Showing 90001 words to 93000 words out of 247770 words

Chapter 31 - BAN FI K'ARFINTA BA

10 Oct 2024

10462

nan daka ɗauko ka saurari mahaifiyarka, lallai zaka ga nasara, Amman ba wai nace karka aure ta bane, saidai inaso tin wuri tin kana wasa, kada abun yazo ya kasance ya zama da gaske ka fara son yarinyar nan a ranka, abun sai yafi rashin daɗi" ya ƙarashe yana waiwaya wa ya kalli cikin ƙwayar idanun abokin nashi.

Lallai ko Bilal ɗin bai faɗa ba zantukan nashi sun ratsa zuciyar abokin kuma aminin nashi, shiru yayi yana sauraren maganar da zata fito daga bakin shi.

Nisawa Ya Ameen ɗin yayi yana Sauke wata gagarumar ajiyar zuciya, saidai ya kasa buɗe bakin shi balle yace wani abu.

Lumshe idanu yayi a karo na biyu yana sake sauke ajiyar zuciyar sannan ya sauko ƙasa ya zauna yana fuskantar abokin nashi cikin ɗaki ya irin ta maza ya fara magana kaman baya so

"Na fahimce ka abokina kuma nima na daɗe ina nazarn hakan, saidai zuciya ta ba zata iya jure ganin su cikin wani hali ba, su ɗin mutane ne masu tawakkali Amman inaso kayi mani wata Alfarma guda ɗaya" ya ƙarashe yana kamo hannuwan abokin nashi duka. Sannan ya ɗora da faɗin

"bana so ina raɓarta nima, bana so ina jiɓintar al'amarin su sosai, gudun ja masu matsala, saidai ba zan iya jure ganin su a mawuyancin hali ba, inaso zamuyi masanyar aiki ne, zan je in cigaba daga inda ka tsaya, ni kuma inaso ka cigaba daga inda na tsaya, inaso in nisanci gidan nan gabaki ɗaya, inaso ka ɗauki alƙawalin kula dasu da karatun Suhan har zuwa gamawarta, ka riƙe mani alƙawali da amana"

Cikin ɗan zaro idanu bilal ɗinmke cewa "Wat? Me kake nufi ne Friend? Kana nufin a kanta zaka bar ƙasar taka da mahaifn naka? Kasan ne kake faɗa kuwa?

Jinjina mashi kai yayi alamar tabbatas da Abunda yake faɗa ɗin sannan ya ɗora da faɗin

" Zuciya ta, ta fara saba wa da bauta mata, ta fara saba wa dajin ɗuriyar ta a kullum, ba zan iya jure zama a muhalli ɗaya da ita ba, ba tare da na kusanci inda suke ba, Nidai kawai inaso ka amince, gobe goben nan nake son barin ƙasar da asuba zan faɗa ma abba zanje yin wani abu, kai ne zaka cigaba da kula da komai, tini na daɗe ina wannan nazarn, wannan tasa na gama shirya komai yanda zaka fahimta"

Ya faɗa yana jawo laptop ɗin tashi, gami da kunna ta ya shiga nuna ma bilal ɗin schedule ɗin aikin, duk da ya ɗan san wasu, saidai ayyukan da aka ƙirƙiro daga baya, "zaka gane abokina, kuma mu cigaba da waya duk Abunda baka gane ba, bayan auren yarinyar na maka alƙawari zan dawo kai kuma ka koma bakin aiki ka"

Ɗan jim bilal ɗin yayi, sai kuma ya nisa yana cewa "Ba damuwa Al'ameen zanyi maka yanda kake so, nima na fuskanci gara tafiyar taka, akan ka zauna matsaloli su taru suyi yawa, gara ka tafi, ita kuma insha Allah ba zan taɓa bari tayi kewar rashin ka ba, zan kula da ita kaman yanda kake yi, harma da mahaifiyar tata.

Ɗan murmushi yayi da iyakar shi leɓo, yana jin wani ƙuna daga cen cikin ɓargonshi, gani yake yi kaman yayi sallama da ita ne. Ya ƙudurta a ranshi cewa zai warware matsalar da ya sanya yarinyar da mahaifiyarta kafin barin shi ƙasar a gobe.

