Showing 198001 words to 201000 words out of 219361 words

Chapter 67 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

47020

sarrafata sai kuma ta tsaya cak dan tunawa da ai bata da no Win AA Win. Jagwab takai zaune a cikin sofa. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran RK ta tambaya number Win AA Win, sai kuma wani sashe na zuciyar ya ?waSeta. Ta hasko AS, shima dai ta ce a'a. Oum. Nanma taji bata gamsu ba. Dama dai tana da layin Yaya Fawzan ne ma, shi kam ?ila ta iya tambaya. To ko RK Win zatace ya bata layin Fawzan Win?. Gamsuwa da wannan shawarar ya sata kai hannu zata Wauka sabuwar wayarta sai idannunta suka sauka akan wayar RK daya bata.
? ? ?? (Mizai hana ki duba a wayar nan ko zaki samu no Win ma) Wani gefe na zuciyarta ya ambata mata. Ai da sauri ta Wauka wayar kuwa ta hau binciken numbers Win Kai daki-daki abinda bata taSa maida hankali tayi ba. Bawani yawane da su ba, dan kusan ma da alama duk contacts na family Winsa ne a ciki. Amma sam babu sunan AA babu alamarsa. Har zata ajiye cike da damuwa sai kuma ta sake scrolling ta koma tsakkiya inda taga My S1 da 2 har ma da 3. Sai kawai ranta ya bata My Son yake nufi, babban yaya 1, Fawzan 2, AA 3. Cike da tabbatarwa ta jinjina kanta. Amma gudun samun matsala sai tace bari ta Wan gwada amma bazatayi magana ba tunda tasan dai RK zai gani ya kira shi ba ita ba.....

______&

? ? ?  Kamila Kano kuma? Wace irin tafiya ce haka ta ujila kin san fa gobe juma'a, kuma na sanar muku Saturday zaku rakani Kaduna ko? .
? ? ? ?  Hakane Abahn su, nima tafiyar ta dole ce. Kuma ai a goben zanje na dawo in sha ALLAHU. Sai nabi jirgin safe na dawo da yamma. Dan ALLAH kayi ha?uri ka barni, ALLAH idan banje a goben ba da wahala na samu lokaci .
? ?  Humm to wai mizaki je yi ne? .
?  Nafa gaya maka Yaya Raliya ce bata jin daWi, tunda aka gama hayaniyar bikin nan sai a hankali. Jiya su gambo sukaje, shiyyasa nace nima bari naje gobe ai kaga dai baza'ace ba'aga mutum ba. Da harda Oum Win yara ma zamu je, to bana son takura mata tunda jikin bawani yayi tsanani bane ba .
? ? ? ? ?an iska kaWan Abah ya furzar daga bakinsa tare da lumshe idanunsa ya buWe kamar yanda AA keyi idan zai yi magana.  Shike nan ALLAH ya kaimu. Aiko sai ki daure ki ?arasa gidan Baba dan kwana biyu yayi mura shima. Ya hana na faWa muku ne dan kar Fateema ta tada hankalinta .
? ? ? ??  ALLAH ya bashi lafiya. In sha ALLAHU can ma zan fara zuwa, har Baban Yola ma saina le?a su dan kwana biyu bamu je ba. Da bikin nan naso zuwa sai kuma tafiyar nan tamu ta ratsa .
? ? Kai kawai Abah ya jinjina mata ya cigaba da aikinsa. Ita kuma ta mi?e cike da farin cikin samun nasara tace masa tana zuwa. Nan ma hannu ya Waga mata kawai.....

