Showing 60001 words to 63000 words out of 261814 words
illar.
Duk tsananin halin dayake ciki kallan Dad dinsa yayi har lokacin yanajin raunin batawa su Dad din Rai dayayi da asarar da shi kansa baisan ta inda zai fara gyara ba.
Rokonsa gafara da sake basa Dama shine abi farko Daya furta Yana rintse idanuwansa.
numfashi Dad din ya sauke tareda Gyara zamansa Yana kallansa cikin nutsuwa yace
"Zan sake baka Daman karshen Amma ba iya akan aikin kadai ba,
Zan nema Maka auren Ameenatou Amma sai idan ka cika alkawarinka ka gyara mummunan Barna da Tsaka me wuyan daka Saka SEELAHs gaba Dayanta aciki idan ba Hakan ba ka manta da maganar aurenta Dan kuwa har abada bazaka auretaba idan ba Hakan ne ya faru ba"
Rintse idanuwansa yayi hawayen ciki masu dumi suna gangarowa ya gyada kansa cikin wani irin sanyin jikin da mutuwar jikin batareda ya iya cewa komaiba sai tsananin tsoro da shakkan Dayake mamayesa.
Dad Lameenu da Baice komaiba gyara zama yayi Yana kallan Haroon din cikin nutsuwa Shima ya Bude Baki yace
"Haroon nayi Maka alkawarin bazamu bar garin Nan ba ayau sai munje munyi gaisuwar iyaye da iyayenta sbd Neman Maka aurenta idan har zaka nutsuwa ka fuskanci nauyin dayake kanka sbd Kaine kaidai zaka iya gyara wannan Barnar data riskemu sbd kafi kowa sanin halinda muke Neman fadawa idan bamu farfado ba.
Tinda suke magana idanuwansa a rufe suka Hawaye masu zafi na gangarowa a acikinsu Saida Dad Lameenu yayi masa alkawarin nema masa auren ya Bude idanuwan ahankali ya kallesa Yana sauke Kai kasa.
Dad dinsa ma Jin yayi yayi Naam da Hakan Dan shine maslaharsu ayanzu kada su maimaita kuskuren Baya gwara su nema masa auren su juyasa akan abinda sukeso tinda zai iya komai akanta din.
Duk yanda wani zai samu Daman sanin matsalar ciwon Haroon Saida Dad ya tabbatarda Bata fita ba hatta siddeeq Bai bari likitocin sun bari yasan duk wani abinda aka bincika aka Gano ba har suka sake kwana biyu a garin Akai sallamarsa a ranar suka kwasa zuwa Nasarawa Dan Kai gaisuwan Neman auren.
#MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
39
****Su babbah da suka samu labarin zuwan da Dad din zasuyi gaisuwa tini aka gyara koina hatta kofar gidansa Saida aka share har kofar gidan makota aka shirya tsaf Dan tarbonsu da Aminansa guda biyu da zasu tayasa karban gaisuwan.
Dayake ranar su Dad din zasu koma da wuri suka iso guraren karfe daya na Rana Dan haka su Babbah suka tarbesu da girmamawa da mutuntawa sosai har cikin fara isowan gidan babban suka zauna a babbar dadduman da aka shimfida musu me kyau.
Dad Lameenu Dayake amsa gaisuwansu cikin girmamawa da kulawa sosai Shima tareda farin ciki me tsananin da tin anan aka fara farin cikin Samun Sirikai irinsu da duk kudi da matsayinsu sunsan mutuncin mutane da iya mu'amalantarsu.
Babbah Dad Lameenu yayi kallan tsaf Mintina Yana tantance kamannin nasa da son tabbatarda idan shine Wanda yake tinanin shi dinne.
Ganin irin kallan da Alh Lameenu kewa Babbah ya sakashi sai farin ciki yake sake shiga Yana sake musu barka da zuwa kafin ya tambaya jikin Haroon cikin kulawa sosai Yana dorawa da cewa sai anjima su Abdul su shiga dubasa Inshallah.
Abinda ya tarasu suka shiga gabatarwa Babu wani Bata lokaci suka gabatar da kansu da Neman auren Ameenatou da suka zo nemawa dansu Haroon Wanda su Babbah sun sanshi kuma sunsan aikinsa da halayensa daidai gwargwado.
Naam su Babbah sukai kafin suka suka sake gabatar da kansu da shi babban amatsayin mahaifin Ameenatou wadda shine ya haifa abarsa da cikinsa Kuma yayi na'am da Hakan ya Kuma bawa Haroon aurenta.