Cikin daren yaba Bilal ɗin number ɗinta gami da goge ta a cikin wayar shi baki ɗaya yayi blocking ta yanda koda ta kira shi ma ko ta neme shi ba zata samu ba. A haka suka kwanta kowa jigum babu mai tanka ma wani.

Duk da kafin su kwanta ɗin saida ya haɗa traveling bag ɗinshi, da duk abubuwan da zai iya buƙata. To dama dai ƙasar ba baƙuwarshi bace a, hasalima kamfanin da bilal ɗin yake running na Alhaji Mustapha ɗinne, wannan ne ta sanya komai zai zo da sauƙi baya buƙatar amincewar kowa.

Bayan an taso sallar asuba ɗinne ya biyo mahaifin nashi har sashen shi, ganin hakan ne Alhajin ya san cewa da magana, sauraren shi yayi tsab, gami da fahimtar yaron nashi, Allah sarki ashe ma babu wata maganar soyayya ko makamancin ta a tsakanin shi da yarinyar, gamsuwa yayi da bayanin Al'ameen ɗin yayi da yace idan Allah ya bata miji kafin ya dawo kawai a aurar da ita ga wanda take so, kuma yana buƙatar ya gaya ma hajiya kubran cewa ya janye sukda daga nan sashen Alhajin wajen Hajiya kubran zai wuce.

Addu'a da fatan nasara ya bishi da ita, yana mai faɗa mashi lallai kafin ya wuce yaje yayi ma kaka zuwaira sallama kuma duk ya jejje gidajen ƙannan nashi domin yaga muhallin nasu.

Hajiyar ba wai ta yarda da maganar da yazo mata da ita bace, saida taga fa lallai shi da gaske yake yi, ba kunya ta rungume shi tana sanya mashi albarka gami da nuna mashi zallar farin cikin ta, harda irin abun nan na Munafurci take cewa "Allah sarki yarinya da har na ƙullace ta, to ai ba komai zasu iya komawa ma bakin aikin su in Alhajin ya amince"

To shi dama burin shi kenan ya warware ƙullin da ya san duk kanshi ne ake ta wannan dambarwr, ko ba komai daga baya idan suhan ɗin ta gane dalilin tafiyar tashi zata sanya mashi albarka da gode ma bakin nasu da ba zai rasa abinci ta dalilin shi ba.

Sashen nashi ya koma yana ba bilal labarin yanda sukayi da hajiya, sunyi mamaki kwarai matuƙa, oh shi kenan ashe shi talaka ba mutum baneba?

Sai da ya kira yayi booking flight kafin gari ya idasa wayewa, aka sanar mashi sai ƙarfe biyar na yamma jirgin zai tashi, hakan ce ta sanya ya gane cewa yana da sauran time da zai gama aiwatar da dukkanin abubuwan da zai yi ɗin.

Bayan na tashi ne na share ko ina na gyara, umman tawa ce tayi mani tuni da zuwa gidan Hafsat ɗin, hakan ce ta sanya ni kiranta domin tayi mani kwatance, ta shaida mani zata turo sadeeq ɗin ya ɗaukeni, ita da har ma tayi fushi, gashi afnan yanzu zata tafi gidan Aunty Saudat, za'a barni ni ɗaya, ƙawayen nata sakkon tafiya sukayi ha yar bata da kyau.

Ƙarfe sha biyu kuwa sai ga sadeeq ɗin, umman tawa ce tayi mani a dawo lafiya gami da cewa in kula kada in kai marece, da to na amsa mata ina mai ficewa daga gidan.

