Showing 177001 words to 180000 words out of 261814 words

Chapter 60 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9889

iya zaman Nigeria din na Amma Kuma duban familyn nasu duka Suna tare zasu zauna a guri daya ne kaman Nan din sai taji qwarin gwiwa da nutsuwan tafiyan.

Fatmah kuwa so tayi abarta ta koma Poland da karatu sbd abinda yake maqale a zuciyarta na ganin wanda zata iya rabuwa da gidansu da qasarta ta koma qasarsa karatu Dan kawai samarwa zuciyarta nutsuwa da ganinsa kadaima.

Dad Omar ne Kai tsaye da kansa ya Hana hakan yace duka Nigeria zasu dawo bazai taba barinta zuwa Poland ba Wani Sabon karatun itama suje kawai aikin zata fara gaba dayansu har AM da Hafiz da ita tare zasu fara shiga office kowa da babban matsayinsa.

Wannan hukuncin na Dad Omar ya Saka zuciyar Fatmah din shiga damuwa Mai tsananin gaske da shakkar ta inda zata fara Amma koma dai yayane Taga Dr JAMAAL SEELAH din datake ji a bakinsu Dad din Kuma a kallo daya ta mace akansa Dan haka bazata iya auren kowanne namiji a rayuwanta ba idan ba JEEY SEELAH ba a duk inda take kuwa.


Shirin dawowa duk wanda yake gidan yafara kowa na kokarin kammala ayyukan dayake dasu a qasar da huldodinsa,
Fatmah ma shirinta takeyi tareda fita kullum Bata wuni gida tana tareda wasu friends dinta guda biyu da koyaushe Suna tare Suna yawon bankwana duk da bawai an rabu dinne ba Dan zata ringa yawon kasashe kaman yanda ta Saba.

AM school dinsu Arfat ta tafi da Dad dinta da kansa sukai bayanin komai tareda karban masa takardunsa via email suka baro school din.

Tin kafin su isa aka Saka a samarwa Arfat best school a Lagos da tsarin gidansu ma dayake kwata kwata ba anguwa daya da seelahs ba tini aka hai gyaransa da tsarinsa kaman na turai daidai da yanda aka San zasu iya rayuwa aciki musamman sbd Arfat da Mum Nur da Arry sai Fatmah da kwata kwata Basu taba sabawa da Nigeria ba bare Arfat da baima San inane hakan ba, Arry ma rayuwarsa kaf so daya aka taba zuwa dashi lokacin auren AM da Haroon hakama Fatmah shine zuwanta na farko da wayonta dai sedai lokacinda tana baby da iyayenta suka taho da ita dangin daddynta,
Mum Nur kuwa itama zata iya kirga zuwanta qasar sbd asalinta ba anan take ba itama,

Irin mahaukacin mansion din da aka Gina din da tsarinsa da uwar Tarin dukiyar da aka zubawa mansion din kaman baa qasarmu ba ya Saka mutane fara yada dawowan tasa Nigeria da iyalinsa,

Mam kuwa ajiyan zuciya kadai ya sauke Yana tabbtarda idan Bai mallaki dukiyar Omar ba kenan dai sunzo a asara sun koma a asara,
Sun dauki rayukan su kasim da Jameelu a banza,

Me hakan ke nufi?
Omar yafisu Kuma ahakan zaici gaba da finsu??
Meye amfanin rayuwar da suka zaba sbd dukiyar da haryanzu ta gagara shigowa hannunsu?
Meye sunan wannan asarar da suke kokarin tafkawa?

Ajiyan zuciya ya sauke Yana sake kallan hotinan mansion din da kudin dayake rubuce na adadin uban millions of dollars din da ake tinanin an kashe a tsarin mansion din a kiyasi ma batareda an tabbatarba Dan da alama ma sunfi hakan

Lameenu ne ya taba Tako Ina Dan kuwa shi Bai taba yadda ya tabe,
Idan dukiyar ta gagara shigowa hannunsa ta hanyar dasuka fi iyawa to kuwa zasu shiga hannunsa ta hanyar zumunci da jinin da zasu hada Dan kuwa lokaci yayi da zai bayyanarwa da duniya AM jden sirikirarsa ce 'dan cikinsa take aure,

