Showing 54001 words to 57000 words out of 219361 words

Chapter 19 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

46990

ce tun ta ?uruciya. Ko lokacin da Sabuwa ta rabu da Alhaji Sajid Win Sabuwa da Malika na tare, kusan ma za'ace da taimakonsu ne aka maida auren bayan Sabuwar taje tayi auren kisan wuta saboda saki uku ne. Shi mijin Hajiya Malika sam ba mazauni bane ba, Wan kasuwa ne da kullum yana wacan ?asa gobe yana waccan kamar wani Wan sama jannati, da wannan damar Mijin Sabuwa ya samu kan Hajiya Malika suke she?e a yarsu. Dan a yanzu haka ?a?an Hajiya Malika ba duka bane Wiyan mijinta idan za'a tantance, akwai gauraye dana mijin Sabuwa saboda yanda suke tare matu?a kamar wata matarsa. UBANGIJI kuma yay musu talala har yanzu babu wanda ya taSa sanin wannan ala?a tasu duk da tsahon shekaru sai wata mai aikin da Hajiya Malika ta taSa yi, ita kam ta kamasu dumu-dumu cikin aikata al'amarin ta tsorata, itama hankalin Hajiya Malikan ya tashi amma sai Mijin Sabuwa yace karta damu ta jira taga mi zaiyi. Aiko taga abinda zaiyi Win, dan a gabanta yayma yarinyar nan ?ar aikinta fyaWe, daga nan yaja mata dogon gargaWi akan idan ma taje ta tona musu asiri saita haWa da kanta, ya nuna mata video Win daya saka Hajiya Malika ta Wauka sanda yake tare da yarinyar. Hankalinta ya tashi, ta dinga kuka tana ramtsuwar bazata faWa ba wlhy. Basubi takanta ba sukace ya haWa kayanta washe gari aka maida ta ?auyensu. To tundai daga nan babu abinda ya sake faruwa sai dai UBANGIJI na kallonsu, ba kuma su san ya musu talala bane ba)

