Showing 63001 words to 66000 words out of 261814 words
kanta Dadah dayake sun Dade da dannewa da rufe Babin Omar gaba Daya kwata kwata rayuwarsu Bata nuna komaiba Dan 'yarsu dai tayi girman da zasu iya Bata kariya daga kowa barshi uban nata da basusan ma Yana raye ko mace ba.
**Har yamma Haroon din Baizoba Dan haka Ameenatou tafara Bata fuska tana shiga fushi musamman da yaqi kiranta bayan Hafiz ya tabbatar mata Daya dawo.
Shigewanta tayi daki taqi fitowa kwata kwata a dakin take komai har dare tana fushi Babbah nata aikin rarrashi da Dadah.
Hafiz dai baima da lokacinda harkokin gabansa yakeyi sbd alamu sun nuna Haroon din ya sauya Kila sbd ciwon da yayi da Kuma Maida hankalinsa dayakeson yayi akan gaggawan kawo sauyi da mafita akan illar data rusa aikinsu gaba Daya.
Washe gari da safe tana tashi kashe wayarta tayi gaba Daya sbd ko Haroon din ya kira karya samu
Fitowa tayi sanye da doguwar rigar atampar A shape data zauna daidai jikinta hula data kasa rufe cikakkiyar gashinta me tsayi ce akanta tana son kunna wayar Amma tana Hana kanta.
Gurin Dadah ta nufa tace
"Dadah kisa Yaya Hafiz ya kaini gurin wanke kan fa ni kitso nakeso zafin kaina nakeji sosa"
Dadah datasan a fushi Ameenatoun take cikin kulawa da lallabawa ta kalleta tana gyara mata zaman hular kanta yanda ta sake mata kyau duk da gashin Bai rufe duka ba Yana daure a cikin hulan tace
"Dauko wayata na kirasa yazo yakaiki yanzun Nan"
Juyawa tayi ta nufi dakin dadahn ta dauko wayar ta fito ta Bata tana sake narke fuska kadan take Jira ta fara Hawaye.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
41
Numbern Hafiz dadah ta Nemo a cikin wayarta ta Saka Kiransa
Ringing biyu ya daga waya Kai tsaye ta sanar masa yazo yakai Ameenatou gurin wankin kai.
Bata fuska yayi zai fara fada ta katse wayar bayan tace masa Maza kazo Ina jiranka kar yamma tayi.
Jin alamun Hafiz ya shaqa ya Saka Ameenatou dariyar da tin jiya taqi yi musu a gidan duk sbd fushin rashin zuwan Haroon din.
Ganin dariyarya ya Saka dadah farin cikin ta saki murmushi tana girgiza kan yanda fadansu da shiryawansu a a tare yake tafiya basa iya zama basuyi fada ba hakama basa iya zama a fadan Basu shiryaba.
Qin dawowa a lokacin Hafiz din yayi Saida ya gama abinda yakeyi ya dawo gidan Kai tsaye wanka yayi Yana fitowa Saida yayi sallan laasar kafin yace ya fito su tafi.
Yaya Abdul ne ya bawa Hafiz din kudin suka fice tana kokarin kunnasa da cewa turarensa qamshin rub yakeyi ba kamshi ba.
Dakatawa yaso yayi yace yafasa Kaita Ashe Yaya Abdul na bayansu zai fita yace
"Yi hakuri kyaleta idan kun dawo ka fasa bakin rashin kunyar kafin Babbah ya dawo"
Cikin Naam da Hakan ya wuce gaba Yana cewa
"Tarata nakeyi duk ranarda nayi cikakkiyar lokacinki zan nuna Miki ni ba abokin reninki bane."
Yaya Abdul da yayi magana tana narke fuska zatai magana yace
"wuce ki bisa Dan idan ya tafi wlh Babu inda zan kaiki inda gurin zuwa"
Bayan Hafiz din tabi ta cimmasa suka fito gidan Yana cewa karta kuskura ta nuna masa reni a waje.
Cewa tayi ta yadda sbd itama tana tsoron yakaita gurin gyaran kan ya tafiyarsa yabarta.
Take suka kama wata firar suna mantawa da fada suka fito gida sunayi Yana Bata labarin sauyawan da Haroon yai ita Kuma tace ya Dena mata maganarsa fushi takeyi dashi Kuma duk ya sake kwana Baizo ya ganta ba ko ya kirata cewa zatayi ta fasa auren karatu zatayi.
