Showing 96001 words to 99000 words out of 261814 words
yace komaiba.
Alh Lameenu dinne ya Kalli fuskan Dr Dee a sake Yace,
"Akwai patient danake buqatan dukkanin bayanan komai akanta tareda sani akan girman matsalanta da duk abinda ya shafi komai dayake cikin file dinta na matsalanta."
Sake kallan Dr Dee yayi Yana mayar da bayansa jikin kujera ya jingina a natse Yana Dora kafarsa Daya kan Daya cikin Kwanciyar hankali kafin yace,
"Ko Hakan zai iya yiyuwa Dr Dee??"
Numfashi Dr Dee ya sauke Yana mayar da nasa bayan ya jingina Shima a natse kafin ya dago ya Kalli Alh Lameenu din kafin ya ka mayar da kallansa kan dalolin Dake gabansa a shimfide.
BB da Shima a natsen yake amsar Dr Dee din yake Jira kallan Dr Dee din yayi Wanda Shima BB din ya kalla,
Numfashi ya sake saukewa tareda sakin murmushi me Fadi da sanyi Wanda ya Saka su daddy lameenu din sakin murmushin Suma ba tareda damuwan komaiba.
Dr Dee wayarsa ya Ciro daga aljihunsa Kai tsaye yana Neman numbern da zai kira harya ganta.
Saka kiran yayi tafara ringing har tsawon lokaci kafin aka dauka cikeda girmamawa kafin ya amsa gaisuwan da Akai masa Kai tsaye yace
"akwai patient danake buqatan cikakkiyar bayani akanta a ayau so Ina buqatan file dinta a office dina kafin na iso akaisa desk dina,
Kallan Alh Lameenu yayi a natse yace,
"Wat's the name???
"AMEENATOU JADEN SEELAH or AMEENATOU NUHU BABBAH Kokuma AMEENATOU JAMAAL SEELAH "
Sunayen a jere kaman yanda Alh Lameenu ya fadosu haka ya fada yace kafin ya shigo Akai masa file dinta office ya kashe wayar.
Wani shegen murmushi Alh Lameenu ya sake Yana kallan Dr Dee Wanda yake dariyar Jin dadin Shima Yana Koro masa bayanan da suke sake kashe alh Lameenu din da dadi Dan kuwa yasan kudi shegune Amma Bai dauka Dr Dee zai zama Dan Kai tsaye haka ba Babu Batawa Kai lokaci bare dalolin gabansa su huce Dan haka da zafinsu BB ya matso ya tattara ya zubasu a cikin farar envelope me sunan SEELAHs a jiki ko rufewa bataiba ya ajiye gefen Dr Dee din Wanda sai a lokacin ya buqaci ruwa aka kawo musu Nan suka shiga fira sosai kaman sun Saba sbd take aka kulla alaqa.
Daga office din Alh Lameenu Kai tsaye asibitinsu Dr Dee ya nufa,
Yana Isa office ga mamakinsa babu file din Daya buqata take ya kira ya sake tambaya da sauri incharge na record office ya iso ya sanar masa file Daya buqata Bai taba dawo musu ba Yana gurin Dr Adams sbd patient din tasa family dinsa ce Dan haka komai nata shine yake kulawa dashi.
Sallamarsa Dr Dee yayi tareda daga wayarsa ya kira office din Dr Adams din Kai tsaye.
Cikin sa'a kuwa Dr Adams na cikin asibitin Bai Riga ya fita ba Dan haka Yana daukan wayar cikin girmamawa ya gaida Dr Dee din sbd shine a gaba dashi.
Babu Bata lokaci Dr Dee ya buqaci files din patient din Dake special A block duka sbd kawar da zargi ko tinanin komai daga Dr Adams din.
Da farko Dr Adams baiyi tinani ko zargin komai ba Dan haka ya tattara duka files nasu Dake office dinsa ya fito dasu da kansa yakai har office din Dr Dee din sbd Daman zasu tattauna matsalan wata sabuwan patient dinsu dake jiwa kanta rauni sosai Dan nata ciwon yayi tsananin gaske gashi itama special patient ce sbd matar babban mutum ce itama.
Ajiye files din yayi akan desk tareda zama Yana sake gaida Dr Dee cikin sakewa
Shima cikin sakewan yake amsawa suna fira cikin sabo da girmamawa kafin Dr Adams yafara jero masa bayanin patient din Yana nuna masa file dinta.