Idan Omar ya nunawa duniya su ba jininsa bane to Shikuma zai nunawa duniya sun sake hada Wani Jinin yanzu Kuma na gasken zbd maganar 'yar Cikin Omar akeyi da nasa 'dan Cikin,
Dan haka Yana zaune hankali kwance Yana jiran saukan jdens din qasar ya Basu surprise din dayafi wanda Omar din yake Basu daya bayan daya Dan kuwa yayi alkwarin a ranar da suka iso zai tabbatarda duniya tasan da 'Dan Mam seelah Dr Jamaal Seelah 'yar Omar jden take aure igiya uku da sai mutuwa.


********Tinda suka fara Shirin dawowa Arfat yafara rashin lafiyan zazzabin kaida kawon da Bai sababa Dan haka hankalinta Dana kowama ya Rabu sbd yanayin jikin nasa ga Kuma tafiyan Tama qarato.

26 ga watan April jirginsu ya sauka Lagos Nigeria gabaki dayansu ahankalin jdens,

Babu wanda baa gajiye yake a cikinsu ba Dan haka Arfat Yana jikin Hafiz wanda yake daukedashi rungume a jikinsa,ita Kuma tana gefen Dad dinta sanye da Riga da wandon Reiss peach color da snickers din Balenciaga fuskanta sanyeda facemask da rolling din Versace silk veil dukda Gajiye take Wani irin lafiyayyan sanyin kyau tayi kana ganinsu kaga wainda suka fito daga turai sbd Dad dinta Yana riqe da hannunta daya kaman yanda ita take riqe dashi din hannunta daya Kuma handbag din tomford ne a hannunta tana qin dagowa ta Kalli Yan jaridar daketa daukan hotinant Dan Dad dinta tareda duka familyn nasu.

Hafiz haya daban yabi sbd Arfat dayake jikinsa daman basa barin a dauko hotinansa ko kadan bare a Wani San dashi.

Uncle Ahmed ma hannun matarsa Dana Fatmah ne a Cikin nasa kaman yanda Dad Omar yake riqe da hannun yarsa sai Mum Nur Dake gefensa.


Motoci kusan hudu ne suka zo daukansu tareda securities masu tsauri
Tin kafin su iso Akai saurin Bude musu kofar motacin
Kai tsaye kowannensu ya shige suka nufa gida.

Koda suka isa gida securities dinsu na mansion din sunkai guda bakwai sai masu aikin Cikin zasu Kai bakwai din Suma daya ta bangaren su babbah wanda gate dinsu daban amma ta Cikin mansion dinma akwai kofar data hade gidansu din wanda hakan shine farin Cikinsu babbah din sbd daman yafi San gidansa ya kasance daban.

Sauran masu aikin duka nasu ne,masu aikin abinci ne da masu aikin tsaftace gida sai wadda take ta AM ce duk da sun taho da Sarrah sbd daman itama ba asalin yar can bace asalin yar Kumasi Ghana ce Amma ta Dade acan Dan itama acan ta tashi,
Ta biyosu ne sbd Arfat bazai yadda da kowacce yar Aiki ba a yanzu dazai taho inda Bai taba ba zaiga rayuwar da ba inda ya Sababa Dan haka tsaf zaiqi yadda da kowacce yar Aiki musamman sbd bai Saba daman can da mutanen waje ba idan ba na gida ba,
Ita kanta Sarrah daman batada niyar qin biyosu din sbd 3 years data fara Aiki a Cikin jdens din ta Tara abinda duka yawon aikinta Bata taba hadasa ba,
Ba qaramin arziki take samu ba Mai girma da albarka ga Sabon datai da Arfat Shima Yana son Sarrah yake fada koyaushe Dan haka ta aminta da biyosu take Babu tsayawa wasa.


Bangaren su babbah 4bedromm 2 sitting room ne da idan ka shiga bama zaka dauka sun dawo Nigeria ba sbd tsarin da dukiyar da aka narkar,
Master bedroom din babbah hade yake da Palo sai lafiyayyan toilet aciki,

Sauran bedrooms din sune a hade da main palon,dakin dadah da ko amare da yawa albarka,sai dakin bakinsu dayake a tsare tsaf sai dayan na Mai aikinsu ne wanda Shima daidai yake a tsaren da ita Mai aikin na ganin dakin Jin tayi tsoro na Neman kamata sbd mamakin kaman baa Nigeria take ba sai kitchen dinsu da store da kofar bayan kitchen.