??
_________&

? ? Kamar yanda Amaal tai al?awari ta iso Abuja kusan takwas na dare. Alhamdullah zuwa sannan Maanal ta farka. Dan shigarta wanka kenan Amaal Win ta iso. Ta fito taci karo da ita a Wakinta sai tayi turus. Dariya Amaal ta sanya mata tare da buWe mata hannayenta alamar tazo gareta. A yanzu kam babu musu Maanal Win ta nufota suka rungume juna, kai kace ba kwanan nan suka rabu ba.
? ? Sai da Maanal ta shirya tai sallolin dake kanta sannan ta dawo tsakiyar yayun nata maganin kukanta ta zauna. Abinci suka fara ci, yayinda Maanal ta shagwaSe musu wai ita hannunta na ciwo bazata iya ci da shi ba. Aiko su biyun duk suka dinga bata a baki. Hakan da sukai mata ma sai taci abincin sosai. Dagan nan ne suka nutsu akan abinda ya tarasu.
? ? ? Da farko dai sun fara lallashinta akan batun aiki tace ita fa ta fasa bazatayi ba. Hasalima tana son komawa Kaduna ne kawai wajen Ammie.
? ? Baki Amal ta taSe cikin Wan Sacin rai dan dama tafi Shahidah zafi ta ce,  Oh Kaduna ko? Kenan auren Yazeed Win kike son yi? .
? ? ??  Yazeed kuma? Didi ni na taSa cema wani zan auri Yazeed? .
??  Ai basai kin faWa ba gashi yanzu kin nuna mana. Wai Manaal mike damun kanki ne dan ALLAH?. Ke gaba Waya tunaninki a bauWe yake dana mutane, sai shegen taurin kai da kafiyar tsiya. To wlhy bari ma na fito miki a mutum ki tattara hankalinki waje guda ki maidashi jikinki. Har mi akai akayi wani Ajwaad can da zai hanaki samun cikar burinki....
?? Hannun Amaal Shahidah ta jim?e a nata tana girgiza mata kai alamar tayi shiru. Hakan ya saka Amaal Win jan ?aramin tsaki.  Didi ki barni da ita. Na kula sam Maanal bata tausayin kanta bata tausaya mana mu ?an uwanta. Wace irin rayuwace wannan ace mutum da taurin kai....
? ? ?  Kinga ya isa haka. Maanal bani hankalinki nan muyi magana ta gaskiya . Shahidah ta faWa tana kamo hannun Maanal data tsurama Amaal idanu cikin nata. Dole ta janye daga kan Amaal Win ta maido kan Shahidahn.  Maanal kiyi ha?uri bazamu takura miki ko tirsasaki akan abinda ba?ya ra'ayi ba. Amma ina son ki fahimci wani abu, mufa a yanzu bamu da maraba da marayu da suka rasa mahaifi da dukkan dangi. ALLAH ne gatanmu sai Ammien mu sai kuma Nene kawai sai kammu. Dolene fa mutattara komai daya faru a baya mu zubar da shi muyi mantawa irin ta AJIYA A DUHU duk da nasan akwai tabo da bazai taSa goguwa ba a zukatanmu amma komai na ALLAH ne. Sannan dole musan kammu mu kuma gina gobe yaranmu masu tasowa. Maanal Daddy ya ri?emu babu banbanci da ?a?an daya haifa a cikinsa tunkan Ammie ta haifa masa Waleed da Hameed. Kuma muma a yanzu babu wanda mukema kallon uba sama da shi. Sai dai fa mu sani iyakarmu kiransa uban ne kawai a iyakar kayinmu, amma a wajen al'umma sunanmu AGOLOLI a gidansa. Maanal ba fata nake ba, amma ki sani a yanzu ALLAH ya Wauki rayuwar Daddy wlhy ko Amminemu bazasu bari ta rayu a wannan ahalin ba. Saboda su Waleed ?anana ne, basu kai girman da zasu ?wata mata ?anci ba. Mu kuma komu yarda ko karmu yarda munada iyakarmu a gidan nan. To mikike tunanin ya kamata muyi? Wannan aikin tu?uru domin gina gobemu da goben yaranmu. Bazamu so mu sake maimaita rayuwar baya ba Maanal, bazamu so mahaifiyarmu ta sake maimaita wahalhalun data sha a kammu ba a shekarun baya, idan sannan muna da ?uruciya yanzu munkai girman share mata kukanta, mun girma Maanal mun girma .