Amsawa Dr Dee keyi Yana duba files din Daya bayan Daya a tsanake har ya gama Babu file din dayake tsananin buqatan ganin Dan haka ya dago ya Kalli Dr Dee din batareda nuna komaiba da kulawa yace
"Duka duka iya patients din special block A kenan?Coz Nan duka 8 files ne and a record Kuma munada 9 patients a block din so meya samu Dayan file din ko patient din zance???
Dagowa yayi ya zubawa Dr Adams idanuwansa Yana jiran qarin bayani batareda tsaurarawa ba.
Numfashi Dr Adams ya sauke Shima batareda nuna fargaba ko Wani damuwa ba yace
"Dayan patient din is my patient, she's family,
Case nata Yans hannuna ne tin kafin Nan so file nata Yana office nawa"
Numfashi Dr Dee ya sauke Yana gyara zamansa yace
"Ok ba damuwa but dole zaka barwa Wani case dinta tinda kace she's family Kuma kasan me Hakan ke nufi so idan ka koma office ka Aiko min file dinta zan bawa Wani kwararren likitan case dinta."
Dagowa Dr Adams yayi da sauri ya Kalli Dr Dee din zuciyarsa na shiga shakka da fargaba tareda tinanin ta yadda zai iya yarda case din Ameenatou ya koma hannun Wani bayan yasan komai zai iya lalacewa hakama tayaya zai iya bari JEEY ya dawo ya tararda matarsa ba a yanda ya bar masa ita ba tinda idan har tabar hannunsa to tabbas zasu iya dorata akan drugs Wanda ba Bata time zai juyar da ita da gasken ba kaman wannan dayake temporary ba tinda wata na qarewa zata saketa ta koma daidai gashima duka duka a wannan lokacin baifi 6days watan ya qare ba.
Ganin yanayin Dr Adams ya Saka Dr Dee Dan sake fuska cikeda kulawa da nuna kaidar aikinsu kenan ya sani dole Wani likitan ne zai kula da Wanda yake family gunka sedai bazaa yi Maka iyaka da shiga case dinba kaima Amma dai Kuma bazaka karba ace Kai kadai ba.
Sanin Dr Adams ma yanada matsayi babba Kuma mugun kwararre ne a aikinsa ya saka Dr Dee kwantar da Kai cikin nuna kulawa Kai tsaye yace,
"Ka Aiko file din zan dubasa a Daren Nan zan karba case din nata da kaina yanda hankalinka zaifi Kwanciya coz zan iya cewa Ina ganin mahimmancinta gareka tin yanzu din."
Babbar matsalan dayake gudu kenan Dr Adams ta fitar Ameenatou hannunsa duk tsawon wannan lokacin daga zuwanta,
Sanin zata iya cike kwanakinta ta dawo daidai kaman yanda JEEY ya buqata ya sakashi karban case dinta gashi Kuma a yanzu datake gab da dawowan daidai ana Neman samun matsala haka zalika Kuma bazai taba iya Hana Dr Dee karban case dinba tinda aka Riga da aka fara maganar.,
Shi kansa Yana cikin manyan Dake karfafa girman dokan da Dr Dee ke magana,
Me zai fadawa Dr Dee idan yashiga file din ya tararda Babu komai face information da Dan sauran tests da ba'a rasa ba na lafiyanta da Basu ma shafi hauka ba kwata kwata na tabbacin lafiyan jiki da jininta ne da suke fes ba cutar komai a tattare da ita.
Hakama me zai fada akan patient din zaman asibitin kawai takeyi Bata kan kowanne drug,
Bugu da qarin matsalan shine idan suka San alluran da Akai mata shi kansa laifi ne Mai girman gaske Dan kuwa shi kansa yayi mamakin Fitaccen kwararran likitan Poland ace da kansa yayiwa macen datake dauke da igiyoyin aurensa irin wannan alluran duk da baisan dalilinsa ba Amma yasan koma menene dalili ne me Girma kadai zai Saka JEEY SEELAH yin Hakan.
Jin shirunsa ya sake Saka Dr Dee maimaita abinda ya fada din tareda basa tabbacin inshallah zai duba lamarinta yanda ya kamata Dan haka ya kawo masa file dinta kafin gobe.
Baiyi dogon musu ba sbd babu abinda zai iya fada a lokacin bayan cewa ok kawai ya miqe ya fice daga office din.
