Showing 132001 words to 135000 words out of 219361 words

Chapter 45 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

46965

batare da su yaran sun san mi ake ba. A haka ranar juma'a akai partyn da Oum ta shiryama Maanal da Ajwaad. Abin kamar wasa sai gashi ya ?ayatar. Anci ansha yara sun sha bidirinsu musamman Maanal da ko zama ta huta batayi. Shi kansa AA duk ta takurama rayuwarsa. Haka dai aka tashi gab da magriba, tsabar gajiyar da Maanal tayi a inda tai sallar magrib anan ta Singire barci. Kallonta kawai Oum tai tana murmushi, dan a tare sukai sallar a Wakinta. ?aukarta tai cak ta maida saman gadonta ta kwanar, ita kuma ta cigaba da lazimin ta.
? ?? Bayan idar da sallar isha'i su Ajwaad suka shigo harda Aban su. Kai tsaye Wakin Oum Abah ya shigo. Yakai zaune bakin gado fuskarsa da murmushi yana kallon Maanal ya ce,  A'a anan surukar taki tai barci? .
? ? ?? Dariya Oum tayi tare da faWin,  Kaji Aban su da wata magana suruka kuma? .
? ?? Murmushin sa ya sake faWaWawa shima da faWin,  Eh mana. Ai abunne na Maanal da autanki akwai ban mamaki. Zan so wannan abotar tasu ?arshenta ya kasance hakan .
? ? ?  To ALLAH ya zaSa abinda yafi alkairi. Idan hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki Gandanga. Dan har cikin raina nake jin matu?ar ?aunar yarinyar nan wlhy .
? ? ? ? ??  Nima haka yarinyar ta shiga raina sosai. Badan kar ace ma na cika zumuWi ba nifa da a yanzu zan Waura musu aure kawai .
?? Dariya sosai Oum keyi. Shima Aba na tayata. Sai da sukai mai isarsu Oum tace,  Ayi ha?uri dai a barsu sukai hankalin kansu. Kar a tauyesu musamman ita da take mace. Gara shi namiji ne yana da damar auren fiye da ita .
? ?  Hakane kuma kema kinyi magana. Kinga nama shafa'a Wazun Baban nasu ke sanar min zasuje gida hutun nan ma, dan mahaifiyarsa tana kewarsa sosai.
? ? ? ?  Kai masha ALLAH, ai ni har ?o?arin su nake gani ma. Musamman Ammien Shahidah. Garama shi tace yaje kusan sau uku. Amma ita tunda suka dawo Kano bataje ba hakama yara .
? ??  Abin ne sai a hankali ai. Kin san idan iyali sukai nauyi tafiya ma wahala take yi. Balle wannan aikin nasu na ?an sanda sai a hankali. Kwanaki ma kamar zasu masa transfer ALLAH dai ya taimakesa aka samu canji. Hankalinsa ya tashi sosai dan yace baya son yawon da yake da yaran musamman a yanzu da suka fara girma .
? ? ? ? ? ??  Yana da gaskiya. Ita kanta takance ALLAH yasa ko ya samu canjin wajen aiki ya barsu su anan Kano dan tana jin daWin zaman garin......
? ?? Sallamar Ajwaad ta katse Oum. A tare suka amsa masa da bashi izinin shigowa.
??  Lafiya Autana? .
Oum ta faWa tana kallonsa. Fuska ya Wan yamutse kamar zai saki kuka ya ce,  Oum kaina ke ciwo. Kuma ina jin yunwa .
? ? ?  Ya rabba. Autana badai duk kai kawon nan baka ci abinci ba? .
?? Kansa ya Waga mata alamar  eh .
Da sauri ta kama hannunsa suka fice tana jan salati. Aba ya mike yana musu dariya....

