Showing 240001 words to 243000 words out of 261814 words

Chapter 81 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9959

da Dad Mam din yai wanda hakan ma Wani tsaron ne am ce kadai a Dan hadarin Amma itama Jamaal zai iya komai akan tsaronta."

"No siddeeq nidai hankalina ya kasa kwanciya kwata kwata akan Arfat da Ameenatou din"

"Tayaya hankalinki zai kwanta Aleena? Mam Dake tsaye kofar palon ne ya Fadi hakan Idanuwansa na sake rinewa zuwa Wani irin Jan dayafi na farko jikinsa har Wani rawa yakeyi sbd abinda yaji.

Siddeeq ne da Aleena din sukai saurin juyawa cikeda mummunan firgita da tsinkewan zuciya.

Siddeeq daya Kalli mum din Yana riqe hannunta Dan ganin yanda jikinta ya Dan dauki rawa Cikin nutsuwa da kulawa Dan kada ta rikice yace

"It's ok Mum,karki damu"

Mam da zuciya ta gama cinyesa kallo daya yayiwa siddeeq yace ya fita ya basa guri magana zaiyi da Aleena din.

Kame fuska dakyau siddeeq yayi zai Kalli Mam din yayi masa maganar da zata kashesa sai Kuma ya fasa sbd tinawa da komai lalacewansa mahaifin Jamaal ne,
Kaunar dayakewa Jamaal da abinda yake tsakaninsu akwai abinda bazai taba yiwa mahaifinsa ba duk lalacewansa Dan haka ya hadiye fushinsa da bacin ransa sbd akwai halas da ake bari sosai Dan kunya.

Ficewa yayi daga palon ya sauko qasa Yana barin palon gaba daya Yana v
Ciro wayarsa Dan Kiran Jamaal Wanda Shikuma acan wayarsa take silent kaman yanda ta Dad Omar take silent din.

Dagowa Aleena tayi ta kallesa Idanuwanta na sauyawa sbd damuwan rashin sanin abinda yake sakawa a ransa da Kuma yanda jikinsa ke rawa.

Shima zuba mata Idanuwansa yayi Wani irin radadin gaske da jininsa dayake Kuna Suna qara masa azabar zafin dayake ji a zuciyarsa.

Takowa yayi ya iso gabanta Bai tsaye komaiba ya Saka hannuwansa biyu ya kamo wuyanta ya shaqeta da karfin gaske jikinsa na sake daukan rawa yace

"ARFAT din Dana samu hotinansa tareda Omar daga bincikena wanda baya barin kwata kwata ana samun hoton fuskansa da kyau shine 'dan Jamaal?
Jinina??
Tayaya Jamaal zai Haifa Dan kansa jinina Yana yawo a jikinsa ku Taru ku boyemun?
Yaron da ban taba sake bi takan jefa bincikena akansa ba sbd ban taba tinanin akwai Wani jinina Dake duniyar ba bayan Jamaal Ashe jikana ne????

Cikin tsananin azaba ta fara kokarin cire hannunsa daga wuyanta tana cewa

"Daman nasan dawowanka ba alkhairi bane sbd har abada Babu tsarki ko Imani a zuciyarka,

Meyasa bazaa boye Maka ARFAT dinba tinda Babu wanda bazaka iya cutarwa akan burinka da qazantacciyar kwadayin duniyarkaba"

Sakinta yayi da qarfi Yana tureta har Saida ta Fadi ta bugu da table ta dago Idanuwanta da sukai jajir sbd sbd shaqan datasha ta kallesa zuciyrta na radadin yanda ya kasance mahaifin 'yayanta wanda har abada bazata Dena Dana sani da radadi tareda baqin Cikin hakan ba.

Hannuwansa rawa sukeyi sosai sbd abinda yakeji a zuciyarsa Dake Jin azabar radadin boye masa yanada Wani jinin Wanda ya fito daga 'dansa mafi soyuwa a garesa,.
Hakam 'da ne da zai kasance qarshen cikar burinsa sbd samun Arfat shine qarshen hada irinsa da Omar wanda ko a so ko Babu dole sai sun zama daya hakama dukiya dole ta zama yanada haqqi da sake cikakkiyar iKon mallakanta.