_________&

? ? ?? Bugun shigar kiran na bugawa ne da bugun zuciyar Maanal. Sai da wayar tana gab da tsinkewa sannan aka Waga. Sosai ta rumtse idannunta ta kasa cewa komai, daga can shima kuma baice komai ba har na tsawon sakanni. Sai zuwa can ?asa-?asa ya furta.
? ? ? ?  Ina massallaci, idan na fito zan kira .
?? Daga haka ya yanke. Da masifar ?arfi ta saki numfashinta data ri?e, tare da buWe idanunta. Kai anya zata iya kuwa? Kodai ta barshi kawai. Kai ina bazata iya ba, maganar videos Win nan sune tashin hankalinta. Kada mutumin nan yaje ya aikata abinda zai zama sanadin bugawar zuciyarta. Ganin lokacin sallah zai ?ure ya sata ha?ura da tunanin ta tashi ta hau cire kaya duk da ba sallar zatayi ba, tana dai son yin azkar Winta a irin lokacin kamar yanda ta saba. Jiki a sanyaye ta wuce bathroom yin wanka.
? ? ?? Har akai sallar isha'i bai kira ba. Ita kuma ta kasa fita dan gudun kada ta fita ya kira. Bata son zuwa da wayar falo kuma ya kirata a gaban Didi da Uncle Sadeeq. Koda Linda ta shigo ta sanar mata abinci ya zama ready catai ta kawo mata Waki yau ta gaji ne. Ta kuma ce tana gaida Didi. Da girmamawa Linda ta amsa mata ta fita, ita kuma ta hau shirin barci. A haka Linda ta sake dawowa Wauke da abincinta. Kasa taSa abincin tayi, ta zauna a bakin gado ta Wauka novel ta hau karatun dole wai duk dan cinye lokaci. Sai dai sam ba wani fahimta take ba sam.
? ? ? Sai ?arfe tara da wani abu kiransa ya shigo. Zabura tayi daga kwancen da take tana duba wayar, ganin shine ke kiranta video call ma sai da zuciyarta ta girgiza. Ji take kamar ta?i Wagawa, amma zuciyarta na ingizata. Haka ta tashi zaune ta warware ?aramin veil Win data naWa a kanta ta rufe jikinta sannan ta Waga dai-dai gab zata tsinke. Ai wani irin faWuwa gabanta yayi lokacin daya bayyana mata a screen Win wayar tar. Jikinta har rawa yake ta kife wayar da sauri tana ambaton sunan ALLAH numfashinta na wani sam da ?asa da sauri-sauri.....

? ?? Daga can shima AA Win kife wayar yayi da sauri yana ambaton sunan ALLAH, harga ALLAH shi duk zatonsa Rafeeq ne fa, ko video call Win yayisa ne dan tabbatar da Rafeeq Win yana a Kanon ne kamar yanda yace zai je. Dan gaba Waya ya manta ne da maganar kiranshi da yace zai yi Wazun sai yanzu yana cikin wanka abin yazo masa a rai, shine yana fitowa batare da tunanin komai ba ya shiga masa video call daga shi sai guntun towel daya saka iya ?ugu zuwa gwiwa. Gashi ya ajiye wayar a saman mirror ne ta yanda ta hasko jikin nashi sosai. Ya jima tsaye hannayensa duk biyu dafe da mirror Win yana ambaton sunayen ALLAH kafin ya samu ya Wan dai-daita. Wayar ya Wauka, har yanzu tana online sai dai baya ganin komai sai duhu. Zama yay da ?yau ya katse kiran, ma?oshinsa sai yawo yake cikin wuyansa da sauri-sauri. Gaba Waya yama rasa wane kalar tunani zai yi akan wayar Rafeeq a hannunta. Sai duk yaji zuciyarsa ma na masa zafi. ?ayar number RK ya shiga kira, sai dai harta katse ba'a Waga ba. Cike da takaici ya sake ajiye wayar, sai da ya bada wasu sakanni zuciyarsa ta Wan sauka sannan ya sake Waukar wayar yay mata normal call.........
'?






