Showing 114001 words to 117000 words out of 219361 words

Chapter 39 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

46981

ga Naufal da RK kema dariya da faWin,  Ko kuma kai ka kusa sakawa ku faWin ba. Aunty ai banyi zaton yanzu zaku ma taho ba.
? ?  Rafeeq ai bana wasa da Baby na sam. Balle kace yau za'a sallameta shiyyasa nace in sha ALLAHU da wuri zanzo. Sai kuma Auta da nake son yaga likita yau shima .
? ? Karo na farko RK ya dubi AA sosai. Ganin yanda idanunsa sukai masifar kaWewa ya ce,  Ya Salam badai kan nasa bane har yanzu? .
? ? ? ??  Shine kuwa wlhy ya?i sauka, jiya haka ya kwana a wahale . Ta bashi amsa tana jan hannun AA Win zuwa gaban gadon da Maanal take. A kwance take yanzu ta juyama ?ofa baya, hakan yasa Oum zama a bakin gadon kusa da ita. Shi kuma yay tsaya kawai daga gefen Oum yana kallon ?ofa dan ya?i sake kallon Maanal. Kujera RK ya tura masa cike da kulawa ya ce,  Zauna anan bara na duba Doctor Rasheed Win muga. Ai da kun sanar min da gida yazo ya samesan .
? ? ? ??  Yayi ?o?ari ne ai Rafeeq, kwana biyun nan yanata zaryar zuwa gidan, kuma dama yace idan bai sauka ba yau asibiti ya kamata yazo ya duba shi da ?yau shiyyasa .
? Jajantawa RK Win ya sake yi kafin ya juya ya fita yana jaddadawa AA ya zauna. Sai dai ko kallonsa ya?iyi balle ya zauna Win. Yana daga tsayensa duk da hajijiyar da yake ji na jujjuya masa kai. Oum kuwa data ri?o hannun Maanal a hankali ta shiga kiran sunanta. Hakan yasa cikin dauriya da jarumta Maanal da tuni ta goge hawayenta tas ta juyo Win. Suna haWa ido da Oum ta sakar mata murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta shige jikinta cike da shagwaSa ta ce,  Oum ni nayi fushi sai yanzu .
? ? ? ??  Oh oh my baby kada kiyi fushi kinji, ayima Oum afuwa yaya jikin naki? .
? ? ?  Naji sau?i Oum. Yaya Rafeeq ma yace zasu sallameni yau .
? ?  To Alhamdullah ALLAH ya ?ara afuwa. Tun jiya naso zuwa shima sai Auta ya kwanta shiyyasa
? ??  Hy Aunty .
Naufal ya faWa yana Wagama Maanal hannu fuskarsa da murmushi. Murmushin itama Maanal Win tai masa. Sai kuma ta Waga masa hannun itama ta ce,  Hy Handsome .
? ? ? ?? Farin ciki ne ya kama Naufal jin an kirasa Handsome, dama Uncle AA ne kawai ke kiransa da sunan. Gaban gadon ya ?araso sosai. Ya ce,  Nagode Aunty da kika kirani Handsome. Kun zama biyu kenan ke da Uncle. yay mata nuni da AA.
? ? Batare data kalli AA Win ba taima Naufal murmushi kawai. Gaisheta yaron yay da tambayarta yaya jiki, ta amsa masa da kulawa tana zaunar da shi kusa da ita. Sai kuma ta kalla Oum tana faWin,  Yana kama da babban Yaya sosai .
? ?? Dariya Oum tayi a karo na farko, idonta akan Naufal ta ce,  Kodai Auta. Dan komai na Naufal Auta ne sak, duk da dai dama suna kama da Fadeel ne shima Win, amma Fadeel ai fari ne, shiko Naufal irin fatanku gareshi ke da Auta .
? ? ? ? Maimakon Maanal ta amsa zancen sai ta basar ta hanyar shagwaSe fuska ta ce,  Oum mi kika dafo min? .
? ? ? Dai-dai Oum zata bata amsa RK ya shigo. Idonsa a kansu sai kuma ya kalla AA, da kulawa ya ?arasa garesa yana faWin,  Wai baka zauna ba. Ko duk ?ulafucin Oum Win kaka ne kazo ka tsaya mata a kai kamar zaka koma ciki kai da Wayar Autar tata. Common malam zauna kada ka faWi . Yanda baiyi magana ba tunda ya shigo yanzun ma bai tanka ba, sai dai ya zauna Win dan shima yasan in ba hakan yay ba tabbas gab yaje da zubewa a ?asa, sam kuma baya son cigaba da tada hankalin Oum, dan kwana biyun nan da baida lafiyar nan har rama tayi, ga shi itama tana fama da kanta.....