Cikin zafin zuciya hannuwansa na sake rawa ya kalleta yace

"Meyasa Kuka boye min?
Kin bawa Jamaal shawaran a boyemun ne sbd daman kin shirya auren Omar din?
Waye ya bawa Omar daman auren matar datake uwar yayana Matata....

Cikin baqin Ciki da Jin zafi ta katsesa da cewa

"Mam Babu ranar da bana baqin Ciki da Danasanin auren daya taba shiga tsakanina dakai,
Badan su Jamaal ba wlh tallahi da tini na Dade da miqaka hannun hukumar qasar Poland sbd acan kaje ka kashe rayuka fiyeda biyar ka tsallake ka tahowarka,
Babu wanda yake tareda SEELAHs yayi mutuwar Allah batareda kune Kuka kashesa ba,
Me zaka fadawa Allah a ranar daya tadaka ya tsayar dakai a tsakiyar wainda kukai sanadin rayukansu?

Kasan meyasa 'danka ma daka Haifa ya tsaneka baya kaunarka sbd kawai ka kasance mara Imani ko digo daya acikin ranka Mam,
Babu ran dayakeda Mahimmanci a gurinka bayan naka,.wace rayuwa ce wannan??


Kanta yayo koina jikinsa Yana rawa sbd Abu biyu Dake Neman kashesa da ransa kallanta amatsayin matar Omar da Kuma boye masa jikansa da daya sani da yanzu Wani labarin akeyi ha wannan ba Dan Babu wanda a duniya zai Hanasa karbansa Koda kaf ahalin jdens da seelahs zasu mutu ne.

Sake shaqeta yayi Cikin tsananin zafi zuciya da tiriri Yana cewa

"Wallhi tallahi alqawarine nayi har abada Babu namijin da zai aureki Banga bayansa Dan haka wlh Omar idan ban kawar dashi akan dukiyarmu da itace silar komai to tabbas tabbas zan kawar dashi daga duniyar gaba dayanta sbd aurenki da Kuma jikana Arfat daya rabani dashi ya boyesa.

Cikin azaban datake ji tace

"Mam Babu wanda bazaka iya kashewaba na sani tinda ka kashe 'dan uwanka Rabin jikinta lameenu da iyalinsa kaf tareda matarsa Ateeka to Amma ka sani nikuma idan Ina Raye inshallah bazaka taba Omar ba sbd bazan barka kayi hakan ba sbd Son danake masa shine Asalin son daka rabani dashi tin lokacin kuruciyat......

Wani Azababben Mari ya sauke mata Yana Jin kansa na Neman kamawa da wuta sbd abinda yakeji Dan gaba daya zarewa yake neman Yi,
Baida komai a Lokaci daya matarta ta aure amininsa Kuma Dan uwansa hakama yanada jinin dayake tsananin so an boyesa hakama baida kowa ko gurin zuwa sannan tana Dora masa da asalin son gaskiya datakewa Omar.

Shaqeta yayi da karfi Yana marinta Yana cewa

"Idan bazan iya kashe Omar sbd Raba wannan auren ba mutuwarki itace zata Raba auren wanda wlh bazan barsaba"

Bakinta ne yafara fidda jinin Marin qarfin dayake mata Yana sake shaqeta numfashinta na kokarin barin jikinta sbd tsananin azabar da bata taba jintaba a duniya.

Hawaye masu zafin gaske ne suka gangaro mata gefen Idanuwanta tana Bude Idanuwanta daqyar ta kallesa Shima wasu irin hawayen ne masu tsananin zafi da Ciwo suke taruwa a Idanuwansa sbd radadin dayake ji a zuciyarsa Amma ya zabi tabar duniyar gabaki daya ya huta..


