Showing 42001 words to 45000 words out of 219361 words

Chapter 15 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

46971

a sabuwar rayuwarta, sai dai anan Win ma ta gamu da wata jarabawar rayuwa a cikin mugayen kishiyoyi da kansu kawai suka sani......
? ? ? ?  Asia! Kuka kike yi? .
? ? Furucin Daddy ya katse mata tunaninta. Da sauri ta saka hannu cikin dabara ta share hawayenta, sannan ta juyo garesa fuskarta da murmushi.  A'a Daddyn Hameed wane irin kuka kuma. Kawai dai na kwanta ne .
? ? ?  Humm Asia kenan, nasan kuka kike, kina kuka saboda kina ganin kamar na tauye hakkin ki dana ?a?ank.....
? ?  Ya arrahaman . Ta faWa da sauri tana mai gaggawar Waura tafin hannunta a saman bakinsa. Zuuuu hawayen da take ri?ewa suka shiga zirarowa. Kanta ta fara girgiza masa da sakin kukan gaba Waya.  Dan ALLAH kada kace haka Daddyn Hameed, ban taSa raba Wayan biyu a tsakanin su Maanal da sauran yaranka ba. Ni kaina inama mantawa bakai ka haifesu ba, saboda kana musu dukkan abinda uba kema ?a?a. Kana musu abinda mahaifinsu ya gagara musu. Taya zan kasance butulu waje rarrabe gaskiya da akasinta. Dan ALLAH ka gafarceni idan nayi kuskure, wlhy ban nema amincewarka ga Maanal tayi aiki dan ba?anta maka rai ba ko ?as?antar da dokar ka b.....
? ??  Shiiiii!! Ya isa kukan haka to .
Daddy ya faWa yana mai jawota jikinsa ya rungume murmushi shimfiWe a fuskarsa. A hankali yake shafa bayanta cike da lallashi. Tsahon minti Waya kafin ya furta,  Nasani Asia. Na kuma yarda dake Wari bisa Wari. Domin nasha gwadaki akan yaran nan batare da kin sani ba ke kanki kuma kina cinye jarabawar. Babu abinda zance dake sai godiya. Domin tabbas a cikin matana kina gaba a wadda nake alfahari da ita. Bance miki suma sauran sun gaza ba ko basu da martabar da nake kallonsu da ita ba. A'a ku dukanku kowa da inda yake tausasa min da kuma inda yake tsaurara min, amma kina da manyan lambar yabo kashi-kashi a gareni da bazasu lissafu ba Asia. Hakama su Shahidah, ni kaina biyayyarsu a gareni da girmamawa yakan sani manta ma bani na haifesu ba, ina jin alfahari da su, ina kuma godema ALLAH daya bani su matsayin ?a?ana a yanzu. Ba aiki bane bana son Maanal tayi, domin nima na fahimci hakan zai taimaka mata ya Wauke mata kewa musamman da nima nasan harkar zane-zane hubby nata ne. Kawai dai ina jin haushinki ne da tunanin baki son haWa jini dani, shiyyasa yau ba fanshe