Farin ciki da hamdala suka ringa miqawa ana sake taya juna murna Dad Lameenu ya cire kudin Neman auren Naira dubu dari biyar ya bayar kafin suka sake miqa godiyarsu har lokacin zuciyar lameenu wani tsalle takeyi cikin rudewa da rikicewa Dan kuwa ya sake tabbatarda Babbah ne suka tana Gani asibiti gurin Omar a lokacinda aka taba Kai masa attack idan Bai mantaba Kuma ya sake dubawa ya tabbata Babbah ne ya Gani Wlh.
Abdul da shine babban yayan Ameenatou Kuma dashi Akai zaman Neman auren Alh Lameenu ya kalla cikin kulawa Yana tambayarsa Aikinsa da karatunsa.
Cikin nutsuwa da ladabi Abdul din ya amsa masa matsayin karatunsa da aikin dayake yi.
Take Alh Lameenun ya nuna raayinsa na Taimkawa yace Abdul din ya hada takardunsa zai Aiko a karba a aika masa Lagos.
Godiya Abdul din yayi su Babbah dasu Alh sabi'u makocin Babbah godiya sukai suna sake nuna Jin dadinsu kafin su Dad suka saki jiki sosai sukai fira da maganganu dasu babban anan ma sukai sallah azahar kafin suka Shirin tafiya su Babbah suka rakosu har waje inda motocinsu da securities dinsu suke suka shiga take aka bar gurin dasu.
Suna barin gurin Dad Lameenu zufan dayake hadawa tin acan yana shanye abinsa a jikinsa ya zari tissue ya goge kafin ya Ciro wayarsa.
Hotunan da BB ya turo musu nasu babban ya Nemo hannuwansa na Dan rawa ya Nemo na Babbah ya zuba masa idanuwansa.
Mam da zuciyarsa kwata kwata Bata cikin dadi Baida energy din tambayar abinda yake faruwa sbd bayajin zai taba barin ya hada zuria dasu Babbah
Ya nema auren ne sbd yana buqatan Haroon din sbd ya Jamaal ya dawo garesa Amma Badan Hakan ba bayajin zai tana yadda ya Kai kansa Neman auren.
Lameenu Daya sake goge zufansa miqewa Mam wayar yayi Yana cewa
"Wannan shine fitilar da zata kaimu ga sanin duk inda dangin matar Omar suke sbd samun Magajinsa"
Kallan wayar Mam yayi kansa na tsananin sarawa da nauyi Amma Jin Abinda Lameenu ya fada ya sakashi cire hannunsa daga goshinsa Daya dafe idanuwansa a lumshe.
Kallan Lameenu din yayi bayan ya Kalli Babbah a wayar Yana jiran bayaninsa.
Cikin nutsuwa lameenu ya tinatar dashi ganin da sukaiwa Babbah a asibiti tareda Omar shekarun Baya.
A saninsu wancan lokacin daga kauyensu Omar yace musu babban yake Amma basusan Menene alaqarsa dashi ba Dan haka dole babba yasan waye yayan matar Omar Kuma bazasu rasa sanin komai ta hanyar Saba Daman a bagiren Neman ko mutum Daya daga kauyen suke amma tsawon shekaru ankasa samu.
Wani sanyayyan sanyi ne ya ciked zuciyar Mam take yaji nauyin zuciyarsa na rayuwa sedai bayajin zasu samu yanda suke so idan suna nesa dasu Babbah din.
Lameenu Dayasan dalilinsa Daman kenan na buqatan daukan Abdul aiki take ya Saka kira yace a tanadarwa Abdul din aiki me kyau da gidan zama a Lagos inda zai dauko iyayensa ya dawo dasu.
*********Su Babbah kuwa A nasa bangaren sunan jeden da Omar yake amfani dashi shine ya hanasa sanin shima Omar din seelahs ne Dan haka farin cikinsu kawai sukeyi.
Da daddare da kansa shi da su Abdul sukaje suka dubo Haroon din Wanda ya danne ya nuna musu karfin hali duk da Yana cikin tsananin tashin hankali da Tsaka me wuya sbd sanin Neman auren bashine aurenba indai Bai cika alkawarin Daya daukanwa Dad dinsaba,
Bayan tafiyarsu da daddare tsananta damuwansa tayi sbd gwara ace baa nema aure ba zai iya runawa ya hakura da Ameenatou Koda zai rasa ransa Dan kawai yabarsu su ta tsira Amma a yanzu da aka nema masa aurenta yasan ba janyewa sedai Kuma irin kaddarar fadila da Dan uwansa yake guje musu.
