Showing 225001 words to 228000 words out of 261814 words

Chapter 76 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9890

ya masa yayi saurin fashewa da dariya Yana cewa

"ok sorry sorry Lady AM"

Motar Jamaal ya Bude mata da Kansa ta shiga kafin ya zagayo Shikuma siddeeq ya Bude masa Dan haka shigewa kawai yayi ya tada motar suka bar galaxy Macau din.

Venetian Macau suka nufa ya kame mata gabaki daya VIP restaurant dinsu na awa hudu sbd taci abinci Cikin nutsuwa.

Abinci kusan kalolin da sukeda dasu irin wanda zata iya ci Babu wanda baa kawo ba sukaci abinci Yana bin duk motsinta da kallonsa me sanyi da nutsuwa har suka gama tace she's okay tukuna suka baro gurin.

Gurin karban kayanta suka nufa sbd a gwada ya Gani idan zai iya barinta zuwa da kayan a jikinta.

Suna zuwa kuwa kusan Saida ta gwada kaya uku ana hudun ne ya yadda tukuna suka karbo suka baro gurin.

Daganan Gidan Wani abokinsa da yayi Aiki asibitinsu Poland suka nufa wanda yasan da zuwansa dan haka Cikin farin Ciki da kulawa shida matarsa Suka tarbesa da babies dinsu guda biyu.


Sai dare suka dawo tayi wanka tayi waya da gida kafin ta kira Ashley wadda batanan ta fita itama tukuna ya sakata kashe wayarta gabaki daya suka kwanta bacci batareda ya mata komaiba sbd yasan a gajiye take hakama baya tinanin sex zaiyi Dadi a Lokacinda gajiya take Cikin mutum Sam.

Ashley tin ranarda ta dawo dakinsu ta tararda kayan console da aka fasa ta sake kame kanta ta bari sai sun gama hutawa tukuna Dan haka tattara bra din data tarar yashe a palon tayi takai daki tareda sauran am din tukuna ta kira hotel din sukazo suka tattara ta biya kudi me yawan gaske na abubuwan da aka fasa din tukuna tayi kwanciyarta tana dawowa hankalinta akan idan suka sake irin last time kawai suka samu Ciki a jikin Ameeenatou me zata fadawa Dad Omar da Babbah daya yadda da ita fiyeda kowa akan Ameeenatou.

Acikin kwana biyun Wasu irin mahaukatan love yake koyar da ita ta yanda gaba daya jikinta suka gama karban sakwanninsa ya sakata mantawa da alkawarin dayake kansa da kowa da komai bayan soyayyarsa me karfin gaske datake kwance Cikin zuciyarta.


Ranar da sukai taronsu da kansa ya kaita gurin Kuma shine ya daukota wanda James duk Basu gansa ba sbd Ashley data kasa ta tsare duk da shikam ko a jikinsa Dan baya shakkar komai ko kowa.

Suna gama Taron komai ya kammala da kwana biyu James suka gama musu Shirin komawa Dan haka a Cikin kwana biyun jikinta yayi mugun sanyi na tinanin abinda zata tarar gidan Dan tsoro da shakka takeji kaman Wani zai iya sanin abinda ya faru da ita.

Har Kuka tayi na kunyar kanta na yanda zata hada Ido da babbah da Dad dinta duk da basusan komaiba Amma tanajin ciwo da kunyar hakan sbd tasan yanda sukai da ita akan JAMAAL da aurensa.

Shi kuwa a nasa bangaren kewan da zai mata ne da yanda zai nisanta da ita idan ta koma dinne kadai ya damesa Shima ba sosaiba sbd yasan zai ga matarsa a duk lokacinda yaso kafin iyayenta su dawo hayyacinsu akan tinaninsu na Rabasa da matarsa.

A daren ranar da zasu tafi ma Wani shegen love ya hada mata wanda ya sakata mutuwar jiki ta kwana jikinsa a kasalance har gari ya waye ya shiryata da kansa yakaisu airport wanda sai a Lokacin James ya gansa sedai Kai tsaye Ashely ta waske masa akan anan suka hadu yau da safen Nan.

Bayan fitowanta mota a gaban kowa ya janyota jikinsa Cikin sanyi da nutsuwa tareda kulawa da sonta me zafin gaske ya hade fuskansu guri daya tareda kama bakinta ya zira harshensa Ciki yayi mata kyakkyawan kiss na minti daya kafin ya saketa ya sake kissing hancinta da gefen fuskanta ya Kai bakinsa kunnenta da sauti me taushi yace

"Ki kula my Halal,
Zan dawo jibi and i love you"

Dagowa kawai tayi ta kallesa kafin ta gyada masa Kai narke tan wucewa gaba.