Ayesha datake bakin kofar tin lokacinda suke magana sbd ganin shigowansa gidan ya sakata fitowa Dan rabonta dashi tin lokacin rasuwar hakama Bata taba waya dashi ba sbd Bata samunsa ba Dan haka ayau din Cikin Jin sanyi da farin Cikin ganinsa tinda shine matsayin mahaifinta ta fito Kai tsaye sbd farin Ciki da tsautsayi batai tinanin komaiba ta bisa saman bayan siddeeq ya fice kenan sedai abubuwan dataji ne suka sumar da ita tsaye bakin kofar palon tana kallansu da jinsu Cikin mummunan shock da masifar datafi karfin hankali da tinaninta.

Ganin Dr Aleena na kokarin mutuwa a hannunsa da Kuma hayyacinta data Dade da ficewa sbd tashin hankalin da firgicin abinda taji
Ko Gani Batayi ta miqa hannunta kan console Dake gurin ta dauki wata qatuwar crystal me tsananin nauyi da tsinin shape din Kibiya ta daga da karfi zata kwada masa Jin motsi bayansa ya sakasa juyowa batareda ta saki Aleena dinba daidai juyowansa daidai Ayesha din na cakowa da karfi take gabaki daya tsinin ya ratsa tsakiyar idonsa na Dama take ya sake Aleena da qargi Yana yin baya jini na Wani irin bartsi daga idonsa.

Ayesha na ganin hakan ta buga Wani irin ihun tashin hankali da tsoro jikinta na jijjiga.

Aleena datake zube a qasa kasa motsawa tayi sai kokarin fidda numfashi takeyi Cikin tsananin azaban gaske.

Maman fadeela da Siddeeq dayake shigowa palon qasa lokacin sbd ya damu Damar magana dasu Jamaal take sukai saman da mugun gudu hankalinsu tashe.

Suna shiga da jinin Mam Dake bartsi suka fara cin karo take maman fadeela tayi baya tana buga Wani ihun itama siddeeq kuwa da tsananin gudu ya isa gurin Mum Yana kokarin kamota sedai Bata iya ko motsawa sosai ga jini bakinta sosai.

Daukanta yayi da sauki gabaki dayanta tareda saukowa da ita daidai Nan su babbah da Hafiz suka shigo gidan sbd dabai samu Jamaal ya dauka ba da Dad Omar Hafiz ya kira sbd tinanin Yana office din Shima sedai Yana gida tareda babbah Suna Jin abinda yake faruwa take babbah ya fito sbd yasan waye Mam da abinda zai iya Yi.

Siyam datake gurin dadah zaune a kujera tanajin sunan Mam take ta sauke ajiyan zuciya me sanyi tareda rufe Idanuwanta Wanda ya Saka dadah kallanta cikeda mamaki sedai Gani Bata motsaba ya sakata tashi tabi bayan Hafiz tana cewa ya kula sbd kada zuciya ta dibi babbah yayi Wani abin.

Babbah na shigowa gidan ganin halinda Dr Aleena take Ciki Cikin tsananin tashin hankali da mamaki ya Kalli Mam Dake fitowa Cikin mummunan hali kafin kowa ya Ankara tini babbah yayi saman ba tausayi ko kadan a ransa Shima ya Saka qafa ya shuro Mam din qasa take yafara gangarowa idonsa na qarasa tsiyayewa Cikin tsananin azaba.

Daidai Nan Jamaal ya fara shigowa gidan kafin Dad Omar sedai kusan a tare suka iso Cikin palon suka hade da Siddeeq Dake dauke da Mum Bata Wani dogo motsi.

Hannuwan Jamaal ya miqa zai karbeta daidai Nan Omar ma ya miqa nasa hannuwan Siddeeq ya miqawa Omar din ita Suna juyawa zuwa mota.

Cikin gaggawa duka motacin kusan guda uku suka fice zuwa asibitin gabaki dayansu.