____________&

? ? ?? A Kaduna kam shirin kai lefe ake gidan su amarya. Shi ango ma baya nan yana Lagos kwana takwas kenan. Kaya ne na garari aka shirya na kuma fariyya. Jiya yini guda masu shiryasu na aikin nan. Akwatina set ashirin daa huWu cif, kaloli daban-daban. Kuma kowane set zaka samu kusan akwati biyar ko uku harda masu goma sha biyu. Ga galleliyar mota new model a 2023 sabuwa dal a ledarta. Hajiya Basariyya dai tana nane dasu a gabanta ake komai duk da zuciyarta a ?untace take, amma yafi yarda data danne ayi komai akan idonta, Ammie ko yanda ba'a gayyaceta ba bata saka kanta a sabgar ba daga ita har Sakina da har yanzu take a gidan. A yau Win ma sai suka ?ir?iri zuwa gyaran jiki abinsu. Duk bidirin shirin kayan da akai basa nan. Aiko Hajiya Yaya da ?a?anta suka samu na zaginsu wai Ammie tana hassada ne saboda ba Wiyarta bace ba. Koda suka dawo gidan haka suka cigaba da habaice-habaicen su Ammie tayi kamar ma bata jisu ba...
? ?? Washe gari tun sassafe gidan ya fara tara dangin Hajiya Yaya. Sai wasu a dangin Daddy dake Wan Wasawa da Hajiya Yayan. Yanda gidan ya cika saika Wauka bikin ne ma ya fara. Har lokacin kuma babu wanda ya zo ya cema Ammie tazo ga lefe kota shirya zuwa kai lefe, ita kuma tayi biris da kowa bata saka kanta ba. Bayan sallar azhar suka cika motoci goma cif sai ta amarya dake tsakkiya da toyota hilux da aka zuba kayan lefen a ciki. Haka suka tafi a jere gwanin sha'awa, duk inda suka gitta sai an tanka kuwa. Dama haka suke so, gari ya Wauka ko'ina ayi zancen wannan aure. To ALLAH ya cika burinsu dan kuwa an fara, sakamakon ?annen Yazeed kaf da wasu a dangi tun jiya sun gama watsa wannan lefe a kafafen yanar gizo tako ina.. A can gidan Aunty Sabuwa ma gida cike yake tan?am da ?awayenta ?an duniya da dangin mijinta. Anyi abinci kala-kala domin tarbar ba?i duk da kuwa aurene na dangin juna. Cikin abinda baifi mintuna ashirin ba anguwar ta gama rikicewa, dan kuwa kiWa suka saki sosai da dj Winsu da suka tanada. Kafin a Wan sarara a shiga buWe kaya, masu video nayi, masu hotuna nayi, masu guWa nayi harda ?awayen amarya. Dan babu kunya hatta amaryar ma tana a gidan abinta sai washare baki take da jin kanta sama ?ololuwa, dan tasan ita kam ta wuce tsara sai dai ta taya ?an baya da addu'a kuma, amma 2025 kam tata ce...??
? ? ? ? Tukuyci na miliyan ashirin aka bama ?an kawo lefe suma da tarin kayayyakin snacks da akai packaging, sai drinks da ruwa katon-katon, dambun kaji, danbun jan nama, soyayyu da gasassun raguna a ?yafe guda biyar. Lallai wannan al'amari ya kai duniya tasan da shi. Dan kuwa ba garin Kaduna kawai ba duniya ce ta Wauka sakamakon yanda komai ke yawo daki-daki a media tako ina. Dan hatta tarbar da suka samu da shagalin da akai a gidan Aunty Sabuwa shima anata Worawa. Hakama tukuyci da kayan alatun da aka ma?are musu motar da ta kawo kaya shima dai duk an Wora. Hakan ya sakama jama'a kwaWayi da shirin son ganin yanda wannan shagalin biki zai kasance na ?warya tabi ?warya. Wanda kuma suka san ainahin waye uban amaryar dan bai kai ko kwatar dukiyar uban ango Alhaji Usman Chalawa ba nata mamakin hidimar da su ma su Aunty sabuwar sukayi.
To kowa dai na son yaga yanda za'a kwashe kam, dan in dai har kawo lefe kawai duk akama waWan nan hidimomin ai taron biki kam dole ko mu ?an kallo mu kasance a cikin shirin shan kallon (=?? lolz)....

