Showing 1 words to 3000 words out of 261814 words
*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar
#BlackMoneyLove
*_Littafin da labarin Ameenatou Wanda ni mamuhgee na rubuta gabaki dayansa sadaukarwa ne ga irreplaceable Besty na AMEENAH ABDULMALEEK (Meenal Maleek)🤍💋_*
1
BismillahirRahmanirRaheem.
Kaman yanda yake a tabbacen zance Salati baya hana ɗaukar rai, Hakama Ƙasar kabari bata shuka sedai ta binne binnanne,
Itadai ƙaddara yashi ce ko an dunƙulata bata dunƙuluwa,
Rayuwa da kaddara a tare suke tafiya tamkar Yan uwa Daya sbd haka kowace rayuwa take tafe da tata kalar kaddara duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya.
****Cikin tsananin sauri da rawar jiki me tsananin gaske dattijuwar dadahnsu ta fito daga dakin da suke ba tareda ta damu da tsananin ruwan saman da akeyiba masu karfin gaske da iska ga Kuma duhu me.
Runfar madafarsu ta girki ta nufa tareda Saka hannuwanta duka biyu ta share ruwan Dake sauka kan fuskarta sbd ta Gani da kyau.
Madafar data gama jiqewa tsaf ta zubawa idanuwanta da sukai jajir cikin nauyin zuciya da tashin hankali Amma Kuma halinda suke ciki a yanzu ya wuce taji radadin baqin ciki ko wanne iri Dan haka ta qarasa inda murhun wutarsu yake ta fara kokarin gyara Yan sauran itatuwan Dake gurin tana hada kansu Dan hura wuta kota Yaya duk da ruwa da iskan da ake zubawa me karfin.
Motsi taji a bayanta sedai Bata iya juyowa ba sbd kokarin hada wutar cikin sauri dan tasan ba kowa bane face babbah mahaifin 'yayan nata mijinta.
Zagayowa yayi ta gefenta Shima a jiqe kayansa na tsiyayar ruwa sosai hakama rawanin Daya zagaye kansa dashi sbd ruwan Shima ya jiqe sosai Yana tsiyayar ruwa.
Duk ruwan Nan da akeyi akansa aka farasu Yana tsaye kofar dakin da suke Tin safiyar ranar har zuwa yamman sallah kawai ke matsar dashi daga kofar dakin har hadarin ya Hadu Yana tsaye duk karfin iskan da aka fara aka fara ruwan Yana tsaye a gefen dakin Yana jiran tsammani ya zauna ya tashi tsaye,yaje farkon Bango ya dawo Babu abinda yake fata Se Allah ya kawo musu wannan lamarin a cikin sauki ko Dan jarabawa da kaddarorin da suka ringa haduwa dasu a rayuwar Nan.
Tayata hada kan itatuwa gurin da hura wutar yafara kokarin yi Yana Dan rife idanuwansa dasuka manyanta sosai tsufa yafara saukar musu sbd ruwan Dake shiga cikinsu,
Ita kanta dada kokarin kunna ashana takeyi amma ruwa da iska Baya bari Amma takasa Dena kokarin kunnawar hannuwanta na kakkarwan sanyi da mutuwar jikin damuwan Dake dabaibaiye da ita Mai hade da tsananin tsoro.
Shi kansa babba dayake tayata kare iska da ruwan da hannuwansa Dan ta kunna wutar yasan wura wuta a wannan lokacin ba abune da zai taba yiyuwa ba har abada sbd ita kanta ashanar tsiyayar ruwa takeyi Amma dukkaninsu sun kasa yarda da sallamawa sbd Babu Wanda zuciyarta take a daidai da tinanin nutsuwa a cikinsu abu Daya ne a ransa shine bazasu iya rayuwa ba idan wani abin ya samu wadda ke cikin dakin gurin haihuwar abinda yake cikinta,
Itace duk wani karfin zuciya da karfin halin dasuke dashi na ci gaba da rayuwa bayan masifun dasuka ringa shiga,
Babba shine shugaban gidan Kuma gatansu Wanda ya kasance jigonsu,shikuma babba itace hasken zuciyarta Kuma nasa jigon Dan idan Babu ita baida jarumtar cigaba da zama shugaba a cikin Iyalin nasa.
Hannuwansa Dake Dan rawa Shima ya miqa ya karbi ashanar hannun nata yafara kokarin tayarwa Amma kwalin ashanar narkewa ma kawai yafara yi a tafin hannunsa sbd ruwan Daya gama jiqasa..