Babu Bata lokaci jirginsu ya tashi zuwa Nigeria su Kuma su Jamaal din da yamma Suma sukabi jirgin yamma zuwa Poland daga can zai hada sauran takardun da zai hada su wuto Nigeria Suma.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
132

https://chat.whatsapp.com/IQ6XVJntkTj5FFJ66euAIR

Assalamu alaikum... Welcome all. Dalilin group din nan shine, muna so mu samu kasuwa da zaka tallata kayanka ka kuma siya kaya in sha Allah.
Akwai tsare tsaren da mukayi ga masu kananun business da kuma wadanda basu ma fara ba.

Ya zaki tallata kasuwar ki?

Wanne irin abu ne ya kamata ki fara saidawa da jari kadan?

Ya ake amfani da social media a samu kasuwa? Da sauran su

Zamu gayyato wasu daga cikin masana akan harkar wanda suyi mana bayanin yaya sukayi? Kalubale da sauran su.

Bayan nan akwai wanda za koya mana business ga wandanda ke da shaawar farawa.

Daga karshe wanda akayi verifying business din su zasu samu membership da zasu dinga tallata kayan su, zamuyi musu business logo da flyer idan basu da shi, sannan zamu tayasu tallata kayan su da sauran su.
Idan kina bukatar register din kasuwancin ki, ki samu slot din farko farko sai kiyi ma daya daga cikin admins din magana.



******Karfe 9 na dare jirjinsu ya sauka Lagos Nigeria Kuma Uncle Ahmed ne yazo da kansa airport ya daukesu tareda Arfat dayake ta tsalle Yan murnan ganin Mommah dinsa da aunt Ashley dinsa.

Yana ganin Mommansa da gudu ya kwace daga hannun Uncle Ahmed yayi gurinta da gudu Yana ambatar sunanta farin cikinsa Mai tsanani a bayyane.

Hannunta ta ware ta daukesa sama ta rungume tana Jin farin Ciki Mai tsanani na ganinsa na mamayeta.

Dago kansa tayi ta Dora lips dinta a kumatunsa ta sakar masa peck kafin ta juyo dayan gefen ta sakar masa tana sake rumgumesa Cikin tsananin sonsa tace

"Nayi kewanka like crazy teletubbie my love,I love you Son"

Dariya yakeyi Cikin murna ganinta yace

"I miss you more mommah and I love you too"

Ashley Dake kallansa cikeda kewa da kauna sunansa itama ta ambata.

Juyowa yayi ya sauka daga jikin mommansa ya fada jikin Ashley din Yana cewa

"I miss you my special"

"I miss you more my love,
Ina babbah dasu Dad Omar?
Yaya Mum Nur and Didi?kanata musu rigimar mommas Dinka basa Nan ko?

Girgixa Kai yayi shidai murna kawai yakeyi.

Kallan Uncle Ahmed am tayi tana Dan shagwabewa tace

"Uncle Ahmed barka da zuwa,
Yayasu Dad?

Amsawa yayi cikeda kulawa da sakewa Yana musu sannu da hanya kafin ya juyo Idanuwansa ya Kalli Ashley datake masa sannu da tahowa ya amsa Yana mata sannu da hanya itama Yana miqa hannu ya harbi jakar hannunta
Cikin muryanta me nutsuwa da sakewa tace "thank you"

Mota suka nufa suka shige bayan angama Saka komai ya shiga ya tada suka nufi gida.

Suna isa gida babbah daman yau Bai fita koina ba sbd tarbon yarsa Dan haka Suna isowa da kansa ya fito har harabar Mansion din ya tarbeta kaman yar budurwansa ta dah haka yake Jin abarsa sbd a gurinsa har yanzu baby ce ita da Baya gajiya da dawainiyarta.

Hannu ya miqa mata cikeda tsananin kaunarta ta kama tana narke masa fuska cikeda shagwaba da kunya a can qasan zuciyarta.

Ashley ma cikeda kulawa ya mata barka da dawowa kaman zai hadiyeta itama.

Mum Nur rungumeta tayi cikeda kewanta datai tana tambayarta hanya.

Didi ma murnarta a fili yake na dawowansu.

Dadah kuwa tini ta shiga kitchen da kanta ta hadawa yar autarta Kuma yar gaban goshinta lafiyayyun abincin gargajiya datasan tayi kewansu kafin ta fito ta tarbeta.