Suna fita gidan Siyam Data biyo hanyar gidan itama ta iso gidan tana shigowa Cikin saa Babu kowa San sun manta da Mam din Dake yashe Cikin jini Yana kokarin tashi zuciyarsa na kokarin bugawa da baqin Ciki me tsananin gaske.

Kansa ta tsaya ahankali tareda zuba masa Idanuwanta da sukai Wani irin Jan gaske hannuwanta na rawa ta dago syringe din dayake hannunta na alluran dabbobi me karfin gaske ta kalla tareda kallansa.

Shima Cikin tsananin azaba da rashin Gani sosai da idonsa daya ya dago ya kalleta Yakuma tabbatarda Siyam dince sedai Bai iya cewa komaiba.

Daga syringe din tayi tareda saka masa a wuya ta tsiyaye masa ruwan hawayen masu zafin gaske na tsiyayo mata.

Wata mummunan fizga yayi tareda fizgota ya shaqe a tsakiyar hannunsa Yana Shure Shure itama fizge fizgen tafara a jikinsa sbd shaqura.

Daidai nan siddeeq da maman fadeela da Ayesha suka dawo Cikin gidan Suna Gani da gudu siddeeq ya iso ya cire Siyam daga jikin Mam din sedai kaman Babu Rai a jikinta Dan haka ya dauketa da gdu ya fice
Sbd tsoro su Maman fadeela ma binsa sukai daidai Nan Ahmed ya shigo gidan Shima da jamian tsaron da take suka kwashe Mam din sedai jinin dayake fiddawa daga bakinsa da hancinsa ya Saka dole asibitis
Shima aka wuce dashi sbd yanayinsa ba kyan Gani.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
141
Bayan barinsu gidan Jamaal Kai tsaye asibitin jdens aka nufa da ita Omar zuciyarsa kaman zata fashe sedai shiru Bai iya cewa komaiba bayan kallan fuskan Aleena din datai tsananin laushi.

Jamaal ma dayake tuqin tasa motar Jin yayi kaman zuciyarsa zatai bindiga sbd tsananin zafi da tafasan datakeyi.

Su babbah ma zagine kala kala yake jifan Mam dasu Yana tsinewa rayuwarsa gabaki dayanta tareda tausayin Dr Aleena Yana Kuma Jin Dan sassaucin abinda yakeji sbd hankadosa da yayi ta benen Yana fatar kansa ya fashe ko dayan idon ya tsiyaye.

Hafiz dai baice komaiba sbd damuwa da tashin hankalin abinda yake faruwa din.

Siddeeq ma Kai tsaye asibitin jdens din ya nufa sedai kafin su isa Siyam tayi Wani irin Nisan da hankalinsa yayi mugun tashi.

Mam ma mummunan hali yake cikinsa kafin a isa asibitin take jikinsa ya Dena Aiki sbd alluran da Akai masa hakama wata azabane da ita yanaji tana quna jininsa kaman ana yanka Naman jikinsa Amma Kuma Bai iya ko motsa yatsansa daya hakama idonsa daya dabai tsiyayeba baya Gani sosai sbd tsananin azabar dayake Ciki.

Duk azabar dayake Ciki radadin da zuciyarsa take Ciki na abinda 'dansa na cikinsa da matarsa sukai masa tareda Omar shine Ciwo mafi zafi dayake ji Dan haka wasu hawayen azaba ne suke gangarowa gefen Idanuwansa.


Dukkaninsu asibitin jigum jigum sukai bayan an karba Mum zuwa Ciki da Siyam ma dasuka iso daga baya.

Omar da Jamaal har lokacin Babu wanda ya furta kalma ko daya bayan tsit da sukai kowanne da abinda zuciyarsa take Ciki wanda baya faduwa Dan haka kowa gurin ya sake shiga damuwa da yin shiru Suna jiran tsammani da fatan komai yaje daidai Dan basa fatan daga Mum din har Siyam su rasa ko daya.


Ameenatou na gida batasan meyake faruwa ba itada Ashley dasu Mum Nur Dan hakane suke fama da tasa gagarumar matsalar Cikin rashin madafa.