haushin ta nan, sai nake ganin kamar baki son wannan haWin da nake sonyi ne Asia. Alhalin ni kuma na ?waWaitu ?warai da gaske da son ganin jinina ya sake gauraya da naki kozan cigaba da samun nagartattun zuria daga tsatsonki a cikin zuri'ata. Hakan zai sake dun?ulemu ya curemu waje guda. Tun akan Amal naso nayi wannan haWin, sai na fahimci hankalin Yazeed akan Maanal yake shiyyasa na ?wallafa raina a kanta.
? ? ??  Kayi ha?uri Daddyn Hameed sam ba haka bane kamar yanda kake tunani. Ka fahimceni dan ALLAH. Wlhy koda bana aurenka zan iya bama Yazeed auren Maanal. Domin ya taimakemu a gaSar da muke matu?ar bukatar taimako. Zanma iya cewa ALLAH ya ?addara Manaal nada sauran kwana ne a duniya amma ya saka sanadin hakan a hannun Yazeed. Domin da ace kwannata ya ?are tun a randa muka fara haWuwa da sai dai wani zancen ake ba wannan ba. Dan haka ban taSa jin bazan bama Yazeed Maanal ba. Kawai dai hankalina na matu?ar tashi kasancewar bakowane Sangare bane ke bu?atar wannan haWin, hakan kuma zai iya cutar da Yazeed Win kansa da ita kuma Maanal Win dake fama da rauni irin na ciwo mai haWari. Amma yanzu masalahar da aka samu zai taimaka komai ya zama dai-dai itama ta samu sassauci haka shima Yazeed Win. Dan koba komai Hajiya Yaya mahaifiyace tana da tata darajar. Sannan Yazeed ya san komai daya shafi rayuwar Maanal, basai anyi sabon zama da zagaye-zagayen faWa masa da fargabar zai amsheta ko zai canja ra'ayi
? ? ??  Hakane Asia. Na kuma fahimceki yanzu Wari bisa Wari. Zan kuma cigaba da addu'ar zaSin ALLAH akan al'amarin insha ALLAHU. Sannan abinda ya shafeta ki daina wani damun a kansa kanki ai ?addara ce, bata wuce kan kowa ba kuma, ALLAH kuma shine shaida bataje takai kanta ba domin yin hakan jarabawace, wanda ma suke aikatawa kai tsaye ko suke zuwa bariki su kama Wakin kansu suke auruwa cikin salama da kwanciyar hankali yanzu a ?asar nan balle ita. Saboda haka na amince Maanal tayi aikinta. ALLAH ya sanya albarka ya kuma sa hakane yafi alkairi.
? ?? Wani irin daWi ne ya ratsa zuciyar Ammie. Ta ?an?ame Daddy da ?yau tana amsawa da amin. Shima murmushi ya saki mai faWin gaske da karSarta sosai ya rungume. A ransa kuwa yana sake ganin fara aikin Maanal Win wata masalaha ce. Dan zai fake da shi bayan anyi auren suyi zamansu acan, ita kuma wannan zaSin uwar Yazeed Win anan cikin gidan yake son ta zauna tare da su saboda wasu dalilansa......

