Showing 15001 words to 18000 words out of 261814 words

Chapter 6 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9956

tinanin wannan burin ko shi Omar din zai iya hanasa cika?
Idan ban mallaki dukiyar Omar ba har abada bana kallona Mai arziki Duk kuwa abinda zan Tara din....

Katsesa Alh lameenu yayi da cewa

"Hankalinmu na kwance ne duk shekarun Nan sbd Omar Bai taba samun haihuwa ba,hakama acan Baya mun Jira ne mr and Mrs Jaden su mutu dukiyarsu ta taru ta zama ta Omar din kafin mu dauko mataki
Yanzu dukiyar ta zama tasa Kuma gashi a kusa damu yanda muke so Amma Kuma yanzu yaqara aure
Baka Tinanin zai iya samun haihuwa idan har yaci gaba da auren Nan??

Shiru Alh mam yayi zuciyarta na daukan nauyi ahankali Dan kuwa basajin zasu iya tsayawa jiran Omar samu haihuwa,idan ma ya fara samun haihuwar to idan yayan dari zai Haifa sai sun kawar dasu gefe sbd Babu wani Rai da bazasu iya janyewaba akan buri da kudirinsu dayafi shekara da shekaru tin suna matasansu.

Tinani suka shiga dukansu musamman lameenu da hankalinsa gaba Daya shi ya tashi akan auren shi tin kafin wani abu ya shigo gabansu yaji Yana buqatan a cire matar da Omar din ya auro daga lissafi.


Rayuwar Amina a gidan mijin data kasa sabawa da shi sbd rayuwarsu akwai banbanci tazarar sama da kasa Amma Kuma sbd masu aikin da aka zuba mata da Mai kulawa da ita da koya mata abubuwa da yawa sai tafara Dan sakewa tana koyan abubuwan da dama Wanda Bata dauki lokaci ba mijinta kuwa ya amsheta amatsayin matarsa.

Zamansu Daya ya Saka soyayyarta da tausayinta masu karfi shigar Omar
Ita kuwa Daman tini ta kamu da sonsa kawai tana kama kanta ne sbd ganin kaman yafi karfinta.

Sabuwar rayuwa sosai suka Bude ta sabbin ma'auratan da suke cikin sabuwar soyayyar juna,
Gogewa tafara yi ta zama matar gidan mijinta Dan kuwa sosai take kokarin kulawa da mijinta kaman wadda tayi boko ta waye sosai.

Shi kuwa sanyinta da nutsuwarta tareda tsananin nutsuwan dayake samu da ita ya saka zuciyarsa kamuwa da Sonta fiyeda yanda yayi tinani gashi ita din yarinya ce sosai take narke masa tana sakashi Jin kansa tamkar sabon saurayi duk ta gama kame gangar jiki da zuciyarsa.

Jamaal ma yaji dadin zama da ita sosai fiyeda yanda yayi tinani duk da batajin turanci shikuma ba sosai yakejin hausar ba Baya ma iya doguwar Hausa duk kame Kame ne,

Jamaal ya koma gidan Dad dinsa sedai Bai wani jima ba ya koma sbd hutunta Daya qare na makaranta.


*********Kaman yanda ake cewa kaddara ta rigayi fata kwatsam sai ga ciki a jikin Amina Wanda ya girgiza duniyar Alh Omar Jaden seelah,
Ya girgiza sosai sbd Bai taba Saka ran zai haihu din ba,
Yanada ciwo a zuciyarsa na shekaru akan rashin haihuwa Kuma ya Riga ya cirewa haihuwar Rai shiyasa bayyanar cikin ya girgizasa matikar gaske.

Ita kanta Amina Bata Saka ran samun haihuwa ba sbd ta Riga ta yaddarwa kanta zata zauna dashi ahakan ba haihuwa so itama samun cikin ya Sakata mamaki me tsananin gaske da farin cikin gaske duk a lokaci Daya.

