Showing 261001 words to 261814 words out of 261814 words
yanajin Wani irin nauyi a zuciyarsa gameda Yan uwansa da suka barsa daya bayan daya.
Jamaal Mam din ya kalla kafin ya Kalli Omar ya sake Maida kallansa kan Jamaal ya Bude Baki a wahalance da sauti mara fita yace
"Jamaal na yafe Maka komai kada Allah ya kamaka da komai akaina na yafe Maka Allah ya shirya Maka zuri'arka ya musu albarka"
Dago jajayen Idanuwansa Jamaal yayi ya Kalli Dad din nasa Yana kasa cewa komai bayan adduar dayake masa Shima na allahyya yafe masa.
Omar ma da Mam din ya kasa kallansa ya Nemi gafararsa sbd yasan cun cutatar dashi mafi cutarwa ajiyan zuciya me zafi da qunci ya sauke ya Kalli Mam din ya Bude Baki yace
"Na yafe Maka Mam duka ku dukan Allah ya yafe Muku ya karbi tubanku Kuma"
Hawaye masu Ciwo ya sake gangaro masa Yana kasa kallan Omar din.
Dr Aleena ce ta shigo dakin sai Ameenatou me tsahon Ciki Dake bayanta sai babbah da dadah tareda Arfat sai Kuma hafiz wanda shine ya kawosu,
Bayan shigowansu maman fadeela ce da Ayesha da siyam Wanda itama ta warware fes ya dawo tana hannun Dad Omar din kaman yarsa.
Kallansu yayi bayan dayan ciwonsa na tsananta sbd zuciyarsa data kasa daukan kallansu sbd a Cikinsu kaf Babu wanda Bai Raba da masoyansa ba Dan haka Bai iya cewa komai bayan ciwonsa dayake Neman rikicewa.
Arfat ya qurawa Idanuwansa Wanda Jamaal ya kamo hannunsa ya kawo masa gabansa tareda kamo hannunsa ya Dora masa Akansa Cikin sanyi murya a shaqe yace
"ARFAT SEELAH"
Wani irin Kuka mara sauti Mam ya sake Yana riqe Arfat din wadda yake kallansa kafin ahankali ya Bude Baki yace "grandpa" kaman yanda Mommah dinsa ta sanar masa gurin grandpa dinsa zasu.
Wannan kalman ta Saka zuciyar Mam kasa dauka take ya rikice gabaki daya Yana kallansu daya bayan daya kafin ya tsayar da Idanuwansa akan Jamaal Wanda ya rungumosa jikinsa Dad Omar Yana karanta masa kalman shahada Yana karba kafin rai yayi halinsa agaban kowa take dakin yayi tsit jikin kowa a mace cikeda tsananin tausayin Jamaal Wanda ya rungume Dad din nasa da kyau Yana rintse Idanuwansa dake radadi sbd rashin kukan daya kasa fitowa daga cikinsu.
Babu wanda a dakin Cikin mata hawaye Bai zubo masa ba a mazan ma Dad Omar Kuka yakeyi sosai sbd ya koma shi kadai ya rage a Yan uwansa duk sun tafi sun barsa Shima Yana fatar idan lokacinsa yayi akaisa kusa da Yan uwansa a rufesa.
****Rasuwar Mam seelah Babu Bata lokaci ta yadu Dan haka Babu Bata lokaci Aka tafi da gawarsa Ashlawa kaman yanda yaso acan Akai janazah dinsa aka rufesa Omar ya zauna gaban kabarin su hudu a jere yayi kukan da kusan ya sakar masa ciwon kirji,
Jamaal ma yayi kukan daya bawa Ameenatou da mum dinsa tsoro sosai Dan haka Suma sunyi Kukan Wanda yake na tausayinsa Dana tausayin Mam din tareda masa fatar rahamar ubangiji.
Bayan rasuwarsa da sati uku Ameeenatou ta haihu a hannun Mum Aleena a asibitinsu ta haifowa Jamaal baby girl kyakkyawa wadda tafi Arfat kama da Mum dinsa kaman an tsaga Kara.
Haihuwan ce ta dawo da farin cikinsa daya rasa na lokacin Dan haka sai alokacin kowa ma ya samu farin Cikin familyn ya dawo sukaita murna cikeda tsananin kaunar Baby Aleena little da aka samu.
Tinda Mam ya rasu lafiya tafara gagarar Dad Omar sbd Saka abin aransa da yayi Dan haka Dr Aleena ta daukesa suka bar qasar sbd treating dinsa da Kuma kwantar masa da hankali.
Tafiyarsa da Dr Aleena ya Saka kusan duka sauran families dinma biyu suka kwashe gabaki daya suka bisu acan Ashley ta haifi baby boy Wanda aka sakawa Mam seelah little.
Fatmah ma namijin ta Haifa aka Saka masa Omar Shikuma.
Saida sukai kusan wata hudu acan tukuna suka tattaro suka dawo Cikin kwanciyar hankali da aminci suka Dora sabuwar rayuwa me cikeda kaunar juna da Jin Dadi tareda tarbiyantar da yaransu a Nigeria.
Dad Omar da uncle Ahmed manyanci yazo sosai Dan haka tini suka ajiye komai zaman Hutu kawai sukeyi sun barwa Yara ragamar komai musamman Hafiz da shine yanzu kusan shugaba a komai na jdens shida Ameenatou da Fatmah wadda ta Jame dasu Ameenatou da Ashley wadda take karatun likita yanzu itama hankali kwance Hutu da nera ta zauna mata.
Jamaal kuwa duk wata martaba da mutuncin sunan SEELAHs ya dawo dashi ya sake daukaka darajarsu xuwa matsayin dayafi na bayan ma Dan haka rayuwa tayi daidai sai hamdala da godiyan Allah yanzu.
#MAMUH
ALHMDLLH
ANAN NA KAWO KARHEN LABARIN AMEEENATOU WANDA INA ROKON ALLAH YA YAFE MANA KURAKURAI DA LAIFIN DA MUKAI BA DAIDAIBA.
SAI MUN HADU A SABON LITTAFI NA GABA INSHALLAH
INA MIQA GODIYA MAI TSANANI GASKE GA MASOYAN DA SUKAI KOKARIN BINA TIN FARKO HAR QARSHENSA.
ALLAH YA SAKAWA KOWA DA KHAIRAN
IDAN AKWAI INDA NAYI MANTUWA BAN TABO BA KO TABOWA BA DAIDAIBA KO YANDA YA KAMATA TO AMIN UZURI AJIZANCI JE JA YAR ADAM
ALLAH YA BAR TARE YA QARO MANA HAKURI DA KAUNAR JUNA.
AMEEN YA ALLAH.