? ? ? Tofa, mi kuke tunanin wai ya faru da Maanal ne?>?z?. Sannan zamuga yanda wannan cakwakiya zata ?are=??
__________&

? ? ? ? Wani irin farin ciki ne ya mamaye Maanal lokacin da sa?on Daddy ya risketa akan amincewarsa tayi aiki. Su kansu su Shahidah sai da suka tsaya suna kallonta ganin yanda taketa murmushi yau kamar ba Maanal ba. Sai suma hakan ya sakasu a farin ciki. A karo na farko na tarihi Maanal taima RK text massage da albishir Win amincewar Daddy. Ai ba'a haWa awa guda ba sai ga bawan ALLAH a gidan. Yau ko lallaSatan da Shahidah keyi na taje ta samu RK Win ba'ai ba. Yana kiranta yace gashi a gidan sai gata babu jimawa ta fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya jarabcesa da son wannan halittar ?warai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta in har hakan shine alkairi a garesu. Maanal ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon ?urillar da yake matan. Baice komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta sharesa kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata da kulawa, kafin ya Wora da tambayar yanda abubuwa suka kasance. A ta?aice ta faWa masa, bai damu ba dan ya gama karantar ta zuwa yanzu. Bata da son yin doguwar magana sai idan itace taso hakan da kanta. Shine ya dinga zuba mata zance da yanda abubuwa zasu kasance. Ya kuma tabbatar mata nan da kwana biyu zaizo ya amshi takardunta. Ya kuma bu?aci ta Wan zazzana wasu samples na agogunan zaizo ya amsa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai sake nunama mai Companyn. Duk da dai ya nuna masa wanda ta zana a asibiti. Ta tabbatar masa babu damuwa zatayi Win, daga haka sukai sallama ya fice ita kuma ta shiga gida.
? ? ? Kamar ko yanda sukai al?awari a wannan daren ta nutsu ta zana agoguna masu shegen ?yau da Waukar hankali fin kala goma. Dan har gabannin asuba tana wannan aikin. Hakan ya saka mata makara. Tana yin sallar asubahi kuma ta sake kwanciya. Bata farka ba sai Waya saura. Ta samu RK yazo ya amshi zanen ma. Dan sun sanar masa tana barci yace kada a tasheta a barta tai barcinta, a bashi zanen kawai. Yana kuwa amsa bai jima ba ya wuce abinsa. Sai da ta tashi take jin yazo Win ya amsa. Har ta Wauka waya kamar zata kirashi sai kuma dai ta fasa kawai. Tata tsumayen nasa kiran amma shima sai bai kira Win ba har dare. Sai da tana shirin kwanciya ne ma sa?onsa ya shigo.
? ? ? ? _ Ina Kaduna yanzu haka. Mun gana da Daddy da Ammie, na kuma amso takardunki suna hannuna. Amma sai da safe zan dawo Abuja in sha ALLAHU. Kiyi barci cikin aminci tare da mafarki mai nutsuwa gimbiyar mata _.
? ?? Baki kawai ta taSe tare da jefa wayar saman gado ta cigaba da saka maSallan rigar barcinta. Sai kuma ta tsaya cak kalamansa na dawo mata. Ya gana da Daddy da Ammie kamar yaya? Kai itafa shishshigin mutum nan ya fara bata tsoro. Kaji bala'i ko mi ya kaisa Kaduna?. Rashin mai bata amsa ya sakata jan ?aramin tsaki ta haye gadon kawai ta kwanta. Addu'a tayi kamar yanda ta saba sannan ta kashe wutar Wakin tana sauke ajiyar zuciya.........
'?


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



.......Maanal bata sake jin labarin RK ba tun ranar. Ya dai kirata washe gari yace ya dawo Abuja. Daga haka bata sake jinsa ba. Gashi ita kuma ta ?agu taji yaya ake ciki. Dan haka kawai sai ta ?wallafa ranta a aikin saboda zaman waje Wayan kuma ya isheta. Da yaran Shahidah sun wuce makaranta itama da mijinta duk aiki suke fita, sai ita sai mai aiki kawai. Bata da aiki sai karatun novels da kwanciya. Amma kasancewarta sarkin kamewa da dakiya sai bazaka taSa fahimtar hakan ba kai tsaye. Sati Waya dayin hakan sai ga Ammie da Amal sunzo. Matu?ar farin ciki Maanal ta kasance a wannan ranar, gashi weekend ne duk masu gidan suna nan. Yini sukai dan Ammie tace bazata kwana ba. Babu irin shagwaSar da Maanal bataima Ammie akan ta kwana Win ba amma tace sam ita bata sanarma Daddy zata kwana ba. Haka babu yanda zasuyi bayan magrib suka rakasu train station kasancewar jirgin ?asan zasu bi. Dama a cikinsa suka zo....

