Showing 3001 words to 6000 words out of 261814 words

Chapter 2 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9854

yafito na biyu Sedai shi Kam Bai samo wani abin arziki,
Jamilu da Omar da kasim ne suka fito karshe Wanda abinda suka samo Saida ya girgiza kusan mutane da yawa Dan kuwa sun samo abinda aka Dade babu Wanda ya samo irinsu.

Hayaniya Ashalawa ta dauka sosai Wanda tini aka fara kokarin nuna musu fin karfi sedai mamman Kara rayuwarsa yayi akan Babu Wanda ya Isa duk da akwai wainda suka fisa karfi da girma Amma zuciyarsa kusan zata iya fin tasu qarfi da soyewa idan har rashin imanin sukeji.

Turawa Dake Ashalawa da larabawa masu siyan danyar zinari tini suka firfito suka kama zasu siye da tsabar kudin dollar ko naira duk Wanda akeso Kokuma ta banki.

Wanke qasar da tacewa aka hau yi Dan fidda zinari daga cikinta aikuwa nan ashalawa ta sake rikicewa da tsananin mamaki Dan kuwa zuciyoyi da dama sun shiga tinani kala kala akansu Omar da kasim da jamilu.

Su kansu manyan Ashalawa a tsaye suke ana aikin wankin zinariyar Dan kuwa kowa ya kasa tafiya Dan yawanta ya tabbatar musu da sai an rasa rayuka akanta Dan Hakan suka tsaya.

Kasimu Dake murna da nasa da Allah ya azurtasa dashi Wanda zai ishesa Gina rayuwarsa cikin rufin asiri da wadata tareda rayuwa me kyau Jin yayi gaba Daya jikinsa ya mutu murnarsa ta koma ciki sbd abinda yake kalla a abinda su Omar suka samu shine har yayansu da jikokinsu Inshallah bazasuyi talauci ba,
Wani zufa da sanyin jiki yaji ya rufewa a lokaci Daya ya juyo a hankali ya Kalli mamman wanda yayi Nisa Shima a nasa tinanin.

Dan goge zufansa yayi da hannuwansa Dake cikeda qasa da ruwan qasar sbd daga qasansu har samansu koyaushe a cikin qasa suke sbd yanayin rayuwar da akeyi a Ashalawa din.

Matsowa yayi gefen mamman ya tsaya Yana Dan sake kallan mamman Wanda har lokacin mamman Bai juyo ya Kalli lameenu dinba idanuwansa da suka Dan sauya suna kansu Omar da kasim da jamilu Daketa farin ciki suna rungume juna Dan kuwa taskar arzikinsu dasukaita yawo tsawon shekaru suna nema Allah ya hadasu da ita.

Numfashi mata sauti mamman ya sauke ahankali Yana dauke idanuwansa akansu ya Maida kan zinariyar da aketa wankewa cikin ruwanta da ake wanketa dasu.

Wani numfashin ya Kuma saukewa Yana kallan tarin daruruwan Jamaar Dake gurin anata ihun zinarin,
A kaf ashalawa duk wani Mai Rai a cikinta idan ya samu dama yanada niya ko kudirin danne su Omar ya karbe zinariyarsu ko a ta sauki ko ata daukan Rai.

Daga yanxu dasu Omar suka samu wannan taskar arzikin rayuwarsu tana Bakin bodar mutuwa da rayuwa Dan kuwa Allah ne kadai ya Isa ya fiddasu ashalawa a raye matiqar ba sune zasu zama masu kashewar ba Dan tsira da arzikinsu Daman cikin Dayan biyun ne ko ka kashe din ko a kasheka.

Tinaninsa tsayawa yayi cak Dan kuwa duk yanda yake tsananin son seelahs dinsa baisan tayaya zai Basu kariyarda sukai alkawarin bawa juna ba har mutuwa.

Shima juyowa yayi ahankali ya Kalli lameenu Wanda daidai lokacin Shima juyowa yayi ya kallesa kowannensu da abinda yake ransa daban,
Kallan juna sukai tsawon mintina Babu Wanda ya furta komai bayan zuciyoyinsu da kowace da abinda take tattauna.

Mamman ne ya fara dauke Kai Yana sake Maida kallansa kansu Omar yayi musu kallan daqiqu kafin ya daga kafafunsu Yana washe bakinsa ya nufesu Yana bayyanarda farin ciki da murnarsa sosai,
Shima lameenu takowa yayi ya taho Yana bayyanarda tasa murnar suka rungume juna suna wani irin ihu da farin ciki Mai tsananin gaske.