Tinda ta samu cikin ya daukesa suka bar kasar kusan watanninsu uku kafin suka dawo lokacin cikin yakai wata shida Babu Wanda yasan dashi bayan shi da ita sai masu aikinta da suka Saba da ita sosai suke mata biyayya.
#MAMUH#
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#HAROON SEELAH
#LOVE
#CRAZINESS
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU

ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class 
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
#ZafafaBiyar


11
ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class 
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku



**********
Ko Nur datake matar Dad Omar din kaman an rufe masa Baki Bai fada mata cikin Amina ba sbd tausayinta Dayaji ya rufesa akan Hakan Dan haka yakejin bayason daga mata hankali ko Sakata damuwa ta hanyar fada mata sai kawai ya share,

Aminansa Yan uwansa su Alh mam na Bai fada musu ba sbd sun Riga sun fara manyanta wane maganar ciki zaije Yana fada musu kawai fatan haihuwan aminan lafiya yakeyi idan Kuma yaga abin zaiyi yawa zai dauketa ne yakaita Poland ta haihu acan sbd bayason ko irinsu bikin sunan Nan yafi son komai nasa quite ba hayaniya hankali kwance yayi naming babynsa batareda wani biki biki sai iya su family da friends kadan suci suci su Sha suyiwa Allah Godia Dan haka yake tsananin kulawa da tattalin aminarsa Dan ta samu babban matsayi a zuciya da rayuwarsa na musamman gashi Kuma zata zama uwar yayansa,macen da zata fara haifar masa jinin kansa.

Su Babbah ma basusan da cikin ba sbd kunya bazata iya barin Amina fadawa dadah tanada ciki ba bare Babba Dan haka tayi shiru batareda ta iya fada din ba har ciki yanata Kara kusantar cike watannin haihuwarsa.


*******Mummunan tashin hankalin farko Daya fara ziyartar rayuwar Alh Omar jeden seelah itace wayuwar gari da Akai da mutuwar secretary dinsa Daya kwana Yana aiki a office,

Kisa ce ta tsafta wadda seda Akai aka Gano ba Alh Omar din bane Dan kuwa a office dinsa yake Yana aikin dasuke buqatan miqawa da gaggawa a washe gari.

Da farko baa dauka kisa bace sai da aka bincika abinda ya kashesa aka Gano allura Akai masa wadda ta tsayar da bugun zuciyarsa take tareda tsiyayo jini ta hancinsa da kinnensa Amma sun goge sedai anga sauran jinin.

Duk iya bincike baa iya Gano komai gameda Wanda suka kashesa ba Kuma duk tsananin securities Dake office din suna Nan Amma sun Bada tabbacin Babu wani baqo ko wani Daya shigo a Daren.

Hakanan case din Alh mam seelah ya kashesa tareda sallamar duka securities din ma'aikata ya zuba wasu sabbi sbd bawa Dan uwansu tsaro.

Hankalin Omar Bai tashi ba sbd Bai dauka shi aka kawowa harin ba Amma dai baiji dadiba sosai shiyasa ma ya Saka familyn secretary din nasa cikin wainda nauyinsu yake kansa Dan tallafa musu.

Alh Mam da lameenu ransu yafara tsananta Baci tareda tashi tsaye ga lamarin Dan kuwa basa son wankin hula yakaisu dare har a samu matsala a abinda sukeso Dan haka suka sauya taku tareda Yanke shawarar Kai tsaye gama komai ba Jira.

A hanyar omar jeden ta zuwa airport da daddare zaiyi tafiya suka samu accident na Kai tsaye da yayi sanadin rayuwar drivernsa da raunin Aron sosai shi kansa ya Dan samu rauni kadan Amma dai Allah ya Hana komai samunsa.

Asibiti Akai dasu aka dubasa gawar drivern Kuma aka miqawa Yan uwansa bayan an gama komai hakama Aron an dubasa sosai tareda Omar din suka dawo gida.

Hankalin Omar da Aron da Ahmed tashi yafara yi sbd wannan shine karon farko da suka samu accident a Yan kwanakin ba Wanda Babu ranar da basa duba lafiyar duk motan da Omar zai hau ba.

Basu sake shiga tashin hankali ba Saida aka kawowa motocin Omar din hari ba da Rana tsaka a hanyar zuwa office hadda Harbin da baa samesa ba aka samu Aron a kafada Wanda ya Sakasa zubar da jini sosai take Yan Sanda da jamian tsaro suka kawo daukin gaggawa Wanda duk kariyarda aka bawa Omar Saida aka samu harbinsa a gefen hannunsa Shima.