09032345899



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________

.........Harta yanke ba'a Waga ba. Haka ya sake kira. Kira fin biyar bata Waga masa ba. Ya cije lips, dan duk duniya Oum kawai yakema kira fiye da Waya sai ko Abah. Amma daga basu ba in har ya maka kira Waya baka Waga ba shike nan, sai in ka kirashi back, bai kuma zama lallai ya Waga maka ba sai yaso koda shike da bu?atar wani abu kuwa.
? ?? Samun kansa yay da sake kiran, yanzu ma har ya fidda rai sai kuma yaji an Waga. ?oyayyar ajiyar zuciya ya sauke acan ?asan ma?oshi, tare da kai hannu ya shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake ji?e da damshin ruwan wanka. Kamar Wazun yanzu ma shiru tai masa, amma sai ya danne yay sallama. Amsa masa tai murya ?asa-?asa, kai daga ji kasan a cikin kunya take.
? ? ? ??  Am sorry nazata Rafeeq ne, shiyyasa na kira a wannan yanayin .
? ??  Uhm .
Kawai ta faWa a can ?asan ma?oshi, alamar matsanancin nauyinsa take ji har ma bata son maganar. Shina ya fahimci hakan, dan haka ya saki batun kawai.
? ? ? ?? Cikin son kauda wancan yanayin ya katse shirun da sukayi da faWin.  Kina son ganina ne? .
? ?? Da sauri ta ce,  A'a, dama.......
? Sai kuma tai shiru. Numfashi ya Wan sake fesarwa, kafin a ?agare ya furta,  Daman mi?....
? ? ? ? Sosai tsigar jikinta ke tashi saboda yanda yake magana can ?asan ma?oshi. Ga wani amo dake ratsa mata zuciya na fita daga cikin silent voice Win nashi. Da?yar ta iya danne kanta, da WaWWaya ta ce,  D..a man akan Abideen ne .
? ? ? ? ? Lips Winsa ya ciza da ?arfi, kamar wanda yake a gabanta idanunsa suka Wan kaWa. Muryarsa na Wan canjawa da ?ara kauri ya furta,  Miye damuwarki da shi Win wai? .
? ? ??  Yazo gidanmu ne .
? ?  Gidan ku? .
 Eh har ya sanar min komai daya faru. Wlhy hankalina a tashe yake da maganar videos Win nan. Kada mutumin nan ya cutar dani kamar yanda ka faWa, kuma wlhy ko saninsa banyi ba, bamma taSa ganinsa ba.
? ? ? ??  Amma yake i?irarin an bashi aurenki? . Yay maganar cike da zafi.
? ?  Ni wlhy ban sanshi ba ?arya yake min. Ni dan ALLAH ka bani number Winshi zanyi magana da shi .
? ? ?? A ta?aice ya ce,  Banda .
Shiru ta Wanyi na wasu sakanni dan jin yanda yay maganar a Zafafa. A tunzure, kuma cike da shagwaSa itama ta ce,  Toni ya kake so nayi? .
? ? Shiru ya mata, har sai da ta cire wayar a kunne ta kalla. Ganin yana online ya sata sake jin haushi. Cike da tsiwa ta ce,  Ni zaka wula?anta dan na nema taimakonka? .
? ? Nan ma shiru. Ai a fusace ta yanke kiran, tare da dangwarar da wayar. Shima a nasa Sangaren wayar ya ajiye kawai ya mi?e. Zuciyarsa sai kumbura take a cikin ?arji. A haka yay shirin barci ya haye gadonsa. Yana ?o?arin Waukar Alkur'ani dan yin karatu wayarsa ta motsa. ?auka yay da tunanin itace ta sake kira. Amma sai yaga number yarinyar nan ce dake damunsa, yayi blocking numbers Winta fin huWu, amma yanzu saita koma kiransa da sabbin lauyuka. Kasancewar kusan irin wannan lokaci take kiransa a kullum yasa ya gane. Maida wayar yay ya ajiye batare daya Waga ba ya cigaba da buWe Alkur'anin. Dan yanda yake jin zuciyarsa karatun kawai zai yi yaji sanyi......
??
_________

WASHE GARI.

