Showing 153001 words to 156000 words out of 219361 words

Chapter 52 - AJIYA A DUHU

22 Mar 2025

47011

ya?i ta shiga neman afuwa da rusar kuka da ban ha?uri tana tabbatar da sharrin shaiWan ne. Hakan ma bai saurareta ba, yace saifa ta tafi. Haka kuwa dole ta tafi gida batare da kowa ya sani a dangin Aliyu ba. Amma sai dai me, a ranar iyayenta suka maidota, suka kuma du?ufa bama Aliyu ha?uri suma da tabbatar masa ?uriciyace ke damun Kamilar kawai. Amma yay mata afuwa ko Fateema kada ya bari tasan wannan al'amarin dan ALLAH. Suka kuma masa al?awarin canjawar Kamilar fiye da yanda yake bu?ata.
? ?? Badan dai Aliyu yaso ba wannan wuta ta mutu a haka. Sai dai kuma ya sharWanta ma Kamila sharuWai masu tsauri game da Fateema in har tana son cigaba da rayuwa a cikinsu. dole kuwa ta amsa da hannu bibbiyu tayi biyya. Sai dai kuma acan ?asa ta Wauke karatun uwarta da ?an uwanta tsaf. A haka Fateema ta tare gidan itama. Da gaske Kamila ta kwantar da kai fiye da zaton Aliyu. Tana bin shariWWansa sau da ?afa. Bawai shariWWansa kawai ba, da gaske Fateema mugun kwarjini take mata, dan matar nada wata irin baiwa da nagarta mai ban mamaki. Ga ?ya?y?yawar zuciyar zama da kowa da gaskiya. Sai dai bata son raini, bata son munafunci da wula?anci. Wannan abinda Kamila ta sani ne tuni, dan haka ta shirya ya?ar Fateema da su har ma da Aliyu. Sannu a hankali kuwa suka fara tasiri, dan duk wata hanya ta gwaji Aliyu yabi akan Kamila game da zamansu bai kamata da kowane laifi ba. Sai ma yanda take bin Fateeman ya fara saka masa jin nutsuwar zama da ita. A gefe kuma ga Fateema kullum damuwarta da fatanta taga Kamila da ciki.
? ? ? To tsakanin mace da namiji kwance a Waki Waya sai ALLAH, yau da gobe kuma bata bar kowa ba. Dan sannu a hankali dai Kamila taci nasara akan Aliyu cikin dabaru da kissa irin na mata ya maidata cikakkaiyar mace. UBANGIJI kuma mai hikima da yin yanda yaso a lokacin da yaso ba'a rufa wata biyu da Kasancewar tasu a ?ar?ashin inuwa Waya ba sai ga Kamila ta fara laulayin ciki. Ya rabba zokuga murna ga Fateema. Sai ma ka Wauka itace da cikin. Gaba Waya ta kwashe kulawarta kacokan ta maida kan Kamila. Hatta shi kansa Aliyun yanzu ba wani yana samun lokacinta bane, har ya fara kishi da hakan sai da ta zauna ta lallashesa. Bawai baya farin ciki da cikin da Kamila ta samu bane, a'a yana dannewa saboda baya son ko yaya zuciyar Fateemansa ta sosu. Dan haka ya barma zuciyarsa nasa farin ciki ita ya bari take nata a bayyane dama zuciya. A haka kwanci tashi ALLAH ya sauko Kamila lafiya, ta haifo Wanta namiji mai tsananin kamanni da Aliyu da Fateema tamkar sunyi kaki, dan in baka sani ba kazo saika ma Wauka Fateeman ce ta haifi yaron. Wannan shine ?alubale na biyu daya sake girgiza Kamila da ahalinta, sai dai sun shanye a cikinsu suma sunata fatan alkairi. Sai ma Waukar jinjiri da Kamila tayi domin sake samun fada ga Aliyu tun a randa ta haifesa ta dam?awa Fateema tare da al?awarin mallaka mata shi na har abada. Ta kuma sake maimaitawa a gaban Baba Sardauna da Umma da dukkan ahalin Aliyu da nata ahalin. Ranar kuka sosai Fateema tayi da sake jin ?aunar Kamila. Tana ji a ranta lallai batayi zaSen tumun dare ba. Hakama Aliyu wata sabuwar soyayyar Kamila ce yaji ta soki ?ahon zuciyarsa tayi tasiri a ciki tare da mamaye komai. Duk wanda zai so Fateeman sa to har abada zai dawwama shima kam yana sonshi da ?aunarsa ne.