Qurawa tafin hannunsa idanuwansa dasukai jajir yayi Yana kasa motsawa bare cewa komai zuciyarsa na daukan wani irin nauyi da dumi a lokaci Daya.
Dadah ma da jikinta ke mutuwa dagowa tayi da jajayen idanuwanta ta kallesa zuciyarta na yankewa da ganin yanayinsa,
Yanda yake tsananin son mahaifiyar Ameenatou da Ameenatou haka take tsananin sonsa Dan haka bazata bari ya sake dandana radadin rashin da yayi a Baya ba na rashin ganawa da Rabin jikinsa Dan haka jikinta na rawa ta juya ta nufi inda tasan akwai wata ashanar ta dauko tafara kokarin wura wutar da idan har gawar Dake Rami zata fito tayi magana to tabbas tashin wuta a wannan lokacin zai yiyu.
Ahankali babba ya Bude idanuwansa dake rintse ya Kalli dadah Daketa aikin abinda bame yiyu bane Amma taqi denawa Se qarawa takeyi kaman batasan ruwane ke tsiyayar daga shanar ba.
Hannu ya miqa ya karbi ashanar ahankali tareda saikinta qasa ya kamo dadan suka bar gurin zuwa kofar dakin da ake komai a ciki sedai kafin su iso matar Dake ciki ta fito dakin gabaki dayanta itama a jiqe da zufa jikinta duk a sake.
Zuba musu idanuwanta tayi kaman yanda suma zuba mata nasu idanuwan suka zuba mata kafin babba ya dauke kallansa daga kan matar ya mayar kan kofar dakin Yana kalla cikin sanyi da wani irin zuciya dayaji Yana saukar masa Yana barinsu.
Dadah ce ta iya samun karfin halin Bude Baki cikin sanyi tace
"Ameenatou ta....??? Kasa qarasawa tayi sbd batasan amsar da Za'a bata ba idan ta qarasa tambayar.
Numfashi matar ta sauke ahankali tareda kallansu su biyun cikin nutsuwa da kaucewa matsala tace,
"Bazan iya ba dole ayi gaggawar kai ta asibiti kafin wata babbar matsalar data fi wannan ta biyo baya."
Shiru dukkaninsu sukayi jin abinda ta fada,
Ruwan dake sauka kansu kawu ya kalla Dan baisan tayaya zaa fita da mara lafiya a cikin wannan ruwan me karfi ba zuwa asibiti yanzu yanzu ba.
Dadah data kasa cewa komai dakin kawai ta shige tana hadiye hawayen dasuke ciko idanuwanta Dan gano 'yarsu.
Babba Kuwa juyawa yayi Shima batareda yace komaiba Dan Nemo abin hawan tafiya asibitin cikin gaggawa duk da Samun abin Hawa acikin ruwa me qarfi irin wannan tamkar shige ruwa neman allura.
Tsayuwar dadah akanta bayan shigowa dakin yayi daidai da fara jijjigarta Dan haka take jikin dadah yadauki rawar discon da Bata shirya ba,murya rikice a karye ta kwada kiran Hafsatu datake wajen tana kamo 'yarta jikinta tana rokon kada Allah ya dauki ranta a yanzu yabarsu da ita.
Hafsatu data shigo dakin a rikice idanuwanta na dauka akan yanayin ta qaraso a cikin sabon rikicewa tana cewa,
"Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Shikenan, shikenan, innalillahi wainna ilaihirrajiun..""
Dadah da kunnuwanta suka dauke ji a take dago jajayen idanuwanta tayi tana kallan Hafsatu kaman wawuya takasa furta komai sbd Jin komai na 'yarta ya tsaya cak a jikinta.
_MAFARI_
_SHEKARUN BAYA!!!!!!_
SEELAH'S shine karbabben sunan Aminai biyar da suka taso tamkar uwa Daya ne Uba Daya ya haifesu,
Kauna,shaquwa,AMINCI,yarda,hakuri da tsananin son juna da sukeyi shine ya samar da sunan SEELAH a tsakaninsu Wanda yake dauke da maanar karfin daukaka.
A farko su din bayi ne da suka taso cikin wahala da bauta tareda leburanci a babbar taskar gino danyen zinarin gwal.,
A rayuwar Gina ramukan Nemo zinari suka taso suka girma har Suma suka gada 'yayansu ma suka gada daga garesu,
Basada lokacin iyalansu sbd wasu lokutan idan suka shiga ramin da tsawonsa da zurfinsa tareda duhunsa da azababben zafin da yake kashe wasu da dama aciki sukanyi kwanaki da Basu fito ba.
