Showing 138001 words to 141000 words out of 219361 words

Chapter 47 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

46977

tattaro sun dawo Sokoto, a lokacin Shahida nada shekara bakwai, Amaal nada shekara biyar da wasu watanni dan tsiransu da Shahidah kaWanne. Saida sukai sati biyu a Sokoto sannan suka je Giro. Babu wanda bai firgita da canjawar Asiya da yaranta ba. Dan ta koma ?ar gayunta kamar batai rayuwar Giro ba. Tuni kishinta da hassada ya shiga zukatan jama'ar gidan kamar yanda suka dingama mahaifiyarta Lubabatu.? A Sangaren Gwaggo ma babu abinda ya canja, dan ?iyayyar Asiya sai wacce tai gaba. Haka su Shahidah ko kallo basu isheta ba dan tace ita ba jikokinta bane ba uwarsu dai tasan inda ta samo su. Hakan na ma Habib ciwo amma baya cewa komai. A wannan zuwa kuma Gwaggo ta tsira sai Habib ya ?ara aure, dan a haifa masa namiji. Kai tsaye ya nuna mata bashi da wannan ?arfin, dan shi dai bamai kuWi bane, dukiyar da yake juyawa kuwa kowa yasan ta Asiya ce da iyayenta suka bar mata duk da ma dangin nasu sun kusa cinye rabi da kwata. Aiko ta tujaresa da masifa da bala'in daya sashi tattara matarsa da ?a?ansa suka koma abinsu. Sai kuma suna komawar sai ga Asiya da ciki. Yayi farin ciki matu?a, ya kuma shiga addu'a da fatan ALLAH yasa Asiya ta haifa namiji dan shima fa yana son a haifa masa namijin, ga maganar mahaifiyarsa ta sake kwaWaita masa abun a rai. Kawai dan bashi da ?arfin aure ne. Amma tabbas a ransa yana son ?ara auren ma. Dan yana Wan neman mata batare da Asiya ta sani ba, tun kafin yay aure yake yi, bayan aurensu ya rage sosai sai dai kuma ita dama zina masifa ce. Faratane mara wuya, amma indai ka fara sai ALLAH ya soka da rahama kake dainawa.
? ? ?? Ammie tayi rainon cikinta cikin aminci da kulawa, har ALLAH ya kai cikin watan haihuwa ta haihu lafiya. Ta samu ?a mace ma a wannan karon. Sai da Habib yaji wani iri a ransa, sai dai kuma yana Waura idonsa akan yarinya yaji ?aunarta ta shigesa. Dan ita kam tayo kamannin mahaifiyarta da ?an uwansa, ta kuma yo kammaninsa ta bangarori da dama da suke a bayyane........
'?