Part din Hafiz daban Shima lafiyayyan Palo da makeken bedroom da toilet harma da dining da qaramin kitchen dinsa Amma Babu gurin girki sedai electrics na kayan hada tea dasu irin sandwich haka ko warming abinci.

Shima akwai Maza biyu da zasu ringa kulawa da makekiyar harabar gidan da da wankin motocinsu dayansu ne zai ringa gyara bangarensa sbd dukkanin maaikatan da aka dauka a mansion din professionals ne akan aikin musamman a Wani kamfanin cleaners aka daukosu da Id cards nasu da komai.

Acan bangaren Masu gida kuwa fadan tsarin Wani aikin ne sbd komai da koina ka kalla kasan gidan masu abun duniya ne kazo Dan wata shegiyar dukiya ta musamman ce koina aka zubar.

A Cikin mansion din bangaren Uncle Ahmed dasu aunt Didi da Fatmah daban sai bangaren asalin me gidan da nasa iyalin daban Dan bangaren Dad hade yake Dana AM da Arfat duka a sama,

Palon AM kaman France daban inda bedroom dinta da bedroom din 'danta suke guri daya,

Dakinta tsaruwansa kusan yafi na kowa sbd kusan komai na palonta da dakinta iri daya ne Dana Mum Nur sedai ita Mum Nur 2 bedrooms gareta duka nata sbd gidan mijinta ne ita Kuma AM dayan ya isheta hakama dakin Arfat baya buqatan bayani sbd tsarinsa.

Dukkaninsu dai a qasa dakin cin abincinsu yake zai asalin main palon gidan wanda ya hada kowa da kowa Kuma dole anan ne zaa hade sai Kuma wasu sitting rooms na musamman a qasan na Bakin alfarma sai wasu bedrooms na baqi kokuma idan Wani yayi niyar kwana a qasan.
##MAMUH


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
108

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL


************
Kowa dakinsa ya nufa sbd buqatan hutawa daga gajiya da hayaniyar tafiyan,

Wanka tayiwa Arfat da kanta kafin Sarrah ta karbesa zuwa dakinsa ta shiryasa har lokacin jikinsa akwai zafi sosai Kuma baida Wani kuzari,

Sarrah na gama shiryasa Cikin kaya marasa nauyi ta sauka qasa ta nufi wata makekiyar lafiyayyan kitchen Da ake aikin shirya musu ingantattun abincin da zasu ci idan sun taso daga hutawansu ta gajiya.

Gaisawa Sarrah tayi dasu ta buqaci abubuwan da zata hadawa Arfat din abincin da zaici kafin ta basa magani.

Cereals ta hada masa da pancake sai Madara me dumi kakkaura da ruwan roba daya da Apple daya sai orange Shima baifi yanka uku ba da mint lemon water na wanke Baki bayan gamawa ta jero a tray me Dan girma da kyau ta nufi saman.

Tana isa ta ajiye tray din ta dayar dashi ta zaunar jikinta Amma itama Saida tayi wankan Suna isowa sbd kaida,
Abincin tafara basa bayaso karshe hakanan da dubara ta samu yaci kowanne kadan kadan sbd su fruits Suma qaida ne duk zaici abincin farko sai an Saka masa fruits yaci.

Yana gamawa magani ta basa ta basa lemon water din ya Dan sha bakinsa ya wanke ta goge masa Baki ta kwantar dashi tareda rufesa ta daidaita Air-con din dakin ta rage haske kadan sbd bayason duhu sosai duk da bacci ya daukesa take.

Ficewa tayi da kayan ta Kai kitchen ta dawo ta sake gyara dakin sai a Lokacin ta Nema couch din Dake dakin ta zauna tana sauke numfashi sbd baa barinsa shi daya idan Yana bacci indai ba Wani aikin nasa daban takeyiba ko na AM Dan haka ta zaune tareda jingina baya tana lumshe Idanuwanta itama take baccin ya dauketa me nauyi ba wasa.