Baa dauki lokaci doctors din dasuke kan Dr Aleena kusan guda biyar sai kace wadda tayi mummunan accident duk da ba Wani rauni bane kawai dai shaqar da yayi mata ne ya galabaitar da ita.

Doctors din na fitowa bayani sukaiwa se Omar akan Babu matsalan komai gameda Dr Aleena bayan galabaita datai na toshewan numfashin Amma inshallah komai ya dawo daidai.

Siyam ce dai itama tana tsananin hali sbd daman ba lafiyayya bace sunyi mamakin samun lafiyanta lokaci daya sai Kuma mummunan shaqar da Akai mata data Riga takusa rabata da ranta Dan haka gaba daya lungs dinta ma sunqi karban numfashi anata kokarin dawo da numfashin dasu oxygen da dubarunsu na qwararri.

Ajiyar zuciya Jamaal da Dad Omar suka sauke a boye batareda sautin kowannensu ya fito ba.

Sai alokacin kowa ya sauke tasa a bayyane Suna Jin tashin hankalinsu ya fada.

Jamaal ne ya miqe ahankali Cikin nutsuwa ya nufi dakin siddeeq ya Bude masa ya shige fuskansa Babu walwala ko kadan sai Idanuwansa da sukai Wani mummunan ja.

Yana shiga mum din na Bude Idanuwanta Cikin nutsuwa da sanyi ta zuba masa tausayinsa Mai tsananin gaske Yana rufeta koina sbd tasan tsananin radadin dayake Ciki gameda Mam wanda yake mahaifinsa Kuma bazai iya masa komaiba daya dangaci zagewa ya masa mummunan wulaqanci Dan hakan ne zuciyarsa take cikin Wani irin suya da qunci me qarfin gaske.

Takowa yayi ahankali ya iso gareta
Kafin ya iso ta tashi zaune ahankali tana share hawayenta da suka gangaro ahankali
Zaunawa yayi ahankali gefenta ya Bude hannuwansa Cikin sanyi ta shige jikinsa ya rungumeta Yana Dan qanqameta Cikin sanyi da tsananin kaunarta.

Itama lafewa tayi jikinsa Cikin sanyi da tsananin kaunarsa ta motsa bakinta zatai magana ya tareta ta hanyar sake rungumeta bayan yayi kissing tsakiyar kanta ahankali Yana Bude Baki da wata shaqaqqiyar murya Mai tsananin sanyi yace

"I love you Mum,
I love you,.I love you"

"I love you too son" tafada itama tana sake lafewa jikinsa.

Sun jima a hakan kafin aka Bude kofar dakin ya dago jajayen Idanuwansa yaga su siddeeq ne da babbah sai Hafiz da uncle Ahmed daya iso Shima sai Maman fadeela da Ayesha dukkaninsu Cikin kulawa da kauna suke mata sannu tana amsawa batareda ta dago jikin Jamaal dinba.

Sama sama suka jajanta kafin suka fito Dan tafiya gida sbd doctora sunce ba zata kwana ba tana sake hutawa gida zaa koma da ita sai zuwa dare ko gobe su sake zuwa gidan a dubata.

Suna fitowa Hafiz da babbah da maman fadeela da Ayesha suka fice daga asibitin a motar Hafiz.

Fara biyawa gida yayi ya ajiyesu har lokacin Ayesha bata Cikin cikakkiyar hayyacinta sbd tsoro da tashin hankali da mummunan firgicin zuciya datake Ciki na abinda duka yafaru da abinda taji akan mutuwar Mum dinta Dan haka Suna isa gidan dakinta ta shige ta rufe tareda zubewa qasa ta fasa Wani irin Kuka Mai tsima zuciya da tausayi tana tinanin ta tabbata kenan ita batada kowa yanzu sbd Mam ne take tinanin Dad dinta da zaici gaba da zama mahaifi kuma ubanta Amma yanzu tsoron Jin sunansa ma da akeyi.



