Showing 102001 words to 105000 words out of 261814 words

Chapter 35 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9988

gameda sakon hakama Bai kirasa ba Dan haka yaji zuciyarsa tayi nauyi Dan kuwa a yanzu bayajin zai iya barin Ameenatou asibitin kota halin yayane shi da kansa zai dauketa inshallah.

Ameenatou din ma harya ya gama ya tafi tana zaune Bata iya ko motsawa ba bare iya cewa komaiba bayan fararen idanuwanta data zuba masa.


Bayan tafiyan siddeeq haka sister Ashley ta koma da ita sukaci gaba da lallabawa tana kulawa da ita.

Washe garin ranar da siddeeq yazo babban tashin hankalin da sister Ashley ta tashi dashi shine laifin siddeeq na hoto da aka kamata dashi itama haka aka sauya mata block aka dauketa daga block A din kwata kwata.

Tsaye take a office din Dr Dee ta kallesa cikin son samun yanda takeso tace

"Dr Dan Allah ka Saka hannu abarni A block A dinnan ko Dan sbd patient Dinka Ameenatou kasan Bata taba yadda kowa ya kusantota gaba Daya ciwonta gaba zaiyi komai zai iya faruwa Kuma idan aka cigaba da Bata wannan alluran please Dr"

Daure fuska yayi zaiyi magana Akai knocking kofar office dinsa tareda budewa a natse batareda da jiran izininsa na shigowanba.

Kofan ya kalla itama sister Ashley kofan ta juya ta Dan kalla sedai ganin doctors dinsu manya kusan guda uku tareda siddeeq ya Sakata juyowa gaba Daya tana musu barka da shigowa kafin ta sake magana JAMAAL dake bayansu yana amsa waya ne ya shigo kai tsaye yana kashe wayar tasa qamshinsa me wani irin sanyi tareda qamshin tsadansa a bayyane batareda an fada maka kudinsa ba ko sunansa ba ya gauraya iskan office din gaba Daya.

Fararen idanuwansa akan Sis Ashley suka fara sauka yayi mata kallo Daya tareda dauke idanuwan nasa Ya amsa gaisuwanta Kai tsaye cikin muryansa da Hausa Bata kama ba yanda ya kamata.

Itama duk rudewa take Neman yi sbd kwarjininsa Daya cikasu hakama Dr Dee miqewa tsaye yai batareda sanin ko waye dinba Amma dai yasan koma waye shi din yanada martaba da kwarjini tareda Matsayi tinda har su Dr Zakeer suka rakosa.
##MAMUH#
#BESTLOVE
#JAMAAL JEEY SEELAH
#AMJEEY
#ROMANCE
#HOTLOVE



*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
64
Sister Ashley ficewa tayi zuciyarta cikeda tinani da shakku da yawa na ganin siddeeq,
Hakama Wanda yake tareda siddeeq ya tabbatar mata da shine Kodai 'yayan Ameenatou ko mijinta Kokuma Wanda zata aura Kokuma Wanda yake tsaye akan lamarinta Dan yanda siddeeq yake tsaye Bai zaunaba a gefensa alamace ta Maigidansa ne a zaune.

Tana fita Dr Dee ya sake fuska sosai cikin girmamawa duk da a bayyane shekarunsa gaba suke Dana Jamaal din Amma hakanan ya kallesa yana masa barka da zuwa.

Su Dr Zakeer ma zaunawa sukai suna sake gaisawa da Jamaal din Wanda har lokacin idanuwansa na cikin black Versace goggles dinsa Babu tabbacin waye yake kallo acikinsu Amma dai farar fuskansa kusan Dr Zakeer yake fuskanta sbd shine wanda tin farko yazo Gani sbd shine sama da Dr Dee din Amma dai kusan matsayi Daya suke duka.

Kallan Dr Dee Dr Zakeer yayi Kai tsaye ya sanar dashi sabon babban likitansu kenan daga Poland Wanda zaiyi aiki dasu na Yan watanni Yana hada Wani research ne akan PSYCH yana gamawa zai tafiyansa.

DR JAMAAL MAM SEELAH Wanda aka Fi sani da Dr JEEY SEELAH.

