Showing 21001 words to 24000 words out of 261814 words
ya fita hayyacinsa Babu abinda yakeji yake Gani bayan Kai kansa gida da abinda Amina ta Haifa wadda haryanxu Bai tsaya ya duba me ta Haifa din ba hakama baisan sanin a raye baby take ko mace.
Tafiya sukayi sosai a cikin duhu harsuka fice daga anguwar gaba Daya batareda angansu ba daga Nan suka samu inda suka shige suka boye.
Sai lokacin ya dago babyn daga dunqular da yayi mata yana Jin motsawarta Dan tinda tayi kukan bayan haihuwarta Bata sake kuka ba tayi shiru.
Suna cikin wani mugun tsohon shagon Akai asuba aka fito.
Ana fitowa sallah suka samu abin Hawa tin akwai duhu suka nufi Tasha.
Suna Isa toilet din tashar shine yabarwa Maryama yar yashiga bayan gidan cikin tashar ya wanke jikinsa tas hadda kayansa dasuke kaca kaca da jini ya wanke ya fito kaman zai qame sbd sanyi Amma haka ya bawa kayan mintina suka Dan sha iska ya mayar jikinsa yake ya karbi babyn itama take ta wanke nata jikin ta dawo suka fara rarraba idon yanda zasuyi.
Koda gari yayi haske sosai tini labarin gaborar gidan Alh Omar jeden tafara Dan yawo sedai baa fidda maganar kisan da akaiwa matarsa da Amintaccensa Daya Aron ba sosai.
Kawu da kansa ya ari waya a tashar ya kira numbern Dadah ya aika Hafiz shagon POS da kudi masu yawa aka Aiko masa a acct din me POS Daya samu Nan Tasha.
Har kudinsa harna Maryama ya biya suka kamo hanyar gombe da jaririyar yarinyarda Allah ya taimakesu batai musu kuka ba hakama ruwan Roba kadai suketa Bata tana jikin Maryama sbd kaucewa zargi har suka kwana suka wuni a hanya suka iso.
Suna sauka Mai tsaye gida suka nufa.
Kallo Daya dadah tayi musu hankalinta yayi mummunan tashi sbd ganinsu da jinjira.
Da farko babba kasa magana yayi sbd zuciyarsa datai wani irin bushewa da nauyin gaske hakama Bai fita daga shock ba har lokacin Amma ya hakanan ya Bude Baki daqyar ya hada kalaman cewa 'yar Amina ce ta shiryata tukuna sbd tin daga Lagos har gombe zindir babyn take dunqule a zanin gadon dakin mahaifiyarta.
Rawa jikin dadah ya dauka kanta Yana Neman juyawa ta Bude Baki zatai magana Maryama ta fashe Da wani irin kuka mai karfin gaske tana kasa magana itama sbd sai alokacin ta samu kukan yazo mata.
Ita kanta Dadah fashewa tayi da kukan batareda sunce mata komaiba jikinta ya Bata tabbas Babu Amina,
Amina ta tafi gurin haihuwa kenan.
Kukan dadah ya Saka babba Dake daki ya idar da sallah fashewa da wani irin kuka Mai qarfi da tsananin radadi me zafin gaske zuciyarsa na yanka.
Tsit gidan yayi sbd kukan da kowannensu keyi me ciwo da qunci.
Dadah na kuka tana yiwa babyn wanka da ruwan zafi masu tsafta sai alokacin babyn ke fasa kuka sosai ba kakkautawa tanayi.
Tana gama mata ta dauko zaninta sabo me tsafta ta nadeta.
Babbah sosai yayi kukan da Saida yakoma Yana bawa dadah da Maryam da yayansa tsoro sosai Dan Babu Wanda ya taba Ganin ko hawayen Babbah bare kukansa hakama kowa yasan soyayyar Amina a ransa ko yayansa bayawa wannan soyayyar.
Fitowa yayi bayan Maryama taci abinci ya Bata kudi me Dan yawa ya sallameta akan itama ta kama hanyar garinsu ta tafi Daman sbd bazai yiyu tafiyarsa da jinjira tin daga Lagos bane ya sakashi tahowa da ita.
Ita kanta Maryama din matse take da Isa garinsu jos Dan haka take ta nufi Tasha komai dare gwara ta Isa nata ahalin itama.