Attackers din kafin ayi yunkurin kama su Daya daga cikinsu ya harbe sauran Daya bayan Daya Kuma ya gudu baa kamasa ba.

Yan jaridu da media tini suka cika wajen ana daukan rahotanni,
Hakama tini gaba Daya familyn seelahs suka shiga tashin hankali da firgici musamman Alh lameenu da Mam Dan harsun qarasa asibitin da aka nufa da Omar din.

Amina ba qaramin tashi hankalinta yayi ba Dan haka tini tafara kuka ta kira Babba ta sanar musu,
Su kansu babban hankalinsu tini yayi mummunan tashi dajin kukan Amina Dan haka ya ringa rarrashinta da Bata tabbacin suna Nan tafe Inshallah.

Washe gari asubar fari babba ya kamo hanyar Lagos a babbar motar Lagos Yana fatan Allah ya tsare Omar ya basa kariya sbd rayuwar Aminarsa taci gaba da zama cikin Jin dadi da gata da Kwanciyar hankali.

Saida ya kwana ya wuni a hanya kafin suka iso Kuma Yana isowa Kai tsaye asibiti yafara Isa daqyar aka barsa ya shiga da taimakon Ahmed ya dubo Omar din Wanda ake kokarin dawowa dashi gida.

Alh Mam seelah da Alh Lameenu seelah duk suna tareda Omar din a lokacinda ya shigo dubasa sedai kallo Daya dukkaninsu sukai masa suka dauke Kai Dan Babu Wanda yasan waye she bare inda ya fito hakama Shima Omar din Bai sanar dasu waye babba din ba.

Gida suka dungumo suka dawo harda babban Wanda Yana saukar da idanuwansa kan cikin dayake gaban Amina Jin yayi idanuwansa suna cikowa da hawayen farin cikin dabaisan zai taba ji ba idan yaga zuriari Aminarsa,
Yau Aminarsa ce daukeda juna biyu zata haifar masa wasu yayan bayan nasa.

Ita kanta Aminar ganinsa ya Saka Hawaye cikowa daga idanuwanta suna gangarowa masu dumi hakanan taji jikinta yayi sanyi da tsananin farin ciki da kewan Dan uwanta Kuma ubanta,
Inama zai zauna da ita harta haihu Kokuma a mayarda ita gida ta haihu a gaban dadanta da Babba Dan tasan Suma zasu so Hakan.

Farin cikinsa karuwa yayi ya qaraso lafiyayyar palon baqin da akai masa iso sanyin ac da qamshin arziki Tako ina Yana tashi ga wani sanyi da laushin carpet din tsakiyar palon dayake takawa suna ratsa jikinsa suna rage masa gajiya.

Qarasawa tayi itama ta zauna gefensa tana masa sannu da zuwa tareda tambayar meyasa Bai fada mata ya taso ba bare isowarsa ba.

Murmushin Jin dadi kawai ya sake Yana Jin kaman ta haihu kafin ya koma yayiwa abinda zata Haifa huduba da kansa kafin ubansa ya masa Dan ganin yakeyi ko uban cikin bazai Kaisa son abinda zaa Haifa din ba tinda 'ya ko 'dan Aminatunsa ne dole suga soyayya da gata uwa Uba idan yayi kudi karbe abinda zaa Haifa zaiyi inshallah.

Abinci aka kawo masa kala kala da abin Sha duk da Yana Jin gajiya Saida yaci ya koshi kafin aka Kaisa har boys quarter yayi wanka yayi sallah ya kishingida dan hutawa da rage gajiya.

Washe gari ma ya samu lokacin Omar sosai sun zanta hakama Amina da daddare kusan raba Daren sukai suna magana tinda asuba ya juya ya koma sbd ya matsu yaje yafara shirin haihuwar aminan yakuma fadawa Dadah Dan ya kasa fada mata a waya.