? ? Kuka ya sar?eta. Suma duk sai suka fara kukan, koda yake dama Maanal ita tuni ta fara hawaye. Kusan mintuna biyu Shahidah ta share hawayenta da cigaba da faWin,  Maanal bamu san mi gobe zatazo mana da shi ba. Dan muma mata ne. Idan har Ammie zata iya riskar kanta a irin rayuwar da mukai a shekarun baya bai kamata mu mushagala da tunanin komaima bazai faru ba saboda a yanzu rayuwarmu ta inganta. Karfa mu manta da irin labarin gata da rayuwar Ammie tasha a hannun iyayenta, amma hakan bai hanata fuskantar ?alubale ba a hannun mijin aurenta da kowa ke gani hakan bazata faru ba. To muma bai kamata ganinmu a cikin irin waWan nan manyan gidajen yasa mu shagala ba. Bai kamata mu cigaba da zaman jiran kullum a mana ba. Saboda haka ki dawo cikin hankalinki Maanal, ki tuna su waye mu a yanzu. Ki ajiye abinda ya wuce baya ki manta da shi, ki kaishi cikin duhuwa ki ajiyesa tamkar ma ba'a taSa yin komai ba. Yanda Ajwaad ya nuna bai sanki ba ki zama JARUMA kema ki nuna baki sanshi ba, ki manta da shi, ki manta da abinda ya shafesa, ki tsaya da ?afafunki, kisa a ranki shi bai isa hanaki kaiwa ga cikar burinki ba, karki wani damu da zamowarsa shugaban kamfanin ko matsayin nasa ke aiki ya kaiki domin kanki. To kiyi kuma aiki tu?uru a companyn nasa domin kanki da cigabanki. Maanal ki duba yanda Rafeeq ke hidima dake da son ganin farin ciki ki, hatta Yazeed ma ni wlhy ban taSa ?in kasantuwar aurenku ba saboda mutumin kirki ne. Koba komai yasan mutuncin mahaifiyarmu, ya taimakemu a lokacin da muka rasa taimako daga jininmu ma. Kawai mahaifiyarsa ce matsala. Idan kuma da alkairi a zamanku sai ALLAH ya Wauketa ku zauna Win babu yanda zatayi. Amma dan ALLAH ki amshi al'amarin Rafeeq ki gwada ki gani shima. Ki kwantar da hankalinki addu'ar mu na zagaye dake ki manta da baya, ki saka a ranki ?addarar data gitta rayuwarki bazata hanaki aure ki zauna a gidan mijin ba har kuma ko samu farin ciki fiye da zatonki. Dan ALLAH shine shaida baki je kin aikata dan son zuciyarki ba. Dan haka ki manta komai, dan ALLAH ki manta komai kije ki fara aiki, abu nagaba kuma kiyi ?o?arin fidda mijin aure tsakanin Rafeeq da Yazeed kodan ki tabbatar ma Ajwaad kina rayuwane domin kanki. Dan kuwa cikakkiyar amsa kika samu a jiyanki game da shi, idan a baya hasashe kawai mukeyi bisa dalili yanzu ya tabbatar miki shi da kansa .
? ? ? Sosai Maanal take kuka yanzu kam, Amal ta jawota jikinta ta rungumeta itama tana kukan, sam basa son tunawa da bata, basa son tunawa da ?addarar data ratsa rayuwar autarsu, basa so ba sa so. Cikin rawar murya da son ture komai Amaal ta ce,  Duk abinda Didi ta gaya miki shine gaskiya wlhy Auta. Ki dake zuciyarki kiyi abinda ya dace da rayuwarki a yanzu. Ki manta da abinda ya wuce kamar ma ba'ayi komai ba. Koda wasa kada ki zubda daraja da kimarki ta Wiya mace. Ki amshi ?addarki kamar yanda muma muka rungumi tamu. Hakan da zamuyi sai ya ?ara ?arfafa Ammien mu, ki duba kiga rayuwar data baro, mai cike da tarin gwagwarmaya amma a yanzu ALLAH ya mata canji, canjin kuma baisa ace babu wasu jarabawoyin ba kuma. Tunda anan Win ma tana fuskantar ?alubalen bawai sun ?are bane. To haka rayuwa take duk yanda ka kai ga samun sauyi da nasara da jin daWi dole ?addararka aminiyar NUMFASHINKA ce Maanal. Tare suke tafiya a jefe ?afa da ?afa. Aminan juna ne tamkar gangar jiki da numfashi. Hakama jarabawarka abokiyar gangagar jikinka ce. Kinga ko har abada babu Wayan da zai rayu babu Waya a tsakanin gangar jiki da numfashi ko? .........
'?