Dad dinta sai da kowa ya gama tasa murnan kafin ya sauko Yana ware mata hannuwansa Yana murmushi dayake bayyanarda irin tsananin girman son dayakewa 'yarsa Yana mata barka da dawowa ta qaraso ahankali ta shige jikinsa ya rungumeta tana cewa

"Dad nayi kewanku sosai."

Ashley ma Cikin kulawa da kauna yai mata sannu da dawowa kafin aka barsu suka hau sama bayan tini su Sarrah suka haye da kayansu aka fara gyarawa a wardrobe saukan Kuma ana Kai komai mazauni daya dace dashi.

Wanka kowannensu ya fara Yi da ruwan zafi sosai suka gasa jikinsu gajiyarsu ta sake kafin sukai sallolin dasuke kansu kafin suka sauko cin abincin dare wanda Akai lattin ci sbd su zuwa lokacin Arfat tini yayi bacci.

Suna gamawa Akai yar fira sama sama tukuna aka barsu dansu kwanta su huta.

Shirin bacci tayi kawai ta haye gadonta ta kwanta Babu Bata lokaci bacci me karfi ya dauketa gashi ta kashe wayarta sbd ta huta da kyau.

Ashley ma wayarta a kashe take sbd ta huta yanda ya kamata shiyasa duk yanda Jamaal yaso jinsu Bai samu daman hakan ba haka ya hakura Shima ya kashe nasa wayoyin Dan ya samu daman hutawa daga tasa tafiya sbd sun isa Poland.

Washe gari ma hutawa sukai sosai Babu inda ta fita tana tareda iyayenta cikeda kulawa da kauna haka suka wuni hankali kwance.

Ashley kuwa kitchen datai missing ta wuni tana aikin baking abubuwa sbd tayi kewan ayyukan Didi ma tayi kewanta sbd a kitchen itace bestynta datake Jin dadin Aiki da ita.

Da daddare saiga Dr Aleena ta taho gidan tareda maman fadeela driver ya kawosu a Cikin wata lafiyayyan roll Royce dauke da tsarabar strawberry cupcakes datai da kanta da Tarin chocolates masu tsadan gaske datai order tin daga wata qasar aka kawo Mata sbd Arfat kawai kaman zata Bude shagon chocolates din.

Tsarabar dawowan am ne tace ta kawowa Ameeenatou din sbd tasan ba ita zata ci ba dole danta zata bawa sai gashi tin a gabanta Arfat yafara murnan chocolates din Yana ci sedai baa bari yaci sosaiba sbd Suna controlin diet dinsa da cimarsa da Dama.

Dr Aleena zubawa Ameeenatou Idanuwanta tayi cikeda kauna me tsananin gaske tana kokarin Janta a jiki da magana
Ita Kuma Ameeenatou ta kasa sakewa da ita sbd Wani irin nauyinta takeji wanda ya Saka babbah Bude mata wuta kan ta sake da Dr Aleena din tinda ba sirikitarta bace.

Maman fadeela ma zubawa Ameeenatou Idanuwanta tayi jikinta da zuciyarta na sanyi sbd Tino Fadeelanta wadda da yanzu itace a matsayin macen Jamaal,.
Jamaal yaso fadeela fiyeda yanda sukai tsammani sedai Kuma irin zafi da girman son datake hangowa Idanuwansa Yana yiwa Ameeenatou daban yake wanda ta tabbatarda ko fadeela zata dawo duniya dole hakura zatai ta barwa Ameeenatou shi sbd Babu macen da zata iya rayuwa da Jamaal idan ba wacce yake so ba,

Wata zuciyarta Kuma sanar da ita takeyi da fadeelan na Raye da Babu macen da zai kalla bare yayiwa Wani son tabbas da 'yartace a rayuwarsa.

Numfashi ta sauke tana yiwa 'yarta fatan tana Cikin rahamar ubangiji tareda kallan Ameeenatou tana sakawa zuciyarta kaunarta kodan halaccin Jamaal da kaunar dayake mata duk sbd son dayayiwa yarta da Kuma tausayinta da kaunar dayake tsakaninsu da Siddeeq.

Maman fadeela kallo daya tayiwa ARFAT tayi zargin yanada alaqa da Aleena da Jamaal sbd kamannin Aleena Zak a fuskansa Dana Jamaal Amma sai Wanda yayi masa kallan kwanciyar hankali yake gane hakan Kai tsaye a kallo daya.

Sannan ganin irin kallan tsananin so da kaunar da Aleena ke masa ya Saka maman fadeelan sake tabbatarda abinda tayi tinanin sedai tinda Babu wanda yace mata komai so itama batada hurumin magana bare tambaya.

