan alluna, an rubuta su aye, ga mutane suna ta fitowa daga wani ɗan ɗaki na glass, tin daga nesa ya hango shi, da ƴar sassarfa ya ƙara so inda muke gefe tsaye Ya Ameen yana ta gabana haka.

Tafasa sukayi lokaci guda suna sakar ma kansu murmushi na tsabar ƙauna irin ta aminai

"Ya dai Friend? Ai ban ɗauka zakazo haka da wuri ba, na Ɗauka sai ka shanya ni kaman yanda ka saba"

Ɗan murmushi na gefen baki ya sake yi, sannan ya shiga cewa "wallahi ai kasan gidan mutane sun yi yawa, duk an cika gidan da Bidi'o'i sun dameni, suna neman fasa man kunne Shiyasa ma na fito haka da wuri"

Juyawa sukayi suka shiga tafiya suna riƙe da hannayen juna.

Da alama ma ƙila ya manta da wata abu wai ita Suhan a bayan shi tsaye.

Ganin haka nima sai na shiga binsu, mu yi tafiya mai ɗan nisa, sannan muka isa ga motar tashi.

Sai sannan ya tina da ita, juyawa yayi a hankali yana kalle kalle alamar yana neman wani abu.

Da yake ina ta gudan ɓarin mota bayan Bilal ɗin sai bai lura dani ba, ganin ya juya alamar zai koma ta inda muka fito ne ya sanya ni cewa "gani nan yaya"

Tsayawa yayi, gami da juyowa, ya sanya key ya buɗe motar, Bilal ɗinne ya juyo a ɗan razabe jin wata irin siririyar muryar mace ta bayan shi.

Kallon tuhuma ya shiga yi ma Al'ameen, yayin da shi kuma ya basar yana mai shige wa motar, bayada zaɓi illa shima ya shiga, zamana cikin motar ne yayi daidai da tashin motar yayi revos ya halba ta bisa titi.

Ba wanda yace uffan har muka yi nisa, ganin shirun tayi yawa ne kowa da Abunda yake saƙawa cikin rai, ya sanya Bilal kauda shirun ta hanyar cewa "Mutumena ya hidimar biki"

"Suna cen suna yi" ya bashi amsa a taƙaice, shiru Bilal ɗin yayi don ya san halin Al'ameen ɗin, tinda ya ji ya fara amsa mashi a gajarce ya san ƴan maganar basa kanshi.

Har muka isa gidan ba wanda ya kuma tankawa, an tashi daga mothers eve ɗin da ya tashi daga evening ya koma night, sai aje ayi ta faman ƙara'in salloli kuma.

Da kwai sauran mutane, Amman jefi jefi, har cikin gidan ya shiga gami dayin parking, dama abunda nake jira kenan, nayi saurin ɓalle murfin motar gami da ficewa, kai tsaye sashen amaren na nufa da yanzu cen ɗakinsu Hafsat nake kwana.

Duk agaji anyi tuɓus, wasu ma duk sun kwakkwanta, hakan ce ta sanya ba kowa ne ya lura dani ba, Hafsat ce kawai zaune tana waya da angonta, ita kau Afnan ta shiga watsa ruwa toilet.

Lallaɓawa nayi gami da kwanciya kafin Hafsat da take tsaye bakin window ta ganni.

"Tashi Tashi na ganki wallahi, gaya man daga ina kuke?" Abunda Naji hafsat ɗin ta faɗa kenan, bansan ma lokacin da ta katse wayar ba, sai ganin ta nayi har ta ƙara so inda nake kwance bisa katifa.

Tashi nayi duk borin kunya ya kama ni, cire hijab ɗin na shiga yi, ina cewa" uhmm wai daga ina muke? Ko dai daga ina nake, ko kin ganni da wani ne da zaki ce daga ina muke?"

" Eh" ta bani amsa kai tsaye, sannan ta ɗora da cewa "ke da Yaya Al'ameen da Yaya Bilal da ganku kun dawo yanzun nan"

Ɗan zaro idanu nayi, kaman ƙasa ta tsage in shige nake ji uwa wadda tayi wa sarki ƙarya.

"Kinga fa wallahi shine ya......" fitowa afnan ce daga toilet ɗin ɗaure da towel ya katse man maganar da nayi niyyar faɗa ma hafsat ɗin.

"Humm" kawai afnan ɗin tace tana ɗan murmusawa, da alama duk taji zancen da mukeyi, saidai ƙala bata ce ba.

