Showing 249001 words to 252000 words out of 261814 words

Chapter 84 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9970

kikasan ubansa?" Sukaji an fada daga bayansu Cikin mamaki da sauti me tattareda bawa maganar Mahimmanci.

Ashley ce tayi saurin juyawa gabanta na faduwa da karfi ta Kalli babban dayake tsaye bakin kofar kafin yafara shigowa palon gabaki daya a natse.

Ameenatou rintse Idanuwanta tayi Suna sauyawa zuwa ja zuciyarta na nauyi batareda ta juyoba.

Fatmah kuwa wasu hawaye ne masu tsananin zafi suka ciko Idanuwanta sbd kalaman Ameenatou da suke a bayyane zaginta ne tayi itada iyayenta da kalaman data fada.

Tsayuwa babbah yayi a gaban Ameenatou din bayan ya Kalli Ashley ya Kalli Fatmah ya tsayar da kallansa kan Ameenatou din lokacin Hafiz Shima ya shigo palon ya tsaya Yana kallan yanda duka sukai cirko cirko babbah Cikin mamakin abinda yaji yace

"Ameenatou kikace kinsan uban 'danki?

Da sauri Hafiz ya Kalli Ashley wadda ta rasa abin cewa bayan hawayen Dake Neman ciko Idanuwanta.

Dadah ma da bataji abinda Ameenatou ta fada ba Saida babbah da a maimaita tambayar ta Kalli Ameenatou din da sauri.

Shiru Ameenatou din tayi tana kasa dagowa ta Kalli babbah sai hawayen Dake Ciki Idanuwanta da sukai ja sosai.

Fatmah da zuciya ta gama dibanta kallan Ameenatou din Tayi Cikin radadin kalaman da suka kasa ficewa daga kanta tace

"Zaki fada ne ko na fada masa tinda kince ni da iyayena bamuda hurumi ko iKon sanin mahaifin danki?

Dawo da kallanta tayi kan babbah tace

"Babbah Wani Cikin ne a jikinta na haihuwa sai ta hada duka ta fada Maka waye uba......." Wani lafiyayyan Marin daya sauka fuskanta ne ya Saka sauran maganarta katsewa tana ganin wasu mahaukatan taurari.

Dad dinta ne tareda su Dad Omar dukansu suke tsaye a bayanta.

Didi ma Wani Marin ta Kuma sauke mata tana son magana Amma zuciya ta cita sbd yanda take maganar kaman hade da rashin kunya ga Babbah.

Hawayen Dake cikeda Idanuwan Ameenatou ne suka gangaro mata tana rintse Idanuwanta tareda yin baya tana kasa dagowa.

Babbah wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke me sanyi kafin ya dago ya Kalli kowa daya bayan daya yaga dukkaninsu shi suke kalla batareda kowannensu ya shiga mamakin abinda aka fadan ba hakama Babu shock ko alamansa a tattareda kowannensu Dan haka Shima saiya Danne yaqi shiga shock din sbd magana ce da baikamata ya dauka da Mahimmanci ba Shima Dan haka Fatmah din ya kalla wadda ke Kuka sosai tana tallafe da fuskanta kafin ya Maida kallansa kan Ameenatou datake hawaye sosai tana bayan dadah ya sake sauke ajiyan zuciya sbd iskan dayaji ya cike masa Ciki kaman ma ya kumbura a take a gurin.

Cikin sanyi da nutsuwa Babu wasa ko kadan ko sakewa a Cikin maganarsa yace

"Ameenatou menene yake faruwa nakeson ji daga bakinki?
Meya hadaki da Fatmah take wannan maganar?
Me Kuma kunnuwana suka Jimin akan uban Arfat??
Uban waye uban nasa da kike cewa kin sani?
Kin sani fa kike fada Ameenatou?

Kuka ta fashe dashi Mai tsananin tsima zuciya da baqin Ciki tareda kunyar kanta da yau take ganin asalin kame fuskan babbah.