? ? ? ?? Yau juma'a, koda Maanal taje office signing kawai tayi ta fito. Dama tama tsayar da mai taxi Win daya kawo ta. Tana ?o?arin shiga taxi Win motar AA ya shigo. Kallo Waya taima motar ta Wauke kanta ta shige abinta. Sai dai tana ?o?arin rufe murfin taxi Win idannunta suka sauka akansa. Shima kallona yake cike da wani yanayi na tuhuma-tuhuma, mamaki, da kuma kewa. Fuska ta yamutsa tare da Wauke idanunta a kansa tace ma mai taxi Win,  Muje . Mai taxi da bai san mike faruwa ba yaja motarsa yay gaba...
? ?? Daga Mawaad Company wajen gyaran jiki aka sauketa. Dan Didi nacan tare da Barrah. Itama gyaran jikin aka shiga yi mata, dan Manaal ?ar gaye ce. Aka mata ?unshi dai-dai misali ba?i da ja kaWan da yay mata ?yau kamar itace ma amaryar. Dan Didi sai tsokanarta take yi. Ita dai murmushi kawai take yi batare da tace komai ba. Basu baro wajen ba sai la'asar. A gajiye suka shigo gida. Nan ma kuma basu zauna ba suka ?arasa shirinsu. Biyar da rabi a train station tai musu. Sun iso Kaduna ana magriba. Amal ce da su Munaya suka zo Waukarsu. Ai fa Munaya ta ma?al?ale Maanal dan ALLAH ya haWa wannan ?auna. Gashi kuma Munaya na kama da Maanal Win sosai.
? ? ? Sun iso gidan cike da mutane, dan yau za'ai mothers event. ?azun akayi Sister & brothers event da ?annen Yazeed suka shirya ma amarya. Kusan ma duk danginsu ne a wajen sai ?awayen amarya. An kuwa rankwashe an ?walle dan ango kansa dole ya halarci wajen bisa tirsasawar Hajiya Yaya. Kasancewar su Maanal na wajen gyaran jiki basu maida hankali a gani ba. Koda yake ita bama tana bibiyar komai bane, Didi ce idan ta gano da Amaal ke bata labari.
? ? ? ?? Koda suka fito a mota da yawan mutane sukai musu caa da idanu. Wasu ma har suna Wan ?us-?us. Cikin ikon ALLAH kuma Maanal na fitowa akan Yazeed ta fara sauke idanunta. Ya fito daga sashen Daddy abokansa kusan shida da duk ta sansu zagaye da shi. Yayi masifar ?yau cikin shadda Winkin tazarce, ga hula ya murza fuskarsa na fidda wani annurin gyaran fuskar da yasha. Sosai ya zama wani sakwakwa saboda ganin Maanal. Har takai suma abokan nasa duk suna zuboma inda sukaga yana kallo idanu. Suma dai kamar sun Wan shiga shock da gannin Maanal Win, sai sukai duru-duru.
? ? ? ?? ?auke kai Maanal tai tare da jan hannun Munaya da Barrah tai wucewarta sashen Ammie. Haka kawai ta Wan ji Waci a ranta. Sai faWi take, (yace bai son aure amma gashi yana faman zuba kwalliya da washe baki kamar tsohon gwauro) a fili kam miskilar fuskarta ta shanye komai. Suna shiga ta saki su Barrah ta Wane Ammie.
? ? ?  La'ila yarinyar nan wai karyani zakiyi ne dan ALLAH .
? ?? Ammie ta faWa tana kai mata mintsini. Dariya Maanal ta sanya da sake mamaye Ammien sosai. Sai kuma ta mata kiss a gefen fuska tana faWin,  I miss you sweetie na .
? ?? Dariya ?an falon suka sanya. Dan dangin Daddy ne da suka sauka anan sashen Ammie Win. Sai yanzu Maanal ta farga da mutane. Sai kuma taji kunya ta shiga Soye fuskarta a jikin Ammie. Nan ma dariya kowa ke mata har dasu Amaal da suka shigo. Sai kawai ta janye jikinta ta nufi bedroom Winta da gudu. Dan tasan duk rintsi Ammie tasan zasu zo bazata bari kowa ya shiga Wakin ba tunda ma akwai na ba?i ai. Aiko babu kowa Win, an dai gyarshi tsaf yanata ?amshi.....