?? ___________&

? ? ? ?? Sosai su Ammie suka shirya wannan tafiya. Yayinda su Shahidah keta zumuWi banda Maanal da tace idan fa bada Ajwaad ba babu inda zataje ita kam. Babu wanda ya tanka mata dai akan batun. Su dai sun cigaba da shirinsu kawai.
? ? A Sangaren Ajwaad Win ma tunda yaji batun tafiya jikinsa yay sanyi. Da farko shima ya nuna son binsu. Har ya samu Oum da maganar tace ita dai babu ruwanta ya sanarma Aba. Bai Musa ba ya samu Aban da batun. Amma sai ya kwaSesa akan maganar. Kai tsaye ya sanar masa bazai iyu ba. Suma zasuyi tasu tafiyar zuwa Adamawa suga gida...
? ? ? ? ? Tafiya ta tabbata, amma ansha fama da bada?ala kafin Maanal ta yarda. Sun tafi tana kuka kashirSan kamar zata shiWe. Shima uban gayyar da taurin kansa yasa baiyi kukan ba da farko yana ganin sun wuce ya shige Waki ya kwanta a gadonsa sai ga hawaye. Daga ?arshe da zazzaSi ya yini ranar. Har washe gari sai da aka sanya masa ?arin ruwa.
? ? A Sangaren Maanal ma kuka taci sosai har sai da Babu ya mata buyagi, itama ?arshe zazzaSi ya rufeta. Taita kwara musu amai a mota. Haka suka isa Kebbi tayi ligiff a wahale. Anan suka Wan tsaya aka dubata. Washe gari suka Wauki hanyar Suru da shima keda Wan nisa daga nan cikin birnin Kebbi Win. Dan a ranar Win ma basu isa ba sai da zuhur..
? ? Gari ne tsaka tsaki a komai. ba ?ato bane can sosai. Ba kuma ?arami bane ba. Suna da wutar lantarki sannan akwai titi har a cikin garin. Kusan zaka iya samun duk abinda kake so naci ana saidawa musamman wanda ake mu'amala da shi ako ina kamar su kayan sanyi, kayan marmari, nama, da ire-iren hakan. Mutanen garin na neman ilimi gwargwadon iko, dan suna da manyan mutane sosai a ?asar da ake damawa da su a gwamnatin jahar dana tarayya. Daga Suru hanyar Giro suka Wauka, nan kam basu isa ba sai yamma sosai. Giro dai ?aramin garine, amma ?auyene mai ?yau da ?ayatarwa. Tun kafin motar Babu ta isa labari ya iso gidansu. Lokacin da motarsa ta tsaya tuni yara sun zagayeta cike da zumuWi musamman ganin harda ba?in fuska da basu sani ba. Dan duk sanda aka haifesu wasu kuma sukai wayo Ammi bata garin.
? ?? Tun daga waje zaka san gidan ?aton gaske ne. Dan ?ofa ce wangamemiya ?warai da gaske. Sai ?atuwar bishiyar ceWiya da kufan wutar makarantar allo irin ta tsangaya an zagayeta da dutsuna. Gefenta kaWan massalaci ne da Wakuna a jere kusan guda goma ko muce shaguna da jikin bangonsu duk alluna ne. Jiki a sanyaye Ammie ta fito fuskar ta Wauke da murmushin ?arfin hali. Yayinda su Shahidah keta kalle-kalle suna son tuno abinda suka manta musamman ma ita da aka tafi da ita da Wan wayonta. Tuni yaran sun fara kwasar kayayyakin suna shiga dasu, yayinda su kuma suka bisu a baya Babu biye da su. ?akuna ne guda biyu masu kallon juna a farkon shiga. Ana hannun dama ke buWe wani dattijo mai farin gashi fatt zaune kan buzu yanata rubutu a wani ?atoton allo. A hanli Ammi ta cire takalman ?afarta zuciyarta na mata Wan sanyi, ganin haka yasa suma su Shahidah cirewa, yayinda Maanal ta dogara tana kallonsu...