Kallan JEEY din Dr Dee yayi da Dan sauri gabansa na faduwa Yana Kuma boye tashin hankalinsa da tinanin dayake Neman shiga ya sake fuska sosai cikin sake bayyanarda girmamawansa ya sake gaisawa da JEEY din Wanda baida Wani bayani me tsayi da zaiyi bayan yi musu sallama suka fito gabaki dayansu tareda sanar dasu gobe zaiyi reporting yafara aiki.

Sosai su Dr Zakeer da sauran manyan harma da MD din asibitin da suka iso suka bayyanarda farin cikinsu da Jin dadin samun Daman aiki da babban kwararran likita kamansa duk da kusan ba qwarensa kadai ne abinda yasaka ake girmamasa ba da kiyaye masa sanin su waye SEELAHs ne,
Sunan SEELAHs nada Wani irin girma da matsayi na girmamawa da kiyayewa sbd tarin arzikinsu da power da suke da ita me karfi.

Dr Dee yafi kowa shiga rawan jiki da rikicewa lokaci Daya Amma Babu Wanda ya gane Hakan ko Lura sbd kwarewansa a iya mu'amalantar Jamaa dan haka zubawa Jamaal idanuwansa yayi Yana son Tantance bature ne ko bahaushe Dan Nigeria Kuma da gaske shine JAMAAL 'dan Mam Seelah tak Daya rage Wanda idan ya fahimta daidai kusan shi da mahaifinsa ne ko sunansu Alh Lameenu Baya kaunar a ambata idan suna tare sbd kada ko a wasa sunansu ya Hadu da sanin alaqan Dake tsakaninsu dashi bare Ameenatou.

Siddeeq ne ya Bude masa kofar gefen zaman banza na gaba ya qaraso a natse ya shige Yana Ciro wayarsa ya Saka Kiran wata number Yana shigewa motan da kansa ya rufe Siddeeq ya zagaya ya shige ya tayar da motan Wanda su Dr Zakeer ke bi da idanuwansu Har lokacin iskan Bata koma musu daidai ba da sauran qamshinsa Daya bar musu.

Sister Ashley Dake jiran fitowan sir siddeeq akan maganar sauyin gurinta batama San sun fito ba sedai motar data hanga tana ficewa harabar asibitin tasu me tsawon katangar da baka ganin waje tabi motan da idanuwanta da suka sauya sbd tashin hankali da damuwan rashin madafa Dan kulawa da Ameenatou kaman Wani sabon aikine me albashi me tsoka da Bata kaunar rasawa ko kadan Dan haka duk ta shiga damuwa hakama har cikin ranta Allah ya Saka mata kaunar Ameenatou din Dan haka hankalinta be kwanta ba da yanda ciwonta yake tashi da dare dole akwai abinda yake faruwa a block din datake son sani Dan haka kwata kwata batada nutsuwan barin Ameenatou a daidai wannan lokacin.

Daga asibiti kuwa Kai tsaye Masaukin JEEY din suka nufa Wanda yake a Houston Astrt Victoria Island kafin ma a qarasa Isa estate din nasu na Houston Astrt suke guda hudu a guri daya masu shegen tsaro da securities hakama kowanne gida kusan yanada nasa securityn na musamman hakama ba hayaniya sam a gidajen dan dabam dbam ne nasu JEEY din sune na marasa yara daga me shi shikadai se me mata su kadai akwai Wanda na masu yara ko family da yawa ne dabam.

Tin wancan zuwan nasa ya Siya gidan Amma Baima shiga ba aka samu tashe tashen hankalin da yabar qasan Kuma ko yanzu Bai dawo da niyar zaman ba ya dawo ne sbd Tafiya da Ameenatou kota halin Yaya so tinda sun kasa samun sallaman tafiya da ita Dan haka dole Yana buqatan Aiki a cikin asibitin na Dan lokaci Dan samun Daman dawo da ita daidai Dan su samu sallaman tafiya da ita sbd duk yanda zaiyi kafin yazo a sallametan su tafi Abin ya gagara sbd kanta ya juye sosai hakama shi kansa yanada hanyoyin amfani dasu ya tafi da itan idan yaso Amma Kuma a yanzu da abin yayi tsanani haka dole Saiya nutsu ya karanci yanda ake treating nata tareda alluran datake Kai da magani yasan girman matsalan da nisanta yanda yana tafiya zasusan ta inda zasu fara tinda tako ina sallaman taqi samuwa.