______________&

? ? ? ?? Sosai kasancewar su Oum a asibitin ya Wan ragema Maanal nauyin da zuciyarta tayi. Dan ma hankalin Oum Win ya rabu biyu saboda AA. Dan shi ma bayan Doctor ya dubashi sosai sun Wan kwantar da shi amma yace na yini Wayan ne kawai. A wannan yanayin Shahidah ta iso asibitin ta samesu. Tayi farin cikin ganin Oum sosai. Kasancewar an hana kowa zama a Wakin da AA yake dan suna son ya samu barci sosai duk sai suka tare anan Wakin Maanal Win. Sai bayan sallar azhar da AA ya farka Oum ta nufi can. A lokacin ita kuma Maanal ta samu sallama. Koda suka gama tattare kaya zuwa mota Shahidah tasa Maanal gaba tai domin duba AA. Bata so hakan ba, sai dai bazata iya musu da Didinta Win ba. Musamman daya kasance RK na tare da su ne.
? ? ? ? ? RK ne ya fara shiga bayan yayi knocking an bashi izinin shiga. Sai Maanal, Shahidah a ?arshe. Oum na zaune a kujera, shi kuma AA na kan gadon ya jingina da filo Oum zata fara bashi abinci a baki, sai faman Sata fuska yake alamar baya son cin abincin ko kuma duk ciwon ne oho masa. Plate Win abincin Oum ta ajiye tana kamo hannun Maanal da faWin,  Masha ALLAHU ?an matana anyi sallamar dai? .
? ? ? ? ? Kai Maanal Win ta jinjina mata a Wan shagwaSe. Ita kuma tayi murmushi da faWin,  To Alhamdullah, ALLAH ya ?ara lafiya yasa kaffara ne.
? ? ? Amin RK da Shahidah suka amsa da shi, kafin Shahidah ta maida hankalinta ga AA daketa kallonta. Duk da yasan dama zai iya ganin nata, amma sosai mamakinsa ya bayyana amma ya gagara iya cewa komai. Wannan ba komai bane daga halayensa, dan haka Shahidah bata damu ba, sai dai zafinsa da suke ji tun na shekarun baya akan ?ar uwarsu taji yana taso mata. Komai dawo mata yake kamar yanzu ne yake faruwa. Da ?yar ta iya dannewa ta tambayesa jikinsa. Karan farko yay Wan murmusa, irin guntun murmushin nan mai tabbatar da ?unar zuciya. Tabbas yaga tsanarsa a bayyane akan fuskar Shahidah, hakan na nufi har yanzu suma basu mance komai ba, basu mance abinda ya faru ba suna ri?e da shi a ransu fiye ma da Maanal.?Baiga laifinsu ba, dan ko shine hakan zai yi, amma inama zasu fahimcesa kamar yanda Oum ta fahimcesa bayan ya zauna da it.....
? ? ? ? Maganar RK ce ta katse masa tunaninsa, ya Wan kallesa sai kuma ya janye idanunsa yana jinjina masa kai. Baya son sakama ransa tsanar Wan uwansa kodan daraja da kimar Oum, amma tabbas zafinsa yake ji, kishinsa yake ji mai tsanani akan Maanal. Ta yanda ya gwammaci ya dinga masa shiru akan abubuwa da dama fiye da yin magana.
? ?? Sai yanzu Maanal da tunda tai masa kallo Waya bata ?ara ba ta furta,  Ya jiki? . Daga haka tai shiru. Shima sai bai amsa ba, ya dai Wago idanunsa ya kalleta kawai. Yana ?o?arin janyewa akai knocking ?ofar. Shahidah ce ta amsa sannan ta bada izinin shigowa. A hankali aka turo ?ofar, yana sanye cikin lallausan farin yadi da yay masa matu?ar ?yawu, sosai kamanninsa da AA ke a bayyane, ta fuska da Wabi'u. Sai a shekaru ne kawai suka banbanta da hasken fata. ?an ja yay ya tsaya turus yana kallon Shahidah da itama take kallonsa, sai kuma tai saurin kauda idonta. Shima janyewa yay ya maida ga Oum, sai kuma ya sake waresu akan Maanal da itama take kallonsa. Cikin kasa daurewa ya ce,  Oum kinga mi nake gani? .
? ?? Murmushi sosai Oum ta saki mai ciwo, sai kuma ta jinjina kanta da faWin,  Na sani Fadeel. Shahidah ce da Lillyn ka .
? ??  Wai da gaske ne kenan? .
?? Yanzu kam har sai da hakwaran Oum suka bayyana a waje, sai kuma hawaye suka ciko mata idanunta. Da ?yar dai ta iya dannewa ta sake bashi amsa........
'?







