Showing 180001 words to 183000 words out of 219361 words

Chapter 61 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

47007

ba, shiyyasa nake so ta gansu da idonta ai.
? ?? Kai kawai ?awar tata ta jinjina alamar gamsuwa.....

? ? ? ? A ?ofar katafaren gate Win gidan nasu ta tsaida motar, hakan ya sashi buWe idanunsa ya kalleta. Ganin tana ?o?arin kunce belt ya ce,  Yanaga kin tsaya anan? Ki shiga mana .
? ? ? ?  No ka ?arasa da kanka, ni zan koma daga nan .
? ?  Bazaki gaida su Oum ba? .
 Next time .
Kansa ya jinjina kawai ya cire nasa belt Win.  Kije da motar zan aiko driver ya amsa .
? ? ? ?  A'a zan hau taxi .
? ? Dakatawa yay daga ?o?arin fitar da yake, ya Wan juyo yana kallonta.  Kin san fa bana son musu, taxi kuma na haramta hawanta daga yau .
? ? ? ? Komai batace da shi ba saboda yanda ya tsatstsareta da idanu. Shima sai bai sake cewar ba ya buWe ya fita. Sai kuma ya Wan du?o ta glass Win windown.  Kije gida magrib ta kusa. Kuma kiyi tu?i a hankali .
? ? ?  Ni Company zan koma Waukar kayana .
? ?  No ban yarda ba kije gida. Driver zai taho miki da su. Ki kula da kanki .
? ? ? ??  ALLAH ya ?ara lafiya .
? ? Ta faWa itama tana maida glass Win ta rufe duka tare da yin baya. Yana tsaye yana kallonta har sai da ta Sace masa. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da furzar da iska. Sai kuma ya shafa cikinsa yana yamutsa fuska kaWan. A hankali ya juya yay knocking gate Win gidan nasu. Maigadi ya le?o yana tambayar waye. Ganin AA ya sashi haWiye sauran maganar, mamaki fal ransa na ganinsa a ?afa. Bai dai ce komai ba ya gaisheshi. Shi kuma ya amsa masa yana wucewa ciki. Da Mamy ya fara cin karo zaune a gaban sashen Oum, sai Naufal da Anum dake wasa da keke. Yanda ta wani zuba masa idanu tun daga nesa ta sashi janye nasa da ga kallonta. Cikin dauriya ya ?arasa inda taken, su Naufal da sai yanzu suka gansa suka she?o da gudu suna masa oyoyo. Daurewa yay ya tarbesu, sannan ya shiga gaishe da Mamyn. Bata amsa ba, sai mugun kallo da take jifansa da shi.
? ? ?  Ina motar taka? .
Ta jefa masa tambaya a bazata. Bai iya ?arya ba, ya kuma tsani mai yi, amma ya fahimci yau dolensa ma ya yi tan. Batare daya yarda sun haWa ido ba ya ce,  Tana gareji Salihu ya kaita. Nima taxi na biyo .
? ?? Rasama abin cewa Mamy tayi, dan yayi wani kicin-kicin da fuska, sai kawai ta zuba masa idanu. Shiko ya sake ciWin-ciWin da fuska. Batare daya yarda ya sake kallonta ba ya saki hannun su Naufal ya nufi sashensa dan ruwa kawai yake bu?atar sakarma kansa. Ko Oum baya son ta gansa a wannan yanayin. Ita kanta Mamy Win bai so ta ganshi a hakan ba....
? ? ?? A Wan tsawace ta dakatar da shi, dole ya tsaya yana mai lumshe idanunsa, sai kuma ya dawo da baya inda take. Mi?ewa tai batare data sake kallonsa ba cike da bada umarni ta ce,  Anjima ka sameni zan yi magana da kai . Daga haka tai wucewarta. Da kallo kawai ya bita, wani abu mai nauyi na masa kai-kawo a cikin wuya da ma?oshi, yayinda idanunsa suka kaWa sosai. A hankali ya furzar da iskar numfashi, sai kuma ya nufi sashen nasa....