Parking Siddeeq yayi a lafiyayyar haraban gidansu dake zagaye ko a cikin estate din ya juyo ya kalli JEEY din da har lokacin fuskansa baa sake take ba sbd abubuwan da ya sun zafafa kansa ciki hadda rashin sanin inda hafiz da baida lafiya ya iya daukan Babbah ya tafi dashi sbd shi kansa Hafiz din yasan dole Baya iya tafiya a daidai tinda kariya nawa ce a jikinsa Amma ace siddeeq din Bai sanar dashi komai yanda ya kamata ba sai yanzu dayayi zuwan da Babu Shiri.

Numfashi ya sauke ahankali kafin ya Bude Baki bayan ya Dan juyo ya kalli siddeeq din a natse da sauti mara karaji yace,

"Babu Wanda zai San Ina qasar kota Yaya,
Duk abinda zaisaka asan Ina qasan a toshe sa tukuna ba yanzu zan dawo ba."

Gyada Kai siddeeq yayi Yana cewa

"Babu matsala duka na gama da wannan"

Gyada Kai yayi tareda Bude motan ya zira kafafunsa ya fice ya nufi kofa.

Password na Bude kofan ya saka ya Bude ya shige lafiyayyar palon da Akai tsarinta daidai da yanda siddeeq yasan Yana gudanar da rayuwarsa hakama koina an gyareda tsaf da safen kafin saukansa Dan Bai sanar dashi Yana hanyar tahowaba Saida ya shiga jirgi ya sanar masa Kuma ya kashe wayan dan haka Babu Bata lokaci gari na wayewa kafin ya iso da safen nan aka gyara koina tareda yin shopping na dukkanin abubuwan buqatansa Daya San dole dasu yake amfani.

Sanyin AC ne ya gama gauraye palon da qamshin turarensa Daya Hadu dana humidifiers da burners da suka gama aiki tinda safen duk da Bai fiya son irin wainnan qamshin ba.

Kai tsaye hanyar bedroom dinsa ya nufa ya shige Yana kashe wayarsa Dan Yana sauka Bai wani huta ba suka wuce yaga Wanda zai Gani akan case din asibitin daga can ya wuce asibitin Dan haka yanzu hutawa yake buqata kansa ya sake kafin yasan ta inda zai Saka a fara Nemo masa su Babbah.

Yana shigewa Kai tsaye wayarsa ya ajiye ya nufi closet ya zare kayan jikinsa ya jefa a laundry ya janyo towel daga inda towels dinsa suke a jere ya daura a qugunsa ya shige toilet.

Siddeeq na shigowa Kai tsaye kitchen ya nufa ya zauna energy drinks din da aka kawo tin kafin isowan JEEY din a fridge tareda ruwa masu yawa kafin ya fito sbd Cook din Daya iso ya basa Daman shiga kitchen bayan ya gabatar masa da komai ya fito ya fice Dan Shima gidansa Dake kusa zai tafi ya huta kafin lokacin gama abincin yayi Kuma yasan JEEY dinma a yanzu hutawan zaiyi Baya buqatan kowa.

Wanka ya fito qamshin Liquid soap din his majesty Yana tashi daga jikinsa fatansa sai daukan ido takeyi kaman ta lafiyayyan mace.

Baya zama gaban mirror sedai ya tsaya Dan haka daga tsayen ya goge jikinsa da towel ya shafa lotion na his majesty din sai body splash me sanyin gaske.

Underwear kawai ya Saka sai armless transparent freesize ya Dora jallabiya Akai yayi Sallah Yana idarwa ya zare jallabiyan ya haye lafiyayyar gadonsa dataji wasu tsaddadun beddings ya kwanta bayan ya kashe hasken dakin.

Ya manta raban Daya samu Daman kwantawa yayi baccin Hutu kawai sai yau din duk da Baya cikin nutsuwan zuciya Amma dai ya kwanta din Dan samun sakewan Kai harma da zuciya.

Karfe uku cook ya gama girka komai daidai irin girke girken da Jamaal din ze iya ci daidai Dana can qasar sbd bayani da siddeeq Daya masa na kalan cimar JAMAAL din.

A dining ya jere komai tareda cutlerys da komai harma da cups duk Saida ya ajiye komai kafin ya tafi saikuma gobe.