Dr Adams baiyi niyar bayarda file dinta ga kowaba Kuma baida niyar bayarwa din Dan haka dole ya nema JAMAAL akan ya dawo da gaggawa ya karba patient dinsa daga asibitin gabaki daya kafin tabar hannunsa barinta asibitin yayi wahala.
Duk yanda Dr Dee yaso tsanantawa ya karba file din a Daren dole hakura yayi sbd kada Dr Adams ya fahimci zalamarsa ga Hakan Dan haka ya bari sai washe gari yabar asibitin gabaki Daya.
Dr Adams kuwa kasa ma barin asibitin yayi yafara kokarin Neman JEEY sedai kwata kwata Baya samunsa,
Siddeeq ya kira ya sanar masa Yana son magana da JEEY akan kwanakin Ameenatou din sun kusa cika na Alluranta.
Siddeeq da tini ya kusan kammala komai na barin qasar da ita kaman yanda JEEY yabar masa komai zuwa lokacin Dan kowanne time ma zasu iya tafiya Dan haka sai Bai raba hankalin JEEY din da maganar ba ya sanar masa inshallah kafin lokacin ya cike zasubar kasar kawai so ma yakeyi kafin ta dawo daidai sun riga sun bar qasar dan tana dawowa daidai komai zai iya dawowa 'danye.
Ganin siddeeq Basu fahimci abinda yakeson fahimtar dasu ba yasa Dr Dee cigaba da kokarin Neman JEEY din da kansa sedai ba wannan time din dan tini duk yanda yaso kaucewa dr Dee abin ya gagara dan shima dr Dee ganin duk yanda zaiyi ya karbe patient din daga hannun dr Adams yayi amma dr Adams yaqi yadda komai nata ya shiga hannun wani take abin yafara tsanani dan kuwa manyan asibitin kusan tini suka shigo zancen.
Qarfi da Iko aka nunawa Dr Adams Wanda ya tabbatar masa da akwai abinda yake faruwa Wanda shi Bai saniba sbd a cikin kankanin lokaci abubuwan sukai nauyi ba zato ba tsammani kwatsam aka daukesa daga asibitin gabaki Daya aka turasa wata qasar ma.
#MAMUH#
#BESTLOVESTOTY
#AMJEEY
#HOTLOVE
#ROMANCE
#BABY
#AMEENATOU
#JEEY SEELAH
#JDENS
#SEELAHS
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
61
Daukesa da Akai daga asibitin cikin kankanin lokacinda Baya yiyuwa ayi Hakan ya Sakashi shiga tashin hankali da damuwa ta bangaren Daya ma JEEY sai a lokacin yake samun bayanin komai Dan haka take ya bawa siddeeq din umarnin karban Ameenatou din daga asibitin su wuto sbd komai na tafiyansu ya kammala.
Ga sabon babban tashin hankalinsu shine case yabar hannun Dr Adams kwata kwata Dan haka ba shine me Iko ko Daman sallamarta ba komai ya dawo hannun Dr Dee.
Dr Adams yayi tashin hankali dasu sosai sedai Babu yanda ya iya sbd karfinsa da akafi Wanda akaso lalata career dinsa dole yanaji Yana Gani yabar qasar yabar Ameenatou a hannunsu wadda tin kafin tafiyarsa aka fara Banka mata allurai da magungunan daya Riga yasan juyewan hankali ya Riga ya zama dole gareta haukan gaske yanzu tariga ta tabbata gareta.
Baqin ciki da kunyar JEEY ya sakashi kasa jiran JEEY ya iso ya tattara ya tafiyarsa Dan yasan ba Hakan sukai da JEEY ba to Amma ya zaiyi karfi aka nuna masa tareda abubuwan da suke kama da ana threatening din safety na familynsa dole ya Yanke komai da zai hadasa da JEEY ya tafiyarsa.