AM wanka tayi itama ta fito daure da towel blue mara tsawo tana qamshin shower gel dinta me sanyi da nutsuwa.

Bata zaunaba sbd sallahn asuban datake kansu daga tsaye ta goge jikinta t shafa Neutrogena oil sama sama tareda designer body splashes dinta da mists masu tsada da sanyin kamshi.

Underwear(panty) kadai ta Saka sai dogon wide leg wandon Prada fari sai farar vest data kama kirjinta dayake a tsaye qyam a cikensa kaman hannu Bai taba Hawa kansa ba.

Free size abaya ta Dora Akai ta nade kanta da original jersey veil ta tayarda sallah.

Bayan gama sallanta da adduointa tashi tayi ta zare abayar da veil din kanta ta zira slippers din bally marasa nauyi se tsada ta nufi dakin Arfat.

Tana Tura dakin ta Kalli Sarrah taji tausayinta ya Saka jikinta mutuwa Dan haka gurinta tafara nufa Cikin nutsuwa ta tayar da ita tace taje daki ta kwanta ta huta itama.

Godiya tayi ta miqe ta fita ta sauka qasa
Bata suce daki ba Saida ta fara zuwa kitchen taci lafiyayyan abinci ta koshi tasha tea tukuna ta wuce dakinta da aka ware mata a qasan ita baa kaita bangaren masu Aiki ba dayake can bayan ma nasu Babbah ta kwanta baccinta daya sake dauketa take a matiqar gajiye.


Gidan koina tsit yayi babu Wani motsi me girma ko hayaniya sbd duka kaf masu gidan kowa ya gama shiryawa da yin sallan dayake kansu sun kwanta hutawa Dan haka masu Aiki Dake aikin hada musu abinci suka sake nutsuwa ba mahaukacin motsi duk da akwai tazaran da ba Wani jinsu zasuyiba Amma dai sbd kiyayewan komai a natse suke yinsa Cikin kwarewa.


A daidai wannan lokacin da suke hutawa a wannan lokacin jirgin JAMAAL SEELAH da mahaifiyarsa ya sauka a Nigeria tareda siddeeq Suma tasu dawowan kenan sbd bazai iya barin Mum dinsa ba wannan karan ya dawo Nan shi kadai kaman yanda itama bazata iya rabuwa dashi ba Dan haka ta yanke shawaran biyo 'danta idan ta Dan gaji da qasar zata koma ta huta ta sake dawowa Amma dai a Kai tsayen magana ta biyosa sun dawo Nigeria din da zama kwata kwata batareda taji komaiba sbd duk inda 'danta yake zata iya rayuwa a gurin Kuma shine kwanciyar hankalinta da farin Cikinta musamman da Siddeeq ya sanar da ita Ameeenatou ta bayyana tana tareda Dad dinta duka wannan lokacin hakama Shima Dad jden din sun koma Nigeria kwata kwata,
JAMAAL dinta da OMAR JDEN ne kadai wainda zata iya zama a duk inda suke batareda taji shakkan komaiba ko damuwan komai sbd nutsuwan datake samu a duk inda suke,

Ita da JDEN sun rabu da dadewa ko communicating basayi tin rasuwar Haroon sbd ciwon data samu kanta aciki da wanda Shima ya samu kansa a Ciki yanzu Kuma 'danta Yana auren 'yarsa Amma Kuma baisan da hakan ba Amma ita koyaushe hakan farin Ciki yake sakata,
Allah baiyi zasu auri juna ba Amma gashi yayansu inshallah zasu cikewa iyayensu wannan burin na hada zuria tin Suna Raye sbd iyayenta sunso ta auri Omar din kamar me Allah baiyiba.

Hadda Jin Omar na qasar Nigeria din ya dawo kenan ya sakata sake Jin dadin hukuncin bin danta data yanke.

Kafin isowansu Nigeria duk yanda Mam zaiyi Dan shiryawa da 'dansa akan ya Aminta ya zauna a kusa dashi saida yabi ta hanyar Dr Aleena din ta Amince Dan haka mansion din da Dad Omar ya tashi ya siye da kudinsa yaqi karbansa a matsayin kyautan Dad din.