Bayan tafiyar Maryama cikin tsananin tashin hankali da kuka Mai radadi babbah ke sanar da mutuwar da aminatu tayi ta kisan gilla jininta na kwarara a hannuwansa da jikinsa Amma Dan karfin hali Saida ta haife cikin jikinta ta rasa tata rayuwar.
Duk abinda yaketa dannewa tin daga lokacinda ya tsaya gaban gawar Amina Jin yayi Yana yunkuro masa take ya fara amai Yana wani irin jijjiga take ya rikicewa Dadah.
Rawa jikin dadah ya dauka itama kuka takeyi haka su hafizu da Basu wuce shekaru goma Sha biyu ba zuwa Sha hudu suka kama mata shi sukai Kai daki sedai jiki Kam ba sauki.
Mota taje ta samo cikin tashin hankali suka kwashesa zuwa asibiti take akai emergency dashi zuciyarsa ta kumbura komai zai iya faruwa.
Barinsu Hafiz asibiti dadah tayi ta nufi kasuwa ta suyiwa babyn kayan sakawa guda uku da man shafawa Se Madara ta dawo gida ta sauko da ita daga bayanta ta shiryata ta bata Madara a fida kaman yanda inda ta siyo suka nuna mata tareda koya mata.
Tana gama Bata ta sake goyata ta koma asibiti.
Isarta asibiti tararda jikinsa ya sake rikicewa Dan haka itada yaran duka kuka sukeyi sosai cikin mummunan tashin hankali.
******
Acan Lagos Koda gari ya waye Omar ya fita hayyacinsa sosai ga uwa Uba mutuwar Amina data jijjigasa sosai ta taba har cikin kansa,
Jamian tsaro sun fidda gawawwakin da tini suka soye sosai Babu dadin kalla Akai jana'izansu hadda Omar din Wanda ko tsayuwa Baya iyawa a wheelchair yake komai nasa ya tsaya.
Babban tashin hankalin Daya sake girgizasa shine Nur Dake Poland ankira itama tana asibiti tsakanin Rai da mutuwa baa San meya sameta ba Amma kaman taci ko ta shaqa abinda yakeda mummunan poison dan haka tana asibiti tsakanin Rai da mutuwa.
Wannan mummunan labarin Bai wani girgiza Omar ba saima sake Sakasa akan tinanin abinda yaketa yaqi da zuciyarsa da tinaninsa ya kasa yadda wato rayuwarsa Yan uwansa ke so kome? Shin da gaske sunada Saka hannu a lamarin dayake bibiyar rayuwarsa ruwa jallo ko tinaninsa ne ke Neman lalacewa yake zargin Yan uwansa?
Idan haka ne abinda aka haifar masa tana cikin mummunan hadarin rayuwa,
Tayaya zai Bata kariyarda Babu Wanda zai tabata sbd dukiyar duniya?
Kozai rasa komai bazai taba barin wani abu ya samu 'yarsa daya tak ba da Aminarsa ta haifar masa.
Wasu Hawaye masu dumin gaske ne suka gangaro masa Yana Jin nauyi da radadin zuciya kansa na nauyi me karfi sbd Bai taba tinanin rayuwarsa zata mutu a dare Daya haka ba harma data 'yarsa da bataji ba Bata Gani ba itada mahaifiyarta data rasu batareda sanin me tayi aka kashetan ba.,
Bai taba kawo tinanin zai samu arzikin samun haihuwa ba Amma ya nesanta kansa da abinda ya samu dan masifar daudar duniya wato kudi ba,
Tayaya zaiyi rayuwa da 'yarsa idan har Yana riqe da wannan dukiyar yasan har abada dashi da ita bazasu taba zama cikin tsaro ba Dan haka bazai bari asan ma da ita a duniyar ba bare kaiwa rayuwarta hari.
Idan har da gaske Yan uwansa ne masu bibiyar rayuwarsa kaman ta yan
Zuciyarsa kusan kasa dauka tayi take Shima ya samu attack aka sake komawa asibiti dashi cikin gaggawa.
A Daren aka Ahmed yabi jirgi ya Isa gombe ya tararda halinda babba yake ciki ya tausaya musu sosai hakama ya tausayawa Babyn fiyeda kowa a halin yanzu sbd zata taso batareda tasan mahaifinta ba bare waye shi indai har tsawon lokacinda komai zai dawo daidai.