Bayan barin kowa asibitin sai alokacin Dad Omar ya sauke ajiyan zuciya Mai Dan taqaitaccen sauti Yana miqewa ya nufi dakin Kai tsaye Shima ya shiga Cikin nutsuwa da kamewa kaman ba Cikin tashin hankali ya fito ba.

JAMAAL da har lokacin Idanuwansa Basu dawo daidaiba sbd zuciyarsa datake tsananin tafasa da Kuna har lokacin ya dago ya Kalli Dad Omar din wanda Shima Idanuwansa suke sauye Cikin yayi kokarin daidaitasu da kansa.

Janye Mum din yayi daga jikinsa Yana miqewa tsaye bayan ya sake kissing gefen fuskanta ya juya ya fice
Siddeeq ma bayansa ya bi uncle Ahmed ma sannu yayi mata tareda juyawa ya five daga dakin bayan yaja kofar aka bar su iya su biyun Cikin dakin.


Shiru dakin yaji Babu wanda ya motsa bare magana.

Itace ta fara dagowa ahankali ta kallesa Taga Idanuwansa kafe suke akanta Yana mata Wani irin kallo zuciyarsa na tinanin da Mam yayi nasarar illatata Yaya zasuyi shi da Jamaal??

Takowa yayi ahankali tareda isowa har inda take tukuna ya zauna inda Jamaal ya tashi tareda miqa mata hannunsa Yana kallan Cikin tsakiyar Idanuwanta data kasa kallansa sedai ta dago hannunta da yayi mata Dan nauyi ta miqa masa tana Dan rintse Idanuwanta.

Kama hannun nata yayi da nasa tafin hannuwansu na haduwa a tare suka sauke Wani ajiyan zuciyan shekarun da suka debo tin kuruciya na jira da fatan wannan ranar.

Dagowa tayi ahankali ta kallesa Shima ita ya zubawa Idanuwansa da jan da sukai har Lokacin Bai washe ba sbd radadin dayake cin zuciyarsa.

Tasan zuciyarsa tafasa takeyi kaman ta 'danta akan duka abinda Akai mata Dan haka ahankali ta daga hannunta daya wanda baya Cikin nasa ta Dora a gefen fuskansa ahankali ta shafa Cikin sanyi da nutsuwa da tsananin kulawa da so da rarrashi tana sauke hawayen da zuciyarta ta kasa riqewa sbd feelings da yawa.

Rintse Idanuwansa yayi Shima ahankali tareda sake damqe hannunta dayake Cikin nasa Yana Jin zuciyarsa na sanyaya ya Bude Ido ya sake zuba mata su zaiyi magana ta Dora hannunta ahankali kan lips dinsa tana kallan farar lafiyayyar fuskansa data manyanta sedai kyansa da ajinsa da lafiyan fatarsa tin ta kuruciya haryanzu Suna Nan musamman yanzu da asalin Hutu da kwanciyar hankali ne da Arzikin gaske suka ratsasa komai nasa kaman ma yafi kyau a yanzu.

Cikin sanyi da nutsuwa tareda son tausarsa ta Bude Baki da rashin kuzari sosai tace

"It's okay,am okay inshallah Babu komai,banajin komai yanzu."

Ajiyar zuciya ya sauke me sanyi Yana Dora hannunsa kan hannunta dayake kokarin sauka daga fuskansa ya maidasa datareda Dora nasa akan nata din Yana sake sauke ajiyan zuciya Cikin nutsuwa da kulawa tareda zafin zuciyarsa daya ragu ya furta

"Thank you for being okay"

Jin tayi zuciyarta na narkewa da kalmansa Dan haka Idanuwanta suka ciko da hawaye sedai Bai bari sun saukoba ya janyota jikinsa ahankali ya shigar da ita tareda rungumeta Yana sauke ajiyan zuciyan data itama hawayenta suka sauko tana sake lafewa jikinsa.

Shiru sukai tsawon mintina ahakan kafin ta Bude Baki Cikin sanyi da nutsuwa tafara fada

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login