('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


.......Matu?ar mamaki Babban Yaya ya shiga da jin komai daga bakin Oum da RK. Sai satar kallon Shahidah yake da jinjina mamakinsa akan canjawar Maanal. Ta ?ara tsaho duk rashin jin nan da rawar kai babu yanzun. Hakan ba abun mamaki bane ba, musamman idan aka tara yanda abubuwa suka kasance zama a iya ganin fiye da hakan daga Maanal. Nan fa ya tasa Maanal da tambayoyi har ma da Shahidah duk da shi Win ba gwanin yawan magana bane ba.
? ? ? ? Maanal ce mai amsa masan, dan itama Shahidah tana amsa Wai-Wai ne. Itafa Family Win nan idan ta cire Oum a ciki da Fawzan da Abah da Mamy bata jin sauran a ranta yanzu. Sai ma wani kalar zafinsu da take ji, amma darajar Oum yasa taketa ?o?arin dannewa dan Oum ta cancanta. Ana cikin hakan sai ga Fawzan shima ya iso, bayansa matarsa ce Nibras, sai Saheeba matar babban Yaya hannunta ri?e da ?ar budurwar yarinya mai tsananin kama da su Babban yayan. Sai budurwar yarinya ?ya?y?yawa a ?arshe biye da su hannunta Wauke da irin box Win nan da ake saka kayan abinci. Ambatar sunan Lilly da Shahidah da Fawzan yayi ya saka Saheeba kallon sashen da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna da Shahidahn. A take fara'ar fuskar Saheeba ta Sace Sat. Itako Shahidah ta janye nata cike da basarwa tana bama Fawzan amsar maganarsa. Ita dai Nibras bata sansu ba a zahiri. Amma sunayen da aka ambacesu da shi ya sata tsatstsaresu da idanunta, dan ta Wan san labarin dangantakar tasu da familyn Darma a wajen mahaifiyarta. Sai dai kuma bata da tabbacin waWan can Win ne ko wasu daban.
? ? ? ? Ita ko budurwar data shigo a ?arshe gaba Waya hankalinta naga AA ne. Dan tuni ma ta kai gaban gadon babu ko kunya ta zauna a kusa da shi. Sai dai hararar daya jefa mata ta sata mi?ewa tsaye zambar tana faWin,  Sorry Yaya .
? ? ?? Komai baice mata ba, ita kuma bata nuna damuwa ba ta Wan rissina tana gaisheshi da tambayarsa jikin nasa. Sai kuma ta jawo kujera dake can jikin Wayan gadon dake a Wakin dan gado biyu ne Naufal na barci a wajen ta zauna kusa da shi sosai. Dai-dai nan Shahidah ta mi?e tana faWin,  ALLAH ya ?ara lafiya bara mu wuce Maanal ta samu ta huta.