Lura da ita ne da Hafsat ɗin tayi ya sanya ta basar da zancen itama, tana mai miƙewa zuwa toilet ɗin.

Duk ina zaune ina saƙawa da warwarewa, har afnan ɗin ta gama shirin kwanciya, lokacin ne Hafsat ta fito da alama itama wanka tayo, "Ki tashi ki bar tinanin hakanan Aunty Suhan kije kiyo wankan kema" Abunda afnan ɗin tace man kenan, ta sake gyara kwanciyar ta gami da juyawa tana murmushi.

Duk fa na bi na tsargu kaina, kaman wadda kwai ya fashemawa haka na miƙe ina jan ƙafafun nawa har na shige toilet ɗin. Da murmushi itama Hafsat ɗin ta bini, tana fatan Abunda take zargi ya tabbata, da tafi kowa jin ɗaɗi, kuma taga ƙarshen Hajiya Kubra da ta ɗauki son duniya da burin duniya ta aza shi akan yaron nata.

Makullin sashen kawai ya miƙa mashi, yana mai cewa "bari in nemo mana Abunda zamu ci" Amsa Bilal ɗin yayi gami da juyawa ya nufi sashen aminin nashi, yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya kaɗa kan motar gami da sake ficewa daga cikin gidan.

A bisa kujera 3seater ya zube, gajiya fal a cikin jikin shi, Amman ba ita ce tafi damun shi ba, ganin aminin nashi da yayi da yarinyar da yake iƙirarin auren ta, kar dai ace da gaske abokin nashi yake akan zancen yarinyar, saidai lura da yayi da yanda ya gansu, da kuma irin zaman da aka yi cikin motar har kawo dawowar su gidan babu wata alama dake nuna maka cewa su ɗin soyayya suke, Amman in ko haka ne, menene dalilin Al'ameen ɗin na yawo da ita cikin mota da daddare haka?

Ya daɗe nan kwance yana saƙawa da warwarewa har Al'ameen ɗin ya dawo, nan ya tada shi kwance yayi zurfi a tinani, ɗan dukan shi yayi a cinya yana "tashi yallaɓai, ba dai bacci kake yi ba haka, ko wanka ba kayi ba balle kaci abinci"

Tashi yayi yana murje ido, yayin da Al'ameen ɗin ya wuce kitchen ɗauko spoons da plate da lemo da ruwan sha, a haka ya dawo ya tada abokin nashi zaune yana narai narai da idanu.

Zuba masu abincin yayi, yayin da ya jawo stool ya ɗora masu akai, Al'ameen ya san darajar baƙo, duk da kasancewar Bilal ɗin ɗan gida kuma aminin shi, haka yake in yaso har ruwan wanka yana haɗa mashi in ya kawo mashi ziyara.

Har suka gama cin abincin, Bilal na ma Al'ameennɗin kallon tuhuma, to abunka da aminai, tini Al'ameen ɗin ya ɗago shi, murmushi yayi yana mai goge baki da tissue

"Bari in gaya maka Abunda kake son tambaya ta tin kafin ka tambaya, yarinyar da ka ganni ɗazu ya ita, na san dai ka santa kasan komai a kanta, kuma har yanzu ina kan baka na a kanta, saidai ita bana tsammani ntasan komai, dalilin da ya sanya kuma ka ganni tare da ita, shine....... " nan ya kwashe komai ya faɗa mashi a gajarce.

Murmushi yayi yana faɗin" Mugu, watau har kasan Abunda nake son tambayar ka ko? To ai shikenan Allah ya zaɓa mafi alkhairi a cikin Al'amarin, Amman dai ka kula gudun ja ma yarinyar matsala ko a wajen mahaifiyarka, kadai ga yanda take iya ƙoƙari wajen bata tarbiyya" yana faɗin haka shima ya ajiye spoon ɗin dake hannun shi ya tashi gami da shige wa bedroom domin yin wanka da rama salloli dake kanshi, sannan ya kwanta, shi kau oga Al'ameen, maida komai yayi kitchen, gami da wanke na wankewa, ya gyara komai tsaf, dama haka yake, baya son ƙazanta ko kaɗan, duk wani abu da ya san zai yi na tsabta baya jira ayi mashi shi keyi da kanshi, saidai Abunda ya san zai ɓata masa lokaci ne. Hatta da girki ba Abunda bai iya dafawa ba, saboda shi ba abincin kowa yake iya ci ba, ko zaman da yayi ƙasashe waje shi keyi a kanshi abinci, matuƙar bai yadda da wanda aka kawo mashi daga cikin hotel ɗin ba.