?r?





('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
=?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



......... Hakane ?an uwana, na gode da shawarwarin ku, kuma in sha ALLAHU zan yi aiki da su. Dan ALLAH kuyi ha?uri da Waga muku hankalin da nakeyi a koda yaushe. Har yanzu ni mai RAUNI ce a cikinku, ina da matu?ar rauni ?an uwana na sani....
? ? ? Kuka ya sar?eta, rungumeta sukai su duka tausayinta na sake ratsasu. Tabbas gaskiya ta faWa ita Win mai rauni ce a cikinsu. Dan ko lokacin ?iruciyarsu kadai faWama Maanal tsiwa da rashin kunya ga shegen tsokanan faWa. Amma akwai tsoro kamar farar kura. Sai kuma da jarabawar tasu ta fara ita ta ninku mata sau biyu, duk da kuwa suma sau bibbiyu ne, amma ita tata tafi tasu ?arfi ne. Ba komai yasa hakan ba sai dan sun fita ?arfin zuciya, sannan su dama basu samu kansu a irin yanayin data samu kanta ba a wancan lokacin kasancewar sun fita hankali da wayo sosai. Sannan su komai dama anyinsa a wasa-wasa ne bakamar ita ba.
? ? Kusan raba wannan daren sukai zaune. Suna sake bama Maanal ?warin gwiwa da nasiha data sake ?arfafata ta kuma ji ta gamsu zataje tayi aikin. Hakan yasa washe gari yanda kowa yay shirin zuwa office itama tayi, yayinda Amaal tun asuba ta kama hanyar Kaduna tunda dama da mota tazo. Sun fito Maanal na ?o?arin shiga motar Shahidah sai ga motar RK ta shigo gidan. Dole ta Wan dakata yayinda Uncle Sadeeq ke dariyar ?eta cike da tsokana ya dubi Maanal Win yana faWin,  Ga majnoon nan lailah sai ki dakata .
? ? Dariya Shahidah tayi itama tana amsa masa,  Aifa sai Majnoon Win, Rafeeq sam baya gajiya shi kam .
?? Maanal dai batace komai ba har RK Win ya daidaita parking ya fito a motar. Yayi matu?ar ?yau cikin farar shadda Winkin tazarce. Sai dai babu hula a kansa. Wajen Uncle Sadeeq ya fara zuwa suka gaisa cike da mutunta juna da kulawa. Dan ta ko'ina fa RK ya kafa jam'iyyar sa. Sai kuma ya juya ga Shahidah itama ya gaisheta da mutuntawa. Itama ta amsa masa da kulawa tana tambayarsa yaya aikinsa. Idanunsa akan Maanal ya amsa mata da Alhamdullah.
? ? ? Ganin irin kallon da yake mata ta Wan hararesa sannan ta gaishesa a cinkushe. Maimakon amsawa sai ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana faWin,  Ashe da banyi sauri ba dana makara? .
? ??  A gaskiya kam daka makara. Amma ALLAH ya taimakeka, bari kaga muma muyi nan karmu makaran wajen kallon lailah Majnoon . Uncle Sadeeq ne da wannan magana cike da tsokana yana kallon Maanal. Yayinda Shahidah ke ?ar dariya itama dai hankalin nata akan Maanal Win. Motocinsu suka shiga suka fice abinsu aka bar Maanal tsaye sororo, wani irin daka zuciyarta ke mata yau a kansa. Sotake ta ?arfafa kanta game da shi ta bashi damar kamar yanda ?an uwanta suka bata shawara a daren jiya. Sai dai ina ji take anya kuwa zata iya hakan? Amma sai wani sashe na zuciyarta ke sake ?arfafata....
? ? ??  Good morning my queen .
?? RK ya faWa yana Wan du?owa kaWan saitin kunnenta. Wani irin numfashi taja tare da jan jikinta baya duk da bawani ya matseta bane akwai tazara a tsakaninsu. Murmushi yayi da Wan Wage mata gira sama ita kuma ta hararesa tana kauda kanta. Sai kawai ya fashe da dariya.  Oh ni Wan Mamana irin wannan harar da akemin sai na sace amarya ai ko a sallar isha'i a Waura mana auren daga baya. ALLAH ki daina mun wannan hararar rikita min lissafi kike gimbiya. Balle irin yanda nai kewar nan taki kwana biyu dubeni har wata rama nayi marayan ALLAH abin tausayi .
? ? ? A yanda yake maganar batama san sanda taji murmushi na neman suSuce mata ba. Amma sai ta dake abinta ta danne tare da Wan girgiza kanta ta ce,  ALLAH dai ya shiryeka .
? ? ? ??  Amin matar Rafeeq Kasheem Kura .