Murmushin takaici ya sake Yana harararta sbd yasan yanda take son Haroon din fada kawai tayi bazata iya dinba duk da Shima Haroon din son dayake mata yafi Wanda take masa shiyasa yake mamakin abinda yasaka Yaki kiranta tinda ya fara rashin lafiyan Kuma yaqi zuwa gidan duk da ya dawo din Amma shi Yana masa uzurin tarin aikin dayake gabansa Mai tsananin mahimmanci ne kawai ya Saka Hakan.
Suna Isa gurin wankin kan ta shiga shikuma yace zaije ya dawo abinda bataso kenan Amma haka ya tafiyarsa yabarta Amma Saida ya Bada kudin ruwa da wani abin ci ko Sha idan ta buqata kafin a gama tukuna ya wuce din.
Dayake sun Saba da me saloon din ana kawo Ameenatou din tin tana yar budurwan yarinyarta harta kawo yanzu Dan haka tafara kokarin tambayarta Ina su dadah da Babbah harma da yayanta Abdul me kame fuska ba sakewa.
Murmushinta me kyau kawai tayi sbd da yawan lokuta batada sakewa da mutane sbd tsananin taka tsantsan da ake Bata da kulawa Bata wani yadda da mutane sosai.
Fira take mata tana mata wankin kan Wanda duk taji surutun ya isheta suna gamawa wankin kan kafin ayi drying kan ta kira Hafiz tace ya dawo ankusa gamawa.
Har aka gama aka daure kan tsakiyar kanta tareda goge fuskanta ta gyara ta fito fes kyakkyawar budurwanta me daukan ido da hankali ta zauna jiran Hafiz din Wanda sai kusan 6 ya iso ya biya ta fito suka wuce tana narke masa fuskan Baizo da wuri ba saita fadawa Babbah baida aiki sai yawon fira gurin Yan matan da babu me kyau bare maana.
So yayi ya buge bakinta Amma sbd suna hanya ya danne zuciyarsa Yana harararta ta saki dariya me sanyi tana cewa
"Akwai wadda takeda kyau ne? bare kace karya nayi Maka ko sharri nai musu"
Shiru yayi mata yana jiran su Isa gida yaga ubanda zai hanasa yimata duka ayau dinnan.
Dariya taci gaba dayi masa kasa kasa tana jiran su Isa gida ta shige da gudu Dan tasan a cike yake suna Isa Saiya daki bakinta idan ba Babbah ko dadah suka ceceta ba.
Gap da magrib suka iso gidan tana Ganin sun kusa Isa kofar gidan tace
"Yaya Hafiz naga Kanata kumbura nidai kayi hakuri to Karka tabani tinda kaga oganka fa yake sona Kuma kana tabani zai iya baka aikin wahala a gurin aiki ka......
Kafin ya qarasa ya daga hannu zai buge bakinta sbd sun kawo gap da kofar gidan Dan haka tayi gaba da gudu ya shige gidan daidai fitowansa daga cikin gidan Da gaba Daya ya sauya iskan gidan da qamshinsa Daya sakata saurin dakatawa sbd kirjinsu Daya Hadu sbd baisan da shigowan kowaba kaman yanda itama data zo da gudun batasan da tahowansaba.
Cak ta tsaya gabansa tareda dago fararen idanuwanta ta zuba masa sauran murmushin dayake kan fuskanta data shigo dashi Bai qarasa bacewaba ta tsayar da idanuwanta akan fuskar Data Saka kirjinta mummunan bugawa hakama bugun zuciyarta qaruwa yayi tana kasa motsawa hakama tinaninta tsayawa yayi cak.
Kafin tayi Baya shine yafara Baya alokacinda kirjinsu ya Hadu batareda ya dago ya Kalli fuskartaba a cikin wani fitinanniyar nutsatsiyar murya me sanyi da kamalan Dake hade da kamewa yace
"Sorry" Yana rabata ya wuce batareda yako kalletaba bare sanin itace Ameenatou din.
Kasa motsawa tayi daga inda take tsaye harya fice daga cikin gidan yabarta da qamshin turarensa Daya cika hancinta Yana toshe kanta daga tinanin komai bayan na mamaki.
Hafiz ma dayayi kusan mutuwar tsaye daga abinda ya Gani din ya faru kasa motsawa yayi Saida siddeeq ya fito daga cikin gida Yana yiwa dadah saida safe daukeda basket din abincin da aka Saba kaiwa Haroon yagansu tsaye baisan meya faru ba Dan Bai dauka sun Hadu ba sbd saurin dayake son suyi Subar gidan kenan kada Ameenatou ta dawo su hade sbd Yasan waye JEEY idan zai iya komai har abada bazai iya kallan wata macenba Koda ba Sonta yakeyiba da sunan sake mata.