? ? ?  Barka da hutawa Baffah .
? Ammie ta faWa a hankali kanta a du?e dai-dai tana shiga cikin Wakin. Sai lokacin tsohon ya Wago ya Wan kallesu fuskarsa da murmushi. Cikin kamala da tausa harshe ya furta,  Lale da mutanen garin dabo .
?? Murmushi Ammie ta sake yi hakama Babu da ya shigo ri?e da hannun Maanal data dogare a ?ofa. Sai da suka kai zaune tsohon ya sake faWin,  Ashe zaka cika al?awari Habibu ka kawo min iyalanka na sake gani kafin na koma ga ALLAH? .
? ? Sosai Babu ya sake sunkiyar da kansa cike da girmamawa ya furta,  Ai min afuwa Baba, ai min afuwa .
?? Murmushi tsohon yay mai faWin gaske. Sai kuma ya mi?ama Maanal dake ta faman kallonsa cikin zare ido hannu alamar tazo gareshi. Da sauri ta matsa jikin babanta tana ma?e kafaWa alamar bazata je ba. Turata Babu yay yana mai daka mata tsawa. Cikin harshen turanci ya ce,  Wuce kije mana ban son raini .
? ? ?? Duk da tsohon bajin abinda Babu ya faWa yay ba sai yay murmushi. Dan ya fahimta ganin yanda Maanal ta zabura jiki na karkarwa ta matso inda yake sai dai duk a Warare. Bai ?iba ya kama hannunta ya zaunar a gabansa. Cikin tausasa harshe ya furta,  Wannan shi ake gudu dama ai Habibu. Shiyyasa muke kwaWayin ku ringa matso da iyalan naku gab damu koda lokaci-lokaci ne .
? ? ??  ALLAH ya huci zuciyarku Baba .
?? Babu ya sake faWa da sauri. Cikin sanyin murya itama Ammie ta nema afuwa. Kafin ta Wora da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta bayan rabuwa. Hakama su Shahidah duk suka shiga gaishesa. Hannu duka ya mi?a musu alamar suzo garesa. Babu musu duk suka matsa. Sai da duk ya taSa kawunansu sannan ya tambaye su sun ganesa?. Kai tsaye Shahidah tace ta ganesa. Amma Amaal na Wan inda-inda. Ta dai san ta sanshi sama-sama. Sai dai a wancan lokacin bai kai haka tsufa ba. Gashinsa kuma bai furace kamar yanzu ba. Murmushi yay da akazo kan Maanal da yana tambayarta kawai ta fashe da kuka. Itafa harga ALLAH tsoronsa take ji. Musamman wannan farin gashin nashi dogo sosai daya zagaye ?ar ramammiyar fuskarsa. Ga farin rawani ya naWa akan nashi. Lallashinta ya shigayi tare da bata farar alewa dake cike da wata ?warya a gefensa. Badai ta sha ba amma ta daina kukan.....
? ? ? Sun jima a wajensa dan har duhu na neman rufawa kafin su shiga cikin gidan. Lallai ?aton gaske ne da sassa daban-daban. Tarin manyan turamen daka dake a ?ar?ashin bishiyar dalbejiya a farkon shigowa gidan zai tabbatar maka da hakan. Sai runbuna da ake ajiye abinci da a?alla sun kai kusan ashirin. Yara ne sosai a haka ma dan mangariba ta rufa ne wasu basa gida. Sai mata da akalla sun kai goma sha biyar dake tsaitsaye wasu ma daga su sai karin ?irji. A hakan kuma ?alilanne a matan gidan, waWan nan wanda bazasu iya ha?uri bane saboda zumuWin son ganin Ammie da yaranta.