? ? Manaal bata kulashi ba, dan wayarta dake neman agaji, ?o?arin cirota ta shigayi a bag shi kuma ya amshi Wan lunch box Winta na abinci data haWa. Yazeed ne ya bayyana Saro-Saro akan screen Win. Hakan ya saka RK taSe baki cike da basarwa yabar wajen. Da kallo kawai ta bisa ?asa-?asa tana mai kai wayar kunnenta a nutsenta tai masa sallama. Da kulawa ya amsa mata da ga can tare da tambayarta jikinta tace Alhamdullah ta samu sau?i.
? ??  Masha ALLAH nima zuwa anjima zan shigo duk kin bi kin tadamin hankali da rashin ganinki tunda nazo aikin ma ya?i yuwumin yanda nake so. Amma yanzu na Wan ji ?arfi tunda na jiki Alhamdullah .
? ? ? ? ? Shiru tai ta kasa cemasa komai. Shima sai kawai ya saki murmushi daga can, tare da faWin,  To sarkin kunya bari na barki nima zan fitane ma na kiraki .
??  ALLAH ya tsare ya bada sa'ar abinda za'aje nema .
? ? ??  Amin ya rabbi mar'atussaliha .
Ya faWa can ?asan ma?oshi cike da shau?in so da ?ara jin tarin ?aunarta har ?ar?ashin zuciyarsa. Wayar tai ?o?arin maidawa cikin bag Win dai-dai da isowar RK wajen da mota. Fitowa yay ya buWe mata mazaunin gefensa ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima yay ma motar key suka fice. Yanata dai WaWWaurewarsa bata kulashi ba. Dan ta fahimci yana masifar kishin Yazeed. Koyaya yaga wani abinda ya shafi Yazeed a tattare da ita zai fara fushi. Itako sai dai yay tayi, dan Yazeed dai tare ya gansu, yazeed kuma abin girmamawarta ne dan ya taka rawar gani a rayuwarsu a lokacin da kowa ya guje musu. Shiko fa daga sama ya tsinceta.
? ?? Sunyi nisa a tafiyar motar shiru dan kansa ya yanke shirun nasu ta hanyar Wan juyowa ya kalleta fuskar dai babu walwala. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faWin,  Har yanzu baki sanarma su Zulaiha kina Abuja ba ne? .
? ?? Shiru kamar bazata tanka masa ba sai kuma a can ?asan ma?oshi ta ce,  Sun sani wani abu ya faru ne? .
? ? ? ??  No babu komai, nagane basu zo dubaki ba har yanzu .
? ? ?  Ni nace su barshi basai sunzo ba.
 Okay .
Ya faWa yana ?ara dam?e steering da ?yau. Daga haka suka sake yin shiru har suka iso Mawaad Company. Yauma kamar wancan ranar komai a tsaftace a kuma nutse yake a companyn. Sai da ya daidaita parking da ?yau tana ?o?arin Salle murfin motar ta fita ya dakatar da ita.  Na musu reporting akan baki da lafiya shiyyasa baki zo jiya ba kamar yanda suka bu?ata. Dan haka ko sun tambayeki sai kisan amsar da zaki basu. Please dan ALLAH ki kula, wajen nan cike yake da ?artin banza kar'a tsinceni a titi muna raba hali da al'umma .
? ? ? ?an kallonsa tai a karo na farko sai kuma ta janye lokaci guda tana mai girgiza kanta. Maimakon amsa masa batunsa ta buWe kawai ta fice abinta. Ta Wan fara tafiya taji alamar ana binta a baya, juyowa tai da taga shine ri?e da ?ar lunch box Winta. Tsayawa tai tare da mi?a masa hannu, amma sai ya girgiza mata kai yana nuna mata hanya alamar suje. Babu yanda ta iya haka suka jera har cikin Companyn...

? ? ? Wani irin lumshe idanu AA Darma dake zaune cikin motarsa daga baya dan driver ne yau ya kawo shi Office Win tare da datse leSensa ba ?asa da ?arfi. Sai dai sam bazaka taSa fahimtar hakan ba kasancewar jarida a hannunsa yana dubawa. Shima isowarsu kenan, kuma tun a hanya a wajen fitilar bada hannu yaga motar RK Win, ya hango mace a motar amma baiga wacece ba. Sai dai haka kawai zuciyarsa ta bashi wacece Win, dan haka koda suka iso kasancewar sun riga su RK Win shigowa Companyn sai bai fita a motar ba. Komai daya faru a kan idanunsa ne dake sakaye a cikin glass mai matu?ar haske daya ?awata ?yawun nutsatstsiyar fuskarsa. A hankali yay wurgi da jaridar hannun nasa a sit Win gefensa.
? ? ?? Shi dai driver bai san mike faruwa ba, amma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login