('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


.........Wannan karon ma dai Giro suka koma suna, sai dai babu wanda ya nuna murna da wannan haihuwa kamar ta Amaal daga Baba Haruna sai uban jegon sai kuma su Shahidah dake murna an haifa musu ?anwa. Wannan karon dai Gwaggo babu damar aibanta yarinya tunda tana kama da ubanta a abubuwa da dama. Amma hakan bai hana sako batun haihuwar Wa namiji ba data fahimci yana tasiri a zuciyar Wan nata. Haka dai akai bikin sunan babu wani armashi sosai sukai shirin komawa Sokoto amma sai Gwaggo ta hana wai su zauna anan suyi wankan jego. Ganin yanda bata kawo tashin hankali ba a sunan yada baba Haruna tunanin ta sauya ne. Dan yanzu ta Wan rage wasu abubuwan a zahirance saboda tsoron kada ta tsinke ?ar sauran igiyar Waya dake a tsakaninsu. Ta koma zuba rashin mutuncinta ta ?asa, dan Habib ta koma takuramawa akan sai ya ?ara aure, ita kuma Asiya ana mata a kaikaice.
? ?? Shima dai Habib wannan karon bai damu ba ya barsu anan ya kuma yarda da batun ?ara aure, dan ya samu damar she?e ayarsa da sabuwar karuwarsa da suka haWu anan Sokoto Win kwanan nan. Zama kamar wasa ya nema zama gaske. Dan bayan gama wankan jegon Maanal Habib bashi da niyyar cewa su shirya komawa Sokoto, sai dai yana zuwa duk ?arshen wata yay musu weekend ya koma. A haka aka tado batun aurensa. Auren daya bama kowa mamaki ya kuma saka Ammie a tashin hankali. Amma sai Baba Haruna ya dinga kwantar mata da hankali da nasiha ta sakama kanta dangana kuwa ta rungumi ?a?anta. Cikin ?an?anin lokaci akasha biki kuwa, yarinya ?arama da bata wuce shekara sha bakwai ba. Inda Ammie ta burge kowa shine tattara komai ta watsar kamar ma ba ita akama kishiyar ba. Sai shima kansa Habib Win ya dinga kiyaye duk wani abu da zai taSa mata zuciya ba kamar yanda Gwaggo taso ba. Itama yarinya da aka Woro akan rashin kunya da zata dinga yima Ammie sai ta dinga jin shakkarta. Abinda ya ragema amarya armashi samunta ba'a cikakkiyar mace da Habib yayi ba, dan tun a daren farko sai da tasha maruka a wajensa a Waki batare da sanin kowa ba. Ko sati kuma bai cika ba na amarci ya tattara ya koma wajen aiki. Aiko akaita gutsiri tsoma wai Ammie ce tayi wani abu, dan Gwaggo har Waki ta sameta ta mata wankin babban bargo. Ita dai batace komai ba. Habib bai zo gida ba sai da yay wata guda kamar yanda ya saba, ya kuma murje idonsa ya sauka Wakin Ammie, itako tanata ro?onsa bai kulata ba, ana cikin haka sai ga Gwaggo har Waki, tas taima Ammie da zaginta akan muna fuka ta tasa Wanta gaba har Wakin amarya Sailu. Ai ko ranar ma maimakon ta samu kulawa a wajensa sai duka taci a banza, dan ya fahimci bata da kunya, Habib kuwa irin mazan nan ne da basa Waukar raini, shi hatta macen bariki tai masa hauka duka take ci a wajensa, Ammie ce kaWai ta tsira da irin wannan halin nasa, duk da yana shan marinta itama a wasu lokutan. To ata?aice dai wannan aure bai rufa wata biyar ba a wani zuwa ya saki Sailuba saki har uku. Nan fa gari ta Wauka Ammie ce ta koreta. Babu kalar abunda Ammie bata gani ba akan wannan rabuwar auren amarya da mijinta, ?an gidan suka kara tsananta, na Gwaggo kam ai ba'a magana. Ga Habib bashi da niyyar cewa su shirya subar garin har sai da Maanal ta shiga shekara Waya da rabi sannan akaima Habib transfer zuwa Kano. Aiko Baba Haruna da'a yanzu ya fahimci Habib na neman matan banza yace ya tattara matarsa da iyalansa su wuce tare. Gwaggo ta nuna bata yarda ba, Baba Haruna ya nuna mata shima bata isa ba. Kamar Habib baya so haka ya wuce da su Ammie Kano, dan yasan an rage masa jin daWinsa ne kawai. Anan ya samu gida ya kama musu haya, daga baya kuma ya saye shi da kuWin Ammie na gado, shine dalilin komawarsu da zama garin Kano. Tunda suka koma kuma basu sake zuwa Giro ba sai dai shi yazo sau uku sai yanzu shekara kusan shidda kenan dan tun Maanal nada shekara Waya da wasu watanni da kaWan ya rage sukai biyu. Ita dam bata san Giro ba bata san ?an Giro ba....

________&&&

? ? ? ? Babu wanda ya sake bi takan su Ammie a gidan duk da wasu suna son kawo musu abinci suna jin tsoro ne. Anan ?ofar Wakin sukai sallar magrib da isha'i. Sai kusan tara saura Babu ya shigo tare da Baba Haruna. Ganinsu a inda ya barsu su da kayansu ya sosa masa zuciya sosai. Baba Haruna kam a fusace ya shiga Wakin Gwaggon. Sosai ya mata tas da abinda tayi Win, ya kuma tabbatar mata wlhy a wannan karon idan tace zatai wani abu to ta tabbatar shi bazai Wauka ba ?ofa a buWe take gareta. Wannan kalmar na tayar mata da hankali akan mijin nata. Dan tasan igiyar nan Waya tak ke ri?e da aurensu yanzu. Bakuma zata so ace ya tsinketa a yanzu da suke a shekarun tsufa surukai cike da gari ba. Shi da kansa ya fito ya shiga dakin dake a mallakin Ammien, Wakin duk tarkace ne ma a ciki, dan haka ya fita babu jimawa sai gashi da almajirai kusan biyar, su ya saka gyaran Wakin, shi kuma Babu ga fita nema musu abinci da maganin da Maanal zata sha dan zazzaSin ya dawo. Dandanan aka gama gyara Wakin, aka kawo katifa da tabarmi aka saka musu. Harda turaren wuta na tsinke baba Haruna ya Wakko a Wakinsa aka kunna, dan yanzu shine ya mayi mahaifinsu a gidan, shine ke da almajirai yake koyarwa, dan haka ya koma Wakin zaure inda suka samesa na mahaifinsu da zama kenan. To da yake tunda yaga Gwaggo na niyyar kashe katifar dakin Ammien sai ya saka aka Wauketa ya maidata can Wakin nasa aka lulluSeta, sai idan Babu yazo ake kawo masa, daya tafi kuma yasa a maidata can.
? ?? Gajiyar tafiya tasa basu ma wani iya cin abincin kirki ba dan ma harda shayi, suna son yin wanka basu san yaya zasuyi ba, dole suka hakura suka kwanta a haka. Dama ita Maanal tuni tayi barci abinta, duk da barcin nata bana daWi bane ba. Washe gari dai sun Wan samu kulawar mutanen gidan sakamakon ganin Baba Haruna tsaye akan al'amarin su. Dan har koko an kakkawo musu a wasu sassan. Duk da ma dai su yaran sun kasa sha sai Ammie ce tasha. Kosan da Baba Haruna da bread ya saya musu kawai suka iya ci, sai naman jiya da Babu Win ya saya musu basu ci ba. Yanda Maanal ta tashi da zazzaSi sosai dole Babu ya Wauketa zuwa asibiti. ?arin ruwa suka saka mata dan jikinta duk babu ?arfi, hakan yasa suka jima can har sai bayan zuhur ya dawo da ita. Anan ne yake sanarma Ammien Abban Fadeel ya kira shi sun gaisa, itama Oum nata nemanta wayar a kashe.
? ?? Sai lokacin Ammie tama tuna da wayar tata, ta bincikota a bag sai taga ashe ta mutu ma babu caji. Dole ta bama su Shahidah tace suje waje su nema yara su rakasu inda ake caji sukai mata. Badan sun so ba suka fita, dan basa ?aunar ganin hararar da Gwaggo ke musu da kallon tsana. Sai zuwa yamma suka amso mata tai kiran Oum, lokacin Maanal ta tashi a barci amma sai ?unci take ta?i kula kowa abinci ma sai da Ammie tace zata zaneta sannan taci sa kaWan. Amma yanzu tana jin ance Oum tai wata irin zabura tazo ta nanu?e Ammie. Dole Ammie ta ta?aita gaisuwar da suke da Oum Win ta bata wayar, dan yi take ma kamar zata warceta. Oum na jin muryar Maanal itama ta saki murmushi...
? ? ?  Oh oh! My Baby I miss you .
? Cike da zumuWi Maanal ta ce,  I miss you too Oum. Oum ina Besty? .
? ? Dariya Oum tayi tana mai jinjina kanta idonta akan Ajwaad dake kwance a gadonta, tunda yaji ta ambaci sunan Maanal shima ta kafeta da idanunsa. Wayar ta mi?a masa tana faWin,  Gashi nan kin barsa da ciwon kewa .
? ? Baki Maanal ta tura gaba, cike da shagwaSa ta ce,  Oum ai nima banda lafiya ina ciwon kewarsa .