? ?? Wani irin Wagowa budurwar mai suna Nuratu tayi jin sunan Maanal a karo na farko. Sai a yanzu ta kalla Oum kasancewar Maanal Win na'a jikin Oum kamar ?ar mage. Tabbas bata san Maanal ba a zahiri itama a wancan lokacin na ?uruciya dan ita ta rayune ba'a gidansu ba, yayar babansu ce ta ri?eta suna zaune a Lagos. Bayan rasuwar mijinta ne suka dawo Abuja, amma tasan komai na labari tsakanin yarinya mai suna Maanal da Yaya AA Winta. Burin ranta, da take fatan ya zama miji a gareta tun a randa ta fara tozali da shi a Lagos. ?o?arin tuna inda tasan fuskar Maanal take yi, dan haka ta kafeta da idanu. ?irjinta ne yay masifar bugawa lokacin da suka haWa ido da Maanal dake mi?ewa Oum ri?e da ita. Sarai Maanal ta ganeta ita, hakan yasa ta janye idanunta cike da basarwa. Itako Nurry ta kasa janyewa dan ta gane Maanal itama, itace yarinyar da suka haWu a wajen saloon ranar Sunday Win data gabata. Jitai jikinta kawai ya fara rawa, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri saboda tsoron abinda take hasashe, cikin rawar murya da suSutar baki ta furta,  Wai itace Manaal Win da nake jin labari a gidan su Mamy na Kano Aunty Saheeba? .
? ? ? ? Ba Saheeba data ambata ba, hatta su Babban yaya sai da suka dubeta, shi kansa AA wani kalar mugun kallo ya zuba mata ita da yayar tata Saheeba duk da matar yayansa ce. Sai kawai jikin Saheeba da Nurry ya kama tsuma. Cikin daburcewa Saheeba da kallon rashin mutuncin da Babban yaya ke jifanta da shi gana AA a gefe ya gama rikitata ta ce,  Wlhy ni ba wani bad abu na sanar mata akanta ba. ALLAH ma ne shaida bani na gaya matan ba. Nuratu ko'a bakina kika ji? . Ta juya tana kallon Nuratu da zuciyarta ke mazari. Dan ta fahimci itama katoSarar data nema yi. Sai dai kuma wani irin jin tsanar Maanal ke sake haWa wutar guguwa a can ?asan ranta. Kai ta girgiza ma Yayar tan, sai kuma ta ce,  No nima fa ba ina nufin wani bad abu bane ba wlhy ko aka sanar min a kanta. Kawai na faWa ne ta yanda zan tabbatar da ita Win ce bawai dan wani abu ba.
? ? ?? Fawzan ne ya girgiza kansa kawai da katse yanayin ta hanyar faWin,  ALLAH ya ?yauta to. Amma wannan maganar ma baida wani amfani. ?anwata muje na saukeku gida ko . Ya ?are maganar idonsa akan Shahidah. (Da ada ne catake ita ba ?anwarsa bace). Suyita musu da jayayya, dan da gaske Fawzan ya girma Shahidah Win da kusan shekara uku, kusan ma za'ace AA ne sa'anta. Amma ta girmesa itama da wasu watanni. Ala?ar Shahidahn da babban Yaya yasa suke ?ar jayayyar da Fawzan Win sarkin barkwanci da tsokana.
? ? ? Murmushi Shahidah tai masa da faWin,  A'a mun hutasheka Yaya Fawzan. Da mota ma nazo shiyyasa nace shima Rafeeq ya huta abinsa.
? ? ? ?? Sai a lokacin RK da komai ke masa kaikawo yay magana. Maanal da tuni tai gaba ya kalla. Dan ita ko kallon Nurry batai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login