*****Abubuwa sunyita faruwa Daya bayan Daya na son daukan ran Omar Amma Allah na basa kariya sedai abubuwan sun fara tsananin gaske Dan kuwa ayanzu duk makusancin Omar yasan rayuwar Omar din na cikin hadarin da baa San daga Ina ne masifar ke fitowa ba hakama baa San su waye masu Neman rayuwar tasa ba a HANYOYI mafi Muni Dan aduk lokacinda Akai niyar illatasa sai anyi sanadin rayuwar wani har abin yakai yafara girgiza nutsuwa da rayuwar Omar.

Suk kansa su Alh Lameenu hankalinsu ma qaramin bayyanarda tashinsa sukayi ba shiyasa suka dauki mataki sosai aka sallami kaf securities na gidajensu da gurin ayyukansu suka zuba sababbi harma da jamian tsaro.

Wannan ne ya Dan kwantar da hankalinsu Ahmed da Omar din Amma kwata kwata nutsuwar Omar da tinaninsu sun shiga wani yanayin daban na tinanin dole akwai mummunan al'amarin Dake bibiyar rayuwarsa ba tin yanzu ba Dan kuwa mace macen da akeyi a rayuwarsa ya fara yawa daga wannan ya mutu sai wannan Dan haka yaji hankalinsa ya fita kwata kwata daga zaman Nigeria Kodan bawa iyalinsa kariya musamman Amina da abinda yake cikinta,
Ya tabbatarda duk me son rayuwarsa sbd dukiya ne to Dan haka bazaa taba son ya samu magajin dukiyarba idan har ita akeso.

To tin farko ma wayene me son dukiyar tasa?
Bayada abokan gaba,hakama shi mutum ne Mai Sirri da son rayuwar kaffa kaffa Bai bayyanarwa da duniya irin Fadi da yawan dukiyarsa ba Dan a idon duniya anfi sanin dukiyar su mam akan tasa Dan shi kusan duk Rabin dukiyar na Poland,bayan Yan uwansa Babu Wanda yasan adadin dukiyar da yake da ita.

To meyake faruwa a rayuwarsa ne?
Da gaske Ahmed yake na kusa dashi ne masu Neman rayuwarsa kokuwa dai bashi Omar jeden din ake Neman rayuwarsa ba?.
#MAMUH#
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#HAROON SEELAH
#LOVE
#CRAZINESS
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU

ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class 
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
#ZafafaBiyar



12
A bangaren su Alh Lameenu abubuwan sun jagule musu gabaki Daya sbd wankin hula na Neman kaisu dare,Daren ma mara kyau sbd rayuwar Omar jeden Daya rak tana Neman gagararsu dauka bayan tsare tsaren da suka ringa yi ana kaiwa rayuwar hari,

Kan Mam ya dauki zafi matiqar gaske Dan gaba Daya kaman anyi masa asiri Jin yakeyi idan ba cike burinsu sukai ba kwata kwata bazasu taba samun Kwanciyar hankali da nutsuwa ba musamman yanzu da kullum Omar seelah ne yanzu a jaridu da labarai,

Shi Lameenu matar Omar ce ta tsaya masa a Rai da maqoshi Dan kuwa jikinsa na Basu zata iya Bata musu aiki kwata kwata daga ranar data samu ciki ko makamancin Hakan Dan haka shi idanuwansa akanta suke tafara barin duniyar gaba Daya yakeso kafin su sake dawowa kan Omar din Dan haka Kai tsaye ya Yanke shawarar ayi me yiyuwa a huta kafin su zauce akan dukiyar da bata shigo hannunsu ba har yanzu kaman abin Baki sai wahala sukeyi shekaru da ciwon Rai da baqin cikin da kullum zuciyoyinsu ba lafiya.

Shi Mam ba iya matar Omar yakeson a gama Dan matsalarta yanzu ba harta Omar din Dan ya gaji da ganinsa a gabansa Kuma samansu,
Ya gaji da Jin sunan Omar jeden na shiga kunnuwansa,
Ya gaji da Jin sunan Omar jeden a kafofin yada labarai,
Shi kansa Omar jeden seelah din ya gaji da ganinsa Yana yawo Yana numfashi Yana samun mutuntawa da respect da cika idanuwan mutane,
Ya gaji da duk wani abu Daya shafi Omar ga uwa Uba 'dansa dayake tsananin son ya kasance a karkashinsa Yana tareda Omar din Yana sonsa kusan fiyeda yanda yake sonsa shida yake ubansa Daya haifesa Dan haka ya gaji a rufe chapter din Omar din kawai a huta.