__________&

? ?? Baki a wangale maigadi ke kallon Maanal daya buWema gate. Taja motar a hankali zuwa cikin gidan. Bawai tu?in nata ne ya bashi mamaki ba, dan yasan tana jan mota idan tazo. Ganin Wirkekiyar motar da take ja Win ce da kuma sanin da yay mata bai taSa ganin ta tu?a wata mota ba sai ta gidan ya sashi a mamakin....
? ? ?? Turus itama ta tsaya tana kallon motar RK lokacin da take fitowa. Sai kuma ta Wan le?a gaba kaWan. RK Win ne shima da kansa zaune a cikin motar tasa ya zubama motar data ajiye ido ko ?yaftawa bayayi. Ta tabbatar kallon ?urillar da yakema motar ya gane ta wacece ne. Sai kawai ta dake abinta ta ?arasa garesa.?A hankali ya janye idanun nasa daga kallon motar ya maida kanta. Batare da ya amsa sallamar da take masa ba ya furta,  Dama kina jan mota haka? .
? ? ?? Guntun Murmushi kawai tai masa ta ce,  Uhmm! .
? ??  Masha ALLAH, kinyi ?yau kuwa da motar . Ya faWa yana fitowa da ?yau daga motarsa.
? ?  Oh harda zolaya ma abin kenan? .
 Babu wata zolaya gaskiya na faWa miki. Naje Waukarki a office AS Win Boss Winki yace kun fita tare tun la'asar. Shiyyasa na wuto nan dan na matsu na ganki .
? ? ?? Murmushi tayi batare data tanka maganarsa ta farko ba ta ce,  Kamar wanda ya shekara bai ganni ba? .
? ?  Miye maraba my queen. Kwana huWu fa. Ya kuka baro su Ammie? .
? ?  Lafiya Lau suke, suna gaisheka. Ya aikin? .
? ?  Alhamdullahi munata fama. Shi AA Win yana office kenan? .
? ? Murmushi ta saki a ta?aice, dan ta fahimci dole dai so yake sai anyi maganar AA Win nan. Sai kawai kanta tsaye ta ce,  Yana gida baida lafiya. Dan da wajenka ma zan kaishi yace na dai ajiyesa a gida .
? ? ? ??  Mike damunsa? .
? ??  Kamar ciwon ciki yace .
?  ALLAH ya bashi lafiya, yasa kaffara ne. Bari nai salla zanje na duba shi.
? ??  Okay ai ni dama da motar tashi ka wuce, sai driver ya bika da ita .
??  A'a, bashi ya baki ba da hannunsa .
 Dama yace zai turo driver ya Wauka ne. Ni kuma bana ma so Didi taga motar a gidan ne .
? ? ??  Dan mi to? .
?  Kawai .
Shiru kawai yay yana kallonta. Yasan ?arshem zancen kenan. Yau ma ai babu laifi an amsa masa magana da tsaho sosai. Ajiye zancen yay shima gefe ya fara wanda ya kawo shi ganin magrib na sake gabatowa.  Magriba na gabatowa. Ga shi inada uziri da daddare. Kuma ina son muyi magana yanzu ALLAH yasa ban takura ki ba .
? ? Kanta ta jinjiina masa alamar eh. Shima sai ya cigaba da faWin,  Maanal na karanta diary Winki duka. Ba kuma zanja wani zance ko neman ?arin bayani ba daga gareki ko daga wani, ina son ki bani dama magabata su shigo cikin al'amarinmu. Idan kuma babu damuwa ina son bikin anan kusa .
? ? ? Duk da wani irin motsawa da zuciyarta tayi haka ta dake. Tai ?asa da kanta tana sakin miskilin murmushi. Sai kuma ta jinjina kan batare data kallesa ba tace,  Duk da ?addarar data shiga cikin rayuwata da mutunci na ka amince zaka aureni a haka Rafeeq? .
