Showing 252001 words to 255000 words out of 261814 words

Chapter 85 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9986

a tare ya gansu a tare ya sansu Kuma alaqa ce data Riga ta zama family bazata taba gogewa ba sbd kaf gidan har Ahmed din kowama yayansa da matarsa da Jaden suke amfani a sunansu kaman yanda yanzu duka harsu Hafiz duka an qara jdens a karshen sunayensu so maganar iyaye da rashin daa ba dabia ko hali bane.


Anyi Taron kwana uku din a Abuja an gama a ranar Jamaal ya dawo Lagos tareda Siddeeq Banda su Mum dinsa da ba yanzu zasu dawo ba sai sun kwana biyu sbd wasu manyan kwararrin likitocin da Omar zai hada da Dr Aleena.

Duk Yanda Omar da Aleena din suke ganin yayansu sun girma Basu San sunada sauran lokacinsu ba sosai Saida suka kasance da juna a kwanakin sbd wata lafiyayyan sanyayyan soyayya ce me karfi da kwanciyar hankali suke gudanarwa hankali kwance.

Omar Jaden Bai baro Abujan ba Saida maganar aurensa ta fita duniya tasan matarsa ta biyu wadda ta fita tareda maganar auren 'yayansu,

Ya gabatar da Dr Aleena second wife dinsa da Kuma son dayake mata itama kaman yanda yakeson matansa duka Dan haka take aka ringa daukansu hotina ana yadawa Kuma kowanne Suna tareda juna kusan ma duk inda zasu hannunsu Yana riqe da juna hotinan ke fita sbd ita dai baturiya ce hakan ba komai bane gareta hakan Shima tinda kusan haihuwansa ne kadai baayi baturen ba Amma Shima turai dinne kawai.


Bayan dawowan Jamaal duk yanda yaso yaga halal dinsa hakan Bai samu ba Dan Babu fuska a gurin babbah Dan haka dole ya fara lallaba babban sbd sai yanzu yake fahimtar zare hannun da Dad Omar yayi yabarsa dashi yasan karfin zuciyar gaske ne dashi saiya masa tasa karfin zuciyar akan son dayakewa 'yarsa zai gane shi kwata kwata ma baisan meye kunyar sirikin da ake magana ba indai akan a Hanasa halal dinsa ce musamman yanzu datake fama da laulayin babynsa a karo na biyu.


Ganin take taken Hafiz akan son fitar da Yan matan zuwa Wani gurin su samu su Sha iska kansu ya sake ya Saka babbah taka masa Burkin karya kuskura ya shiga Cikin masu karban hukuncin sbd shi kansa me laifin ne sosai a gurinsa sbd duka halinda Ameenatou take Ciki ya sani shine suka Taru suka ci amanarsa aka barsa a iska qaton ga Babbahn mahaukata ko?
Ya kiyayesa sbd Yana laifi daya wlh dashi zai hada ya Basu baqin mamaki.

Hakan ya Saka Hafiz Dan kama kansa sbd yasan babban idan ya Riga ya dauki zafi akan Abu bare yanzu laifi ne akan duka wainda yake ganin sun Saka 'yarsa taci amanarsa Dan Bai yadda yin kanta bane zugata yake ganin anyi Kuma ba kowane yayi wannan aikin ba bayan Ashley da Siddeeq da Jamaal din kansa harma dashi Hafiz din.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
147
Siddeeq ne ya turowa Ashley txt a kusan karo na Kila Dari Amma Bata basa reply sbd Shima fushin ya shafesa Dan haka shima baida nutsuwan Dan kusancinsa da Ashley din ya Saka ma yakejin duk ya shiga damuwar rashin daga wayar tasa da fushinta Dan haka ya dage gashi Kuma Jamaal na son magana da AM duka dole sai Ashley din ta basa hadin Kai Dan haka Bai denaba a wuni hakai zaita kira Bata dauka Yana bi da txt tinda shi yasan tana karantawa so da sauki ko Bata bada reply dinba indai ta Gani.