Suna gama murna kan harkar tace zinarin suka koma sai alokacin su mamman ke sake tantance tsananin yawan arzikin dasu kasim din suka samu.

Ahankali yaji wani abu me nauyi na tasowa daga cikinsa zuwa kirjinsa Yana dannewa.
Dago idanuwansa yayi ya Kalli kasim dake sake shiga farin ciki Yana rungume Omar hadda sumbatarsa a gefen fuskarta yana cewa

"Ahhh Omar ahhhhh Omar burinmu na ratsa ilimi me kyau zai tabbata,
Zamuyi Tarayya da ilimi a cikin wadatar Ubangiji da rufin asirinsa."

Wani farin ciki me sanyi dayake fitowa daga qasan Rai yake bayyana a kan fuskar Omar din Yana sake rungume kasim da mamman Wanda yake washe Bakin dole Shima.

Jamilu kuwa gaba Daya hankalinsa baa kwance yake ba idan ba ganin yayi dukiyar zinariyar ya shiga hannuwansu ba sunbar Ashalawa zuwa rayuwar arzikin Dake jiransu a duniyar wajen Ashalawa Dan kuwa Ashalawa kamar duniyar kafiran da ko sunan Imani ba Basu sani bane,
Ashalawa kamar wata qabilace me zaman kanta da Babu kalar zunubin da baa aikatawa a bayyane cikin izgilanci Dan haka shi a matse yake da barinta a yanzu Daya samu Arzikin da zai wadatar da duk zuriar da zai Tara har tsawon lokacinda Bai saniba.

Lameenu duk yanda yakejin murnar nasa samun a farko gabaki Daya ya dakushe Baya murna ko yar kankanuwa,
Daci da nauyi yakeji a zuciyarsa fiyeda yanda yayi tsammani Dan Bai taba dauka zaiji qyashin samun Daya daga cikin seelahs dinsa ba.

Har dare har safe suna aikin cire arzikin zinariyarsu ba har kusan wata yamma kafin suka samu aka gama cireta gaba Daya aka narka aka ajiye a jere wanda nauyinsu ya sake girgiza Ashalawa.

Sai a Daren su kasim suka samu kansu suka dawo rumfarsu bayan sunyi magana da masu Siya,
Na Omar wani bature ne zai Siya,
Na kasim da jamilu kuwa balarabe ne zai Siya Dan haka Basu baro tent na turawan Dake gefen manyan Ashalawa ba dayake da masu tsaron gaske na samudawan Ashalawa.

Karfe Daya da Rabi da wani abu suka shigo rumfarsu inda mamman da lameenu ke kwance suna bacci Dan haka Basu tayar dasu ba suna cikin tsananin farin cikinsu Daya dadu Dan kuwa wannan Daren shine darensu na karshe a Ashalawa washe gari zasu bi turawan zuwa sabuwar rayuwar Dake jiransu Kuma zasu tafi ne da Yan uwansa lameenu da mamman Dan kuwa dukiyarsu ta seelahs ce gaba dayansu.

Jamilu kaf rayuwarsa Bai taba samun kansa a cikin asalin farin ciki ba irin Daren Dan kuwa mahaifansu mata zasu samu rayuwar kulawa da tattalin da mahaifansu Maza Basu samu damar Basu ba suna gurin yawon nema har suka rasu.,
Zai Tara Iyalin kansa su taso cikin Hutu da wadata ba irin tasa rayuwar Daya taso tin qanqani a yawon duniya ba.

Omar da kasim ma kwantawa sukai kusa da juna suna kallan juna kowannensu zuciyarsa kaman zata zage sbd farin ciki da murnan samun rayuwar nutsuwa da Kwanciyar hankali da ilimi da suka Dade suna buqata da fatan samu.

Omar ne me tsananin burin son rayuwar nutsuwa da ilimin dayake tattare da Kwanciyar hankali da rashin damuwa,
Ahankali raayin Hakan da tsananin so da burin Hakan ya shiga kasim sbd tsananin kaunarsa da Omar Wanda sunfi kusanci sosai sbd kasim din Dake matiqar son Omar tin suna qananun kaunar Omar daban take a zuciyar kasim duk da suna son junansu duka su biyar din Amma Omar ya samu qarin matsayin da babu wanda ya samu a Aransa.

Tsakiyar dare guraren karfe uku bayansu da zagayensu yayi tsit Babu motsin komai da kowa sbd runfarsu tana daga baya Baya sosai inda dagasu sai daji.

Dukkaninsu sunyi Nisa a bacci me karfi sbd wahalar dasuka Sha ta shafe kwanaki acikin tsananin zafin Rami da duhu da wahala shiyasa idan ka fito kake bacci sosai sbd wuyar da gangar jiki Tasha.