? ? ? ? ?  Maanal! Ke nake so ba jikinki ba. Kuma kema kince ?addara ai. ?addara kuma babu wanda ya isa faruwarta ga kansa balle wanninsa. Haka ALLAH ya tsara miki rayuwa ai. Dan haka ki manta da baya kamar ma bata faru ba. Ni ke nake so Maanal, ke nake so ki zama uwar ?a?ana. Halayenki, tarbiyyarki sune gaba a komai. Yanda na fara sonki ban san ke Win wacece ba, sanin ke wacece bazai sa na taSa canjawa ba. Ni dai kawai fatan da nake da ro?o ki soni koda kwatar soyayyar da nake miki ne, wanda nake mikin ta ishemu rayuwa in sha ALLAHU .
? ? ? Karan farko Maanal ta Wago tana kallonsa, idanunta na zubar da hawaye.  Nagode Rafeeq. Nagode sosai da Wunbin soyayyar da kake min. Kuma ni ban taSa ?inka ba, ba kuma zan taSa ?inka ba. Sai dai kasan akwai ?alubale a gaban mu .
? ? ? Sai da ya mi?a mata handky Winsa sannan ya ce,  Nami? .
? ? ?  Yaya Yazeed, ya taka rawar gani sosai a rayuwata, shima bai gujeni ba duk da yasan wacece ni. Wasu dalilai ne yasa kawai nake gujema aurensa domin samun zaman kafiyarsa shima. Amma a yanzu ban san yanda zan tunkare shi shi da mahaifinsa ba, kai har ma Ammie .
?? Ta faWa tana share hawaye. Murmushi ya saki mai faWi har ha?oransa na bayyana. Sai kuma ya gyara tsaiwa sosai.  Sweetheart na fahimce ki, kuma abinda kika faWa gaskiya ne. Amma muyi addu'a, da. ban taSa kallon Yazeed a ?alubalena ba game dake dama. Duk da ina fargabar kada ki zaSesa ki barni, ta wani gefen kuma jin rawar daya taka a rayuwarki ta ?ara sani ganin girmansa da jin kimarsa a raina fiye da da. Amma tunda kece kika bani dama a yanzu da kanki na samu dukkan ?warin gwiwa. Zan iya karawa da kowa domin mallakarki. Karki wani damu zanyi maganin wannan matsala Win in sha ALLAHU. Ke dai kawai ki kasance cikin shirin zama amaryar Rafeeq Kasheem Kura anan kusa kaWan .
? ?? Murmushi tayi da juya masa baya. Shima sai yay dariya. Leda ya ciro a mota ya mi?a mata.  Ga wannan ki shiga da shi ciki bara naje, idan na gama da wuri zan dawo. Idan kuma dare yayi a shirya mini lokaci na musamman zan kira waya mu ?arasa anan. Amma dan ALLAH bana son ganin hawayen nan masu daraja suna fita. Baki ji yanda nake jin zafin a zuciyata ba .
? ? ?? Kai ta jinjina masa kawai. Ta amsa ledar tai godiya. Sai da taga ya shiga mota sannan ta nufi ciki, ya Wan bita da kallo ta cikin mirror yana murmushi. Sosai yake jin zuciyarsa na ?ara samun nutsuwa. Tabbas yana son yarinyar nan. Ba kuma yajin akwai wani abu da zai bari ya rabasu. Ala?arta da AA ta baya ko a ?asan slippers Winsa bai ji ta damesa ba. Tunda a kaf labarin bai ji a inda ko sau Waya AA ya furta yana sonta ba ko ita tana son shi. Daga ?arshe ma da bakinsa yace shi baice yana son aurenta ba. Hakan na nufin babu soyayya kenan sha?uwace kawai da kowa kema kallon soyayyar. Da wannan tunanin ya fice a gidan.....