? ? Itama Ammien ganinsu yasa tuni ta manta da fargabarta. Fuskarta da murmushi ta nufesu. To suma dai bakunan nasu a washen suke. Duk da dai wasu fara'ar tasu bata kai ciki ba. Su dai su Maanal na raSe jikin Babu da matan nan keta faman yima sannu da zuwa. Garama Shahidah da Amaal na ?o?arin gaishesu da kalmar  Ina yini . Lallai shekara shida ba kwana shida bace. Suma sai kallon yaran suke da mamakin canjawarsu. Sun yi girma kuma sosai musamman ma Maanal da aka tafi da ita daga garin tana ?ar shekara biyu. Yanzu ko gashi tana ?ar budurwa shekara takwas ai ba wasaba su a wajensu. Dan yara sun ma fara kula samari. Kamar Shahidah kuwa masu sha biyar ai sun haihu ta biyu kota farko dana biyu a ciki. Kamar Amaal mai sha uku sune amaren wannan shekarar..
? ? ? ?? Har sashen gwaggo akai musu rakkiya. Inda anan ne Wakin da Ammie tai rayuwa a ciki yake. Wajene aka dan katange da Wakuna guda uku. ?aya na Gwaggo mahaifiyar Babu Waya nata. Sai Wayan na kishiyarta da bata wuce wata biyar a gidan ba ta fita. Fitar tata ce kuma ya ?ara mata ba?in jini a gidan da ma wajen surukar tata da bata samu sassauci ba sai da suka bar garin da zama. Gwaggon na saman wani Wan dutse daga ?ofarta tana alwala. Sau Waya ta Wago ta kallesu ta maida kanta. Amma haka Babu ya nufeta fuskarsa da fara'a yana faWin,  Barkanki da wannan lokaci Gwaggona .
? ?? Ganin haka itama Ammi da sauri ta matsa ta tsugunna tana faWin,  Sannu Gwaggo! Mun sameku lafiya? .
? Maimakon ta amsa su su duka a da?ile ta jefama Ammie wani kallo ta maida idanunta akan su Shahidah dake tsaye suna kallonsu sannan ta maida ga Babu ta sakar masa murmushi.  Babana kasha hanya .
?? Murmushin ?arfin hali yayi dan abinda taima Ammin ya Wan sokesa. Sai dai bai nuna ba ya danne abinsa ya maida mata da murmushin yana faWin,  Aiko dai Gwaggo. Bara na je salla gashi har za'a shiga damma ina da alwala .
? ? Kanta kawai ta jinjina masa. Ya mi?e yana kallon su Shahidah dake rakuSe suna kallon Ammie dake du?e kanta a ?asa har yanzu.  Ku kuma kukai tsaye anan. Ku shigo mana .
? ? ? Jikinsu a sanyaye suka Waga kawuna. Shi kuma ya fice batare daya waiwayesu ba zuciyarsa duk babu daWi. Yasan dole sai ha?uri, dan hutun nan sam bazai zame musu na farin ciki ba sai abinda suka gani. Tsakaninsa da mahaifiyarsa babu wata damuwa. Amma yanda takema matarsa da yaransa abun na damunsa matu?a. A ganinsa matarsa bata cancanci hakanba kodan hallacin iyayenta a garesa ya kamata Gwaggo ta rangwanta mata. Amma ina, ya rasa wace irin ?iyayyace wannan mai zafi........
'?
? ?