Dadah ce ta kalleta tana cirota daga bayanta tace

"Me yake faruwa akace ba Kuma zakiyiba"

Ashley ce ta motsa zatai magana babbah ya kalleta Babu rahama ko daya a fuskansa yace

"Ayshatu ki kiyayeni a daidai wannan lokacin Kuma idan kin jira ai kanki zanzo"

Shiru Ashley tayi jikinta na sake nauyi da shiga Wani mummunan fargaba.

JAMAAL ganin kowannensu yayi shiru ya sakasa matsowa gaban Ameenatou ya Ciro handkerchief dinsa zai share hawayenta ta ture hannunsa da karfi tana sake fashewa da kukan.

Kallan babbah yayi yanason ya sanar dashi duka amsoshin tambayarsa Amma Dad ya girgixa masa Kai sbd babban girman da zaa bawa babbah shine barinsa yayi magana da Ameenatou din da kansa.


Hafiz ne ya dage gefen Ameenatou din ya Kalleta kafin ya Kalli babbah ganin yanda ransa yayi mummunan Baci yace

"Babbah kayi hakuri Nima nasan waye baban Arfat din tare muka boye hakan sbd kada ranka ya sake Baci tinda haryanzu baka yadda da aurensa ba"

Tari ne ya kufcewa babban ya dago ya Kalli hafiz Yana cewa

"Wane auren?
Tanada auren ne daman?
Inace anbar maganar auren dayake kanta ma bare Wani auren"

"Jamaal da Bai iya wannan kwana kwanan zancen ba Jin yayi ya kasa riqe zancensa sbd kukanta dayake cizon zuciyarsa ya Kalli babban Cikin nutsuwa da girmamawa irin tasa yace

"Duka abinda suke son fada shine Arfat 'dana ne,nine mahaifinsa"

Qin kallansa babbah yayi Yana kokarin Danne abinda yakejin Yan taushe kirjinsa ya juya ya Kalli Dad Omar wanda ya sauke ajiyan zuciya Yana kallan babban Cikin tsananin Jin nauyi Shima.

Hakan da Omar yayi ya tabbatar masa da abinda ake fadan gaskia ne.

Juyawa yayi batareda yace komaiba zai bar gurin JAMAAL ya Bude Baki Cikin sanyi yace

"Babbah kayi hakuri ko yanzu Wani Cikin ne a jikinta"....

Saurin juyowa dadah tayi da karfi ta Kalli Ameenatou Wanda ta sauke Kai kukanta na tsayawa.

Babbah kuwa kafafunsa kasa daukansa sukai ya juyo Yana kokarin riqe shock dinsa ya Kalli Ameenatou ta Bude Baki muryanta na rawa da Kuka tace

"Babbah Dan Allah kayi hakuri wlh sharrin Shedan ne"


Sarewa kafafunsa sukai yayi Wani mugun zama a kujeran Dake kusa dashi rigarsa na jiqewa da Wani irin gumin gaske.

Da sauri Hafiz ya nufesa Jamaal ya datakar dashi ya isa gurinsa shida siddeeq dayayi saurin daukan magazines Dake ajiye a table da alamar Wani yayi karatunsu ya bari a gurin suka fara masa firfita Jamaal na kokarin dubasa sbd da alama attack yake kokarin samu.

Ameenatou na ganin hakan itama ta matso gurin babban tana durqusawa gefensa sbd a zuciyarta ko Arfat tanajin kaman Bata masa tsananin kaunar datakewa babbah ba sbd shine uwarta Kuma ubanta shi kadaice jini dangin mahaifiyata,

Shine Wanda rayuwarsa ta kuruciya ta qare a gurin tsananin so,reno da dawainiyar mahaifiyarta ya Kuma qarar da manyancinsa a tsananin sonta fiyeda rayuwarsa da Kuma dawainiyarta Dan haka Bata hada sonsa da komai a rayuwarta ba.