Yau ma txt yayi mata wanda ya saka jikinta sanyi sbd itama tana Cikin damuwar daurewa ne kawai takeyi tana sharewan sbd daga shi har Jamaal su San sun tabasu.

Zubawa sakonsa Idanuwanta tayi kafin ta sauke ajiyan zuciya tana dagowa ta Kalli Ameenatou Dake zaune ta zubawa tv Idanuwanta itama kewane sosai a Cikin ranta Amma Kuma fushinta yaqi sauka ko kadan.

Kiransa siddeeq ne ya shigo wayarta bayan sakon nasa Dan haka sake sauke ajiyan zuciya Ashley din tayi tana daukan wayar sbd babbah bayanan Yana gurin sallan laasar masallaci su Kuma suna palon a zaune Suna Dan kokarin ragewa kansu damuwa, dadah Kuma tana kitchen tareda Mai aikinsu Suna girki.

Ganin sunan siddeeq a wayar Ashley kafin ta daga ya Saka Fatmah Dake kusa da ita sauke ajiyan zuciya sbd ganin kwana biyun Dad dinta Ashley din yake kira yaji Yaya suke sbd Ameenatou ta kashe wayarta gabaki daya ta ajiye ita Kuma Fatmah din Baya kiranta kwata kwata ya Dena Dan haka Ashley dince dole wadda zai kira yaji Yaya suke Dan haka hankalin Fatmah baya kwance sbd Tino rantsuwar babbah duk Wanda ya kamaka kana waya dashi shi zai aura Maka.

Duk wayar Ashley tayi ringing hankalin Fatmah tashi yakeyi sbd kada Kiran Dad dinta ya shigo daidai babbah Yana kusa Dan haka yanzu ma da Kiran ya shigo sai dataga siddeeq ne taji nutsuwanta ya dawo daidai musamman da Ashley ta dauki wayar Dan haka take tafara adduar Allah yasa babbah ya dawo daidai lokacin ya samu tana wayar da Siddeeq tinda ba Wai girmansa tayi ba sedai suzo shekaru daidai da ita sbd Jamaal ya girmesu dukansu.


Tana daukan wayar ajiyar zuciya me qarfin gaske Siddeeq din ya sauke Yana ambatar sunanta Cikin sanyi sbd Bai dauka zata iya fushi haka sosai dasu ba tsawon kwanaki.

Amsawa tayi a sanyaye Cikin sanyin murya tana cewa

"Meyasa bazaka tsaya a iya txt din ba sbd kasan hukuncin da babbah yake jira?"

Ganin hakan Fatmah ma datakeson waya tini tana tsoro ta dauki wayarta ta turawa Hafiz txt din Dan Allah ya shigo mata da Maganin daya siyo mata last time na ciwon Kai datake tsananin fama dashi a kwanakin sbd Kuka data kasa denawa ya qare sbd itada Ashley suke Sha dan Ashely dince ma ta rubuta masa ya siyo musu shi.

Tana Tura masa txt din saiga kiransa ya shigo wayar kofa ta fara juyawa ta kalla batajin motsin dawowan babbah ba Dan haka ta dauki wayar tana sauke ajiyan zuciya.

Tambayarta yayi me zatai Kuma da maganin bayan dai komai ya Dan lafa gwara karta fiye shan magani musamman irin wannan zai iya zamar mata illa ta kasa Dena shansa.

Hawaye ne suka ciko Idanuwanta Cikin sanyi tace

"Nidai inaso zan Sha kaina sosai yake Ciwo ko bacci bana iyawa idan nasha zan samu saukin da zanyi baccin,ka siyo min kawai"

"To idan ban siyo bafa?"