Ahaka suke rayuwa wadda babu ranar da baa samun mutuwa a cikin ramin Dan kuwa ginar zinari Yana tafiya ne da ginar kabarin binne wainda jininsu yake tafiya a cikinsa.
MAMMAN SEELAH,OMER SEELAH,LAMEENU SEELAH,KASIM SEELAH da JAMIL SEELAH sune Aminai biyar da suka taso a tare cikin tsananin shaquwa da tsananin hadin Kai tamkar iyayensu da suka taso a Hakan tare tin kuruciya har girma har suka rasu Daya bayan Daya duka a harkar zinari Dan haka suka a tare suka taso tamkar iyayensu dauke da sunan SEELAH Wanda aka shedasu da shi gabaki Daya kauyensu da zagayenta.
Da farko su din sun banbanta da iyayensu sbd halayensu dasuke a Dan banbance tareda raayoyi Amma duk da Hakan kusan su kansu sun shedan da Babu wata kauna ko shaquwa bayan tasu shiyasa da yawa baa San ba iyayensu dayaba a idanuwan mutane su din yayane na uwa Daya Uba Daya.
##MAMUH#
#BLACK MONEY
#BEST LOVE STORY
#ZAFIN KAI
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#AMEENATOU
#2024ROMANCE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_* _Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar
#blackMoneyLove
2
Kaman yanda suka Saba duk zasu shiga Rami a tare suke shiga basa yadda su shiga ba tareda Dan haka Basu taba shigar ba tareda junansu su biyar din ba.
Gyara tsayuwa mamman yayi Yana Dan gyarawa daurin jakar kayansa a qugunsa Yana kallan omer da kusan shine koyaushe me zama karshen Shiga Dan ya yaddarwa kansa idan kullum suna shiga su fito wataran yasan idan suka shiga bazasu fito din ba.
Shiga sukai da karfin gwiwansu tareda qarfin zuciya Dan kuwa ginar zinari Se me taurin zuciya da rashin tsoro,
Rami ake ginawa me zurfin gasken da idan ka shiga zafinsa da duhunsa kadai zai iya kashe me qaramin karfin jini ko me tsoro,
Da fitila ake shiga tareda batiran fitila da ruwan Sha duk a jikinka daure sbd idan ka shiga bawai Kai tsaye kake fitowaba wasu sai suyi kwana Daya a ciki wasu fiyeda kwana Dayan da kwanaki ma duk sunayi a ciki sbd ba wai Rami ne da zaka ringa shiga Kai tsaye kana fitowa ba,
Idan wainda suke ciki suna ciki to ko magana zaayi musu Saida loudspeaker sbd sunyi Nisa a cikin qasar da ba zasuji magana Kai tsaye ba.
Aduk lokacinda zaa samu zinari ko ginosa to tabbas jinin rayukan mutane da dama zasu salwanta sbd hadarin Dake ciki tareda wani irin son zuciya me qarfin gaske,
Rijiyar Gino zinari bawai Rami ne na qasa ba zaa ringa ginawo Rami ne dazaa ringa ginawa a cikin qasar tareda dutsina masu karfin gaske Wanda shiyasa hadarinsa yakeda yawan gaske sbd wani dutsin kana bugosa a cikin ramin zai rufeka gaba Daya ya zubo ya danneka ba iya Kai Daya ba zai iya zubowa ta koina yayi sanadin Rai fiyeda adadi Wanda da yawa ana ji ana Gani za'a samu Ciro wasu wasu kuwa qasa ta ciny shikenan sbd bazaa iya cirosu ba alokacin,
Idan zaa haqo rijiyoyin zinari a gurinda ake da tinanin akwaisa ana haqo akalla rijiyoyin da fadinsu da zurfinsu bamai misaltuwa bane a gurin akalla daga rijiya goma Sha biyar zuwa sama har dari biyu Wanda jiri ma zai iya Kamaka idan ka tsayu a gurin.
Zinari nada wani Sirri Wanda shine a duk lokacinda jinin wani ya zuba to takan qara yaduwa ne tamkar Shukan da ake bawa ruwa.
Su mamman tin iyayensu na raye suke yawon nahiyoyi daban daban dan Gino zinari Wanda idan suka bar gida akalla sukan shafe watanni da yawa basu dawo ba sunacan cikin daji da Sahara da yawon kauyuka masu Nisa da hatsarin gaske Dan Neman zinari Amma har Allah yayi musu rasuwa Daya bayan Daya duk a harkar Basu samu komaiba bare Tarawa Dan haka yayansu suka dauki Niya da damara tareda alkawarin ko da dadi ko ba dadi,Koda jinin wasu ne saisun samu bazasu qare a wahalce kaman yanda iyayensu suka qare a daji da nahiyoyin nesa Dan Neman zinari ba.