#MAMUH#
#MAM#LAM#OMAR#SEELAHS
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#HAROON SEELAH
#LOVE
#CRAZINESS
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU SEELAH
ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabook@Mamuhgee
#ZafafaBiyar
15
KISSA TRAINING CLASS📢
MASU SO SU KOYI KISSA🎊
MASU SO SU IYA KISSA🎊
MASU SO SU SAN KAN KISSA🎊
MASU SO SU ZAMA HATSABIBAI AKAN KISSA🎊
GANE IDAN AN SHIRYA MIKI KISSA🎊
KISSAN IYA KWACE DANGIN MIJI🎊
KISSAN IYA KWACE MIJI🎊
BA BOKA BA MALAM BAKUMA MAGANI KAWAI KISSA KADAI🎊
ZOKI SHIGA AJIN KISSA DA NAIRA DUBU KACAL!!!
5DAYS TRAINING CLASS WANDA BABU YANDA ZA’AYI KIYI TRAINING DIN NAN BAKI IYA KISSA DA KISISINA BA.
KISSA SHİNE BABBAN MAKAMIN MATAR AURE❤️
ZOKI SHIGA KAFIN KISHIYARKI TARIGAKI SHIGA💃🥳
KISSA CLASS PAYMENT IS 1k
GUESS WHAT 5 LUCKY ACTIVE MEMBERS ZASU CI NAIRA DUBU ASHIRIN EACH💃💃💃 20k EACH
ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN SET NA TURAREN WUTA BY RUKY💃💃
ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN KAYAN MATA FROM HONEYDROPS KAYAN MATA💃💃
JOIN YANZU YOU MIGHT BE THE LUCKY WINNER
CHAT ME UP DON SHIGA WANNAN KISSA TRAINING CLASS
07012181461
**************
Shi kansa Ahmed wani tsananin kaunar yarinyar yakejin Yana shigarsa har cikin Rai da jininsa,
Jinin Omar abin so da girmamawa ne garesa,
Ahalin Mr Jaden Koda Baya duniya abin kauna ne garesa,
Son duk wani ahali na Mr Jaden tamkar ya tabbata ne garesu shi da Aron Wanda ya tafi Shima yabarsa,
Kaman yanda Aron ya Bada rayuwarsa Dan Bada kariya ga Omar tabbas Shima bazai taba kasa a gwiwansa ba gurin bawa Omar da abinda ya Haifa kariya ba,
Sedai kaman yanda Omar ya yanke shine idan har sunason Bata kariyar da zatai rayuwa a sake batareda tsoro ko fuskantar hadari da barazana ga rayuwarta data Wanda take hannunsu shine barinta a hannun Babbah tareda yin nesa da ita tareda Yanke alaqa dasu gaba Daya har sai ranarda komai ya fito fili ya tabbatarda abinda yake zargi akansu tinda Babu hujjoji manya a hannunsa.,
Wannan shine babban gatan da zaiyiwa 'yarsa ya Bata kariya shine Yanke alaqa dasu batareda duniya tasan shine ya haifeta ba,
Batareda duniyama tasan yanada 'yar da zata gajesa ba.
Rungume babyn a jikinsa Ahmed yayi tareda Jin kaman ya tafi da ita ga mahaifinta da zuciyarsa ke cikin tsananin qunci me nauyin gaske akan rashin mahaifiyarta da ita,
Wayarsa ya fiddo ahankali ya Saka Kiran Amintaccen Daya baro a asibitin gurin Omar da securities masu tsananin gaske yace ya bawa Omar wayar.
Duk da Yana cikin wani irin mawuyacin hali ya amsa wayar sbd sanin me Hakan ke nufi.
Ahankali cikin sauti mara karfi da sanyi da nutsuwa yakewa yarsa huduba ta cikin wayar da Ahmed ya Kai kunnenta sautin muryar mahaifinta na shiga kunnan ahankali.
Da sunan mahaifiyarta ya kirata bayan hudubar wato AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH.
Yana gamawa Hawaye masu radadin gaske suka sauko daga idanuwansa daidai Nan ya kashe wayar tareda lumshe idanuwansa yanajin bazai taba warkewa daga wannan quncin baqin cikin da aka jefa rayuwarsa ba kaman yanda bazai taba yafewa duk Wanda yakeda Saka hannu a cikin duk kowace kisar da akaiwa Yan uwa da iyayensa harma da matarsa da 'yarsa da aka tilasta masa rabuwa da ita ba Koda kuwa su Lameenun ne da gaske.