Tsabar rikicewa babbah ganin yayi kaman ma baya Gani sosai take jininsa ya haye sama.

Jamaal na ganin hakan ya fara basa taimakon gaggawa Yana Hanasa shidewa.

Ganin hakan kowa ya shiga tsoro da tashin hankali sbd da gaske dai babban ya rikice.

Mum Nur tsoronta kada babban zuciyarsa ta buga su shiga uku.

Kamasa dole Akai zuwa bangarensa aka kwantar dashi a kujera Jamaal ya dubasa da kyau aka samu bugun zuciyarsa dayake yawan da baa so ya dawo daidai ya masa abinda zai masa suka samu ya rintsa badan ya samu sassaucin abinda yakeji ba sai Dan dole yayi baccin idan ba hakan ba zai iya samun bugawan zuciyar.

Bayan sun fito dadah zubawa Ameenatou Idanuwa tayi Yana karantar yanayinta ta tabbatarda da gasken dai Cikin ne.

Numfashi ta sauke ahankali tareda kama hannun Ameenatou din sukai dakinta bayan ta kira Ashley itama.

Zaunawa sukai ta kallesu su duka biyun Cikin nutsuwa tace

"Ayshatu da gaske Cikin ne kenan?

Numfashi Ashley ta sauke tinda dai ankai karshen zance kowa ya sani ba Damar boyewan

Gyada Kai tayi tana dagowa cikeda kunya.

Mamaki ne ya sake kama dadah ta juya ta Kalli am din tana mamakin yaushe hakan ta faru bayan tana tareda su.

Samun nutsuwa da farin Cikin Jin Jamaal ne mahaifin Arfat Kuma Cikin na yanzu ya saka mamakin nata taqaituwa da Jin kwanciyar hankali sedai tasan babbah Kam sai anyi fama Dan haka kallan Ameenatou din ya sake Yi kafin ya janyota jikinta tana cewa ta Dena kukan hakan kada Wani ciwon ya shigo Kuma.

Ashley kallan Dadah tayi tace

"Dadah Dan Allah ki rarrashi babbah kada zafinsa ya haura wlh nidai nasan nayi kuskure Amma bazan sake ba."

Dariya suka so sakata musamman Ameenatou da duk tayi Sanyi ga zazzabi tana ji me qarfi sbd kukan datake fama dashi tin ranar da Cikin ya bayyana a Cikinta har yau din Amma Kwata kwata batajin ma zazzabin bayan babbah tinda su Dad sun sani tin jiya su.

Jamaal barin gidan yayi Dan Basu Damar daidaitawa Amma da Arfat ya tafiyarsa hakam idan cikinma sunqi amsa kaman yanda sukaqi amsar auren mamaki zai bawa kowa.

Fatmah kuwa Kuka takeyi kaman ran zai fita sbd Jin Jamaal ne uban Cikin Kuma yasan da hakan yabarta ta tsaya gabansa take sanar dashi Ameenatou nada 'dan shege Ashe kallan sakarya ma yake mata duka wannan lokacin.

Gasu Dad take kowa ya dauki mummunan fushi da ita Jin itace ma tafara fadawa Jamaal Ameenatou na da Dan shege.

Wannan kalman ta girgixa kowa musamman iyayenta duk da Dad Omar yayi kokarin Danne fushinsa sbd Ahmed daya bayyanarda nasa sosai da Mummy dinta.

Ta bangaren babbah ma zuwa dare Yana warwarewa haukace musu yayi da kowa gidan fada ne yakeyi sosai akan mummunan cin amana da taadancin da Akai masa Yana zaune da 'yarsa an sake cutarsa an mata Ciki a karo na biyi bayan an San zaman dagar da yayi na Raba auren sbd matiqar b Jin yayi ance Mam ya rash an rufesa da qasa ba bazai iya bada yarsa a zuriar gidan ba Ashe kallan Mai saman ruwa suke masa,sun cucesa sunci amanarsa.