Ganin Ameenatou da Hafiz Basu ce komaiba ya Sakasa silalewa ya fice.
Ameenatou kasa motsawa tayi sbd duk da Babu haske sosai magrib tayi tana ita tantance sauyin Haroon dinta Koda ta iskan Daya bar mata tana shaqa ne da qamshinsa yake daban da dukkanin abinda hancinta ya taba shakar mata.
Hafiz dayaji ana kokarin tada sallah wucewa yayi ciki Yana cewa
"Ki wuce ciki naje nayi sallah na dawo mu Dora inda muka tsaya"
Daga kafarta Daya tayi datai mata sanyi tayi tana wucewa ciki bugun zuciyarta har lokacin Bai dawo daidaiba,batama tantance Menene ya faru ba mintinan da suka wuce,
Haroon dinta ne a gabanta ko kuwa sabon Haroon aka sauya mata a duniyarsa Babu abinda yake masa kyau da kasa Dena kalla idan ba itaba.
Tana shigowa cikin walwala dadah ta kalleta tana cewa
"Yanzu Haroon ya fita sedai baima zaunaba gaisawa kawai mukai siddeeq yace Abuja zasu koma da Daren Nan acan ya zasu kwana"
Hafiz Dake alwala Bai juyoba yace
"Mun Hadu zai fita Amma dai inaga kaman Bai gama warwarewaba Dan baima ganemu ba a duhun duk da Babu wani duhun"
Ameenatou data kasa magana har lokacin sai Daya gama maganarsa ta Bude Baki tana kallan Dadah da idanuwanta da suka sauya tace
"Kaina ciwo yakeyi Dadah aban magani"
Kallanta Hafiz yayi Yana ficewa tafiya sallah,
Dadah kuwa wayar hannunta ta karban mata tana cewa
"Kiyi alwala tukuna idan kin Sallah kunci abinci be Dena ba sai asha maganin"
Gyada Kai kawai tayi ta wuce tana Dora tana kirjinta dayake buga mata ba daidaiba Bata taba Jin Hakan ba sai tsoro ma yake Neman kamata inde na zuciyarta ta samu matsala bane aikuwa bara Babbah ya dawo.
*******Daga kofar gidan Kai tsaye Abuja suka nufa siddeeq ne Mai tuka motar shikuma Yana waya da mum dinsa wadda yake magana da ita a natse cikin Kwanciyar hankali Babu hayaniya bare daga murya ko sauri,
Kaman yanda yake komai a natse haka yake wayoyinsa a tsanake da aji.
Suna Isa Kai tsaye lafiyayyar gidan da aka kama masa aka sauya mata komai zuwa yanda zai iya rayuwa a cikinta kaman Yana Poland haka Akai mata siddeeq ya nufa dashi ga securities sosai a anguwan Amma dai shi Babu Wanda ya dauka Dan qasar ne sbd yanayinsa Dan kamanninsa tareda irin tsarin rayuwar dayake gudanarwa.
Sama da qasa ne Dan haka Kai tsaye sama ya wuce siddeeq Kuma bedroom dinsa aqasa yake.
Yana shiga bedroom dinsa wayarsa ya ajiye tareda id card na Haroon dayake jikinsa ya kwabe kayan jikinsa dagashi sai wani tsadaddiyar underwear Dake jikinsa ya nufi toilet Yana shafa gashin kansa me tsayin gaske Daya Yanke sbd Haroon.
Wanka yayo kusan mintina masu Dan tsayi kafin ya fito dauresa towel dinsa datake Neman zamewa ta Fadi fatan jikinsa fresh sai kyalli takeyi ya nufi mirror Yana kokarin miqa hannunsa kan body oil dinsa wayar Haroon Dake kunne gefen tasa kira ya shigo cikinta Wanda ya sakashi dakatawa daga abinda zai dauka Yana kallan sunan sake rubuce kan screen din da manyan letters 'DAD'
idanuwansa ya dauke daga sunan Yana qin daga Kiran Kai tsaye har Saida ta tsinke Kiran ya sake shigowa daidai lokacinda ya ajiye towel Dake hannunsa qarami yayi receiving call din Wanda Dad Bai tsaya komaiba yace
"Haroon Ina buqatan ganinka a Lagos gobe kome kakeyi ka ajesa ka biyo flight"
Bai tsaya Jin amsar Haroon din ba bare tambayar jikinsa ya kashe wayarsa.