Ahmed baicewa Dadah komai ba Saida ya miqa mata AMEENATOU kafin ya sauke jakar dake rataye a jikinsa ya miqa mata ya Bude bakinsa da yayi nauyi ya sanar da ita maganar data qamar da ita daga tsayen tareda dorawa da kalmar
"Allah ya Raya AMEENATOU"
tana kallonsa kaman gunki harya bacewa ganinta ya fice daga asibitin gaba Daya.
Yana fita Kai tsaye a ranar ya juya ya koma sbd Bai yadda da kowa a tareda Omar ba yanzu idan ba kansa ba.
Ko da ya Isa cikin dare Kai tsaye asibitin ya nufa ya tadda jikin na Omar ya sake rikicewa hakama ga babban mamakinsa Alh Lameenu seelah harma da Mam seelah ya diro qasar suna asibitin harma da iyalansu cikin mummunan tashin hankalin da damuwa me tsananin gaske data Saka zuciyar Omar kasa dauka take yaji zuciyarsa na Neman fashewa da yanda suke nuna baqin cikinsu akan abinda ya faru da damuwa shiyasa jikinsa ya rikice.
Abinda yake sake taso masa yaji kansa na Neman bugawa shine sauyin securities da ko yaushe akeyi masa Yana daukan tsananin kulawa ne Ashe na daukan ransa ne.
Kaman yanda Basu nuna komai na haka ya danne nasa baqin cikin yana fatan samun lafiyarsa data Nur tukuna yasan ta yanda zai fara bincike akansu Dan kuwa mutuwar kasim data aminatu itace mutuwa mafi zafi dasukaiwa Yan uwansa.
Ahmed ma Sam Bai nuna komai a fuska ba saima Shirin barin kasar a take Daya fara yiwa Omar Dan ko zasuyi bincike bazasuyisa Omar na kusa dasu ba Dan akwai hadari me girma tattare da Hakan,
Hakama idan a hukuma zasu miqa zancen meye hujja ko evidence nasu Kuma maganace akeyi ta cikin gida me duniya zata fada akan Omar idan Kai tsaye ya fito ya fada Yana zargin Yan uwansa na jini akan kisar matarsa da Yan uwansa a Baya batareda yanada hujja ba.
Ahmed Bai fadawa kowa kasar zasu bari ba shi kadai ya gama shirye shiryen komai hakama washe gari dukkanin abokan kasuwancin Omar take ya hada meeting na gaggawa dasu ya sanar dasu barin Omar kasar kwata kwata Dan haka dole a nada sabon president a kamfaninsa.
Ta bangaren kadarorinsa kuwa duk masu kulawa dasu ya qara musu tsaro da ma'aikata.
Su mam irin kulawan da suke bawa Dan uwansu tareda tattalawa yasa Shima duk da baida lafiya sosai yake nuna Jin dadinsa Yana jinjinawa kaunar da suke masa sukuma Hakan na sake musu dadi sosai ba qaramin tashin hankali suke ciki ba na Lameenu dayace kaman Omar yaso ganesa Dan haka suke ta bibiyar Omar din da kulawa me tsananin gaske Dan su Gano idan ya fahimci wani abin Amma basuga alamar Hakan ba dan sosai yake nuna musu Jin dadinsa akan kulawansu da kaunar junansu na asalin jinin Seelahs.
Basu San da tafiyar ba sai ranarda su Omar din zasu wuce ya sanar dasu zai koma Poland sbd jinyar kansa da Nur da har lokacin take kwance ba sauki.
Kallan juna sukai a sace zufa na Dan jiqa Alh Lameenu ta cikin tsadaddiyar shaddar Dake jikinsa kansa ya Dan Sara Dan kuwa idan har Omar ya tafi me Akai kenan?
Su da suke fatan daga asibitin Nan sai barzahu sbd sun gama kammala komai a asibitin mutuwar tsafta zeyi irin tsarin mamman seelah,
Banbanci Aikin mamman da lameenu shine shi mamman Baya aikin gilla sbd ya tsani Bata jikinsa ko hannuwansa da jinin Wanda ya kawar,
Koyaushe yafison neat aikin da bama zaa San wani ne yayisa ba,
Zai aikaka batareda ko kadan ansan wani ne yayi Hakan ba shiyasa duka ayyukansa dayayi da kansa suke neat ba zargi ba hukuma ba komai,
Ko a qasar turawa dasukeda bincike aikinsa neat ne,
Tin daga kan sirikinsa mahaifin Dr Aleena har sirikarsa da Mr Jaden babu Wanda zai taba kawo tinanin kisa ce ba mutuwar Allah ba Dan haka Babu wani bincike Daya hau kan mutuwarsu komai nasa a natse hankali kwance yake yinsa shiyasa ya masifar iya takunsa ko a gurin mutane anfi ganin girmansa da mutuncinsa ake masifar girmmamasa Dan ya iya Jan zarensa cikin aji da dubara.