Ameenatou da Ashley dayace auren dole zai Mata idan Bata fidda miji a satin ba zaune zuke gabansa Suna kuka musamman daya sake tabbatar musu da ita Ameenatou bazata sake fita aikin kowa ba saita haihu ya kaiwa Dr Aleena abinda ya Haifa ita Kuma Ashley ba ja da Baya auren dole zai Mata koma da waye ya samu Kuma ya bada umarnin Maza Maza a dawo masa da Arfat.

Gabaki daya gidan dauke wuta sukai tareda kama kansu sbd ba qaramin zafi babbah ya dauka ba Dan Babu wanda ya ragawa hadasu yayi har Omar din yaci musu mutunci bayan hakuri Babu abinda suke basa sbd tabbas kowa yasan an masa laifi.

Jamaal kuwa damuwansa gabaki daya ta koma ne akan matarsa datake fama da kanta Kuma ana sake sakata tsoro da Kuka gashi ko wayarsa Bata dauka kwata kwata ta Dena yadda kota Yaya ya ganta Dan haka yake Cikin tasa gagarumar damuwar.

Fatmah ma tsananin fushin da uncle Ahmed yakeyi da ita yanke shawaran maidata France karatu yayi babbah na Jin hakan yace ba inda zata a hadasu duka ai musu auren sadaka shine kadai zai daidaitasu.

Take uncle Ahmed ya amince da hakan hakama Dad Omar Dan haka Fatmah na Jin hakan tafara Kuka da birgima tana rokon babbah ya taimakesu sun tuba.

Ashley ma tayi rokon babbah da Neman tuba harta gaji.
#MAMUH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
146
Mam a ranar daya cika kwana hudu a asibiti Omar ya bada umarnin kawai a miqasa asibitin mahaukata sbd cigaban da Babu ko kadan a tattare dashi sbd duka matakin dayaso dauka ma akansa ganin yanda gaba daya fatar jikinsa yayi Wani mummunan baqi a Cikin kwana hudun sbd balain ruwan alluran da suka shigesa Wanda likitoci sun tabbatarda qwayoyin Cikin ruwan alluran sun Riga sun kama ruwan jikinsa sedai idan zaa fiddasa waje ne.

Ahmed baima bari Omar ko Jamaal sunji wannan sakamakon ba ya sanar da Dad Omar abinda zai sanar Anan ne Omar din yace a miqasa asibitin mahaukata kawai.

Jamaal kuwa baima San meyake faruwa ba sbd ya Riga yabarwa Dad Omar din yaji da komai.

Haka aka nade Mam din da idonsa daya aka kaisa asibitin qazanan mahaukatan Dake wajen gari aka basa daki bayan an cike masa komai.

Yanaji Yana Gani baya iya magana bare motsawa aka ajiyesa da Ido daya tsiyaye aka barsa Cikin dakinda gwara wata bolar dashi sbd tsananin wari da sauro ga Kuma wasu ruwa Dake kwance gefen dakin wainda har sunyi baqi da alama ruwan sama ne ke zubowa idan anyi Suna taruwa aciki.

Ko ficewa Basu gama yiba sauro da quda suka fara yayyabesa daga kwancen dayake.

Sama ya Dan kalla ahankali yaga Babu ko ceiling take wasu hawaye masu radadi da Ciwo suka gangaro gefen Idanuwansa Yana rufe Idanuwansa yanajin wasu irin qwari ja shigewa rigar jikinsa da ko ita Bai samu an sauya masa ba duk jinin daya zubar mata ya bushe yayi Wani irin baqi.

Duhun dakin kadai idan dare yayi wata azabar datake firgita ruhin dan Adam dayake cikinsa ne,

Sanyi jikinsa yayi Yana sake rintse Idanuwansa hawayen cikinsa suka gangaro sbd yasan har abada bazai taba qara moruwaba sbd shi kadai yasan azabar dayake ji a jini da jikinsa.