? ?? Dariya Oum ta sanya, hakama Shahidah da Amaal. Ammie kama sai ta girgiza kanta kawai. Ganin su Shahidah na mata dariya ta tashi tana harararsu da murguWa musu baki ta fice a Wakin. Ammie na kiranta akan ta kawo mata wayarta kar tai mata Sarna bata dawo Win ba. Gwaggo na tsakar wajen nasu tana haWama dabbobinta dusa, suna haWa ido da Maanal ta harareta, itama ko ta rama da murguWa mata baki ta Wauke kanta. Ai sai Gwaggo tai mutuwar tsaye da mamakin wannan fitsararriyar yarinya. Ita zata harara ta rama wannan jaririyar ?ar?.
? ?? Oho ko'a jikin Maanal, dan kujerar Gwaggo dake a ?ofar Wakinta ta zauna abinta. Sai kuma cikin shagwaSa ta ce,  Besty! .
? ?? Wata irin ajiyar zuciya Ajwaad ya sauke yana lumshe ido da ya zame masa Wabi'a duk da ?arancin shekarunsa. Sai kuma a cikin muryarsa mai sanyi da zurfi ya amsa da,  Oummyim! .
? ? ?  Haushina kake ji dan na tafi na barka? Banfa da lafiya nima, yau har asibiti Babu ya kaini akamin karin ruwa . Ta ?are maganar muryarta na rawa alamar son yin kuka. Tashi zaune Ajwaad yayi sosai, cikin damuwa ya ce,  To kar kiyi kuka, nima banda lafiyan ai, jiya saida aka min ?arin ruwan .
? ?? Kukan ta sakar masa kuwa, da faWin,  Besty nidai kace Babu ya dawo dani wajenka. Ni bana son nan. Akwai muguwar mata a garin. Yanzu ma ka ganta sai hararata take... kuka sosai yaci ?arfinta
? ? ?? Sosai hankalin Ajwaad ya sake tashi daga can, sai ?o?arin lallashinta yake yi amma tana ?ara ?arfin kukan harda tutturza ?afafu. Ga Gwaggo ta zuba mata wani shegen kallo. Kukanta yasa Shahidah fitowa. Sai dai suna haWa ido da Gwaggo ta koma ciki da sauri. Dama a tunaninsu ko wani abu akama Maanal Win tunda sun san halin muguwar kakar tasu sai a hankali ce. Sosai Maanal take kuka har sai da Oum ta amsa wayar daga hannun Ajwaad da duk ya rikice da kukan nata itama tana lallashinta da tabbatar mata Bestien nata zaizo ya sameta. Da ?yar tai shiru sannan Oum ta maida ma Ajwaad waya suka cigaba da hirarsu mai cike da shirme da shiririta musamman ga Maanal dan ko yaya shi Ajwaad ya Wan tasa ya fara hankali....
? ??
? ?? Sam rayuwa a Giro batama Ammie da yaranta daWi. Maanal ce ma dai babu ruwanta, tashin hankalinta kawai ace ta yini batai waya da Ajwaad ba. Anan ne zaka ganta kamar mara lafiya. Amma da sunyi waya sai ka walwalarta ta dawo. Sai ma ta fice wasa cikin gida abinta. Maanal dai dama jaruma ce a fagen iya faWa da tsokala, anan Win ma duk da matsin da suke a ciki bata canja ba. Dan kuwa jibgar ?a?an mutane take yi, idan kafi ?arfinta kasha ?asa a cikin ido. Gwaggo kuwa idan ta harareta itama ta rama. ?akinta kuwa kai tsaye take shiga tace tana son abu kaza. Idan Gwaggon ta korota da zagi ta?i fitowa. Kota warto abinda take so Win ta fito a guje. Wannan hatsabibancin nata yasa Gwaggo tafi tsanarta fiye da kowa. Kullum cikin aibantata take da zaginta. Abin na damun Babu da Ammie sai dai babu yanda zasuyi, dan Ammie tama Maanal faWa akan shiga harkar Gwaggon amma yarinyar nan data faki idon Ammie sai tasan abinda taima Gwaggo. A haka dai sukai sati uku a Giro, duk sun fita hayyacinsu sunyi ba?i sun rame saboda rashin abinci mai inganci. Suna a kwana na ashirin da biyar Babu yazo ma Ammie da batun wai zai yi aure. Sannan suma kawunan sa sunyi magana akan Shahidah da Amaal ya kamata a musu aure dan sun isa, musamman ma Shahidah data fara zama uwar mata. Dan haka sun yanke hukuncin ita Shahidah ta auri Lado Wan wajen Badaru. Ita kuma Maanal ?asimu Wan wajen Sagiru. Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci Ammie. Ita ba auren Babu Win ne damuwarta ba, batun Shahidah da Amaal.........
'?