Wayar JAMAAL ya zubawa idanuwansa da suka sauya take kafin ya saki wani mayen numfashi a natse.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
42
Kayan baccin Avves masu santsi da tsadan gaske ya Saka sedai baima rufe gaban riganba ya fito lafaffiyar cikinsa dake fidda murdewan jikinsa sbd motsa jiki ya sauko kasa sbd Yana buqatan ruwa da drinks sbd aikin da zai kwana yanayi sallah Kuma Daman kafin su baro Nasarawa sunyi ishai ma kafin su shigo gidan sunyi.
Siddeeq ma tini yayi wanka ya shirya cikin gajerun kayan baccin da sukaiwa jikinsa kyau Shima Dan Shima Yana motsa jikinsa sosai Dan hakane ma yafi Haroon budaddiyar jiki kaman ubangidansa.
Shima fitowansa kenan yaji saukowan JEEY da kamshinsa Dan haka ya dakata harsaida ya sauko kallo Daya yayi masa ya dauke idanuwansa sbd JEEY SEELAH ko namiji Dan uwansa yake kallansa zai iya kamuwa da sonsa bare mata Danma Baya mu'amalantar inda mata suka yawaita da baasan irin matan dazai samu masu jiransa ba, har mamakin yanda JEEY din ya kamu da son fadila yakeyi da yanda zuciyarsa take riqe da iya ita kadai yakeyi.
Ruwa Jamaal din ya buqata da E-Bull energy drink dinsa.
Daukowa siddeeq yayi ya kawo masa ya ajiye a gefe hakama already tarin manyan takardun abinda zasuyi suna gurin zube.
Kafin ya fara aikin bayan ya zauna dago fararen idanuwansa yayi ya Kalli siddeeq ya Bude Baki a natse yace
"Zamu bi morning flight zuwa Lagos ka duba mana idan akwai"
Dagowa siddeeq yayi ya Kalli JAMAAL din cikin mamakin ta yanda zasu fuskanci juna da Dad dinsa batareda ya gane shi bane,
Hakama shi kansa Jamaal bazai iya kwantar musu da Kai ba komai tsanani kaman yanda Haroon kansa bayama dagowa a gabansu saita Baci.
Cikin nutsuwa da tinani siddeeq ya sake kallansa Yana cewa
"Dr ko zan kira Dad din na sanar masa wani uzurin dazai daga tafiyar gobe zuwa jibi idan Barr da Mum din sun iso"
Girgiza Kai yayi a natse Yana cewa
"Ba buqatan Hakan,zangansa da kaina"
Sake shiga fargaba Siddeeq yayi duk da yasan idan Jamaal din ya fada ta zauna Amma a gaban Dad Kam Abu ne me wuyan gaske idan baa take zai sheda Jamaal ne gabansa ba ba Haroon dinba ko daga kamshinsa da Baya boyewa kowa da Kuma fatansa data banbanta data Haroon duk da idan suna rarrabe baka ganesu Se Wanda yayi da gaske gaske idanma kayi musu farin sani kenan hakama izzar Jamaal har abada ba Daya take data Haroon dinba.,
Tayaya Jamaal zai iya tsayuwa a gaban Dad dinsa batareda yayi masa kallan dazai Saka Dad din take Ji ajikinsa Jamaal ne.
Jamaal Daya miqa hannunsa a natse ya dauki drink din gefensa ya Bude yakai bakinsa yasha kusan Rabi ajiyewa yayi Yana Bude laptop din Dake gabansa ya kunna kafin ya fara janyo takardun Yana budewa tareda jerawa a gabansa sbd acikin kankanin lokacinda bazai ci masa time din komawa rayuwarsa ba yakeson kammala dukkanin aikin project din sabo da zaiwa Dan uwansa ya tattara ya koma bama tareda wani yasan ya shigo qasar ya fice ba.
Shima siddeeq tattara hankalinsa yayi sbd nutsuwa ga aikin da Jamaal zasuyi.
Nutsuwa yayi sosai Yana aikin cikin kwarewa da tabbatarda komai ya tafi daidai,Shima siddeeq mayarda hankali yana Wanda zaiyi a cikin aikin.
Har kusan hudu saura na guraren asuba suna aikin kafin suka ajiye suka nufi dakunansu.