Wani numfashin Jin nauyin zuciyarsa na rayuwa Lameenu ya sake Jin abubuwan da Mam din ya fada Dan Shima Kam yakai maqura,
Wani mugun nauyi ne danne da zuciyarsu duk tsawon shekarun Nan tin daga ranar da arzikinsu kasim ya bayyana a ashalawa.


*******
Koda cikin Amina ya shiga wata Tara ya Isa haihuwa har lokacin Babu Wanda yasan dashi bayan uban cikin da Aminansa Ahmed da Aron sai su Babbah,
Duk huldarta da muamalarta dasu mum Atey Basu taba lura da ciki a jikinta ba sbd boyewa takeyi cikin hijab hakama ko gidan lameenu Basu San da cikinba sbd Aminar nada zurfin ciki sosai hakama faruwar tashi tashen hankalin Daya ringa samun mijinta ya sanar da ita kada kowa yasan da cikin shiyasa ta sake Adana kanta ma da cikin ya tsufa kwata kwata ta Dena fita koina ko gurin mum Atey din ta Dena zuwa kwata kwata sedai Haroon ne ke shigowa sosai Kuma Shima Bata taba barin yaga cikin ba.

Shirye shiryen fita da ita ta haihu a Poland Omar keyi hakama su Babbah sunacan sunata zumudi da Shirin haihuwarta Dan sunso abarta ta dawo haihuwa Amma Sam Omar yaqi yarda da Hakan dole suka hakura suka bar zancen Amma dai zasu taho idan ta haihu.

Dayake tamkar yar cikinta dadah Kejin Amina tini ta hada mata kayan fitar zaqin haihuwa da wasu maganin gargajiyar da zai Sakata samun saukin nakuda babba zai kawo mata ya dawo kafin ta haihu su taho tare.

Shi kansa babban cikin zumudin zuwan yake Dan duk yaga Omar wata sabuwar jakar arziki yake samu daga garesa Dan haka Baya ganin wahalar Nisan tafiyar kudin yake kalla da Kuma Amina dazai Gano.

Ranar asabar da asuba Babba yabar gombe yahau motar Lagos zuciyarsa cikesa zumudin haduwa da 'yar uwarsa wadda hakanan yake Jin sabuwar soyayyarsu ta jini tana qaruwa a ransa har kirjinsa na nauyi
fatansa dai ya Isa lafiya.


Acan Lagos kuwa tin safe da Amina ta tashi takejin yanayinta Babu dadi kwata kwata,ciwon mara da nauyin marar takeji sosai gashi Omar Yana gida kwata kwata ya Dena fita a kwanakin sbd hatsarin da rayuwarsa take ciki yayi yawa Dan haka aka dakatar dashi daga fita sai an gama bincike.

Rashin fitarsa ya Saka masu jiran fitowan tasa basuda zabin Daya wuce kawo aikinsu har cikin gidansa sbd tarkonda aka hada masa a waje Yana jiransa bazai taba tsallakesaba Daya fita da tabbas sai yabar duniya a ranar Daya fitan shiyasa ma daga Aron har Ahmed sun Kai matiqar wuyan lameenu da mam sbd sun zama kamar wasu makaman kariya ga Omar din.

Batareda ta nuna halinda take ciki ba sbd kada ta damar da Omar din Amina ta ringa kulawa dashi sbd Shima Yana fama da ciwon Kai gashi masu debe masa kewa da firarrakinsu idan har suna gida to suna babban garden na Bayan gidajensu dashine ya hade gidajen nasu uku ta kofofin Baya acan suke zama suna hutawa tareda wayoyinsu hatta abincin Daren yawanci acan sukeci tare wani lokacin gaba dayansu harda iyalinsu tare suke ci cikin kulawa da shakuwa.

Mam Baya kasar Yana Poland yaje dubo Jamaal haka kawai,
Lameenu ma a ranar yayi tafiya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login