Dr Aleena daga karshe itada Dad Omar palonsa suka nufa Dan tattaunawa a tsakaninsu wanda Mum Nur Bata damu ba ta barsu su samu tattaunawansu sbd tasan shaquwa da kaunar dayake tsakaninsu
tin ba yanzu ba tasan asalin kaunar da Omar yakewa Jamaal ta Aleena ce bawai Dan Yana Dan 'dan uwansa Mam ba,
Kaunace yake masa wadda ta fito daga wadda yakewa mahaifiyarsa
Ita Kanta Dr Aleena Babu lokacin da batai fatan inama ace Omar dinne mahaifinsu Jamaal din sedai kaddara haka ta zuwar musu Allah baiyi iyayensu da sukazo aurensu zasu gansu a tare ba.

Ameeenatou ma tinda taji maman fadeela itace maman fadeelan Jamaal take jikinta yayi sanyi Dan haka ta Dan sake janyewa daga palon karshe ma sama ta koma sbd tanada shiga office washe gari dan haka Aiki ma ta koma tafara a laptop.

Hafiz da Fatmah Basu dawoba sai a satin Suma zasu dawo Dan haka shigarta office dole zatai Aiki idan sun dawo sun huta su fara fita ita Kuma ta zauna gida ta huta kafin ta sake komawa.

Sai dare sosai su Dr Aleena suka tafi Mum Nur ta Rakata har harabar gidan Suna fira kafin suka wuce ita Kuma ta dawo Ciki.


Washe gari Ashley ta rigata fita aikinta da zata fara itama a ranar na tsadaddiyar clinic din JDENS da aka Bude sbd ita din tareda daukan likitoci masu kyau harma da Dr Aleena a Cikin manyan likitocinsu da zata ringa Dan zuwa time to time tana duba manyan cases nasu.

Da sabuwar motarta Lexus GX grey color Ashley ta fita daga Mansion din sanyeda wata tsadaddiyar jallabiyan Cairo sai designer handbagsm dinta tana qamshin me sanyi ta fice.

Ko data isa asibitin wadda Suna Macau Akai bikin budeta Dan haka Kai tsaye Cikin girmamawa aka tarbeta ana Bata girmanta na sune masu asibitin tukuna ta nufi inda zata fara aikinta duk da ba Wani dadewa zatai ba karatu zataci gaba bisa ga shawaran Uncle Ahmed daya bayar akan ta wuce ta zama likita kawai.

Ameeenatou ma sai sai 10 saura ta fita itama ta wuce Aiki Cikin tata motar.


Ashley ta Riga Ameeenatou dawowa Dan haka Koda Ameeenatou ta dawo da dare harta huta ta sauka kitchen Suna tareda dadah tana tayata Aiki sbd yau Didi Bata Nan ta fita.

Wanka tayi da sallan magrib ta sauko ta nufi gurin Dad dinta da zai Yi tafiya tareda uncle Ahmed gobe suka zauna sun jima Suna magana kafin Akai dinner ta gida gaba daya harsu babbah sbd hakan sukeyi indai akwai baqi gabaki daya ake cin abinci a table hardasu babbah kokuma idan Wani zaiyi tafiya hakan sukeyi.

Dan haka gaba dayansu sukai dinner cikeda kauna da kulawa da juna tareda bankwana tukuna kowa ya wuce dakinsa.

Washe gari itace da kanta takaisu airport kafin daga can ta wuce Aiki Dan haka gidan tsit sbd mum Nur ma ta fita ta tafi gidan Jamaal gurin dr Aleena itada Didi.

ARFAT kuwa Yana gurinsu dadah Shima Hafiz kadai ake jiran ya dawo shine zai masa komai na school din dazai fara zuwa daman anbari ne yafara sabawa da Sabon gurin tukuna.

Kwanasu Dad dinta biyu da tafiya Jamaal suka sauka Nigeria Kai tsaye tin a airport Yan jarida suka rufesa da ihun tambayar rashin ganinsa a gurin rasuwar wanda yake tamkar uba a garesa wato Mam da iyalansa da suka rasu lokaci daya.

Cikeda shock da tsananin mamaki ya juya ya Kalli siddeeq wanda yakeda tabbacin ya sani dole boye masa yayi sbd shine idonsa da jinsa a harkar komai dayake gudana a duniyar media.

Siddeeq sallamar Yan media din yaji tareda securities har suka samu Jamaal din ya shiga mota Yana Jin kansa na riqewa da Wani irin nauyin gaske sbd Bai taba tinanin daddy lameenu zai rasu da familynsa duka a Lokacin daya Bai jiba,

Tayaya?
Meya faru bayan tafiyarsa?