('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR GOLDEN COLLECTIONS TA TANADAR MUKU KAYAN ADO N FITA KUNYA KAMAR SU ATAMFA,LACES ABAYA SHOES AND BAGS DA KAYAN DECORATIONS D FURNITURES A FARASHI ME SAUKI

__________

.........*_SU WAYE SU AMMIE?:-_* Alhaji Umar da mutane sukafi sani da Alhaji Umar Giro Wan asalin jihar Kebbi ne a garin Giro dake ?ar?ashin Suru LG. An haifesa a babban gida da yay suna matu?a a cikin garin Giro saboda kasancewarsu manyan mutane masu ?arfin ilimin addini. Su kusan ashirin da bakwai mahaifinsu ya haifa, maza sunfi yawa, dan mata huWu ne kawai a cikinsu, sauran su ashirin da uku duk maza ne. Malam Ibrahim shine mahaifinsu, sai iyayensu mata su uku. Ta tsakkiyar itace mahaifiyar Alhaji Umar, shi kaWai kuma ta haifa a duniya, sauran ?a?a ashirin da shida duk na matan biyu ne. Dan matarsa ta farko haihuwarta goma sha Waya amma ?a?a goma sha shida duk nata ne. Sai amarya nada goma cif duk da itama dai wasu sun rasu a ciki.
? ?? Kishi sosai ake zubawa a gidan Malam Ibrahim, hakan yasa ?a?ansa suka tashi da zafin ?an ubanci. Kowa Wan Wakinsu kawai yake so. Wannan a?idar tafi wahalar da Umar, dan shi kaWai shi mahaifiyarsa ta haifa shiyyasa sam baya wani jin daWin zaman. Yasha wahala ?warai da gaske a hannun ?an uwansa, har takai karatun ma baya fuskanta dan anan cikin gidansu suke Waukar karatu wajen mahaifinsu, ?an uwansa manya kuma sune gardawa a yanzu.
? ? ?? Ganin yanda Umar Win ke cikin tsangwama da ?yara yasa mahaifinsu Waukarsa ya bama wani amininsa shima malami ne amma a can cikin birni, yanada tarin almajirai kuma Alhamdullah ana karatu. Mahaifiyarsa tasha kuka, amma hakan yafi mata kwanciyar hankali akan zamansa a gidan. Umar ya koma cikin birnin kebbi, kuma Alhamdullah yana samun ilimi, ya kuma kwantar da hankalinsa sosai dan Malam Khamisu ya saka shi cikin ?a?ansa babu banbanci. ?a?an malam Khamisu su suna karatun boko, hakan yasa shima Umar aka saka shi a boko.
? ?? Zamu iya cewa Umar ya fara karatunsa cikin nasara, kasancewarsa yaro mai basira cikin ?an?anin lokaci yay zarra. Ga kuma ilimin addini shima alhmdllh. Umar na zuwa Giro akai-akai saboda mahaifiyarsa, dan haka canjin da rayuwarsa ta samu a bayyane yake ga kowa. Cigabansa na saka ?an uwansa sake jin tsanarsa da hassadarsa su da iyayensu, sai dai babu yanda zasuyi. A haka ya gama secondary school ya fara jami'a, yana level 2 ALLAH yay ma mahaifiyarsa rasuwa. Ya shiga tashin hankali matu?a daga shi har mahaifinsu, sai dai babu yanda aka iya da hukuncin UBANGIJI. Bayan rasuwar mahaifiyarsa ya sama ransa dangana ya maida hankalinsa ga karatunsa, har ALLAH yasa ya kammala jami'a. A kuma wannan lokacin ALLAH yay ma uban ri?onsa Malam Khamisu rasuwa shima. Umar ya sake shiga ruWani, dan komai ya fice masa a rai. Dan haka ya tafi yin sarvese Winsa nesa da Kebbi. A jihar Niger cikin garin Minna Umar ya fara Sarvese, inda anan kuma ALLAH ya haWashi da matar aure. Lubabatu yarinya ?ya?y?yawa mai ilimin addini da nutsuwa. Gata da ha?uri da tarbiyya. Cikin ?an?anin lokaci soyayya ta ?ullu tsakaninta da Umar da hidimar ?asa ta kawosa garin Minna. Lubabatu su biyu ne a wajen mahaifinsu, daga ita dai ?anwarta Shamsiyya. Suma ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa matar uba ke ri?onsu, suna matu?ar shan wahala a hannunta. Hakan yasa Umar na nuna yana son Lubabatu mahaifinta ya bashi.
? ?? Cikin ?an?anin lokaci aka gama komai, dan kafin ya gama sarvese har ranar aure an saka musu. Yana kammalawa akasha biki. Nan Giro aka kawo amarya family house Winsu, dan ba auren nasu kaWai akai ba harda wasu a cikin ?an uwansa da suma akayi duk a ranar. Sai da aka gama shan biki, bikin da aka nuna matu?ar banbanci dan sam Umar baida wani gata a cikinsu, gashi itama Lubabatun duk sai a hankali tunda basu da wani gata suma sakamakon rashin uwa. Haka dai akayi biki aka gama, amare suka tare da mazajensu. Umar baya son zama a Giro, amma saboda kunyar mahaifinsa ya kasa magana. Ga aiki ya samu a Kebbi, sai ya zam dole ya koma Kebbin sai weekend yake zuwa. Sam Lubabatu bata jin daWin zama a cikin waWan nan ahali, dan kishi da ?an ubancin da ?an uwansa ke nuna masa duk sai ya tattaru ya koma kanta a yanzu. Ga matan ?an uwansa suma sun sakata a gaba, facalanci mai muni ake zubawa a tsakaninsu. Musamman ma da Matar yayansu na biyar wanda Umar ke bimawa a wajen mahaifinsu mai suna Talle. Talle irin matan nan ne masu mugun hali da hassada da ?yashi, duk wani cigaba tafi son ace itace da shi. Yaranta biyu a gidan, Habibu da mace, sai ?aramin ciki da take laulayi. Tayi matu?ar tsanar Lubabatu a gidan, dan tafisu wayewa da cigaba. Ita tayi karatun boko har zuwa secondary kuma gana addini dan tayi sauka. Suko mafi yawansu musamman ma Talle kota

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login