__________&

? ? ? ?  Hajiya! magana ta gaskiya yaron nan al'amarinsa nada matu?ar nauyi da tsauri. Ni kaina na shiga mamaki da ruWani da Hajiya ta sanar min aikin da duk mukai masa bai shigesa ba. Shiyyasa na tsananta bincikena a kwana biyun nan, dalilin ma ce miki ki dakata da zuwa sai yau kenan .
? ?? Cikin matu?ar damuwa Hajiya Basariyya ta ce,  To malam yanzu yaya ake ciki kenan? Dan gaskiya yarinyata na sonshi sosai. Kuma nima ina mata sha'awar aurensa .
? ? ?? ?ar dariya malam yayi, sai kuma ya kalla Huznah da keta faman kuka a jikin Maman Yaseerah. Janyewa yay ya maida ga Hajiya Basariyya.  Hajiya ku kwantar da hankalinku komai zai yi dai-dai. In har za'abi dukkan matakan da zan bayar zata aureshi. Sai dai akwai ?alubale babba a gabanta....
? ? ? Cikin sauri Huznah da tun da malam ya ce zata iya auren AA ta Wago da sauri ta ce,  Kowane irin ?alubale ne zan iya Wauka Malam, wlhy ina son shi, zan iya Waukar komai in har zan zama mallakinsa .
? ? ?? Dariya malam ya sake yi da faWin,  Kin tabbatar zaki iya? .
? ??  Ko miye kuwa Malam .
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya mi?a mata zabgegen carbin hannunsa. Da sauri ta amsa, zaSar Waya yace tayi, tako zaSa Win. Amsar wanda ta zaSa yayi ya rufe idanunsa yana muy-muy da bakinsa. Su dai duk idanu suka zuba masa kawai.........
'?





('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


.......Fin mintuna uku ya buWe idanun nasa tare da ajiye carbin sannan ya dubi Maman Yaseerah.  Wato Hajiya babban ?alubalen shine akwai wadda ke'a zuciyar yaron gaskiya da jimawa. Dan haka ya?i biyu kawai da zamuyi zai sa ta samu damar aurensa. Na farko shine cire yarinyar daga zuciyarsa gaba Waya, ba kuma zamu iya yin hakan ba sai mun san wacece ita. Na biyu zamuyi aiki akan iyayensa, ta yanda ko baya so zasu sakashi dole amsarta. Mu kuma idan ta shiga daga ciki sai muyi aikin karSa mata zuciyarsa ta yanda bazai sake kallon wata mace ba a duniya sai ita. Kai hatta uwar data haifesa wlhy sai dai tabi bayanta .
? ? ? Gaba Wayanzu babu wanda fuskarsa bata washe da murmushi ba.?Sai Hajiya Basariyya ce ta ce,  Amma malam taya zamu san wadda ke cikin zuciyar tasa ne to? Sai naga kamar hakan zaiyi wahala .
? ? ? ? ?  Bazaiyi wahala ba Hajiya. Wannan aikin na yarinyarki ne. Ita zata bincika mana ai .
? ??  Karka damu Malam zanyi ?o?arin hakan. Sai dai akwai wata yarinya Nuratu da muka haWu, itama tana sonshi, ban sani ba ko ita ce a zuciyar tashi, dan har ciwon nan itace ta jimin shi .
? ? ? ? ?  Nuratu! .
? ??  Eh malam .
? ?an jimm yay, sai kuma ya sake Waukar carbi ya bata. Amsa ta sake yi ta zaSa. Kamar dai Wazun yanzu ma ido ya rufe na wasu mintuna sannan ya buWe.  Gaskiya ba ita bace. Abinda na gani a kanta mahaifiyarta ke son ta aureshi da wata ta kusa da ita dake a cikin gidan su yaron. Suma kuma suna aiki a kanshi sosai, a yanzu haka ma suna shirin yin mai zafin gaske duk dan itama ya aureta.
? ? ? ?  Eh lallai, ashe suma waWan nan shegun kansu ne. To aiko Malam ai mana maganinsu, dama nace bazan yafe mata ciwon da ta jima Huznah ba. Jiba yanda ta maida min da fuskar yarinya kamar ?ar yarbawa ko goburawa. Ashe itama ba sonta yake ba shegiyar yarinya kawai .
? ??  Karki damu da wannan Hajiya nasu mai sau?i ne. Yanzu zan haWa mata abubuwa taje ta cigaba da amfani da su. Nan da kwanaki uku zan kammala aikina nima. Itama sai tai ?o?arin samo mana wadda ke'a zuciyar tashi .
? ? Godiya suka shiga jera masa kamar shine mai basu biyan bu?ata. Maybe ma basu samun lokacin yima UBANGIJIN dake basun magiya irin haka ba. Gidan su Maman Yaseerah suka koma, dan anan zasu yini zuwa anjima su koma Kaduna......