Ahankali mamman da idanuwansa biyu bacci ba yaji motsi na kusanto runfarsu Wanda motsin yake cikin sanda.

Bude idanuwansa yayi ahankali daga kwancen dayake batareda ya motsa ba Yana sake saurarawa.

Tabbas motsin tahowa ne gurinsu
Tashi zaune yayi ahankali cikin qaramin hasken dayake gurin na farin wata Yana kallan inda lameenu yake kwance Shima idonsa biyu baiyi bacci ba yanajin motsin mamman din.

Wajen rumfar ya juya ya kalla daidai da isowar mutum uku Bai iya ganin fuskokinsu ba sbd ba haske sosai
Sharbebiyar wuqar Dake hannun Daya daga cikinsu idanuwan mamman suka sauka wadda yasan kaifinta Bata fitowa cikin mutum idan an soka batareda ta yanko kayan cikin mutum ba.

Da sauri mamman din ya miqe Yana Ciro tasa wuqar Dake karkashin pilon Kwanciyar sedai kafin yayi yunkurin Isa gurinsu lameenu yayi saurin riqesa daga kwancen dayake Yana kallansa cikin wani irin kallan Daya Saka mamman din kallansa Shima duk da duhu ne.

Zuciyoyinsu bugawa sukeyi sosai da sosai kaman zasu faso kirjinsu daidai lokacinda mutanen sukayi kansu Omar Dake kwance sedai kafin su afka musu kasim ne yafara tashi yayi saurin tarewa Yana ambar sunan Omar da karfi.

A rikice Omar da jamilu suka tashi lokaci Daya suna miqewa tsaye kowannensu na lalabo wuqarsa da wasu irin gora masu qarfin gaske.

Kokawa me qarfi ce ta kaure tsakaninsu suna ambatar sunayen su mamman da Basu ga tashinsu ba Amma Sam Babu motsin su,

Kokarin kashesu mutanen keyi sosai cikin rashin Imani ko kalilan hakama ga duhu basa ganin juna Amma sunqi yadda Dan haka fadan yafara Muni sbd jini ne ke zuba Tako ina a tsakaninsu sbd kaifin makaman hannuwansu bana wasa bane.

Ba qaramar yanka jikin kasim Dana Omar yasha Amma Sam sun qi yadda a kashe su,
Jamilu yanada karfi sosai Dan haka shi Bai jiqata kaman su ba sedai Shima yasha yankan har a fuska.

Mamman da zuciyarsa ke wani irin rawa da jijjiga daga inda yake yasan ko baa fada ba kashe su Omar zaayi to Amma meye amfanin lafewansu Dan akashe Yan uwansu su gaje zinariyar bayan idanma an kashesu din wainda suka kashesun zasu kashesa su tafi dashi su anbarsu a biyu babu an kashe musu Yan uwa Kuma an tafi da zinariyar.

Idan har Yan uwansu zasu mutu to gwara su mutu a hannunsu su su gaji zinariyar Dan kosu da zasu mutu sunfi son su Yan uwansu su mallaketa.

Abinda yake cikin ransa shine yake yawo acikin zuciyar lameenu Dan haka juna suka kalla a lokacinda suke Jin kasim na ambatar sunansu cikin rauni sbd tinanin ko an Riga an kashesu ne basa motsi.

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar
#Arewabooks@Mamuhgee



4
Hankalin Omar tashi yayi mummunan yi rashin Jin motsin mamman da lameenu Dan haka ya fara sarewa Dan kuwa idan har an kashe mamman da lameenu anyi musu mummunan raunin da seelahs zasu bace gaba Daya Dan Suma ba tsira zasuyiba.

Jamilu da Shima yafara gabalaita bazai iya taresu ba ya juyo inda su mamman din suke zai ambaci sunan lameenu kawai lameenun ya daga wuqarsa Dake wani irin daukan ido a duhun ya kutsata gabaki Daya a cikin jamilun take jamilun ya dago jajayen idanuwansa da sukai jajir ya Kalli fuskar lameenu,

Shima lameenu jamilun ya kalla tareda zaro wuqar ta sake kutsata a gefen cikinsa tareda cirowa jinin jamilun na gangara a hannunsa har qafafunsa,
Jajir idanuwansa sukayi wasu irin hawaye masu tsananin zafi suna cika a cikinsu dukkanin jikinsa rawa yakeyi hakama.