Juyawa yayi ya Kalli siddeeq Dake gefensa Cikin motar batareda yace komaiba

Shima siddeeq din batareda yace komaiba ya kamo bayanin komai daya Adana a iPad dinsa ya miqawa Jamaal din.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
133
Zubawa ipad din Idanuwansa yayi Yana karanta duka labaran dayake rubuce akan rasuwar Aliyah zuwa ta Mum Sarat da Daddy lameenu tareda Mum Atee.

Labarin Dad dinsa da Baya qasar bayan ya yanke jiki ya Fadi sbd rashin Dan uwansa da matarsa ya zubawa Idanuwansa Yana kalla Idanuwansa jajir.

Radadin rasuwar Aliyah data Mum Sarat yafi ji fiyeda ta sauran Amma ko Daddy lameenu uba ne tinda suka kasance iyayensa Dan haka ko yayane akwai ciwo da radadin rashinsa,

Yasan ya aikata abubuwa da yawa Amma Bai cancanta hakan daga Dad ba sbd koma menene suka aikata a tare suka aikatasa dole akwai gurin ragawa,
Shi kansa baida niyar qyalesu dukan Amma Bai taba tinanin aikata kisa garesu ba Amma dai yaso rabasu da abinda suke so fiyeda rayukan duniya da mutanen Cikinta,

Yaso rabasu da komai sai sun koma nera goma tana Basu shaawa Amma basuda halinta ta yanda sunaji suna Gani zasu dandana baqin Cikin dayafi na rashin Rai da suka ringa kashewa ba tausayi.

Jajir Idanuwansa suka sake tareda cikowa da Wasu irin ruwan hawaye masu radadi da Ciwo ya rintse Idanuwansa Yana Jin abinda Bai taba ji ba akan mahaifin daya haifesa,

Mahaifinsa ne me wannan mummunan rayuwar ta rashin digon Imani ko kadan harga wanda suka kasance Rabin jikinsa.

Kasa riqe hawayensa sukai Saida suka gangaro ya sake rintse Idanuwansa Yana kasa cire tsananin ciwon dayake ji na kasancewan Dad dinsa mahaifinsa.

Handkerchief ya Ciro ya goge fuskansa datai ja take abinka da farar fata.

Miqawa siddeeq iPad din yayi yace

"Kasan duka takardun dukiyarsu da signing Dina suke Akai lokacinda Haroon ya tafi Poland na taho a matsayinsa duka ka hadasu komai na dukiyar Dad zai bar hannunsa

Wainda ba signing Dina bane Akai a hada musu takardun zan Sakashi signing dinsu batareda saninsa ba."

Gyada Kai siddeeq yayi Cikin shiga nazari da tinanin abinda zai biyo baya sbd Mam Babu abinda ya hada da dukiyarsa,
Jamaal ne kadai a duniyarsa yanzu dayafi masa dukiyarsa Amma bayan Jamaal Babu wanda bazai iya kawarwa akan dukiyarsa daya zubarda shekarunsa tin na samartaka har tsufa Yana tarawaba data tafi da rayukan duka Yan uwansa da abokan arziki da yawa,

Dan haka ayanzu abinda Jamaal zaiyi shine babbar balain da Mam bazai iya daukaba ace ya wayi gari kaf dukiyarsa ta koma ta Jamaal din Kuma a gaban Idanuwansa ya rabar dasu ga Al'umma yaqi barin komai???

Hummmm" ya sauke ajiyan zuciya da numfashi a Lokaci daya marasa sauti.

Koda suka isa gida Jamaal gaba daya baya Cikin dadin zuciya ko kadan sbd labarin rashin,

Yana isa gidansa ya tararda Ayesha a Cikin su Mum dinsa itama ta fito Cikin sanyin jiki tayi wata irin ramar data sauya kamanninta a qanqanin lokacin.

Su Mum na kulawa da ita sosai kaman yarsu sbd tausayinta da tinanin rashin kowa datake Ciki Amma sun dage sun zama gatanta Suna debe mata kewa musamman dukkaninsu dasuke shaawa da kewan rashin 'ya mace,

Maman fadeela na mata kallan fadeelanta ita Kuma Mum na mata kallan batada 'ya macen dayake shaawa samu tin lokacin baya.

Ita Kanta Ayesha tana Jin yanda suke kaunarta hat zuciyarta sedai rashin mahaifiyarta Abu ne da bazata iya mantawa lokaci daya ba musamman daya kasance itace uwarta itace ubanta.

Ganin Jamaal ya sakata fashewa da kukan data kwana biyu bataiba tana tausayin yanda idan zai iya karbanta kaman yanda mum dinsa ta karbeta sbd tasan baya shiri

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login