Sun daɗe suna fira kafin su kwanta, yayin da ni kuma har bayan na kwanta ɗin juye juye kawai nake yi, hafsat ɗin na kula dani, har yanzu bata gaji da wayar ba haka, tinani nake yi na abubuwa da dama, Amman tinanin nawa yafi karkata ma ga Jarabawa da na rubuta kusan kwanaki da dama baya.

Sai daga baya ne tinanin Al'ameen ɗin ya faɗo mani, lallai ni bansan ma me zan kira Abunda yayi mani dashi ba

Gashi in akula har yaja hafsat ta fara mana wata fassara ta daban, ɗan guntun tsaki naja ina mai sake gyara kwanciya ta gami da karanto addu'oin barci, banga dalilin ma ɓata lokaci yin tinanin abun ban haushi ba, ko in kalle shi inji me? Ko ya ɗauka nima ina cikin ƴan matan da suke rububinshin ne oha? 🤷🏻‍♀

Washegari ansha bacci, yayin da maree da mahaifiyarka mama talatun baccin su ragagge ne, suna ta saƙa yanda zasu yi su mallaki Al'ameen ɗin, domin suna hango ma kansu rayuwa ta jin daɗi da zasu iya fuskanta nan gaba kaɗan ba da jimawa ba, saidai Abunda ya ƙara ɗugunzuma hankalinau shine ganin da mareen tayi ma Suhan ɗin a motar Al'ameen lokacin da suka dawo, haka ta koma fa tayi ta rusa kuka, da gaske son Al'ameen ɗin ya kamata, yayinda ita kuma mama talatun ba ta wannan take ba, abun duniyar kawai take hange, haka kawai ta shiga ce ma mariyar zauna nan abun duniy ya kashe ki, akan waccen kucakar da na san ko kyauta aka bashi ita ba amsa zai yi ba, kawai dai ita ce da uwar ta ke shisshigi mashi, Amman zanyi ma abun tufkar hanci.

Kowa hidima yake yi fafa, gida fa ya kacame, wasu irin garƙama garƙaman tuƙwane ake ɗorawa, bayan abincin da ake yo order ɗinshi daga manyan restourent.

Ƴan kankiya sunyi bajinta ta nan fannin, domin duk wata sanwa da za'ayi suna kamawa, yayinda ƴan uwan Hajiya kubra kejin sun wuce nan, kaman su ba zasu iya fitowa yin girkin hidima ba, rarraba ake da abinci kaman ba'a so.

Kowa sai shirin yin ƙauyawa yake yi yau, da yake duka amaren yau zasu yi, ko wanne ɓangare shiri akeyi, sai shigowa akeyi da dami damin kara, da su goruba, magarya ɗinta, nan cikin gida kuma an sanya ayi lafiyayyen dambu, da zogala ɗanya, ga lafiyayyar fura da amma da taji lafiyayyen nono da yoghurt da madarar ruwa, abun dai gwanin ban sha'awa.

Hajiya Kubra taji haushi wannan event ɗin, saida taga cewa kowa na murna dashi ne sannan ta sake, to muma ta ɓangare namu mun yi murna, saboda yau ne za'a zama ɗaya, da mai ji da kanshi da mara ji da kanshi duk za'a zama ɗaya, matan sunyi shiga irin ta Fulanin usul, musamman suka ɗauko wasu Fulani suka zo sukayi masu kwalliya irin tasu ta filani, an zane masu fuksokinsu ram da kalli baƙi da ɗige ɗige, sai suka ba kansu dariya, kuma suka burge kansu, masalan da suka ji angunan na cewa sunyi kyau.

Banso banso nake cewa, Amman a haka saida Hafsat da afnan suka matsa aka yi man saisa saisa, nima kayan Fulanin na sanya sun matuƙar amsa ta, sun yi man cif cif, dama saida Hafsat ɗin ta zaɓo mana saƙi mai kyau harda jikkarsu ta Fulani.

A haka kowa ya hallara aka fara event, kasancewar da marece ne, da sauran Haske kuma ga maza a tattare guri guda, ya sanya ni takura, gefe na koma gami da zama bisa wani kututture ƙarƙashin bishiyar gwaba, ina ta kallon su ina dariya, hannuna riƙe da ƴar sandarsu ta Fulani ina wasa da ita.

Kwallon su nake tayi, ina tafaman murmusawa, yanda maza ke gatsar rake suna sha suna santi, gefe mata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login