Mamman ma tasa wuqar ya Ciro ya daga sama tareda warawa da qarfi zai kutsata gefen cikin Omar kasim da acikin duhun idanuwansa suka sauka akan abinda yake Shirin faruwa yayi saurin karawa da niyar ture mamman din sedai tini wuqar ta kutsa gefen cikinsa ta shige gaba Daya.

Kafin ya zare wuqarsa acikin matune ukun wani ya sake sokawa kasim wuqar daga bayansa take mamman yayi saurin cire tasa wuqar Yana ja da Baya sbd juyowar Omar Yana ambatar sunan kasim da karfi.

Ihun Omar da sunan kasim dayake kira ya Saka aka juyo hayaniyarsu kafin su lameenu suyi kan Omar tini mutane suka yo runfar kowa suka juya kan fadansu kan wainda suka kawo musu farmakin suka illata su sosai Dan haka Koda aka taho da fitilu masu yawa ana duba mummunan lamarin dayayi Munin da Babu me iya kalla Dan kuwa jini ne na kowa da kowa da aka zubar Amma na kasim da jamilu da suka mutu a take shine yake gangara kwance a qasa hakama Omar yaji rauni sosai.

Su kansu mamman yajiwa kansa rauni sosai sbd fita daga zargi duk da a duniyarsu duk Wanda yasan seelahs yasan bazasu taba illata junansuba koda kalmomin bakinsu ba kuwa bare irin wannan mummunan kisan Gillan rashin tausayi da Imani tareda tashin hankali.

Acikin wainda suka kawo musu farmakin Daya Shima take ya rasu sbd raunikan Daya samu dagasu mamman da lameenu sauran biyun ma sunji raunin sosai Dayan har idonsa Daya ta tsiyaye.

Duk tsananin halinda Omar ke ciki kuka yakeyi sosai kaman ransa zai fita da ganin gawar kasim a gabansa da jamilu,
Su kansu mamman da lameenu kuka sukeyi suna ambatar sunan Yan uwansu cikin tashin hankali da dacin zuciya.

Fada ne ya sake kaurewa akan gawawwakin uku sbd zinariyar dasuka bari take aka fara kokawa ana fidda makamai ana ihu batareda ko gawar an dauke daga gurin ba.

Hankalin lameenu Dan mamman tashi yayi suka Kalli juna Dan kuwa bazasu yarda ba bayan uban sukan bayan da akwai aminansu Yan uwansu na alkawarin har mutuwa duk akan wannan zinariyar Kuma suxo su rasata.

Omar gabaki Daya ya fita hayyacinsa sbd tsananin tashin hankali da girgizan wannan balain Dayake shedawa na mutuwar Rabin jikinsu biyu a lokaci Daya Kuma kisan rashin Imani.

Dayasan samun zinari zaiyi sanadin ran yan uwansu daya raki Allah ya hanasu samunta har karshen rayuwarsu.

Fada sosai kaman yaqi ya kaure a take gurin inda har an sake illata wasu mutum biyu an cinnawa rumfar wuta.

Omar da sauri duk rauninsa ya miqe ya dauki jakar zinariyarsu da shi kadai yasa inda suka ajiyeta ya daure a jikinsa tareda Jan gawar kasim ya fara fitarwa su mamman suka kamo ta jamilu suka fito da ita har lokacin kuka Omar keyi sosai Yana kallan gawarsu Yana juya ta yanda zaiyi rayuwa ba kasim hakama yanda zaije ya sanar da mahaifiyar kasim din kasim ya rasu ya barta hakama mahaifiyar jamilu.

Irin kukan dayake yi ne sosai ya Saka da yawa dakatawa daga tashin hankalin manyan Ashalawa din suka iso gurin ana haskawa da fitilu ana ganin Munin lamarin.

Akan gawar su kasim aka tsaya tareda wainda suka mutu duk akan fadan.

Gefe Akai dasu aka rufe Saida safe zaa musu sallah a rufe.

Omar kuwa dole dashi suka tafi Dan basa kariya idan ba Hakan ba Shima kafin safiyar ba samunsa zaayi ba Dan haka Suma su mamman duk tashin hankalin da suke ciki na yanda komai zai kasance Bai hanasu bawa Omar din kulawa ba daga raunikansa ba.

A rayuwar Omar bai taba tinanin zasu samu kansu a irin wannan mummunan yanayin ba duk yawonsu da hadarukan da suka Saba shiga,
Sun dauka zasu samu kyakkyawar rayuwar da iyayensu Basu samu ba Ashe zasuyi mutuwar kaskanci ne wadda iyayensu su Kam basuyiba sunyita ta rufin asiri daidai gwargwado sbd su a cikin rijiyar zinarin suke mutuwa.