Kusan zubar dashi Akai aka Dora Wani fitinannen Sabon ginin daya kere kyau da tsari tareda girman na Dad din Dana daddy lameenu da har lokacin Sauki ya kasa samuwa daga yafara samun sauki Mam ke sakawa ana sake masa alluran datake Hana saukin zuwa gabaki daya sbd Yana buqatan ganinsa ne daga kwance har saiya kammala hadewa da Omar lameenun naji na Gani ahalinsa Dana Omar sun hade sbd baiganowa kansa mutuwar auren dansaba da 'yar omar,

Hakama Yana buqatan lameenun a kwance ne lokacinda zaa kawo masa gawar Aliyah ya fara dandana abinda ya dandana Kuma ba Dan ya gama dashi ba ko gama fansar ran Haroon dinsa ba.

Saukansa da dawowansa Nigeria shima kusan yaduwa yayi Amma kwata kwata Bai bari Yan jarida sun daukesaba sbd Baya buqatan hakan musamman dadewan da Akai baa samu ganinsa ko yada hotonsa ba a koina Dan haka a matse suke da su samu wannan damar.

Daga shi har Mum dinsa fuskokinsu sanye suke da nose mask da farin glasses shi harda fcap din Fendi
Jikinsa sanyeda black tsadaddun kiton sweatset freesize Dan haka hannun Mum dinsa na Cikin nasa suka fito Arrivals Mum din tasa kaman wata yayarsa koma kanwarsa sbd yanda take cif cif Baturiyar Poland hakama yanayin jikin nasu bama daya ba sbd qarfinsa da budewansa na geamin.

Siddeeq ma Yana dayan gefen Mum din Dan Bata kariya Shima sanye yake da nose mask din sbd ana ganinsa take zaa gane JAMAAL SEELAH dinne a tareda shi sbd ansan ana ganinsa anga Jamaal din Dan haka kusan har suka wuce Yan jarida tareda securities biyu na airport din Babu wanda ya ganesu.

Motoci biyu ne sukazo daukansu Suna kokarin isa mota motocinsu seelahs suka iso airport din daukansu.

Siddeeq na ganin motacin ya juyo ya Kalli JAMAAL wanda ya Dan lumshe fararen Idanuwansa da sukai Dan Ciki sbd gajiya Dan yasan Dad dinsa ne wanda ya tabbtarda bazasubar gurinba saiya bayyanarwa duniya shine ya dawo din.

Dr Aleena ma na Gani tasan Mam dinne da kansa Dan haka ta Dan sake kame hannun Jamaal Cikin nata tana dagowa ta kallesa shi kuwa Dad din da aka budewa mota Cikin tsananin respect ya kalla da Idanuwansa da sukai Ciki Ciki kafin kowannensu yayi motsi Yan media suka zagayesu Tako Ina daukan hotunansu da jeho ta tambayoyin da Babu wanda a cikinsu ya tsaya Jin ko menene.

Hannun Mum dinsa ya sake Dan kamewa tareda daga hannunsa daya ya rungumota jikinsa Yana wucewa gaba siddeeq na bayansa Yana sallaman Yan jaridan hakama securities sunata karesu.

Cikin farin Cikin da a duniya Mam ya manta rabon daya samu kansa acikinsa ya fara sake murmushin farin Cikin 'dansa ya dawo garesa tareda Aleena data kasa zaman r
Nigeria ta rabu da aurenta sbd bazata iya ba Amma ayau tadawo zata zauna sbd 'danta,
Hakama Jamaal Bai dawo qasar ba garesa sbd Yana mahaifin daya haifesa sai akan mace sbd ya sani Kai tsaye Jamaal ya dawo Nigeria ne sbd Omar daya dawo da 'yarsa.

Shidai koma yayane hakan ya masa daidai sbd Jamaal bazai taba sake barinsa ba daman sbd Aleena yake barinsa Kuma Aleenan yanzu gatanan duka Suna guri daya,tayaya bazai bari Yan media su San da hakan ba a fadawa duniya 'dansa ya dawo gurinsa,
Sauran Kuma surprise na gaba.

Budewa Mum dinsa mota yayi da kansa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login