Sabon tashin hankali siddeeq ya shiga Wanda Bai taba tinanin samun kansa acikinsa ba sbd a yanzu tabin hankalin gaske ne Ameenatou take ciki Wanda Babu wani sauki sai abinda Allah yayo,
Sister Ashley itace nurse da Dr Adams yabawa Amanan cigaba da kulawa da Ameenatou,
Siddeeq ya kukan baqin ciki me tsananin gaske na sheda wannan mummunan ranar sedai kwata kwata ya kasa bayyanewa JEEY abinda yake ganin Ameenatou din acikin sbd acan din Baya cikin Kwanciyar hankali Shima sbd mum dinsa da abubuwan sai sake lalace a sukeyi haryanxu basa samo kanta ba,
Wannan ne ya Saka siddeeq taqaitawa Jamaal halinda take ciki ya Maida dukkanin hankali da kulawansa akanta kafin lokacinda JAMAAL din yake jiran ya samu kan Mum dinsa ko yayane sai ya juyo ya dawo shi ya dauketa da kansa daga asibitin da take suka tsananta dokokinsu masu karfin gaske akan patients dinsu kwata kwata ma andena bari ziyara sai manya ko waye Kai bakada Daman ganin patients dinsu a yanzu.
Wannan ne yayiwa Daddy lameenu daidai yanda yakeso sbd a yanzu ya gama komai burinsa ya cika Ameenatou ta zama cikakkiyar mahaukaciyar da bazata taba moruwa ga Mam ba Dan bazata taba mallakar dukiyar mahaifinta Omar ba bare Mam da 'dansa JAMAAL su mallaki dukiyar Dan haka baida sauran damuwa a yanzu.
Ta bangaren Dadah kuwa samun fara samun saukin Hafiz ya Sanyata dawowa kusan daidai Dan itama jinyar kanta takeyi a kwance Dan haka tana fara ganin alamun sauki da Rahama ta fara warwarewa sedai abin farko da Hafiz ya buqata bayan dawowansa daidai shine su tafi Subar garin gabaki Daya su koma gida suyi jinyar Babbah.
Dayake itama dadah din a matse take da su farfado din Subar garin datake Jin kaman siqewa zatai da numfashin datake shaqa a cikinsa kullum Babu musu ta amince sedai Kuma Ameenatou da zasu tafi Babu ya Saka zuciyoyinsu shiga tashin hankali mafi girma Amma sanin tana asibiti inda Babu me iya cutatar da ita ya Saka su amincewa da tafiyan nasu idan Hafiz ya warware zai taho ya tafi da ita itama suyi jinyarta.
Siddeeq duk yanda yaso hanasu tafiya gagara lamarin yayi Dan haka Babu ma saninsa suka nema sallama a asibitin ta Babbah suka tattarasa suka tafiyarsu ba tareda ya saniba sai daga baya Wanda Hakan ba qaramin sabon tashin hankali ya sakashi ba Dan kuwa Shima Neman Juyewa yaji kansa nayi Amma hakanan ya daure yaci gaba da tsayuwa tsayin daka akan Ameenatou dasuke kokarin daukewa subar qasar da ita.
Bayan barin Dr Adams Babu yanda Jamaal beyiba Dan samun sallaman Ameenatou din batareda ya baro Mum ya taho ba Amma kwata kwata Hakan ya gagara samuwa gashi da gaske sba sauke Dr Dee Banka mata allurai kawai yakeyi da suke Neman wuce hankali Dan kuwa sosai tayi Wani irin laushi rayuwanta ya koma abin tausayi gaba Daya dole JEEY yafara kokarin barowa ya taho ba shiri shikuwa siddeeq kudin gaske yake sakarwa sister Ashley Dan ita kadaice wadda ya yarda da ita a cikin asibitin akan Ameenatou Dan haka ta hanyarta suka samu allurai da maganin da ake bawa Ameenatou suka ragu sosai sbd itace me sauya maganinta tareda qin yi mata allura lokuta da dama idan itace zatai Dan haka suka Dan samu sassaucin azaban tashin hankalinsu harma ya sanar da JEEY an Dan samu sassaucin lamarin.
Duk da Hakan JEEY dole yafara shirin tahowa sedai kusan tafiyan tasa Bata samu tabbatuwaba Saida kusan lokaci me Dan tsayi ya qara ja Wanda yayi daidai yanzu da watanta uku acikin asibitin Wanda Kuma yayi daidai da samun saukin jikin mum dinsa data farfado ta samu lafiya ba laifi sedai a Bata iya tafiya hakama kusan abubuwa da yawa Sai anyi mata.