? ? ? ? Haka dangin Aliyu da Fateema ma suka zo aka haWu akasha shagalin suna yaro yaci suna Fadeel (Babban yaya =??=?M?).
? ? ? Bayan shan shagalin suna aka bar masu Wansu. Gaba Waya Fadeel a ?ar?ashin kulawar Fateema yake. In dai ka ganshi a hannun Kamila to lallai za'a bashi abincinsa ne. Sai ko dare yayin yin barci. Amma dukkan wahalhalu na raino da kulawa Fateema ce. Kai hatta daren ma yana fara kai watanni shida ya koma kwana hannun Fateeman. Dan ALLAH yayisa bamai fitina ba. Tama kai ba wani ya damu da shan nn bane ba.........
'?


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________

.........Fadeel da kansa ya yaye kansa. Dan wata irin sha?uwace a tsakaninsa da Fateema da ita yakema kallon uwa ta ha?i?a ba mahaifiyarsa ba. Yayinda Fateema ke nuna masa wata irin soyayya mai girma da ko Wan data haifa a cikinta iyaka kenan. Son Fadeel take da zuciya Waya, so irin wanda koda wasa bata taSa kawoma ranta ba itace ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
mahaifiyarsa ba balle tunanin cuta masa. A haka suka kammala karatunsu. A lokacin Fadeel nada shekara uku, har lokacin kuma Kamila bata sake samun wani cikin ba. Sai kuma ta Wan shiga damuwa. Idan Aliyu yayi magana saita nuna masa tana son haihuwar domin cikama Fateema burinta. Sotake ta cikama Fateema Waki da ?a?a ta yanda zata kwaranye mata ?ishirwar su. Idan ta faWi hakan na saka Aliyu sake jin ?aunarta mai yawan gaske. Sai dai kuma a zuciyar Kamila sam wannan ba shine gaskiya ba, tana faWar ne domin sake farautar zuciyar Aliyu kawai, so take ya sota fiye da soyayyar da yake i?irarin yima Fateema, so kuma take ta haihun ta yanda zata mallake komai daga garesa, dan ta san dai komansa nata ne tunda itace mai haihuwa.
? ? ?To? ALLAH bai sake kawo haihuwar nan ba sai da Fadeel ya shiga shekara ta huWu sai ga wani cikin. Zo kafa murna da farin ciki a wajen Fateema (Oum) kamar yanda Fadeel ke kiranta yanzu. Kamila kuma (Mamy) Aliyu (Abah). Hakama dangi nata mata fatan alheri musamman ta Sangarenta. Fatansu shine ta sake haihuwar namiji, haka itama kanta wannan shine fatan nata. Ga Oum da Abah kuwa basu da wani zaSi, duk abinda ALLAH ya bada so suke yi. A haka dai ciki ya shiga watan haihuwa, ranar na zuwa ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo Wanta namiji again. Ya ALLAH burin Mamy da zuri'arta ya cika, dan sun san ta kuma gama kama gida da mai gida. Ga Abah yayi murna ya kumayi kukan tausayin Oum a Soye kamar yanda yake yi a Soye tun haihuwar Fadeel. Ga Oum kuwa ko'a jikinta, dan ko sau Waya bata taSa jin hassadar Mamy ba akan tazo ta haihu a gidan ita bazata haihu ba. Ita tun bayan kukan samuwar ?addararta bata sake zama ta damu kanta da tunanin shike nan bazata haihu ba, balle saka kanta a damuwa. Tuni ta fawwalama UBANGIJI komai, ta kuma amshi jarabawarta da hannu biyu, kullum cikin godema ALLAH take. Tayi imanin maybe haihuwar ba alkairi bace a gareta shiyyasa UBANGIJI ya jarabceta da yankewarta da wuri. Kuma ai ba sai ka haifi ?a?a da cikinka bane suke zame maka ?a?a, Wa na kowa ne, maybe ma bazaka amfani wanda ka haifa ba sai na wani, nakan kuma wani ya amfana. Wannan yasa bata taSa jin wani ?ai?ayin hassada ga haihuwar Mamy ba. Dan zuciyarta duk Waya take Wauka...