Daga nesa ya hango fitowarta har zuwa shiga motar tata, kauda kai yayi, baya so ya sake shiga Al'amarin ta tinda anyi Wancen ta kwaranye, bilal ɗin na kula dashi, dama tare zasu fita zuwa office ɗin tare suke da dogarawan da aka bashi, wanda yace duk kansu suit zasu sanya ɗaya daya iya mota ya dingabjannbilal ɗin ɗaya kuma ya zama massinger ɗin office ɗinshi kowanne zai biya shi albashin shi mai tsoka, aikuwa sunyi murna, kuma sun yaba da karamcin ubangidan nasu da kullum suke jin labarin tarin alkhairanshi ga mutane

Office ɗin suka isa ya nunnuna mashi komai, sannan yayi mashi maganar ɗaukar matasa ƴan family ɗin sadeeq mijin hafsat ɗin, sannan suka wuce ya nunnuna mashi building ɗinshi na estate da aka kammala komai sai lounching da za'ayi, sannan ya kikkira manajojin shi na sauran kamfanonin da suke sauran jihohnn ya haɗasu da bilal ɗin ta yadda komai zasu tunkari bilal ɗin kai tsaye.

Daganan suka wuce gidan Aunty Saudat bayan sunyi sallar azahar, sun matuƙar yabawa da tsarin gidan, gida ne tanƙamemen babu Abunda babu na kayan more rayuwa, cen suka tadda Afnan har yanzu akwai sauran mutane ƙawayen Saudat ɗin a gidan, daganan suka wuce tare harda Afnan zuwa gidan Aunty Nihal ɗin, Afnan kuwa tin a gidan Saudat take rigimar barin ƙasar da zai yi, sukda zai koma kusa dasu ne, kuma zasu fi saurin ganin shi anan, saidai bata so yayi ma suhan ɗin nisa, gani take yi idan suhan ɗin ta kucce mashi da wuya ya iya samun wata mai nagartarta, ita kau Saudat ɗin a take tayi murna, ko ba komai sun san waccen maganar ta wuce.

Itama Nihal gidan ta yayi matuƙar kyau, kowa da kalar kaya ta wanda su suka zaɓosu da kansu, basu wani jima ba, saboda suna sauri ne, kuma itama akwai dangin mijin ta sosai a gidan kusan ma cike yake sosai da yake ita dangin shi suna zaune ne Abuja.

Gidan hafsat ne na ƙarshe don haka daga cen zasu koma gidan yayi ma iyayen nashi sallama.

Bamusan da zuwan su ba, da yake abokan sadeeq ɗin na gari yau zasu wuce suma, ya sanya na kama mata mukayi masu special girki ko ƙarasowa ba suyi ba sai ga su Ya ameen ɗin.

Ko ba komai taji daɗin zuwan su, dama tana so ta ƙara yi masu godiya akan irin hidimar da suka sha da su da dangin mijin nata.

Ceman tayi in shirya masu abinci, nace mata ban iyaka kunya nake ji, tace ai dole inji kunya na san Abunda muka tafka rannan, sai dole kowa ya gane kuna soyayya.

Ƙyaleta nayi ban tanka mata ba, har ta gama shirya masu abincin, da sunce ba zasu ci ba, Amman jin ƙamshin girkin yasa bilal cewa ta zuba masu kaɗan, har yake tambayar ta ita kaɗai a gidan?

Cemashi tayi mu biyu ne, baƙi zata yi ne ma Shiyasa Suhan ɗin tayi masu girki, don da ita cewa tayi sunsha lemo, Amman suhan ɗin tace masu akwai fa masu barin ƙasar ke kin yarda azo maku kara kubar mutum ya tafi da yunwa.

Duk zubar da take yi Ya ameen ɗin na jin ta bai tanka ba, ya dai ɗan ci abincin, duk da test ɗin abincin ya mashi daɗi, saidai kuma bai san Abunda ya to kare mashi maƙoshi ba da ya hana shi walwala ayau.

Hafsat ɗin ce take ta kawaici ganin bai nemeni ba duk kuwa da ta sanar dashi cewa ina gidan, ni kuma na kasa fitowa daga kitchen tin da ɗazu naga text ɗinshi yana tambaya ta wai ne ya hanani fitowa ɗazu? To ban dai bashi amsa ba tinda banda abun cewa ɗin.

"Yaya ko in turo maka Suhan ɗin?" ta tambaye shi daidai lokacin da yake goge baki da ƴar tissue.

"Ɗan kallon bilal ɗin yayi sannan yace" Ƙyaleta kawai Hafsatu Sauri mukeyi tafiya zanyi n.... "." Kirawo ta" cewr bilal ɗin da ya tari numfashi abokin nashi.