? ? ? Kwanakin su Ammie biyar da zuwa da daddare tana shirin kwanciya sai ga kiran RK. Ido kawai ta sakama wayar tana kallo harta tsinke sannan ta kauda kanta. Sake kira akayi nan ma kamar bazata Wauka ba sai kuma dai mita tuna oho mata tai yun?urin Waukar, sai kuma taga bashi Win bane Ya Yazeed ne. Fuska ta Sata shima kamar bazata Waga ba ta dai daure ta Wauka. Gaisheshi ta farayi da girmamawa kamar yanda ta saba. Shi kuma ya amsa mata cikin nutsatstsiyar muryarsa dake nuna alamar a kwance yake. Sun Wan yi shiru sai kuma ya katse shirun da faWin,  Ina muka kwana akan batunmu Maanal? .
? ? ? Shiru tai kamar bazatace komai ba. Sai da ta mula dan kanta ta amsa masa da,  Yaya ni mikake son nace to. Ni duk abinda su Daddy suka yanke zanyi biyayya a kansa kawai .
? ?  Saboda dama baki sona? .
?  Ni dai Yaya bance ba. Amma ka tausaya mun mana. In dai kai namiji ka ha?ura ka musu biyayya ni kuma sai naje nace ba haka ba.
? ? ?  Humm shike nan, amma ke yanzu baki jin kishin na fara auren wata kafin ke? .
? ?? Karan farko ta saki murmushi mai faWi, sai kuma ta zame ta kwanta.  Yaya ko naji kishi yaya zanyi. Ni dan ALLAH mubar ma maganar nan kawai ALLAH yasa haka shine yafi alkairi .
? ?? Murmushi taji ya saki da ga can, sai kuma ya ce,  Okay shike nan an barta. Tunda dai na gane ana kishina na gode .
? ? Shiru ta masa batace komai ba. Shima daga haka yay mata sallama akan maybe gobe ma ya shigo Abujan,? zai kuma le?o ya fara ganinta kafin ya fara sabgoginsa. Daga haka sukai sallama. Kamar jira RK yake dama, Yazeed yana yankewa kiransa na shigowa shi kuma. Sai yanzu ma ta lura ya mata kira yafi goma ashe sanda take wayar. Kanta kawai ta Wan girgiza. Sai da tana gab da zata tsinke sannan ta Waga. Muryarsa a cinkushe ya mata sallama. Amsawa tai itama ciki-cikin tai shiru. Tsahon minti Waya babu wanda ya sake magana.
? ? ??  Oh bama zaki gaisheni ba? .
? ? RK Win ya faWa daga can. Yitai kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta ce,  Good evening .
? ??  Humm good evening to baturiya. Fatan kin yini lafiya? .
??  Lau .
Itama ta amsa masa a da?ile jin yana mata magana cikin wani ji da kai.
? ? ? ? ?  Humm! saboda kina waya da wannan tsohon tuzurun saurayin naki da baya dariya shine kika shareni.
? ? Ita dariya ma zancen nasa ya bata. Amma sai bata dara Win ba ta ce,  Hummm ashe kaima tsohon tuzurun ne tunda ba girmarka yay ba .
? ?  Oh zaki shigar masa faWan ne kenan? .
? ? Shiru ta masa ta?i tankawa. Shima sai ya saki zancen kawai. Amma ransa fal kishin Yazeed Win.  Baki da kirki ALLAH, kwana kusan goma baki jini ba amma baki neman ba. Wannan wace irin soyayya ce? .
? ??  Kai dai ka sani. Rashin jinka kuma ai nasan lafiya ce ke Suya .
? ?  Humm borin kunya, ALLAH dai ya shirya min ke. Duk da baki tambaya ba bara na faWa miki. Auntyna ce bata da lafiya a randa na dawo Kaduna da yamma jikin ya tsananta, dole mukai gaggawar barin ?asar da ita. Tashin hankali yasani manta wayar da number Winki ke ciki. Jiyan nan muke dawowa .
? ? ? ? ? A hankali Maanal ta sauke numfashi da faWin,  ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. A wace anguwa take? .
??  Amin ya rabbi nagode sosai. Zakije dubata ne kike tambayar anguwarsu? .
? ?  Ina ruwanka to. Kai dai ka faWa min mana .
?? Murmushi yayi daga can har tana iya jin fitar sautinsa. Sai kuma ya ce,  Okay ba damuwa zan tura miki address Win. Sai dai kuma yanzu ma na kiraki ne akan batun aikin can. Sun bu?aci ganinki, sai ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu kamar around eleven thirty haka zanzo na Waukeki .
? ? ? Wani irin sanyi ne ya tsargama Maanal. Amma sai ta danne cikin dakewarta ta ce,  Miyyasa bazaka bani address Win ba kawai naje da kaina .
? ? ?  Kina tsoron na saida ki ne? .
?  Ai nasan nafi ?arfin siyarwa .
 Hhhh haka dai kikace. Bari na barki ki kwanta lokacin barcinki na wucewa. Sai nazo .
? ? Daga haka ya yanke kiran kafin tace komai. Murmushi ta saki itama, ta jima da fahimtar bayan naci RK Wan rigima ne na bugawa a jarida. Sam daga ganinsa baya jin magana. Bazatace tana sonshi ba. Amma wasu abubuwa nashi sun Wan fara birgeta kaWan. Fasa kwanciyar tayi, ta tashi ta Wauro alwala ta hau nafilfilin neman nasara da zaSin alkairi akan wannan aiki. Duk da dai dama tunda aka tsira zancen taketa gayama ALLAH. Tayi raka'a biyun farko ta sallame ta Wauki wayarta ta turama Ammie text. Tasanta bata wasa da ?iyamullaili, kusan za'ace ma ita suka gado dan tun suna yara tai musu wannan horon na ibada. Kuma Alhamdullah su dukansu sun horu da wannan tarbiyyar tata. Dama itace mai Wan raunin cikinsu lokacin tana a ganiyar rashin ji. Amma yanzu Alhamdullah kam komai ya sauya kamar yanda jiyanta ta zama tarihi mai ciwo da raWaWin tunawa agareta.....