? ? ? Kwana biyu da wannan haihuwa Mamy ta fahimci kamar Abah bai murna da haihuwar ba, sai hankalinta ya fara tashi, da dare ya shigo mata sai da safe ta daure cikin damuwa take masa tambaya. Ya jima shiru kafin ya kai zaune tare da Waukar jaririn ya rungume a jikinsa. Cikin kulawa ya ce,  Kamila ba farin cikine bana yi ba. Nama fi kowa farin ciki kuma ina cikin godiyar UBANGIJI daya bani abinda arzi?ina ko ilimina baya badawa balle tarin dangi da nasabarsu. Zuciyata ce kawai, zuciyata ce ke tsananin tausayin Fateema. Kamila Fateema MATAR ?WARAI CE RABIN ADDINI, ke shaida ce akan ta da ?yawawan halayenta a Wan rayuwar da kikai da ita ta ?awance har zuwa ta zaman gidan nan. Munci buruka da yawa tsakanina da Fateema akan ?a?anmu, sai dai ashe ba haka UBANGIJI ya ?addara mana ba. ALLAH sarki Fateema baiwar ALLAH, koda wasa koda ganganci ban taSa ganin damuwa ko jin ?yashin samuwar haihuwa daga wata ba ita ba a gidan nan......
? ? ?? Takaici da zafin da zuciyar Mamy keyi akan kalamansa na yabo ga Oum ya sata saurin katsesa ta hanyar faWin,  Dan ALLAH ka daina faWin Fateema bata haihu ba, ka daina raba Wayan biyu akan yaran nan da Fateema. Tabbas ni ce nai rainon cikinsu da na?udar su kawai, amma tun kafin suzo duniya mallakin Fateema ne. Ka shaida ni Kamila kamar yanda na mallaka ma Fateema Fadeel da al?awarin bazan taSa canja hakan ba koda a kan fuskata shima wannan jinjiri Wan kwana biyu na mallakashi ga Fateema har abada. Da zarar na yayesa ta Wauka nata ne, kai in ma zata sha wani abu ne ta shayar da shi da kanta ni tama amshesa yau ikonta ne . Hawayen Waci da tiririn fitar kalamanta da iyakar bakinta suke banda zuciyarta suka shiga silalo mata....
? ? ?? Tabbas kamalanta ratsa Sargo da zuciyar Abah suka dinga yi, har bai san ya jawota jikinsa ya rungume taba, sai jera mata addu'oi yake hawaye na zuba masa shima. Sosai ?aunarta mai yawa take sake samun gurbi a dukkanin jinin jikinsa bawai a tsokar zuciyarsa kawai ba. Baiyi ?wairon baki ba ya shiga jera mata kalamai masu nauyin gaske da ta jima tana ?ishirwar jinsu da bu?atar saurare daga garesa. Shi Win dai shi Aliyu da tun a haWuwar farko ta kamu da soyayyarsa. Duk da so da ?aunar da takema ?a?anta guda biyu masu tsananin kamanni da shi ta gwammace ta sadaukar koda na wuccin gadi ne domin samunsa shi da zuciyarsa gaba Waya. Daga baya sai tayi ha?in ?watar ?a?anta a tsakaninta da Fateema. Dan tabbas wannan ?yautar duk biyu a iya fatar bakinta take bawai a zuciyarta ba. Amma ta fahimci dolen dole sai ta yita kafin ta samu zuciyar mijinta da dukkan kulawarsa fiye da wadda yakema Fateema. Dan haka zatai dauriya da juriya na wani lokaci...
? ?? Haka kuwa akayi, shima jinjiri da yaci sunan Fawzan Mamy ta tabbatar a gaban kowa ta mallakawa Oum har abada. A wannan gaSar kam Oum kukan da tai har sai da ta dinga bama kowa tausayi, dan kuka ne na farin ciki da dukkan jin ?auna dake fita tun daga zuciya. Ita kanta batama san inda zata ajiye martaba da kimar Mamy ba zuciyarta. ?an uwan Mamy kam da mahaifiyarta sun balbaleta da masifa da nuna mata kuskurenta. Amma sai tayi murmushi kawai tana mai kallonsu...