A cikin Daren siddeeq ya koma Abuja Bai kwana ba Saida ya samu report na komai da akaiwa Haroon ya turawa JEEY Wanda sakonsu ya isar masa a daren daidai lokacinda ya fito wanka daure da towel dinsa gabaki Daya jikinsa wata irin sheqi takeyi kaman Bai taba Shiga rana ba.
Hannunsa yakai ahankali ya dauki wayar Yana ganin report din ya Bude sakon Kai tsaye Yana karantawa.
Tsayar da fararen idanuwansa masu gigita Wanda suka kalla yayi akan report din idanuwan na sauya ahankali zuwa ja zuciyarsa na daukan wani nauyi take.
Shigowan kira ne ya sakashi rintse idanuwan ya budesu ahankali akan sunan Haroon daya bayyana kan screen din wayar.
Iska me dumi ya sake fitarwa daga bakinsa kafin ya daga Kiran batareda yace komaiba ya Dora wayar a kunnensa Wanda yayi daidai da Haroon din na kasa riqe kansa daga zubar da hawayen radadi da kuncin dayake cin zuciyarsa da rubabbiyar rayuwarsa gaba Daya.
Shiru Jamaal din yayi har lokacin Bai furta komaiba sbd wannan shine Karan farko da Dan uwansa ya bayyanar da tsananin kunci da baqin cikin rayuwar dayake ciki garesa,
Bai taba fada musu rayuwar wulaqanta da qasqantar dayakeyi a hannun su Dad ba,
Bai taba barin sun sani ba,
Bai taba nuna musu ba
Ya shanye komai ya hadiyewa kansa baqin ciki da radadin shi kadai Amma ayau dayake cikin tsananin hali ya kasa danne zuciyarsa daga Neman taimakon Dan uwansa Dan idan ya rasa Ameenatou zai iya rasa rayuwarsa gaba Daya batareda yasan rayuwar tasa tana cikin mummunan hadarin tsaka me wuyar da kowane lokaci komai zai iya faruwa ba.
Kasa magana JEEY yayi sbd sautin fitar kukan Dan uwansa dayake tarwatsa zuciyarsa Yana Kona jinin dayake yawo a jikinsa kawai kashe wayar yayi tareda Saka Kiran Siddeeq wadda Kiran na shiga ya daga cikeda girmamawa.
Magana yayi da siddeeq Yana gamawa ya kashe wayar gabaki dayanta tareda jefar da ita.
********Ameenatou gabaki Daya ta daga hankalin mutanen gidan sbd kwanakin Haroon kusan shida bata samun wayarsa Kuma ya Dena fita koina ko Hafiz yace kwata kwata ya dena fitowa aiki,
Yaya Abdul yaje dubosa harso biyu Amma Sam Baya samunsa hakama siddeeq Sam baa samunsa.
Daga hankalinsu Babbah tayi dadah batada aiki saina rarrashinta Hafiz ma kusan sosai suka damu gurin aiki Amma dai Sir siddeeq yace musu Yana hutawa ne sbd rashin lfy da yayi.
Babbah da kansa yaje dubo Haroon din Amma dai kaman duka kwanakin Bai samu ganinsa ba hotel din sunce Yana Abuja.
Ranarda ya cika sati Hafiz na Isa gurin aiki da safe sunfara aiki kenan lafiyayyar sabuwar motar Haroon Daya sauya batareda sun saniba tayi parking bakin site din.
Siddeeq ne ya tuqo motar Dan haka shine ya fara fitowa kafin aka Bude Dayan bangaren Haroon ya fito sanye cikin black Armani's da sunglasses Daya masifar fitarda hasken fatarsa dayake wani irin kyallin Daya Saka dukkanin ma'aikatan gurin ajiye aikinsu suna kallansa sbd kwarjininsa na yau din daban yake Dan duk Wanda yake gurin saida kwarjininsa ya cika idanuwansa hakama hasken Daya Kara a kwanakin Dan hutun Daya samu ya bayyana fiyeda mamaki.
Manyan ma'aikatansu da sauran manyan Dake cikin project din tasowa sukai dukkaninsu suna tahowa gurinsa Dan ganin sauyi sosai a fuskansa na Babu sakewa ko kadan Dan Kuma kamewa.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
40
Takowa yayi ahankali Yana nufar cikin site din Kai tsaye dukkanin sauran abokan aikin na biyo bayansa.
Siddeeq Dake gefensa umbrella yafara kokarin Bude masa Amma ya girgiza Kai ahankali batareda ya juyoba yana kallan site din da gaba Daya ma kusan aikin Daya bari bama ko kusa dashi ne ake kan yiba.
Hafiz Daya aje aikinsa Yana goge hannuwansa ya nufi ruwa ya wanke hannun zai nufi inda su Haroon din suke saiyaga sunzo sun wuce ya inda yake tsaye Yana murmushin Jin dadin ganin Haroon din da lafiyar Daya samu wadda ta sauya musu shi gabaki Daya Dan shi kansa Jin yayi gabansa Yana faduwa da ganinsa tsaban cika ido da wani irin sauyawan da yayi Dan har gashin kansa dayake kwance kaman na mace tsaban gyara ya sake sauya musu shi,
Wucesa sukai batareda Haroon ya Kalli inda yake ba sedai Dan gyada Kai da yakeyi a natse cikin wata irin class da kamewa idan sun gaidasa tareda masa barka da dawowa.
Dukkanin Wanda yake gurin kusan mamakinsu a bayyane yake Dan ganinsa sedai Kuma ganin hadda sauyin rashin sakewa a halayyan nasa ya Sakasu shiga taitayinsu harya shige tent din da Akai masa a site sbd aiki da meeting da sauran manyan Dake cikin project din.
Suna shiga sauran ma'aikatan suka tsaya waje shi Kuma da sauran suka shiga Kai tsaye kujeran zama siddeeq ya gyara masa Yana Bude takardun Dake zube a table din Yana dauko wasu Dake gefe Yana Bude masa Suma Yana fara yimasa bayani shi Kuma Yana bin takardun da idanuwansa dasuke farare tas.
Dukkanin sauran Manyan Dake sauraron bayanin siddeeq dayake karantowa shiru sukai suna sauraron bayanin hakama hancinsu na shaqar iskan gurin Daya sauya gaba Daya da qamshin da suka tabbatarda daga jikin Haroon din yake fitowa Dan haka saiyi sukeyi suna kallansa gashi baice komaiba har lokacin sauraron bayaninsu yakeyi Daya bayan Daya kowa na gabatar da nasa bayanin Wanda yake tabbatarda Taron marasa amfanin da aka Tara ne ya Saka aikin duka ya lalace yaqi zuwa koina.
Sun dauki mintina masu yawa anata gabatar da sabbin bayanan Yana sauraronsu kafin suka gama yayi shiru tsawon lokaci kafin ya karbi takardun hannun siddeeq din Kai tsaye ya zuba su cikin takardun da basuda amfani kwata kwata kafin ya dago idanuwansa ya kallesu yace ya bawa kowa hutun kwana uku suje kawai Nan da 3 days za'a gabatar da sabon tsarin project din.
Shiru sukai tareda dagowa suka kallesa sedai Sabon Haroon seelah suke Gani a gabansu ba Wanda suka sani a Baya ba Dan haka cikin girmamawa suka amsa umarninsa suka fito Daya bayan Daya suna son juyawa su saci kallansa Amma ba dama sbd ba fuska hakama kwata kwata ba alaman wasa yakeyi a zancen.
Suna fita rufe idanuwansa yayi ahankali tareda budesu Yana Dan duba time din Tsadaddiyar Rolex din hannunsa kafin ya kalli siddeeq a taqaice yace
"A sanar da dukkanin sauran ma'aikatan da leburas 3days hutun da zaayi Ina buqatan kwanakin"
Cikin girmamawa da yar sakewa siddeeq yace
"Anan ma kana buqatan a tanadi sabon masaukin ne??
Girgiza Kai yayi sbd kwata kwata bazai iya zama anan din na Abuja zai koma daga can zai ringa zuwa.
Fitowa siddeeq yayi ya Tara duka ma'aikatan ya sanar musu hutun da aka samu na kwana uku take suka fara murna da farin ciki Dan haka suka fara hada ayyukansu Dan kammalawa su tafi gida.
Dawowa ciki siddeeq yake kokarin yi Hafiz ya karaso Yana murmushi da sakewa yace
"Oga siddeeq barka da Rana,
Kasan ko yau da safe Saida nayi Kiran wayar Barr Bata shiga Kuma kaima na kira taka itama Bata shiga ba"
Murmushi siddeeq ya sake Yana kallan Hafiz din yace
"Network ne da Kuma Kila sbd inda kan hanya,
Yasu Babbah da Dadah??
"Duk suna lafiya,mutuniyar dai ce Kam ta Hana tsoffin gidan zaman lafiya akan rashin Jin Barr"
Wani murmushin siddeeq ya sake Yana cewa
"Ai yanayin jikin nasa ne Amma inshallah ai yanzu yaji sauki ayyuka dai ne Kam gasunan sun tarar masa Amma dai nasan zai samu time din zuwa"
Suna cikin maganar ya fito daga ciki Yana Amsa waya a kunnensa cikin nutsuwa har lokacin sunglasses dinsa suna fuskansa.
Qamshinsa ne ya fara sauya iskan gurin Hafiz ya zubawa hannuwansa Dake riqe da wayar dayake amsawa cikin wani turancin da kwata kwata Baya gane kalma ko Daya Daya fada duk da Yana Jin turancin daidai gwargwado,
Yatsun hannuwansa da kaman Basu taba shiga Rana ko taba komai ba yake kalla cikin mamakin tayaya mutum zai sauya acikin kwanaki kalilan haka.
Akan fuskarsa dake wani irin kwarjini me kyau da Asalin kyau da Hutu ya zubawa idanuwansa hakama kunnuwansa na sauraron sautin muryansa Dake magana kamanma wani yaren daban yakejin turancin Dan haka Saiya samu kansa da kasa karasawa gurin Haroon din ya tsaya gurin siddeeq Dayake jansa da zancen harya jasa suka bar gurin Yana cewa su barsa yagama waya tukuna.
Waiwayowa kadan yayi ya sake Satan kallan Haroon din Yana tafiya zuciyarsa na shiga shakkar Anya basuyi gaggawan karban maganar auren Haroon akan Ameenatou ba sbd yafi karfinsu sosai da sosai duk Bai lura da Hakan ba sai yanzu dayake Jin Yama kasa kallan cikin idanuwansa tsabar cika masa nasa dayakeyi.
Fira siddeeq yajasa sosai suna tafiya har suka fice gaba Daya daga site din ya fada masa sunanan tafe daga Nan zasu taho gida.
Sallama sukai Hafiz ya wuce gida Kai tsaye Jin suna Nan tafe Dan yasan yau budurwan gidan zata barsu su huta da rigimar rashinsa ba kunya ba tsoron Allah.
Yana wucewa siddeeq ya dawo har lokacin waya yakeyi sedai baima gama ba ya wuce ya nufi mota ya shige siddeeq ya shiga yaja suka bar gurin.
Budurwan Babbah Jin Haroon ya dawo farin cikine ya cike ranta Dan haka ranar ko islamiya qin zuwa tayi tai wanka ta shirya jiransa gashi har lokacin wayarsa Bata shiga Dan haka ta San bazai kwana ba Saiya taho ya ganta.
Su dadah ma Kwanciya hankalinsu yayi musamman Babbah da farko harya shiga damuwa Dan ya dauka rawa maganar auren take kokarin farawa shiyasa ma da Abdul aka kirasa Lagos maganar aikinsa dayaje Babbah ya Sakasa yayi masa bincike sosai akan Seelahs din Kuma suka samu yabo a gurin mutane da Dan abinda aka sani akansu Dan haka yaji ya sake samun nutsuwa da auren kodan yanda Ameenatou ya kwallafa son Haroon din a ranta.
A ranar Dasu Dad suka koma a washe gari aka buqaci zuwan Abdul Wanda hatta ticket din jirgi Siya masa Akai daga Abuja yabi jirgi zuwa Lagos acan ma cikin mutuntawa da girmamawa aka aika mota ta daukosa daga airport bar masaukinsa saida ya kwana ya wuni ya huta da kyau aka Kaisa SEELAHs CPN acan dinma Koda ya Isa anriga an samar da aikinsa Wanda zai fara a matsayin sabon secretary din Alh Lameenu na musamman.
Yayi godiya yayi farin ciki sosai hakama ya yaba Dan kuwa table dinsa ko a bankin da yayi aikin security sai manager ne yakeda irinsa.
Bai gama shiga shock da sabon farin ciki ba Saida aka basa gurin zaman da zai tattaro iyayensa ya dawo dasu sbd karatun Ameenatou da zata fara a Lagos din da Kuma saukin sha'anin aurenta.
Sosai ya Nuna farin cikinsa da yabawa tareda alkawarin yin duk iya kokarinsa da ladabinsa akan aikin harma da girmamawan gaske.
Saida ya Kara kwana biyu a Lagos din kafin ya dawo tukuna daga baya yayi Shirin komawa su Babbah sai daga baya zasu bisa.
Duk tsananin qiyayyar da sunan Lagos da Babbah Baya ko kaunar a fada hakanan ya danne a cikin ransa ya boye sbd farin cikin Ameenatoun Dake murna sosai akan karatunta da Kuma zama da zatai kusa da Haroon Koda yabar Nasarawan.
Ita