"Nidai ka siyo wlh bana iya bacci duka kwanakin Nan,ka siyomin Dan Allah.." hawaye ta sake kaman Yana ganinta tana sake narke murya kaman zata fasa Kuka"

Shigowan babbah da Babu wanda ya lura sai Ameenatou wadda ba itace take wayar ba Amma Jin tayi gabanta yayi mummunan faduwa gashi da alama Yana tsaye hankali kwance Yana jinsu da kallan Ashley da Fatmah din wanda babu wadda ba a narke take magana ba musamman Fatmah da gata ya riga ya gama lalatata Ashley kuwa Cikin Wani Dan Jan aji da basarwa take maganar.

Ameenatou data gama shiga mutuwar jiki da tausayinsu duka biyun sbd ankarar dasu ta Bude Baki Cikin sanyi tace

"Babbah sannu da dawowa"

Fatmah Cikin tsananin tashin hankali ta juyo tana sakin wayarta batareda ta kashe ba hakama Hafiz ta can din yaji lokacin da Ameenatou ta ambaci sunan babbah din Dan haka tsit yayi zuciyarsa na Neman tsinkewan Shima Amma ya Dake sbd Fatmah ta sake ajiye wayar ba lallai yagane wayar takeyiba Dan haka ya Dan saurara yaji abinda babban zaice.

Ashley ma Jin maganar Ameenatou din Tayi saurin kife wayarta gefenta itama batareda ta kashe ba Kuma Shima siddeeq din a kunnensa am ta ambaci sunan babban Wanda ya sakasa kallan Jamaal Dake tareda shi ya Bude Baki a natse yace

"Babbah ne ya shigo"

Kallansa Jamaal yayi da fararen Idanuwansa Yana cigaba da karanta Mahimmin bayanin da aka turo masa ta iPad yace

"Allah yasa yaji dakai take wayar nakai masa sadakin auren kawai a daura ni na samu hanyar daukan tawa matar musan inda mukai Dan naga tsohon Nan nata so yake na Saka ayi kidnapping dinsa saina nabar qasar da Matata na Saka a sakesa.

Siddeeq dinma kallan Jamaal din yayi da fararen Idanuwansa Yana Saka maganarsa a zuciyarsa Dan bata matsuguni sbd Bai taba tinanin soyayya da Ashley ba bare ta aure sedai akwai wata irin shaquwa da kauna a tsakaninsu shi da ita harma da kusanci Bai taba kawo sonta a ransa ba sedai idan har aurenta zai Saka Jamaal ya samu Damar samun macensa ya dauketa su tafi to tabbas zaiso ace babban yajisu Shima Dan Babu abinda bazai iyaba sbd farin Ciki da samun abinda Jamaal ke so,
Take yaji ma fatarsa daya babbah yajisu ya Kuma tabbatarda shi dinne yake wayar da Ashley Dan haka daga wayar yayi ya sake Saka kiranta hankali kwance batareda Jamaal yasan ya sake Saka Kiran bane sbd bazai barsa ba tinda ya fada ne Amma shine farin Cikin siddeeq Yana Cikin abinda shine nasa farin Cikin.


Acan kuwa babbah takowa yayi Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Yana Jin nutsuwa da farin Cikin wannan lokaci Dan haka qarasowa yayi ya zauna kan kujeran zamansa ya dago ya kallesu cikeda nutsuwa farin cikinsa na bayyana.

Fatmah na Gani Hakan Cikin firgici da tashin hankali tareda son wanke kanta tace

"Babbah bada kowa nake waya ba ni da Hafiz ne wlh tallahi Kuma magani ne zai tahomin dashi sbd shi kadaine yasan Wanda nakeso..."

"Dakyau" babbah ya fada Yana kallanta Yana qara dorawa da

"Hafiz dai nawa na Nan gida kike magana ko??