? ? ?  Ku daina min kallon wawuya sarai nasan abinda nake yi. Amma bazaku gane ba sai a nan gaba kaWan. Domin kuwa fatsa na jefa a kogi tare da ?ananun kifaye a jikin fatsar dan samun damar sha?o manyan kifaye mamiyo. Har yanzu baku san wanene Aliyu akan Fateema ba....
? ? ??  Oh ke a naki haukan kina nufin duk kinyi hakan ne dan samunsa da matarsa? .
? ?  Tabbas hakane Mama, dan ta hakan ne kawai zan mallaki Aliyu da komai nasa, ta hakanne Aliyu zai bani dukkan yarda da aminci. Ta hakanne zan saka Fateema a kwalba na rufe rufewa ta har abada. Daga ?arshe na dawo da ?a?ana hannuna cikin sau?i. Shiyyasa ma na sake tabbatar mata a gabanku a gaban Aliyu, a gaban dangisa haihuwata ma ta gaba mallakar Fateema ce. Zan bata ?a?a uku kafin wanda zasu biyo bawa su amsa sunan nawa....
? ? ??  To idan kuma haihuwar ta tsaya miki daga ukun kuma fa Yaya? .
?? Autar su ce tai tambayar. Kallonta Kamila tayi da murmushi. Sai kuma ta dafata da faWin,  Humm Gambo kenan, ina ji a jikina sai nayi haihuwa Wai-Wai har goma anan gidan, dan na sadaukar da uku kuwa ai ba komai bane, bama sadaukarwa bace ba ajiyar ce. AJIYA A DUHUn da FATEEMA bata sani ba. Dan komai daran daWewa sai ?a?ana sun dawo gareni a gabar da Fateema ke murna da jin alfaharin zata amfana. Zan bata fili ne a yanzu ta gama min wahala da su iya iyawarta, ni kuma na mora kayana a lokacin girmansu .
? ? ?? Murmushi kawai Gambo tayi dan ita kam ta gamsu da bayanin Kamila, yayinda yayarta da mahaifiyarsu kawai suka girgiza kawuna, dan suna ji a ransu lallai Kamila ta tafka babban kuskure. Kuskuren da bazata fahimci kuskure tayi ba sai anan gaba....
? ? ?? To koma dai yaya ne Mamy ta cigaba da shayar da Fawzan shima, yayinda komai nashi ke'a hannun Oum, shan nn kawai ke kawosa tamkar yanda akai da Fadeel. Shi Fawzan ba kamar Fadeel ba, ba yaye kansa yay ba, yana da shekara Waya Mamy ta sake samun ciki, wannan shine dalilin yayesa gudun samun matsala. Nan ma Abah da Oum suka cigaba da kula da ita da kaffa-kaffa, dan wannan cikin ma sai yafi bata wahala fiye da na Fadeel da Fawzan. Ga cikin da tsirfar tsiya, yana son wancan baya son wannan. Tun yana watanni biyar yay wani irin girma na tsiya kai kace tagwaye ko ?an uku ta Wauka, dan Oum da Abah har tsokanarta suke akan wannan karan kodai ?an uku ne ko twins. Murmushi kawai take yi akan batun, amma a can cikin ranta tana ma kanta fatan hakan itama. A lokacin da cikin ya shiga watanni bakwai sai wahalar ta ninku matu?a. Har takai bata iyama kanta komai sai da taimakon Oum da Aba. A haka aka shiga watan haihuwa da ?yar, har ALLAH ya kawo ranar haihuwar. Ansha gumurzu, gumurzu na ha?i?a dan kwananta biyu akan gwiwa kafin a na uku ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan karan ma dai namiji ne sargaWeWe mai kamanni da ?an uwansa, sai dai shi ya Wan Wakko duhun fatar Mamy saSanin Fadeel da Fawzan dake farare tarr dasu tamkar mahaifinsu da Oum. Jaririn nan ?ato ne na gaske, dan bayan fiddosa hatta ma'aikatan asibitin zuwa kallonsa suke da mamaki. Haka dai aka sallamesu suka koma gida, a wannan karon ma dangi tako ina sun cika gida anata huWar arzi?i.
? ?? ?alubale na farko akan wannan haihuwar shine tunda Mamy ta Waura idonta akan jinjiri wata kalar ?aunarsa mai zafi data bambanta data ?an uwansa ta shigeta. ?alubale na biyu tun a asibiti ya?i kama nn. ?alubale na uku Abah da kansa suna dawowa gida gaban ?an uwanta da nasa ya sake tisama kowa al?awarin Mamy na ranar haihuwar Fawzan akan mallakama Oum wannan Wan ma a karo na uku, dan haka ya sake tabbatar musu wannan al?awari na nan daram bai canja ba. Sai dai suyima Mamy addu'a kuma da fatan alkairin ALLAH ya kawo ?a?a na gaba da suma zasu kasance matsayin nata mallakin. ?alubale na huWu shawarar da Umma ta bada akan tunda jinjiri ya?i kama maman Kamila bazai yiwu a barshi a haka ba fa sai a koma asibiti, koda aka koma asibitin sai likitoci suka fahimci fa akwai matsala ne, matsalar canjawar kalar nn Mamy daga fari zuwa yellow, dole suka shiga binciken ainahin matsalar, suka kuma bada shawarar sai dai a shayar da yaron madara gudun kada a shiga hakkinsa, dama gashi yanata kukan yunwa. Ita kuma aka Worata akan magani da tabbatar musu in sha ALLAHU komai zai wuce ta samu lafiya kamar ba'ai ba. Jin haka sai Umma tace baza'a bashi wata madara ba Oum ce zata sha magani ta shayar da shi. Baba Sardauna ya yarda da wannan shawara ta matarsa, hakama Abah da sauran dangi. Dan haka mahaifin Oum wato Dr Kasheem Kura da kansa ya aikoma Mamy ingatattun magunguna tun daga Paris da zai bata ruwan nn. Dan su basu zo ba a lokacin babu jimawa da sake haihuwar matarsa (Maryam kenan mahaifiyar Oum ina fatan kuna fahimta). Itama ta samu Wa namiji cikin na huWu da yaci sunan Rafeeq. Oum bataje ba saboda yanayin da Mamy ke ciki a lokacin.
? ? ? Cikin amincin UBANGIJI Oum nashan magani kuwa sai ga ruwan nn mai ?yau. Aiko ta hau shayar da jinjirinta da yaci suna Ajwaad. Yayinda aka bar Mamy da jiyyar zuciya da kukan Soye. Gashi kuma babu yanda ta iya, dan ita dai tai al?awarin nan babu wanda ya tirsasata, a zahiri kuma ta?i nuna ma kowa damuwarta saboda neman soyayyar Abah da take ganin saita wannan hanyar kawai zata iya samunta. Ita dai Oum ranta fes, ?a?anta uku cif sun kammala, tsakaninta da UBANGIJI sai godiya. Sai kuma aminiyarta Kamila da har abada take jin a ranta bata da kamarta a wannan duniyar idan ka cire iyayenta da iyayen ri?onta da mijinta. ?aunar yaran nan uku take da zuciya Waya, da iya gaskiyarta. Bata taSa jin ?ai?ayin cewar ba itace ta haifesu ba. Kai ita mantawama take da ba itan ce ta haifesun ba. Dan a zahirance dai Mamy kawaici take yi. Bata taSa jingina kanta da yaran koda wasa. Sai ta faki ido ta dinga aibanta Oum a zuciya, gefe ga tsananin kishinta da take ji da hassadar finta komai na rayuwa da tayi. Wanda ada can iyakar kishin soyayyar mijinta Aliyu kawai take ji. Amma bayan auren data sake fahimtar wacece Oum a wajen Aliyu da nasarorin rayuwa dana iyayenta ke da shi sai hassadar hakan ta shigeta.
? ? ? ? (Wannan hassadar al'adace kamar a zukatan matanmu akan kishiya. Ya rabba ALLAH ka yaye mana hassada dan mugun dafi ce mai kassara rayuwa da cigaban cikinta)........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:-

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login