___________&

? ? ? Bayan sallar magrib AA ya baro massallaci. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa. Bai sameta a falon ?asa ba, dan haka ya haye sama. Sai da yay sallama a ?ofar bedroom Winta ta amsa da bashi izinin shiga sannan ya shiga. Tana zaune kan abin salla, tunda ya shigo kuma ta zuba masa idanu. Hakan ya sashi tsayawa yay shiru. Wani irin Sacin rai taji ya tokare mata ma?oshi, a kausashe ta ce,  Ni zan taso kenan .
? ? ? ? ? Komai bai ce ba ya ?arasa takowa har gabanta ya zauna a saman lallausan carpet Win wajen ya tan?washe ?afafu. Kansa a ?asa ya gaisheta. Kai da ka gansa kasan babu wata sha?uwa a tsakaninsu. Sai ma shakka da girmamawa irin ta na sama akan na ?asa. Sai da ta gama shan ?amshinta cikin kaushin harshe ta furta,  Ajwaad miye matsayina a wajenka? .
? ?? Idanunsa ya lumshe a hankali, ma?oshinsa na kaikawon Sacin rai a cikin wuyansa. Da ?yar ya iya amsa mata da,  Mahaifiya .
? ??  Ai baka Wauke ni a mahaifiyar ba. Saboda Fateema ta fini. Inda ka Wauke ni da ban sharWanta maka sharaWi ba harda ALLAH ya isa ka?i bi. Ya mukai dakai a shekarun bayan akan wannan shegiyar yarinyar ?ar matsiyata? .
? ? ? ?? Kasa bata amsa yay, sai dai fuskarsa tai masifar rinewa. Mamy ta daka masa tsawa jikinta har yana rawa.  Wlhy zan mareka. Wane al?awari ka Wauka min akan Maanal! Da zaSin matar aurenka? .
? ? ?? Karan farko ya kalleta da rikiWaWWun idanunsa da sukai masifar kaWewa, sai kuma ya maida kansa ?asa. Cikin kwantar da murya da girmamawa ya ce,  Mamy ban karya al?awarinki ba. Kuma ni yarinyar nan babu abinda ke tsakanina da ita yanzu sai ma'aikaciya a company na. Shima kuma aure nace zanyi .
? ? ??  Karma kayi, nace kadama kayi. Idan aka Waura maka auren dasu ka sake su a washe gari. Dan kama karkaWe kunnenka kaji nan da wata guda za'ayi bikinka da Nuratu da Huznah. Sannan Maanal na baka sati huWun kacal ka sallameta daga kamfaninka. Idan ba hakaba wlhy wlhy duk abinda na maka kaine kajawosa ciki harda muguwar addu'a. Dan ko mutuwa nayi ban yarda ka cigaba da mu'amala da ita ba. Inko ba haka ba ALLAH ya isa ban yafe maka ba wahalar Waukar cikinka da nayi dana na?udar haihuwarka. Kuma wlhy zan taka har gidan iyayenta a wannan karon naja musu kunne itama kuma Fateeman zanyi fito na fito da ita dan na fahimci itace ta dawo da yarinyar rayuwarka ita munafuka anmimiya. To zan bata mamaki a wannan karon dan ban haifa mata ?a?an banza ba balle tace....
? ? ??  Dan girman ALLAH Mamy kada kiyi haka. Kada kije musu gida. Ni kike da iko a kaina, zan kuma yi miki biyayya. Amma dan ALLAH kada ki Sata yardar da Oum tai miki, kada ki raunana mata zuciya akan abinda ke da hannunki kika Wauka kika bata harda shaidu. Hakama Abah bana son yayi nadamar yardar da yay miki.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login