Mamman a cikinsu shine Wanda yafi kowa karfin hali da rashin yadda Koda wasa a tauyi haqqinsu Dan haka suke Dan samun na abinci a harkar duk da Suma har lokacin Allah Bai Basu tasu nasarar ba Amma Basu cire Rai ba Dan yanzu suke matasansu.
Omar a cikinsu Kuma shine Wanda yafi kowa sonsu,
Yana tsananin kaunarsu fiyeda kansa sbd shi Kuma duk abinda ya samu su yake miqa Se yanda Akai dashi duk da Suma sauran suna tsananin kaunar junansu.
Dukkaninsu dai marayu ne tinda Babu me Uba a cikinsa hakama iyayensu mata biyu rasu, mahaifiyar Omar da mahaifiyar mamman,
Tinda suka fara Dan tasawa Suma idan suka bar gida suka kutsa nema saisu share watanni fiyema da yanda iyayensu ke dadewa batareda sun dawo ba sedai duk inda dayansu ya Saka kafa suna nan a tare kaman kashin awaki a manne da juna shiyasa kusan ake da saurin saninsu a duk inda suka yada zango sbd Yan biyar seelahs da ake kiransu.
Shekaransu bazasu wuce Sha takwas zuwa ashirin ba a lokacinda Allah ya bayyanar musu da babbar sa'ar rayuwarsu Kuma babbar musibar rayuwarsu ba.
A babban dajin kauyen ashalawa Dake wani yankin Daya raba shiga nijar da Nigeria suka yada zango kusan shekara Daya har sun zama Yan gari Yan gida Dan kuwa duk kusan da yawan jamaa sun Sansu Kuma suna Jin dadin aiki dasu Dan kuwa sunada karfin halin gaske da taurin zuciyan neman arziki ido rufe Dan kuwa sun dauki alwashi sun duqufa bazasu koma gida ba batareda arziki ba Wanda kusan zuciyar kowannensu ta sauya kudin arzikin zinariya kawai kota yaya.
A ashalawa wata babbar duniyar Neman zinari ce sbd asalinta ba gari bace bare kauye,
Tarin matafiya da Yan kwadago da Yan cin kasuwar gari gari tareda asalin buzaye masu harkar danyar zinari da Yan Nigeria Suma masu harkar rijiya da Kuma danyar zinari ne suka taru suka Maida asalin dajin da aka Gano tarin arzikin zinariya acikinsa gari guda,
Sun Maida dajin ya koma kusan babbar garinda kasuwar duniya kawai akeci a cikinsa,
Ashalawa baida dare baida Rana bare asuba,
Kowanne lokaci su a gurinsa lokacin harka ne Dan haka Koda yaushe a hargitse yake kowa na abinda yake gabansa,
Babu Mai auren da zaka samesa da iyalinsa a ashalawa sbd gurine da babi yiyuwar kawo iyali Dan kuwa Babu kalar kaddararrun mutanen da babu masu rayuwa daban daban,
Tarin karuwai masu aji da masu saukin kudi Babu kalar wadda babu a ashalawa,
Idan Maza kake so kayi muamala dasu akwaisu,
Akwai matasa akwai manya,
Hakama ta bangaren yare da kabila kusan Babu kalar Wanda Babu,
Babu wasu gine gine a ashalawa sai runfuna da tinti da kusan sune suke cikewa ashalawa sunfi dari biyu zuwa dari hudu ma,
Gine ginen Dake ciki ko dozin bazasu kaiba Suma na wainda suka riqa ne suka samu zinariya sosai suka Gina suka zuba karuwansu da suka koma tamkar matayensu Dan kuwa duk Wanda ya jiqa a ashalawa bazai rasa akalla karuwan kansa kusan guda shida zuwa sama ba,
Marasa karfi sosai sune suke da karuwai bibbiyu haka ko Daya zuwa uku Amma dai sauran har me goma akwai.
Masu siyar da abincin ashalawa dukkaninsu Suma kaman mata Maza suke wasu kuwa karuwan ne Dan kuwa idan baka bazaka iya kashewa ko illatawa ko zama busashiyar zuciya bazaka taba iya zama a ashalawa ba.