Yana fita Bai wuce ba a gurin securities ya Jira Saida siddeeq ya taho bayan la'asar shirye cikin qananun kaya marasa tsayi sai qamshi yakeyi Shima me sanyi sbd yar nutsuwan Daya samu ta dawowan Mai gidan nasa ya miqa masa id card na shigowa kullum batareda an dakatar dashi ba ya wuce shikuma ya qarasa yayi parking.

Fitowa yayi motan Yana kunna wayarsa da Shima take kashe ya nufi ciki.
Dagashi sai JEEY dinne suka San password Dan haka Kai tsaye ya Saka ya shige Yana duba sakwannin Dake shigowa wayarsa harda na sister Ashley akan tana buqatan magana dashi sbd daga daren yau dole zata koma inda aka maidata kuma akwai tazara daga block din su Ameenatou zuwa block da aka maidata bare ta ringa zagayowa.

Numfashi ya sauke ahankali tareda qarasawa dining Bai taba komaiba kallan yanda aikin cook din yayi ya wuce kitchen ya dauko ruwan Roba Daya da milk drink me sanyi ya fito daidai fitowan JEEY Wanda qamshin Paco Rabanne ne yafara iso masa yasan ya fito Dan haka Yana ajiye kayan hannunsa kan dining ya dago idanuwansa Ya kalli hanyar bedroom din.
#MAMUH#
#JEEY SEELAH
#JAMAAL SEELAH
#DR JAMAAL JEEY MAM SEELAH
#JAMAAL
#JJ SEELAH


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
65
Sanye yake da black Dior loose fit tshirt da guntun wide leg wandon AG Shima black sai slippers Suma dai black dinne,

Kallo Daya siddeeq yayi masa yayiwa Allah godiya Daya halacci JEEY din a cikin wadatacciyar ni'iman rayuwa sbd wahalan rayuwa take zata narkar da fatar JEEY din yake Gani da a cikin marasa arziki ya fito sai gashi Allah me yi kowa a inda yaso.

Dining din ya nufo Yana kallan time din agogon palon kafin ya dawo da kallansa kan dining din.

"Barka da fitowa" siddeeq ya fada Yana komawa ya dauko masa ruwa da drinks tareda fresh tangerines masu kyau cikin bowl masu Dan sanyi ya ajiye sbd JEEY din yanada wuya yaci abinci ya gama baisha oranges ba dai tangerines din dai yafi buqata sbd ya saba ne tin yana yaro mum dinsa ce ta saba masa da hakan.

Zaunawa sukai kusan a tare Yana cewa

"An samu Wani bayani daga binciken inda su family dinta suke??"

Fara serving na abincin sukai siddeeq na cewa

"No Babu wani bayani a yanzu Amma dai na bawa Wanda zai tafi Nasarawa komai da zai ishesa ya nutsu sosai ya binciko sai aje a taho dasu.

Gyada Kai yayi ahankali cikin gamsuwa da zancen Yana daukan roban ruwa ya Bude yakai bakinsa yasha a natse batareda ya tsaya zubawa a cup ba.

Abincin da Akai ya kalla,
Penne pasta ce dataji cheese da qananun Naman Kazan broiler,

Zuba masa siddeeq yayi tareda white rice kadan ssaiya zubawa kansa White rice din da sauce din kidney dayake gurin Dan bazai iya cin cheese ma shi Kam kusan cimar JAMAAL din ya kowace iri ya kasa sabawa ko iya cinsu Dan abubuwane da Bai taso shi Kam Yana cinsu ba so bazai iya koyan cinsu lokaci Daya ba.

A natse JEEY din yake cin abincinsa siddeeq ma abincin yakeci Yana sake duba wayarsa kafin ya dago ya Kalli JEEY din yace

"Sister Ashley gobe zata bar Ward din da AM take take"

Kalman AM din da siddeeq yayi amfani da ita ne ya Dan Saka shi dakatawa daga tauna abincin dayake bakinsa na seconds kafin ya Dan dago ya Kalli siddeeq din da idanuwansa masu haske sosai tukuna yaci gaba da cin abincin bayan ya gyada Kai alaman yaji.

Siddeeq kuwa tin daga ranar da Ameenatou ta zama matar JAMAAL din Bai sake kiranta da Ameenatou din ba sbd ta zama matan maigida Kuma ubansa Dan haka AM din shine sauki saukin abinda yake kiranta.