****Barin Dr Adams daga asibitin harya zama labarin Dan tini aka maye gurinsa da wani kwararren likitan,
Juyewan hankalin Ameenatou din ya daidaita a yanzu akan farko da hauka tayi tuburan sbd qarfin alluran da Dr Dee ke Banka mata Wanda kusan so sukai ta mutu tabar duniyar gaba Daya Amma Hakan Bai samu ba gashi Babu ikon kasheta ta wata hanyar bayan wannan Indai a cikin asibitin ne sbd tsananin karfi da dokan da asibitin suke dashi Dan haka dole sedai ta hanyar alluran da sukafi karfinta na haukan da sukewa patients dinsu kadai zaa iya kaudata sbd Hakan ne kadai zai Saka mutuwanta ya zama clean Babu zargi ko bincike.
Daddy lameenu shi ko a Hakan ma yayi masa Dan haka yace abarta hakanan tinda yasan bazata moru ba kawai dai Dr Dee ya lura sosai ya Bata dukkanin hankalinsa da anga tafara dawowa daidai aci gaba da aikata mata abinda yakamata.
Kudi sosai ya sakarwa Dr Dee ya bar masa kulawa da komai ya Maida hankalinsa kan harkokinsu da suka fara dawowa daidai sbd Mam Daya dawo aiki Shima sbd ya warware huldodinsu na Ashalawa tini Mam ya Bude wuta aka ci gaba da harka gadan gadan cikeda sabuwar rashin tausayi da rashin Imani Dan shi a yanzu baida baqin cikin mutuwar kowa tinda ya rasa nasa.
Maganar JEEY a zuciyarsa kuwa tana Nan daram Babu abinda yakeji a yanzu cikin ransa Daya Kai girman son 'dan nasa da tsananin buqatansa Amma tinda yasan Hakan a yanzu bame yiyuwan bane Saiya ajiye gefe tinda yasan duk inda Omar yake zai warke ua dawo Wanda dawowansa zata dawo masa da 'dan sa tinda a yanzu duk abinda yayi Omar yariga yayi Jamaal tinda sirikinsa ne Kuma Magajinsa ta anan gaba.
Lameenu bayan abinda yayiwa Haroon da Ameenatou Babu wani abu na rayuwarsa Daya taba aikatawa batareda sanin Mam ba ko bisa umarninsa,hakama Baya iya aikata komai ko gudanar da komai na rayuwarsa batareda Mam din ba shiyasa yake a gigice da yanayinda Mam ya shiga a lokutan da suka wuce amma ayanzu da Mam ya dawo daidai yafi kowa farin ciki da jin dadin harkokinsu da suka dawo kan hanya hakama su BB ma sun shiga farin ciki da Kwanciyar hankalin ganin dawowan Sir Mam daidai Dan kuwa kusan shine shugaban gasken Amma dukkaninsu a kiyaye suke da duk abinda zai Saka Mam sani ko fahimtar wani abin daya gudana.
******Watan Ameenatou uku harma da sati Daya Babu Wanda ya sani a Babin rayuwanta na yanzu bayan sister Ashley da siddeeq Kuma su kadai ne suka rabarta kwata kwata Bata yadda ko kusanto inda take kowa yayi bayan su din gashi shi siddeeq din bama ya cika ganinta ba yanzu sbd dokokinsu kullum qaruwa sukeyi.
Kama hannunta sister Ashley tayi bayan ta iso bakin gadon nata tana kallan kafafunta data kame guri Daya taqi sakko kafafun qasa har lokacin sbd taqi yadda da Babu ruwa a qasan dakin.
Murmushi me sanyi sister Ashley tayi tareda dauko slippers dinta na Valentino masu taushi ta ajiye qasa tana cewa
"Sauko ko saka Babu wani ruwa a qasan."
Maqe kafada tayi tana sake kame kafafunta idanuwanta na qasan har lokacin.
Ajiye roban ruwan da Ameenatou din Tasha ta rage tayi gefen gadon tana qarasowa ta kama kafafun cikin kulawa zata sauko mata dasu Dan Saka mata slippers din, Ameenatou tayi saurin janyewa tareda yin Baya ta kame tsakiyan gadon tana zubawa sister Ashley idanuwan batareda tace komaiba.
Rokonta sister Ashley tafara yi sbd kanta zataje ta wanke mata kaman yanda ta Saba duk sati tana wanke mata Kai ta gyara mata farce harma da kunnuwanta duk sai an tsaftace mata.
Sanin ba zata sauko dinba ya Saka sister Ashley juyawa taje ta kirawo cleaner akazo da mopper dole aka hau mopping din dole Wanda babu ruwan komai aka ringa matsewa ana nuna mata.
Saida suka share Mintina sosai ana goge koina a dakin kafin sister