? ? ? *_WASHE GARI_*

? Da safe ta sanarma Shahidah da mijinta komai. Sun tayata murna da fatan alkairi suma. Ta kumayi waya da Ammie da Daddy dan itace da shi jiya da yau. Hakama Amal. Bayan wucewar su Shahidah nasu ayyukan itama tai nata shirin. Kasancewar ta mai jinkirin shiri yasa ten nayi ta fara shirin nata. Sai ya zam kafin eleven ma tayi ta gama komai duk dama bawani shiri bane na'azo a gani. Amma tayi ?yau sosai cikin Abaya ?irar saudia ba?a. Daga ciki ta saka wandon jeans blue mai duhu da farar riga datai mata ?yau. ?an kwalin abayar kawai tai rolling a kanta ta saka turare mara ?arfi bayan na wuta da kayanta keyi dama jikinta gaba Waya da yuni gyara yasa ?amshi ya kama. Sai ?an tarkacenta data haWa a hand bag Winta sannan ta fito. Kitchen ta shiga ta saka ruwa a ?ya?y?yawar bottle water Winta ?ar zamani sai ta Wan saka Linda ta daka mata snacks da basa rabo da shi a gidan kaWan wai ko taji yunwa. Dan ta tsani sayen abincin waje a rayuwarta. Shiyyasa da wahala kaga Maanal ta fita anguwar data san zata yini babu wani abin ci a tare da ita. Tun Ammie na faWa har ta saka mata ido ma. Falo ta dawo ta zauna kasancewar akwai sauran mintuna ashirin, sai kawai ta buWe novel Winta ta cigaba da dubawa. Tanayi tana Wan cin shawarma Winta guda Waya data Wakko da drink a kofi. Batafi mintuna goma a wajen ba kira ya shigo wayarta. ?aramin tsaki taja a ranta tana addu'ar ALLAH yada ba Yazeed bane ba. Numfashi ta Wan sauke ganin RK ne. Sai da ta kalla agogo sannan ta Waga. Yau dai bai ro?aba ta gaishesa. Sai shi kuma batare daya amsa ba yace ta fito gashi a waje. Sake kallon agogo tayi da mamaki ta ce,  Akwai fa sauran ten minutes .
? ??  Oh kona koma sai ya cika na dawo? .
? ?  Humm . Ta faWa kawai tana yanke wayar. Linda ta ?walama kira. Da sauri sai gata tana faWin,  Yes Aunty kina bukatar wani abu ne? .
? ? ??  No Linda zan wuce ne dai. Dan ALLAH ki kula sosai da gidan duk da dai nasan kina ?o?ari dama. Ai baki manta ba dai Didi tace kima Uncle tuwon shinkafa ko? .
? ?  Eh aunty ban manta ba har ma na Wora .
? ?  Yauwa to yayi, sai su Barrah kuma kisaka musu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login