Harsu suka gama cin abincin bayanai ne Daya bayan Daya na dukkanin abubuwansu da JEEY din ya bari yaci gaba da kulawa yake jero masa a natse tareda yanda ake kulawa dasu sosai Dan kuwa dukiyar Dad Omar din da kusan su Dad Mam Basu San da ita ba itace JAMAAL din yake kulawa da ita ya saka wainda Babu Wanda yasan dukiyar waye suke juyawa siddeeq na kulawa da sauran Wanda Hakan ya Saka siddeeq din duk da ana cikin tashe tashen hankalin nan yayi nasa kudin daidai misalin Dan kuwa harkokin na tafiya cikin nasara da yanda ake son Dan Shima siddeeq din yanada iliminsa sosai da qwarewa akan Aiki Dan nesa ba kusa ba yafi Haroon sanin aiki da kwarewa.

Suna gamawa siddeeq ne ya fita ya Siya sauran dukkanin abubuwan da JEEY din zai buqata a asibitin da zai fara shiga gobe sai dare ya dawo ya kawo masa yabar wainda zasu tafi dasu cikin mota,

Masallacin dayake gaban Houston Astrt da Dan tafiya suka tafi da mota acan sukai sallan magrib da ishai daga can ya dawo da JEEY din gida shi Kuma ya wuce nasa gidan da motarsa Daya bari gidan JEEY din.

Ya shigowa gidan Kai tsaye laptop dinsa ya kunna ya fara duba sabon reports na mum dinsa da akace an Turo masa na yau din.

Yana gama dubawa Dr Adrian ya kira suka jima suna magana akan mum din sbd saukin data fara samun shi kansa yafara basa mamaki Dan kuwa baiyi tinanin saukin zuwa haka sauri sauri ba daga bayan Nan bayan sun gama Shan wuya.

Godiya yayiwa Dr Adrian din kafin ya kashe ya kira Aunt dinsa ta bangaren mum din wadda take tareda ita itama Muslim ce Dan yanzu dangin mum din tasu ya kasu ne akwai musulmai akwai Christians Amma dai baa qyama ko gudun juna sbd sun yadda da Addinin raayi ne kowa yayi Wanda ya yadda dashi.

Ya jima Yana magana da Aunt Mariam Yana kallan Mum dinsa ta screen din laptop dinsa sbd vcall ne,

Zubawa Mum dinsa idanuwansa yayi suna Dan sauyawa Yana Jin kewanta da kaunanta me tsananin gaske Dan har yau ban dandana son datakai wadda yakewa Mum dinsa ba,

Rasuwar Dan uwansa yabar Wani mummunan gibi a rayuwarsa da har abada bazai cike ba hakama radadi ne da harya mutu bazai taba Dena Jinsa ba sedai ciwo da radadinsa ya ninku ne sbd Mum dinsa datake cikin wannan halin sbd rashin 'danta datai,

Shi kadai ne yasan irin yanda mum ke tsananin son Haroon sbd Bai rayu da ita ba,
Bai zabeta ba ya zabi Dad dinsa,
Da wannan ciwon a cikin zuciyarta take rayuwa kowace Rana,
Babu rana ko Daren da Bata kewa ko mararin son kasancewa da 'dan nata ba tin daga ranar Daya zabi zama da mahaifinsa akanta harya tafi ya barta da wannan ciwon a ranta.

A yanzu mata biyu ne a rayuwarsa masu mahimmancin da zai iya komai akansu,
Da mahaifiyarsa da ko rayuwarsa zai iya Badawa akan sai macen da har 'dan uwansa ya rasu itace a bakinsa itace burinsa itace ya yadda yabi bayan hanyar mutuwarsa akanta yakuma rasa,yancinsa,jin dadinsa,iliminda daga qarshema rayuwarsa duk akanta.,

Alkawari ne ya daukawa Haroon da Dad Omar bazai taba barin kowace irin cuta kusantota ba matiqar yanada Iko da Rai da lafiyan hanawa sai Kuma Wanda Allah yariga ya kaddaro mata kaman wannan matsalan ta gabansu a yanzu Dan kuwa Bai taba tinani ko hango Hakan zai iya faruwa gareta da gaske ba daga ya tafi ya dawon duk da abubuwan duk Basu tafi yanda akeso

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login