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
=?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________

.......Kuka sosai Ammie ta sanya ma Babu da ro?o da magiya, amma sai ya nuna mata shima bada son ransa bane. Dan bazai so yaransa suyi rayuwar garin ba, ba kuma zai so a yanke musu karatunsu ba. To amma bazai iya jayayya da ?an uwan mahaifinsa da ?an uwansa ba. Ina sam wannan batu bai shigi Ammie ba. Dan tasan wannan ba umarnin kowa bane sai Gwaggo. Hankali tashe taje ta samu Gwaggo da kuka da ro?o, sai Gwaggon ta rufeta da zagi ta kuma juya maganar. Dan kuka ta sanya da kururuwa wai Ammie ta sameta har Waki tana mata gargaWi idan bata saka Babu ya janye batun ?ara aurensa ba sai tabi dare ta kasheta. Dandanan wajen ya cika da mutanen gidan harda makwafta. Kasancewar Ammie nada tabon fitar kishiya yasa kowa ya yarda da batun Gwaggo. Nanfa akaita cancana magana da zagin Ammie har saida Baba Haruna ya shigo gidan ya tsawatar.
? ? Sam Ammie bata san miya rufema Babu ido ba, yana dawowa gidan Gwaggo ta faWa masa ?arya da gaskiya sai ya hau ya zauna. Aiko ya birkice mata yayta tujara a tsakar gida mutane naji, shi bazai yarda a raina masa mahaifiya ba. Ai ba a kanta aka fara kishiya ba. Shi ya gaji da ba?in halinta. Idan bata gode masa ba bata tsine masa ba. Shekara nawa yana zaune da ita zaman ha?uri badan ya taSa jin sonta a zuciyarsa ba ko sau Waya. Sai dan kawai kar ace yama iyayenta rashin halacci ya kasa ri?eta. Shima namiji ne, yana son ya auri wacce yake so, yana son haihuwar Wa namiji.. kai tujara dai kala-kala data sanya Shahidah da Amaal kuka sosai. Ita dai hajiya Maanal hidima bata san ma anai ba. Tana can tare da Baba Haruna daya fita da ita gaisuwa gidan wani abokinsa. Ammie tayi kuka har ta godema ALLAH, taji inama iyayenta na raye, ashe duk zaman da take da Babu ba soyayyarta a ransa har zuwa yanzu...
? ? ? Anyi haka da kwana huWu Babu baya kulata hakama ?an gidan kowa ya ?ara Wauke mata wuta ita da ?a?anta sai ga batun yima Shahidah da Amaal wai baiko. Ranar ji Ammie tai kamar tabar duniya ta huta. Karon farko ta sami Baba Haruna da ro?o. Yayi mamakin jin bada son ranta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login