? ? ? Bayan sun huta Ammie ta sakasu shiryawa domin zuwa wajen event Win. Maanal taso ta turje. Amma Ammie taita lallashinta. Dan bata son Manaal Win ta zauna a gida a fassara zaman nata da wani abu daban. Haka badan taso ba ta shirya tsaf cikin wani swiss lass fitted gown datai masifar zauna mata a jiki. Ta zauna tai kwalliya dan a Sangaren kwalliya ma Maanal artist ce sosai. Ta koya kuma ta iya saboda sonta da ado, dan ma yanzu kura tayi lafiya. Su Amaal ma har Ammie duk itace ta musu kwalliyar, tai Wauri daya saka kitsonta fitowa Was kamar ka lashe. Koda suka fito babu wanda bai yaba ba a falon. Wasu a dangin Daddy Win har suna faWin,  Kai jama'a yarinyar nan ma ai tafi amaryar ?yau da komai ga nutsuwa wlhy. Amma uwarsa na neman cuta masa. Ga yarinya mace har mace Masha ALLAH .
? ?? Ita dai Maanal da su Ammie babu wanda yace komai. Haka suka fito compound. Kusan duk an wuce. Sai Wai-Waikun mutane a gidan da suka rage. Dan ana kai wasu ne ana dawowa. Dole Maanal taja mota Waya, Amaal taja Waya Shahidah ma haka. Dan mota uku sukai, a hakan ma a Wan matse suke dan Ammie tace bazatai driving Win dare bane dan Daddy ya hana.....

? ___________&
? ? ?
? ? ? ?? Gida ne katafaren gaske daya amsa suna gida. Komai a cikinsa tsari ne irin na gogaggun ?an boko da sukaci suka yada kai aka kuma tashi a cikin rayuwa irin ta turawa. A nutse farar bafulatanar dattijuwar ke sakkowa daga staircase Win dake tsaye ?am a tsakiyar katafaren falon tamkar an zana. Sosai ta manyanta, sai dai tsufane irin na masu jin daWi da babu wahala. Ga ?aramin jikin Fulani ALLAH ya bata. Cike da girmamawa masu aikin dake ta ?o?arin shirya abinci a ?aton dining table suke mata sannu da fitowa. Amsa musu tai da kulawa. Kafin ta furta,  Babu wanda ya fito ne har yanzu? .
? ? ? ?  Eh Mah-mah, amma Alhaji ?arami da Yaya Rafeeq yanzu suka dawo suna a sashen Yaya Rafeeq .
? ? Kanta ta jinjina kawai. Sai kuma ta sake juyawa upstairs Win tana faWin,  Ku ?arasa wani yay kiransu. Bara nama Doctor magana . Daga haka ta sake hayewa saman.
? ?? Fin mintuna goma sai gasu sun fara firfitowa. Kamilallen tsoho da akaga jiya akaga yau Dr Kasheem Kura ne ya fara fitowa matarsa Hajiya Maryam Ishaq Darma biye da shi. Sai ga kuma wata matashiyar mata da bazata wuce shekaru talatin ba da Woriya itama. Sosai take kamanni da Mah-mah da su Oum. Hakan na nufin itama ta fito daga tsatson Baffa Ishaq Darma ne. Yara biyu biye da ita ?yawawa da shekarunsu zasu iya kaiwa biyar da bakwai. Da gudu suka barta suka nufi tsoffin kakanninsu. (Rufaidah kenan, itace Autar su Abah, dan Baba Umar Ishaq Darma mahaifin Abah ne ya haifeta. Itace kuma ke auren Sulaiman ?anin Oum dake bima Hajiya Majdiya, RK kuma ke bi masa. Yaransu uku duk maza, babban mai shekara tara bai kai ga fitowa ba. Suna zama a dining Win RK da Sulaiman da suke kira Alhaji ?arami suma suka sakko. Hira suke suna dariya kamar wasu abokai, duk da Alhaji ?arami ya girmi RK nesa ba kusa ba akwai sha?uwa mai yawa a tsakaninsu. Rayuwar Turai sun tashi sune abokan juna, sune ?an uwan juna. Suma duk kujera suka ja suka zauna, bayan RK ya gama Waga yaran sama suna dariya.
? ? ??  Barka da dare Abbu, Mah-mah barkan ki .
? ? Murmushi Hajiya Maryam da Dr Kasheem sukayi a lokaci guda idanunsu akan RK da yay gaisuwar. Cike da kulawa Mah-mah ta ce,  Auta anya tuzurancin nan bai isa ba haka nan? Na fara gajiya da baka abinci

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login