A garin ashalawa Babu ranar da zinariya Bata kisa hakama Babu ranar da wani Baya illata wani ko kashewa,
Idan baka zuciyarka bata bushe qamas ba Kokuma Daman Tim farko Kai din me busashiyar zuciya ce zaka iya komai Dan ka tsira to bazaka rufa sati Daya a ashalawa ba batareda ka Isa kofar barzahu ba Dan kuwa rayuwa ce akeyi ta ko ka kashe ko akasheka Dan haka zinariyar ashalawa take sake habbaka da yaduwa koyaushe sbd jininda babu ranar da Baya zuba Kuma jini irin Wanda takeso wato me zafi na fitar rashin Imani maana jinin kisar gilla.
Tafiya me tsayi ta kwanaki da satika harma da wata ce ta kawo su mamman Ashalawa inda sukaga duniyar da Basu taba Gani ba Dan kuwa ashalawa wata duniyar ce ta daban me zaman kanta.
Da farko sunsha wuya sosai daqyar suka tsira suka Kai lokacinda suka fara gane kan rayuwar tsira ko mutuwa akeyi a Ashalawa Dan haka mamman ne ya fara tsayuwa ya jefar da tausayinsa gefe ya dauki rashin imaninsu da rashin tausayinsu ya tsayawa Yan uwansa suka fada harkar haqar rijiyoyin zinariyar ashalawa wainda akalla akwai rijiyoyin da aka Tona a gurin sunfi dari uku Kuma Babu wadda idan ka tsaya gefenta zafin ciki kawai idan ya huro Maka zaka iya Yanke jiki ka Fadi sbd tsananin zufinda zaka share fiyeda awanni masu yawa baka Isa kasanta ba.
Duk bulayin yawon shekaru masu yawa da iyayensu sukai harma dasu wanda sukai sai da suka iso Ashalawa suka San sun iso inda ya kamata ace sun samu isowa tin lokacin iyayensu Dan haka gabaki dayansu su biyar din Babu Wanda baisan a yanzu duniyar dasuke buqata ce suke.
Tinda suke a rayuwarsu tin daga lokacinda suka fara takawa da kafafunsu Basu taba zuwa koina ba batareda juna ba har suka girma wanka ne kawai yake rabasu Shima ba koyaushe ba sbd a ruwan gulbi suke wanka a tare sai Kuma su share kwanaki kafin su sake samun wata damar wankan sai zuwansu Ashalawa suka fara abubuwa ba tareda Shima shiga rijiya ne kawai sukeyi Hakan Wanda idan sun shiga sukan kwana Basu fitoba Dan haka kowa ya dage Dan kuwa yanzu kowa arzikinsa na hannunsa idan ya dage musamman Omar Dake da burin bawa kansa ilimin boko sosai da tasa dukiyar sabanin sauran da babu me dogon alkhairi a ransa.
Shekaransu Daya a Ashalawa sun goge sun zama gaba gaba acikin matasan da ake ji dasu a harkar,
Ba wasa ko tausayi aharkarsu,
Mamman kaf ashalawa bayan Yan uwansa seelahs babu Wanda bazai iya zubarda jininsa a qasar Ashalawa.
Kaman yanda kowa arzikin da Allah yayi masa daban haka Allah ya fara bayyanarda arzikin Dake tattareda kowannensu sbd sun fara Tara abin kansu suna samun zinariya sosai Dan yanzu zubar jinin a ashalawa yawa yake sake yi Kuma kullum samun baqin da Suma imanin Bai ishesu ba akeyi suna zama Yan gari Suma.
Turawa da labawa dakuma wakilansu sosai suke shigowa ashalawa wasu ma da helicopter ake kawosu suyi huldan su hau helicopter din su koma.
A taqaice ashalawa headquarter ce me zaman kanta ta huldar danyar zinariya wadda ake hadawa da gudanarwa cikin rashin gaskia Dan haka turawa da labarawa sosai suke Hulda da Yan Ashalawa Kuma Suma Yan ashalawa sunfi Hulda dasu sosai Dan baka iya fita Ashalawa da danyar zinari idanma ka hada sbd ta kowanne dajin da zaka fita masu jiran ka fito su kasheka su karbe suna Nan suna Jira.
#MAMUH#
#BESTLOVE
#ZAFIN KAI
#BLACKMONEYLOVE
#ROMANCE
#JAMAAL JEEY SEELAH
#TOOTOOHOT
#ZAFAFABIYAR
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_AMEENATOUH_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar
3
Da yamma ne sosai suka fito daga rijiyar zinarin bayan kwanaki da share a ciki,
Lameenu ne yafara fitowa da kyakkyawar sa'arsa ya samo zinariya me Dan yawa,
Murnarsa kasa biyuwa tayi duk da jikinsa Dake rawa sosai na tsananin wuya da wahalar Daya debo a ciki.
Mamman ne