Sabanin Alh Lameenu da shi Kai tsaye yakeyin Abu Babu kwana kwana Babu sauki ba sassauci idan zaiyi aiki da kansa na danyar jini yakeyi Dan kuwa shi jini ne zaa zubar ba Imani ba tausayi bare gudun abin zaije ya dawo shiyasa ma ya buqaci ko yanzu yayi aikin Omar da kansa sbd tabbatarda matsalarsu tazo karshe yasan shine ya kawar da ita matsalan da kansa abinda yake zuciyarsa na shekaru ya fada masa yaji sanyi.
Maganar tafiyar Omar ta girgizasu musamman mamman da yanzu ne yake buqatan daukaka kansa sbd yayansa dasuke gab da Isa riqon dukiyar mahaifinsu su zama matasan da Suma zaa ringa ambatar sunansu da mutuntawa a matsayin yayan Alh Mam seelah,
Hakama babban fargabar Mam itace Omar na komawa Poland 'dansa dayake jiran ya gama karatunsa ya dawo dashi hannunsa Hakan bazata yiyuba sbd matiqar Omar da Mum dinsa na guri Daya Jamaal bazai taba dawowa Nigeria gurinsa ba shikuwa yanzu Yama fi Jin tsananin so da kaunar Jamaal a tareda shi fiyeda Haroon Dake tareda shi sbd Jamaal Dake nesa yafi shiga ransa sabanin Haroon da kullum suna tare.
Lameenu kuwa shi a yanzu yafi buqatan rayuwar Omar din fiyeda dukiyar tasa,
Idan Omar yabar duniya shine zaiji ya samu nutsuwa sbd ya kasa yadda da Omar Bai ganesa ba yaqi nunawa ne kawai Dan haka shi yanzu asirinsa baa rufe yake ba matiqar Omar na duniya gashi Yanxu Yana maganar yabar inda suke ganin duk wani motsinsa zai tafi inda basa ganinsa Dan haka komai zai iya faruwa Dan haka hankalinsu su dukan baa kwance yake ba da tafiyar.
Ga babban mamakinsu da shock dinsu kafin suyi wani yunkurin rarrashinsa su hanasa tafiyar a ranar ma jirginsu zai daga Ahmed Babu Bata lokaci ya buqaci securities aka rakasu har airport suka daga.
Su Mam Basu sake shiga tashin hankali da firgici ba Saida suka samu tabbacin ba Poland Omar ya koma ba Nur ma tini aka bar Poland din da ita Ashe Kuma daga Dr Aleena har Jamaal Babu Wanda yasan kasar da suka koma Dan Ahmed baibar kowace irin clue ta inda ma suka tattara suka koma din ba sbd Yana buqatan lafiyar Omar da Nur ayanzu fiyeda komai da nutsuwa da samun Kwanciyar hankalisu su dawo daidai tukuna kafin su fuskanci komai.
Kaman bacewar hayaqin Daya tashi sama haka suka bacewa kowa bat Babu labarinsu,
Duk wainda suke communicating dasu Yan amanar asalinsu ne da ko zasu mutu bazaka ji sirrin Omar a bakinsu ba.
Shi kansa Jamaal hankalinsa tashi yayi sosai da Hakan sedai mum dinsa ta kwantar masa da hankali tareda basa tabbacin duk inda Omar yake ya kebance kansa ne Dan bawa kansa kariya da damar samun lafiya tukuna duba da abinda ya samu iyalinsa a lokaci Daya.
Wanna ya Saka hankalin Jamaal Kwanciya Badan ya Dena binciken inda Dad Omar din yake ba.
Su Mam kuwa tini hankali ya tashi musamman da suna zaune cikin damuwa da tsananta binciken akan Neman Omar da kwata kwata ya Yanke kansa daga kowa hatta su duk alaqa da kusancinsu suna matsayin Yan uwansa Bai nemesu ba ya datse hadda su kenan Hakan ya tabbatarda Kila yasan wani abun gameda su kenan ko me?
#MAMUH#
#MAM#LAM#OMAR#SEELAHS
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#LOVE
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH
#ROM
ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku