Showing 69001 words to 72000 words out of 261814 words
na kan Ameenatou da yayi magana tayi masa shiru kaman Bata ji ba Kuma kowa yasan ta jisa Daman sun San sai anyi Hakan.
Dadah ce ta Dan rarrasheta tana cewa
"Budurwa bakiji ana Miki ya jiki bane?
Duka fushin bana rashin kiransa da zuwan bane gashinan ai ya taho saiki sauko,
Yi masa hakuri kinji¿
Maganin ta daga duka ta Saka a bakinta tareda binsa da ruwa ta shanye batareda ma tasan tayi Hakan ba sbd fushin Daya taso mata.
Tinda ta fara zazzabin ko ruwa Se ta Saka anbata ko hulan kanta Bata iya sakawa sai an Saka mata sai gashi ta miqe tsaye da kanta ta wuce dakinta tana cewa bacci zatayi.
Hafiz ne ya Bude Baki yace
"Ke meye haka wai?
Inace Wanda ake fushi da ciwon akansa gashinan yazo,Kuma Ashe Zaki iya tashi da kanki kika ringa wahalar Dani da Dadah tin jiya ko bacci na fara saita kirani na kawo mata ruwa Ashe tsaban rashin tausayi ne to Zaki San dawa kikai."
Tana jinsa Bata ce komaiba saima hararan kofar datai tana Jin zafin abinda yayi mata ranar Yana dawo mata.
Dadah murmushi ta sake tana sake tambayarsa nasa jikin ya amsa mata sbd yasan halin mutuniyar sarai basai an tsaya basa hakurin abinda tayin ba,
Abdul ma sake tambayar jikin da aikinsa yayi kafin suka fada firar tafiyansa Lagos gobe zuwa nxt week Kuma su dadah ma zasu taho duk da ba zuwan kenan ba zadai suje suga inda Allah ya Kaisa dasu.
Duk firar dayaketa yi hankalinsa na kan kofan dakinta Amma Sam taqi yadda ko motsi tayi yaji dadi Bare fitowa.
Sallan magrib suka fita sukayo suka dawo gidan tareda Babbah daya masa ya jikin da fadan rashin Kiran tinda koyayane Daya samu ko mintina bibbiyu a wuni ya ware ya kira din zasuji dadi itama me fushin da bataiba.
Gashi tanata fushi da maimaita shariyan dayayi mata.
Hakuri ya bawa Babbah har suka shiga wata firar inda Babbah din ya sanar masa su Alh Lameenu sun kira akan maganar auren sukeson ta taso ayita kusa tinda dai ba amfanin jiran ko tsaiko.
Har cikin ransa yaji farin ciki Yana mamayesa sedai Kuma fushin da Ameenatou keyi me zafi akansa Yana cin zuciyarsa sbd yasan Jamaal ne yayi mata koma Menene Dan haka Shima take yaji Yana buqatan ganinsa Dan haka anan yayi sallar ishai yaci abinci suna gamawa harya fito Bata fito a dakinba Kuma babbah ya Hana kowa takurata fitowa saita huce da kanta taji ta hakura tukuna.
Yana fitowa da wayar hannunsa ya kira layinsa dayake hannun jamaal Amma Jamaal din yaqi dauka sbd Shima Yana sane da Haroon din ya dawo guje masa yayi.
Kiran dayake yi Jamaal yaqi dagawa ya Sakasa dawowa hayyacinsa akan abinda yake jiransa Dan haka dole ya shirya tinda safe ya nufi Abuja.
Koda ya Isa Jamaal din Yana bacci Dan haka siddeeq na ganinsa ya saki murmushi Mai hade da sakewa Yana masa barka da dawowa.
Kallan hanyar stairs na Hawa sama yayi kafin ya dawo da kallansa kan siddeeq din fuskansa a sake Shima Yana amsawa ya ajiye keys din hannunsa da wayarsa Daya ya nufi dining da aka cikesa tsaf da breakfast din Jamaal din ko zama baiyiba Yana Isa dining din Jamaal ya sauko daga saman sanyeda silk pyjamas farare Kal sai slippers dinsa masu shegen tsada da taushi a qafa kallo Daya yayiwa Haroon ya matse fuskansa datake sheqi kaman ba bacci ya taso ba Yana qarasowa ko zama beyiba Haroon ma ya Dan matse tasa sbd kada Jamaal din yayi masa fada a gaban siddeeq yace
"Meyasa nake Kiran wayanka baka dagawa tin jiya fa da daddare bayan isowana?"
Sai alokacin Jamaal ya juyo ya kallesa da idanuwansa da suka Sakasa Jin kunyar Dan uwan nasa na Abinda ya boye masa duk da haryanxu Yana shakkar idan gaskiyar abinda su Dad keyi ne yaji sbd da bazai zauna haka calm ba.
Ciki muryan dayake kokarin danne bacin ransa yace
"Ka taho ne sbd ban dauka Kiran ba kokuwa sbd kana son sanin abinda na sani gameda ainihin abinda kuke aikatawa a boye?"
Maganar tasa ta Saka Haroon kallansa Yana cewa
"A boye Kuma?
Me kenan??
Me kaji?
Kuma daga bakin wa?
"Daga bakin manyanka,Amma koma Menene baka buqatan sani
kaman yanda ka iya boye sirrinsu bana son sanin komai daga bakinka Amma dai ka fada musu taba Dad jeden shine babban Barna da kuskuren da zasu tafka sbd jinin wani karfi ne dashi baa zubar dashi a sake zama lafiya,
Wannan shawara ce da zaka sanar da daddies Dinka."
Yana fadar Hakan ya taba sa ya wuce zuwa dining din sbd yin breakfast.
Kasa motsawa Haroon yayi sbd Baisan me zai fada ba.
Yana gurin tsaye Jamaal ya gama breakfast dinsa ya koma sama yayi wanka ya shirya ya fito a shirye qamshinsa na cika iskar gidan ya fice shida siddeeq sbd sosai yake aikin dayake gabansa Dan kasar gaba Daya Jin yayi fita ransa tafiyansa yakeson yi batareda yabar Haroon din ba Koda me zaayi kuwa,
Aikin kawai yake son gamawa ayi auren su tafi Babu ranar dawowa.
A gidan suka bar Haroon yanata sakawa da kuncewa har sai dare suka shigowa gidan ya fice Dan a matse yake dayake ya duba Ameenatou tinda yanzu Kam baida aikin yi bayan zama guri Daya harsai jamaal ya dawo.
Yauma kwata kwata Bata saukoba duk rarrashinta da duka gidan suka taru sunai mata haka ya gama ya koma Amma dai gwara yau din ta zauna Bata shige dakinta ba.
********Jamaal gaba Daya Jin yakeyi kaman ana konasa aqasar Dan haka ya toshe dukkanin hanyar da zata Bata lokacinsa akan abinda ya kawosa ya dukufa sosai akan aikin Wanda tini ya dauki hanyar kammaluwa sbd sosai ake Aiko na masu zallan ilimi gadan gadan ba wasa ba shirme.
Hafiz dayake ganin sauyi sosai a Haroon din dayake Gani Gurin Aiki da safe da Kuma Wanda yake Gani gidansu da daddare sai ya Saka Hakan akan gurin aiki daban da gida Shima Saiya janye daga nuna kusancinsu da Haroon din gurin aiki saisun hade gida suke fira da gaisawa yanda ya kamata.
Jamaal kansa mamakin Haroon din yakeyi sbd yanda zuciyansa ta gama mutuwa akan yarinyar bayaji Baya Gani Baya gane komai idan bana Yarinyar ba da har lokacin shi Yama kasa tsayawa ya riqe sunan.
Fahimtar irin son dayakewa yarinyar ya Saka Jamaal din Jin bazai iya barin Haroon ya rasata ba.
Ta bangaren su Dad kuwa duk lokacinda ya buqaci ganin Haroon Jamaal ne yake zuwa sbd bayason Haroon ya sake tsayuwa a gabansu Dan kada su lalata masa aikin treatment Daya basa shida mum akan lafiyansa da suketa kokarin ganin samunta Dan kuwa shiyasa suka buqaci komawansa tareda sakashi alkawarin komawan acan Dan kuwa abinda yake Sha Wanda Basu gane Menene ba yayi masa Mummunan illan da basason ma ya sani kwata kwata.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
45
Ranar da Abdul ya cike kwana hudu a Lagos Dan fara aiki a ranar su Dad Lameenu suka sake dawowa nasarawa maganar tsayar da aure hadda Abdul din aka taho Wanda Dad Lameenu ya jasa a jikinsa sosai yana masa kallan kaman 'dansu duk Dan sbd ya sake dasu sosai ya samu aminta dasu har zuci ya yanda komai zai taho a sauki.
Sun sake zama anyi magana an tsayar da ranar auren sati uku hudu masu Wanda daqyar dai su Babbah suka aminta da Hakan sbd kwanakin sun musu kadan duk da ba wani biki sosai akace zaayiba Tinda a Lagos zaayi komai Amma hakama sun buqaci yafiyan duk wani abu da amarya zata buqata Amma Babbah ya nuna amincewa da Hakan gaskia sbd duk fafutikan rayuwar dasukeyi shi da su Abdul na inganta rayuwarta ne su Bata gata Dan haka dole zasu wadata ta da dukiyan aure kaman kowace 'ya yar asali yar gata daidai karfinsu.
Su Dad din Basu wani ja da Hakan ba Daya dage Dan haka take suka gabatar da komai aka Yanke sukai Godia Suma su Babbah sukai godiya.
Wannan Karan harda dadah aka kirawo musu suka gaisa da ita da Ameenatou din wadda take sanye cikin doguwar Riga maroon sai veil data doro Akai.
Sun nuna yabawansu da nutsuwanta a fili sosai suka ringa sake yiwa Babbah godiya Wanda tini ya sake Jin hankalinsa ya kwanta dasu da mutuncin da suke dashi hakama Abdul ya sake tabbatar masa da mutuncin dasuke dashi harma agurin mutane Dan haka yake sake godewa Allah akan zabin da yayiwa Ameenatou dinsa Dayake ta addua da fata.
Da farko babbah baida niyar zaman Lagos din Amma a yanzu da Aure yakai 'yar budurwansa yaji bazai iya zama a nesa da inda take ba tinda harsuna da inda zasu zauna din agidan Abdul Dan haka ya aminta da komawa Lagos din gashi Daman Hafiz ma Lagos din zaibi Haroon kaman yanda yayi masa alkawarin dashi zai koma Koda aikin site ya kammalu acan zai basa aiki a kamfaninsu.
Tsayar da ranar auren ya Saka Haroon shiga lokutan farin cikin rayuwarsa Dan haka ya sake nutsuwa sosai Yana mayarda hankali cikin aikin project din da Jamaal ya tsayu akansa Dan kammalawa ya tafiyansa Dan kullum Jin yake Yana sake matsuwa da barin kasar.
Haroon ganin irin kulawa da kaunan da mahaifinsa yake nuna masa ayanzu Dayake alfahari dashi dakuma ganin abubuwa nata dawowa kan hanya sai yaji soyayyar Dad dinsa na kashe masa jiki kaman bazai iya tafiya ya barsa ba Amma Bai bar Jamaal ya fahimci Hakan ba Dan Jamaal kwata kwata ya Dena bayyana a gaban su dad din sbd yanzu kauna zalla sosai Dad yake nunawa Haroon Dan haka yabarsa ya samu kaunar dabai samu daga Dad dinba Wadda yake tsananin so da burin samu.
*****Su Babbah kuwa A nasu bangaren sosai hidiman tayi musu yawa sbd ga hidiman Shirin biki gata tashinsu duk da ba siyar da gidansa zaiyiba Yan haya aka Nemo zaa Saka Dan haka suketa shirye shiryen tafiya da siyarda abinda ba dashi zaa tafin ba.
Su mum Atee ma da zasu taho kawo kayan aure su lefe da masu gyaran amarya Babbah cewa Yayi su barshi acan tinda suma a satin zasu iso Daman sun zabi yin auren acan ne sbd kawowa kowa sauki dangin angon masu zuwa da Jamaar seelahs din da duka manyan mutane ne da manyan qasa hakama da Yan kasashen qetare sbd sosai Mam ya fito ya nunawa duniya auren dansa zaayi Kuma aure na alfarma na Manyan masu abin duniya Dan haka aketa shiri da Kuma miqa gayyatansa ga abokanan huldansu da manyan masu kudin da suke tare harma da gwamnoni.
Ita kanta amaryan Haroon Kuma budurwan Babbah farin cikinta kusan kullum Baya boyuwa sbd a kwanakin Dan kullum auren yake matsowa cikin tsakiyar ranta take sake Jin tsananin kauna da son Haroon Wanda ya tsayu tsayin daka ya tabbatarda ya dawo da sonsa sabo fil cikin ranta.
Daga shi har ita Hafiz yace ya rasa wanne yafi rawan kafar aurenba ita dai bata tanka Hafiz din sbd ta shirya masa duk abinda Bai zata ba bayan auren tinda a karkashin mijinta zaiyi aiki.
Duk hidiman auren da akeyi Jamaal Bai shiga ko dayaba sbd baida time ko kadan na batawa aiki yakeyi gadan gadan ba dare ba Rana Kuma Hakan saka su dad farin ciki yakeyi.
Ranar dasu Babbah suka gama parking zasu wuce Lagos Kuma jirgi zasubi dukkaninsu sbd murna Ameenatou har fita tayi yau ita kadai a Karan farko rayuwanta taje gidan kawarta Aminiyarta Khadija Tayo mata bankwana itama Khadijan satin zaa fara bikinta shiyasa bazata samu binsu ba ayi bikin da ita Dan haka suka hakura dole da samun bikin juna.
Fitowa sukai tareda Khadija din ta rakota har kusan Rabi kafin ta koma ita Kuma ta wuce.
Dayake hanyar site ne gidansu Khadijan tana kawowa gurin hanyar site din ya hango motar Haroon ta tsaya a bakin hanyar da zatabi ta wuce bakin shago batareda an Budeba.
Glass ya saukan aka miqo masa Abu daga shagon Wanda take kyautata zaton ruwa ne sbd bayan motarsa aka Saka masa.
Wani kyakkyawar murmushi me sanyi ya sauke daga fuskanta tana kallan motar ta tabbatarda shine a ciki bayan yanzu da sukai magana cemata yayi Yana Abuja.
Motan ta nufo tana daga wayarta Dan Saka Kiransa taji me zai fada mata yanzu Kuma.
Tana isowa motar ta miqa hannunta Daya akan mabudin kofan Baya Dan tasan anan yake zama siddeeq ne me jan motar
Tana budewa daidai Yana dagowa daga abinda yake Karantawa daga iPad din hannunsa ya kalli kofan motar da aka Bude Idanuwansu suka shiga cikin na juna
Shikuma a Karan farko Daya Kalli idon wata 'ya mace rayuwansa bayan rasuwan matarsa.
Itama nata idanuwan kusan shine karanta na farko kallan cikim idan mutum Dan haka ta dauke fararen idanuwan nata tana sake wata fitinanniyar murmushi tareda shiga ta zauna Kai tsaye tana juyowa suka fuskanci juna qamshinsa na shigan hancinta Kai tsaye zuwa zuciyanta murmushinta Bai daukeba sedai yau din ta kasa kallansa sbd kunyar takusa zama matansa Kila yau takeji da wani shagwabbiyan murya ta dago ta zuba masa idanuwanta tace
"Shine kacemun kana Abuja sbd kada muyi bankwana kafin na wuce ko??"
Siddeeq Daya rasa ta inda zai fara gyaran matsalan Dake kokarin faruwa fitowa yayi da sauri daga motan ya zagayo ya rufe mata kofar Data shigo ya sake dawowa mazaunin driver da sauri ya zauna sai alokacin ya juyo ahankali ya saci kallan JEEY Daya zuba mata fararen idanuwansa Yana kallanta cikeda mamaki da shakkar ko tanada matsala ne Dan baisanta ba baima taba ganinta ba yake ganin.
Hadiye numfashi siddeeq yayi cikin Dan daidaita murya ya riqa JEEY din magana Yana washe Baki da nuna kulawa yace
"AMEENATOU,
barka da fitowa,yau ke kadai kika fita ne??
Hakan daya fada ya fada ne Dan JEEY yasan wacece din shiyasa ya ambaci sunan nata Kai tsaye Yana tada motar yaja ahankali suka bar gurin Yana juyawa Dan maidata gida.
Dauke idanuwansa JEEY yayi akanta tareda rufe iPad dinsa daidai lokacin ta sake motsowa kusa dashi tanason fada masa maganar da batason siddeeq yaji sedai tana motsowa da fuskanta Dan fada mata din Yana juyowa da tasa fuskan kadan ya rage fuskokinsu ya Hadu tayi saurin yin bayan kirjinta na bugawa ta dago ido ta kallesa Shi kuwa Kai tsaye ya Bude Baki yace siddeeq ya ajiyesa site.
Kasa magana tayi sbd kirjinta Dake bugawa har lokacin shiyasa har motan ta tsaya Bata iya cewa komaiba harya Bude motan ya fice yabarta zaune tana kallan inda ya tashi da ido fuskansa da numfashinsa Daya bugu fuskanta na dawo mata.
Gida siddeeq ya wuce ya ajiyeta Yana mata zancen aikin Dake gabansa ne duk suka Saka kansa daukan zafi shiyasa Baya cikin mood kwata kwata yau din.
Bata iya cewa komaiba ta Bude motan ta ficewanta tareda shigewa gida.
Mota ta musamman ce tazo ta daukesu guraren 2 na Rana tayi Abuja dasu daga can suna Isa airport ba Bata lokaci jirginsu ya daga zuwa Lagos.
Suna sauka Lagos Abdul ne da kansa yaje da motan Aliyah 'yar Alh Lameenu wadda tinda Taga Abdul din taji yayi mata sbd batason namiji me kudin da shine zai juyata tafison Wanda itace me kudin Kuma yar me kudin dazata ringa yanda takeso baya hanata bare ma Saka ido Dan Bata wani zama kasar itama kullum tana yawo karatun ma duk ta kasa tsayawa tayi sai yawon kasashe.
Dayake Dad ne yace yaje da motan ya daukosu shiyasa ya taho da motan ya daukosu.
Gidan Abdul din a kusa da tsadaddiyar anguwan masu shi da mansions din seelah din suke yake Dan haka daga gurin mum Atey driver ya kawo musu abinci bayan isowan nasu.
Gida ne me maana Wanda ya bawa Babbah da Hafiz mamaki sosai sbd ace anbawa sabon ma'aikaci gida irin wannan me Dan yalwa da kyau da tsari Kuma komai akwai a aciki gaskia sedai Dan zasu hada zuria ne Amma tinda a cikin kudin aikin Abdul din akace kamfani zai ringa cire kudin haya sai sukafi Jin nutsuwa da Kwanciyar hankalin sakewa da Hakan.
Daki uku ne a gidan sai Palo biyu da kitchen sai back door da store sai kowanne daki da toilet dinsa.
Kowa daki Daya ya dauka Abdul Daya,Hafiz Daya sai su Babbah Daya sbd Ameenatou tafiyanta zatai gidanta Nan da kwanaki Dan haka baa Raba dakin da ita ba Amma dai na Hafiz itace a ciki da komai nata shikuma yana kwana Palo kafin ayi bikin Amma kayansa suna dakin Yaya Abdul Wanda nasa dakin na daga gefensa daban nasu Babbah ma Yana daga gefe daban na Ameenatou dinne a tsakiya.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
46
Haroon yanason dawowa Lagos Amma sbd kada ya zama ana ganinsa a Lagos Kuma ana ganin Jamaal a site yasakashi hakura ya zauna tareda Jamaal din Wanda Shima yafara kokarin Maida hankali ya gyara career dinsa data watse ta matsayinsa na lawyer.
A bangaren su Dad kuwa tsarin katin gayyatar Omar na musamman ne,
Duk tsawon shekarun Nan da basa tare bawai sun yanke muamala ne kwata kwata ba aa Suna waya da sauran gaisuwa a waya batareda kowannensu ya nunawa Dan uwansa komaiba,
Shi Bai taba yi musu wata maganar bare nuna wani abin daban kaman yanda suka Basu taba cewa komaiba bare nuna shakka fargaban yasan wani abin kawai dai kowa na nesa da Dan uwansa duk dubaru da nuna kaunarsu Bai Bata zuwa inda suke ba kaman yanda ya toshe hanyarsu ta zuwa inda yake iya Hulda da zumuntar waya sukeyi tareda nunawa juna kauna da kulawa a iya wayar sai yanzu da wannan kyakkyawar Daman ta taho musu wadda baida kowanne uzuri ko dalilin Badawa na qin zuwa auren Haroon Wanda sune ma ya kamata ace sinje Neman auren nasa batareda anje dashi Mam dinba Dan shine iyayensa.
*****Ta bangarensu Amarya Ameenatou kuwa suna fama da kadaici da bakuntar sabon guri Amma irin rayuwar da suka samu kansu a ciki ta wadata ta Saka bakuntar zuwan musu da sauki ga Kuma hidiman