"To tace gami da miƙewa ta shiga kitchen ɗin da nake tsaye zafi duk yabi ya isheni.

" Kije inji Ya Ameen da Abokinshi" haka kawai ta faɗa tana mai juyawa zata fice

Saurin jawo hannunta nayi ta dawo baya, cikin ɗan waro idanu waje na shiga cewa

"Ke... Kina nufin a haka zan fita babu ko gyale jikina? Kalli fa skirt ɗina ya kama ni sosai...

" To miye? Ba yayyenki baneba?" ta faɗa tana janye hannuwan ta gami da idasa ficewa ta ƙyaleni tsaye ina ta rarraba idanu.

Ganin ba mafita kuma na kusan share minti biyar ya sanya ni shahadar fitowa

Daidai lokacin da Al'ameen ɗin ya kai duban shi ga agogon da yake ɗaure a wutsiyar hannun shi na hagu

"Kaga fa Malam idan ba zata fito ba mu wuce kawai kasan fa...."

Maganar ta maƙale daidai lokacin da na fito ina ta matse matsen jiki da dukkan alamu ni kaina kunyar kayan nawa nake ji.

Idanunmu suka sarƙe cikin na juna, ya kai kusan second biyar yana kallon a, lokaci guda ya janye idanun nashi ga barin kallon nawa, daidai lokacin ni kuma na kai zaune bisa kujera ina gaida su.

A gaggauce suka amsa gami da tambaya ta lafiyar mu lau dai ko? Lafiya na amsa mashi, bilal ɗinne ke ƙara mani congrat na Jarabawa lokacin da Al'ameen ɗin ya kai kallon shi kaina yana mai cewa

"Tafiya ta kama ni, ga Bilal nan ko me kenan sai ki tuntuɓe shi, zai gama maki komai insha Allah" yana gama faɗar haka ya miƙe yana shirin ficewa.

Hafsat ɗince ta fito riƙe da wata jikkar kwali mai kyau a hannuwan ta, ta ƙara sa ga Al'ameen ɗin gami da miƙa mashi tana mashi fatan Allah ya tsare ya kiyaye hanya.

Bilal ne ya maida kallon shi kaina shima yana mai miƙewa gami da ce mani "Ya bani number ɗinki insha Allah zan kira ki" ya ƙara sa shima yana mai juyawa ya fice.

Har gaban danƙareriyar motar tashi da his excelency ya bashi ta raka su tana mai waving ɗinsu har suka fita a harabrr gidan da mai gadi ta wangale masu gate. Domin gidan na Hafsat duk yace ma na sauran ban wuri a kyau da haɗuwa.

Hatta kayan da aka yi ma hafsat ɗin saida sadeeq ɗin ya cire su ya cenza mata wasu sabbi dal masu masifar kyau ba tare kuma da dangin shi kun sani ba gudun ƴan tsogunguma.

A falin ta iskeni zaune jikina sanyi ƙalau, to me ke shirin faruwa ne? Nidai na san Al'ameen ɗin ba haka yake yi mani ba, na kula ma ko kallon a baya son yi a yau, ko na bashi haushi ne rannan dana ruga ɗaki? Ko dai banyi ƙoƙari bane......

"Ke Suhan lafiyarki ƙlau kuwa? Naga jikin ki yayi sanyi, da ɗina dake wallahi wani lokaci ke baƙauya ce, ko irin ƴar rakiyar nan ma baki Iya ba"

Firgigit nayi ina mai binta da ido bansan lokacin da na samu kaina da tambayar ta ba "wai da gaske Ya Ameen tafiya zai yi?"

"eah mana Suhan, waike da kina nufin baki sani ba? Bai gaya maki ba?"

"Huh..." Na sauke ajiyar zuciya lokaci guda ina mai ce mata "wallahi ban sani ba Hafsat"

Mamaki ta shiga yi, har tana zaulayar ta wai wannan wace irin soyayya ce?banza nayi mata ban tanka mata ba, Amman fa gaskiya zan faɗa jikina ya mutu murus wallahi.