Dare nayi gurin ya dauki tsit bayan kukan sauron masu yawan gaske dayake tashi a dakin Babu sautin komai,
Wasu azababbun cinnaku ne ke cizonsa Tako Ina azabarsu na ratsashi Amma baya iya ko motsa ko yatsansa bare Wani abin
Ga Wani irin duhun da ko a Lokacin da suke shiga gino zinari a Cikin duhun Rami me zurfi da tsayin gaske Bai Kai wannan ba sbd wancan akwai hasken fitila Amma ayau ko wanda zai kunna masa hasken fitila Babu,

Wannan duhun duhu ne da Yan uwansa Dake kwance kabari Kila sunfisa samun rahamar hasken kabari akan wannan dayake Ciki.

Haka ya kwana Babu sauki ko rahamar ubangiji ko daya har gari ya waye sai guraren 10 aka shigo aka Bude dakinsa Wani qazamin dattajo ne da yake a Buge ya zauna ya tayar dashi zaune ya fara Tura masa abincinda ta ringa dawo masa sbd azabar dayake Ciki ta Fi masa abincin Dadi da saukin wucewa a cikinsa.

Ganin hakan me basa abincin ya Saka hannu ya dame tuwo da miyar kaman kunu ya zuba musu ruwa suka sake sakewa ya maqure bakinsa ya dura masa shi gabaki dayansa a bakinsa ya wuce cikinsa.

Yana fita amai ya fara feso masa har jikinsa har qasa take gurin ya lalace da Wani irin qarni da qazantar Aman Amma Babu wanda yazo ya sake dubasa haka Nan ya wuni Cikin aman tareda ruwan qazanta.

Haka ya wuni sai dare aka sake zuwa basa abinci Nan ma Babu Bata lokaci Aka dura masa ya sake feso Wani Aman Cikin azabar ciwon Ciki Mai tsananin azabar daya sakar masa gudawa.

Anan ne aka zo aka daukesa suka wanke masa jikinsa Shima bayan ya wuni Babu wanda ma yasan halinda yake Ciki bayan wari da qazantar sun ma fara bushewa a jikinsa.

Lokacinda suka zaune dashi a bakin Wani fanfafo Cikin qazanta suka fara sheqa masa ruwa qarnin amai Dana jinin rigarsar daya bushe Dana gudawar suka fara Wani mummunan tashi a jikinsa take suka suka rufe hancinsu Suna sake Dan yin baya daga jikinsa suka sheqa masa ruwa kaman Wani Dabba.

Wani irin kukan baqin Ciki da qunci ne ya taso masa Yana rintse Idanuwansa.

Suna gamawa Wani gajeran wandon dinki suka Saka masa suka kaisa dakin hakanan suka kwantar dashi suka tafiyarsu.

Sanyi ne Me karfin gaske suka fara ratsa fatarsa zuwa namansa har zuwa qashinsa suna ratsasa cikeda azaba da qaiqayi Amma ba halin motsawa.


***A daidai wannan lokacin Omar na tareda Dr Aleena wadda sukai tafiya a safiyar zuwa Abuja shi da ita da Ahmed gurin Wani Taron manyan likitocin da zaayi na qasa Wanda tana Cikin manyan baqin likitoci masu Mahimmanci da aka gayyata sbd shi Omar din daya Saka sunanta sbd ta daukaka a qasarsa kaman yanda takeda daukaka a tata qasar akan aikinta.

A lafiyayyan luxury Bangalore dinsa suka sauka Wanda yake tsare da securities da luxuries Tako Ina hankalinsu kwance.

Ahmed bangarensa daban a gidan Dan haka Shima a nasa bangaren ya sauka hankalinsa kwance.