Zazzabi ne take me karfin gaske ya rufesa Babu inda Baya kakkarwa a jikinsa gashi jikinsa har lokacin jini na zubar masa.

Mamman ne ya Kalli lameenu
Shima lameenun shi ya kalla kafin suka fara kokarin cigaba da tattalinsa suna basa kulawa da share masa jinin fuskarsa suna kukan rashinsu jamilu.

Duk da antaho dasu Omar din bangaren manya kafin safe fadan Ashalawa din be kwanta ba saima qara girma yakeyi Daman lokuta da dama karamin fada ko fada kadan sai a tayarda fadan da fitinarsa zatai babbar illa ga kowa sai anyi rashin rayukan da dama shiyasa koyaushe zinariyarsu Bata karewa habbaka takeyi.

Fatinar Bata lafaba ko kadan take ta zama babba Ashalawa ta dauki hayaniya,
Koda asuba tayi sallah kawai Akai turawan sukace tafiya zasuyi sbd tashin hankalin dayaketa sake rikicewa.

Tini sukai waya helicopter zai taho ya daukesu ya fidda su dajin.

Babban tashin hankalin Daya Saka mamman da lameenu kusan Yanke jiki a gaban manyan Ashalawa da turawan da zasu siye danyar zinarin shine Sanar dasu gabaki Daya tarin danyar zinarin kasim ya bawa Omar tin a daren jiyan da Akai rubuce rubuce komai sunan Omar aka Sanya sbd Omar shine zai riqe musu dukiyarsu dashi dashi din Dan haka gaba dayanta ta Omar ce gashi kaf acikinsu ukun da suka samu me yawan gasken ta kasim din tafi ta kowa yawa hakama ta Omar din Dan haka lissafinta ma da aka hada din hankali bazai taba daukaba.

Wani mummunan hayaqin tashin hankali ne mamman yaji Yana fita kunnuwansa Yana gurbata numfashinsa dake fita da daqyar.

Lameenu kuwa manyan idanuwansa ya fiddo waje suna sauyawa zuwa jajir hannuwansa na daukan rawar tashin hankali yayi saurin qanqame hannuwan Yana kasa boye firgicinsa duk yanda yaso.

Juyawa yayi ya Kalli inda mamman yake zuciyarsa na dauka wani irin radadin zafi da 'dacin baqin cikin da Bai taba sanin da akwaisa ba.

Akan Omar dukkaninsu suka mayar da kallansu lokaci Daya zuciyoyinsu naci da wata irin wutan tafasar zuci.

Me kenan?
Omar sukaiwa kisan su kasim din kenan tinda shine yafi kowa arziki a Ashalawa kenan yanzu ko me?
Me Hakan ke nufi da cewan kasim ya bawa Omar taskar arzikinsa gaba Daya?

Lameenu a tasa zuciyar kuwa abu Daya ya sani shine tinda suka riga suka kawar dasu kasim akan zinariyar to kowama yayi musu shamaki da ita inda suka aika su jamilu can zasu aika koma waye,
Sun Riga sun fara aikinda Babu tsayawa sai sun mallaketa,
Omar bazai taba hanasu mallakarta ba Dan zai musu zarran da bazasu taba kamosa ba har abada Kila,
Tayaya zasu kallesa a samansu su suna qasansa bayan sune sukai dirty work din Daya basa Arzikin dukiyar.

Sake kallan juna sukai shida mamman har lokacin Babu Wanda zuciyarsa ba tafasa takeyi cikin tashin hankali da tsoron tabbatuwar abinda aka fada din ba.

Omar kuwa har lokacin Yana cikin halin rashin lfy Daya rufesa da kukan rashinsu kasim Daya kasa dawo dashi daidai.

Zinariyar kuwa baa tsaya komaiba aka ware ta Omar da kasim aka ware masa abarsa shine zai kula da mahaifiyar kasim Daman tamkar itace ta haifesa yake.

Ta jamilu kuwa batareda tinanin komai ba ko bin tsarin Daya kamata ba haka aka Kara rabe musu su uku,mamman da lameenu Da Omar din Wanda yace ya yafe musu aka barmusu su biyun.

Kason da suka samu ba qaramin kaso bane da zai ishesu Gina rayuwarsu cikin wadata sosai da Kwanciyar hankali tareda samarwa Kai suna da wani matsayin ma Amma duk wannan Bai saukar da mummunan nauyin Daya Riga ya danne zuciyarsu ba data rikide a dare Daya Takoma wata sabuwa daban da kadan Baya isarta.

Gabaki Daya baqin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login