Su kansu ƴan kankiyan sunyi mamakin tafiyar, Amman da yake sun san yana yin aikin nashi sai sukayi mashi fatan alkhairi, sun ɗauka zuwan na aje a dawo ne.

Ƙarfe biyar bilal ɗin ya kai shi airport ɗin, ba ɓata lokaci jirgin nasu ya ɗaga zuwa america.....


#cying

Wash gaskiya na gaji fans gashi nan nayi maku na kwana uku.
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~30~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Zaune yake cikin jirgin, saidai ya ma rasa tinanin da zai yi, gaskiya wani sashe na zuciyar shi na raya mashi yayi wauta, idan har sonta ne baiyi bai kamata ya baro ƙasar ba, sai yayi tinanin hanyar da zai warware ƙullin da shine ya ƙulla shi da kankin kanshi.

Har jirgin su ya dira ƙasar ya kasa natsuwa a zuciyar shi, sai yayi kaman ya juya ya yanki ticket ɗin komawa sai wata zuciyar kuma ta hana, da haka dai har driver ɗin da zai ɗauke shi ya ƙara so bai lalubo mafita ba.

Haka ko da ya isa zuwa gidan, komai a sanyaye yake yin shi, gani yake yi kaman yayi sallama da ita kenan.
Shi me ma ya hau kanshi da har tinanin barin ƙasar yazo kanshi? Bayan ya san mahaifiyar ta Suhan tana da gagarumar lalura ta ciwon zuciya, me zai faru in tashi mahaifiyar ta cigaba da ƙuntata masu da gallaza masu? Meyasa ya baro ƙasar ba tare da ya gano munafikin cikin gidan ba mai ƙulla dukkanin makircin?

"Ooops*

Ya faɗa yana mai dafe kai, lokaci guda ya faɗa bisa tafkeken gadon da yake mallakin shi, tsuru yayi yana mai lumshe ido, kewar gidan har ta fara damun shi, saidai ya gaza gane kewar ta mecece, tin da mai yasa idan ya baro gidan baya jin irin wannan kewar?

Waya ya lalubo gami da danna ma Bilal ɗin kira, ringing biyu kuwa ya ɗauka, shaida mashi yayi ya sauka lafiya, sannan ya ke tambayar shi sauran abubuwa. So yake ya tambaye shi suhan ɗin da ya san dai iyanzu bacci take yi domin idan ya kintata daidai yanzu zai kama kusan ƙarfe sha biyn dare a ƙasar tashi nigeria.

Saidai ya kasa tambayar, ganin Bilal ɗin bacci yake ji sosai, ga dukkan alamu ma ya fara baccin ya tashe shi ya sanya shi datse kiran yana mai ce mashi zasuyi waya dasafe idan Allah ya kai mu.

Shima Bilal ɗin da yake ya fara bacci bai wani ja ba, ya kashe wayar tashi yana mai tura ta ƙarƙashin fillow ɗin, shi kau ta ɓangaren Ya Ameen jifa yayi da wayar tinani fal a ranshi, ya rasa dalilin shi na tinanin ta har haka, to me ma ya hana shi tambayar abokin nashi ita?

Saidai kuma fa yana tsoron kada Bilal ɗin yace bai fita sabgar yarinyar ba, gashi kuma har ya sanya shi zama ƙasar tashi domin ya taimaka masu.

Jawo wayar yayi yana mai ɗan sakin ɗan ƙaramin tsoki, ji yake yi kaman yayi unblocking ɗinta ko status ɗinta ne ya dinga dubawa, saidai fa so yake yi ya manta da Al'amarin ta, so yake yi lokacin da zai koma ta riga da tayi aurenta ta yanda ma ba zai sanya ta a gaban shi ba balle yayi cousing wata matsalar tsakanin shi da tashi mahaifiyar.

Saki wurga wayar yayi bisa gado yana mai miƙewa ya shiga tuɓe kayanshi, so yake yi yayi wanka ko yaji sauƙin Abunda yake ji a jikin shi da kuma zuciyar tashi, domin tinda ya baro ƙasar tashi tsikar jikin shi take a tashe ya rasa kuma dalili.

Da haka ya wuce zuwa toilet

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login