JAMAAL ma dashi a Cikin Manyan likitocin da aka gayyata Dan daga sunan Mum dinsa sai nasa Dan haka Yana Abujan sedai bama tare suka taho ba Dan yaso tahowa da tasa halal din Amma Sam ko muryanta taqi barin ya sake ji daga ranar bare ganin fuskanta Dan ba qaramin fushi da zafi ta dauka dashi ba Dan haka duka yake Cikin dacin zuciya.

Siddeeq ma duk yanda yaso magana da Ashley ta samu Damar fitowa da am din Dan su dauketa kawai su tahowarsu ya kasa samun Damar wannan maganar da ita sbd babbah daya Saka musu mugun Ido musamman Ashley din dan yafi qin yadda da ita akan kowa ma Dan haka ya Saka mata Ido tareda rantsewa akan duk Wanda ya kamata tana waya dashi shi zai aura mata ko waye sbd maganinsu.

Fatmah ma hakan ya fada mata hakama gabaki dayansu ya sakasu dawowa sashensa ya Kuma hadesu a daki daya sbd su duk abinda zasuyi su shirya Babu shegen da zai zauna zaman shiryasu tinda ba Wanda ya hadasu fadan da hassadar tareda qyashin da zage zagen.

Fatmah kusan zaucewa take Neman Yi sbd ganin su Dad Omar da Dad dinta ko ta kan zancensu Basu sake bi ba alaman hukuncin babban yayi musu daidai Dan haka ta sake dagewa da rokon babbah tana Neman tuba da bazata sakeba Amma ko bi ta kan tubanta baibiba.

Ameenatou dai batada ta cewa bayan komawa salihar gaske sbd Cikin kaman Yana jiran asan dashi sai laulayinta ya dauke tsaf Bata Ciwon komai ko Wani amai saima fitowa dayek kokarin farawa sbd tasowa da mararta tafara Yi hakama fushin datake cikinsa akan Jamaal din Bai saukoba ko kadan sbd kunce mata zani a kasuwa ne yayi duk da tasan a gunsa shi ba komai bane tinda bature ne Amma meyasa baima fara fada mata yasan tana dauke da Cikin nasa ba Wanda itama harga Allah taji tana tsananin son Cikinsu yanzu sbd na Arfat Bata hankalinta ta dauki Cikin ya Renu a Cikinta har haihuwansa.

Ashley dai itama taitayinta ta shiga ta Dena waya da kowa se babbah baya gidan dan sanin rantsuwarsa akan duk Wanda ya kamasu Suna waya shi zai aura musu indai auren ya halasta tsakaninsu.

Hafiz da dadah ne ke tausaya musu matiqa musamman Fatmah data kasa Dena Kuka haryanzu gaba daya ta shiga Wani mummunan hali akan abubuwa da yawa Ciki harda Dad Omar data batawa Dan tasan zuciyarsa ta sosu ko yayane da jin abinda tayi hakama iyayenta fushi sukeyi sosai da ita ga Ameenatou da batajin zata sake ganin mutuncinta ga Jamaal din datai abin akansa ma Ashe mahaukaciya ya dauketa ga Babbah da dauren sadakansa gabaki daya ta rasa inda zata Saka kanta a Cikin dakin ma Ashley da Ameenatou Babu me mata magana mugun zama ne sukeyi gashi kowannensu bai Saba da kwanciyar qasa ba idan ma ka Saba sanyin AC kadai da tiles ya dauka zai iya illata rayuwarka Dan haka bame yafewa haka suke shigewa lafiyayyan gadon dakin Anne suyi bacci Cikin Rufa daya.


Hafiz ne da dadah ke Dan rarrashinsu Suna tarairayansu Amma Didi ko gaisuwan Fatmah din Bata amsawa itada Mum Nur Ameenatou ma Mum Nur tayi fushi da ita akan maganar data fadawa Fatmah sbd tsakanin Dad Omar da Ahmed yanzu Yan uwantaka ce data Fi ta jini karfi Dan kuwa kowa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login