Jamaal na shiga bedroom dinsa Kai tsaye toilet ya nufa yayo alwala ya fito ya Dora gatuwar jacket akan kayan jikinsa na bacci ya rufe batiran rigarsa Dake Bude ya Saka qaramar hulan sallah fara akansa ya tayarda sallan nafila.
Yana gama sallolin nafilansa ya miqe Dan sallahn asuba da Akai kira har ana kokarin tayarwa daga masallatan nesa Dayake jiyowa.
Bayan gama adhkar da adduoinsa miqewa yayi ya cire hulan da jacket din ya nufi gadonsa ya haye tareda kashe komai tin daga kan wayoyinsu da wutan dakin ya shige bargo a nitse Yana lumshe idanuwansa.
Bacci sosai yayi ya samu hutun jikinsa Dana kansa harma Dana zuciya kafin ya tashi guraren 10 da wani abu.
Toilet ya nufa Kai tsaye yayi brush da sauransu tukuna yayo wanka ya fito daure da towel ya nufi inda wayoyinsa suke ya miqa hannu ya kunnasu kafin ya wuce gaban mirror Dan shiryawa.
Bai wani dauki time ba ya shirya ya fito cikin Ash kaftan din Tsadaddiyar yadin cashmere data tsananin sake sauya kamanninsa zuwa wani bakon baturen bahaushe hakama hulan Daya Saka ya rufe gashinsa Daya sake banbantasa Dana Haroon ta qara masa kyau sosai.
A Karan farko rayuwarsa dayayi amfani da wani turaren daba nasa ba Dan haka yakejin Baya wani Jin dadin iskan Daya bayarwa a jikinsa duk da Wanda yayi amfanin dashi Shima mugun designer ne sedai qamshinsa Daya Saba dashi daban yake a gurinsa.
Siddeeq da tini yayi musu booking tickets din 12 Dan haka Shima ya shirya tsaf cikin kaftans din Shima sai Jakar takardun aikinsu Dan laptop din dasuke hannunsa.
Jamaal na saukowa cikin girmamawa ya masa barka da saukowa kafin ya biyosa suka fito tare Jamaal din suna magana.
Siddeeq ne me tuqin Dan Jamaal Kam bayajin zaiyi tuqi harya gama ya tafiyarsa inda ya fito.
Kai tsaye office din dazai fara gabatar da aikin anan Abuja ya nufa ya zauna dasu ya gabatar musu da sauyin aikin dayayi tareda sababbin plans din dasuka matiqar Basu mamaki da sakasu farin ciki me tsananin gaske Dan kuwa tini suka fara Shirin gabatar da takardun soke aikin kwata kwata tareda raba hannunsu Dana Seelahs,
Hannu suka miqa masa cikin Jin dadi tareda taya junansu murnan sake samun damar aiki a tare Shima hannun ya miqa musu Yana sake gabatar da kansa BARR HAROON SEELAH.
Cikin farin ciki suka sake amsar tayin aiki da juna take akai hotuna da sabon Saka hannu akan new project din dazai maye wancan.
Sai guraren 11:20 suka baro Kai tsaye daga Nan office din airport suka nufa suna Isa suka ajiye motar anan airport suka shige jirgi sbd sunma iso kusan late.
A cikin jirgin yayi breakfast dinsa hankinsa kwance da nutsuwa sabanin siddeeq Daya kasa samun nutsuwa ko Kwanciyar hankalin sbd abinda zai iya faruwa idan aka samu matsalan Dad suka gane.
Suna sauka Lagos drivern Dad dinne yazo airport daukansu sbd shi Jamaal din da kansa Daya turawa Dad text din azo a daukesa daga airport Nan da awanni.
Da farko kaman Bai gane ba Saida ya sake karantawa ya tabbatarda Haroon dinne yayi masa sakon A tura driver ya daukosa daga airport.
Numfashi ya sauke ahankali Yana jinjina lallai Haroon din yafara samun karfin zuciya tinda ya iya masa sakon Kai tsayen Nan Mai kama Dana Bada order.
Driver na Isa airport Kai tsaye siddeeq ne ya budewa Jamaal kofa ya shige bayan kafin Shima ya zagayo ya shiga gaban motar driver Dake Satan kallan Jamaal din ta mirror cikin girmamawa yace
"Barka da dawowa Sir Haroon"
Gyada masa Kai kawai Jamaal yayi sbd hankalinsa na kan sakwannin asibitin Haroon da aka turo na can Poland Yana karantawa.
Suna isowa mansion din Jamaal ya hadiye wani abu Daya danne maqoshinsa Yana kashe wayarsa