"Gyada Kai tayi da sauri Dan sake wanke kanta tace

"Eh Hafiz ne Allah babbah ni kama duba wayar wlh Ba Wani bane"

"Ba saina duba ba ai Fatmah sbd kin Riga ke kinyi naki mijin Abu me sauki ma basai mun tsaya yiwa Yan Wani wajen bayanin mun tashi Yi Miki aurenba Kinga a Cikin gida ma zaa gama komai can ku qarata da maganin dayasan kinaso harma sa sauran duka abinda kikeso"

Zubewa qasa Fatmah din tayi da sauri gaban babban tana fasa Kuka me karfi da rokonsa ta tuba Dan Allah karya mata auren dole bataso Shima Hafiz din bayaso.

Hafiz dayake jinsu a wayar har Lokacin kashe wayarsa yayi zufa na feso masa Tako Ina Cikin motarsa hannunsa na rawa ya qarawa ac din motar karfi tareda juya kan motar zuwa gidan.

Ko kallanta babbah baiyiba daidai lokacinda dadah ta fito kitchen da sauri sbd kukan Fatmah din ya Maida kallansa kan Ashley data gama jiqewa da zufa sharkaf Cikin wide leg jeans din dayake jikinta da qaramar Riga mara nauyi Idanuwanta sun sauya tana Neman Hana hawayen Dake kokarin taruwa a idonta saukowa.

Kai tsaye babbah yace

"Kefa Ayshatu da wane gogan ne ake wayar??

Shiru Ashley din tayi tana sake jiqewa da zufa tana dagowa ta kallesa zata shimfida karyan da mace ne take wayar
take ya hango karyan zata shimfida masa Dan haka ya jefa mata maganar da zata sakata fadar gaskia yace

"Ko kema Hafiz dinne a hadaku ku biyu a aura masa duka ma Kun hutar damu saiku cigaba da......

Cikin tashin hankali Ashley din ta katse babban da cewa

"Wlh babbah ba Hafiz bane siddeeq n....

Rufe bakinta tayi da sauri tana kallan babban da sauri Cikin firgici
Ameenatou ma Cikin tashin hankalin ta rintse Idanuwanta tana ayyana shikenan.

Babbah kuwa sake cewa yayi

"Dakyau Ayshatu Allah dai ya biya Hafiz da Siddeeq yayi Muku albarka ku dukan"

Zamewa qasa Ashley din tayi itama da sauri hannuwanta na rawa tafara rokonsa tana fashewa da kukan itama sedai Baima tsaya sauraron su ba ya miqe yabar palon Yana duba kwanan wata a wayarsa Dan ko sati bayason su mayar batareda an daura auren ba sbd kada ma Wani lamarin ya gifto.

Ameenatou ma shiga tsananin tausayinsu ya sakata fara hawaye tana rungume Ashley dinta duk da tasan best candidate for aurenta sbd kusan komai na halayensa irin na Jamaal dinta ne so zata samu farin Ciki da kulawa sosai a hannun siddeeq da Jamaal.

Fatmah kuwa dole dadah ta janyota jikinta ta rungume tana rarrashinta da kokarin kwantar mata da hankali lokacin ne Hafiz ya shigo a natse Yana kallan yanda manyan Yan mata dasu masu ilimi da wayewa suke Kuka kaman gidan mutuwa.

Daidai Didi ma ta shigo palon ta tararda rikicin take taji Wani sanyi da farin Ciki a boye ya rufeta sbd Hafiz shine wanda hankalinta Yafi kwanciya dashi akan duk Wanda zaa samo a daurawa Fatmah din Dan haka ita Kam Bata ga abin Kuka ko tada hankali ba.

Barin jikin dadah Fatmah tayi ta nufi hafiz ta rige hannuwansa duka biyu tana sake fashe masa da Kuka tana cewa ya fadawa babbah ba soyayya sukeba.

Daidai Nan babban ya sake fitowa ya kallesu yaga yanda ta cukuikuye Hafiz din Shikuma Yana kokarin kwantar mata da hankali take ya dauke Kai Yana sake cewa "dakyau" ya ficewansa.

Hafiz sakin Fatmah din yayi ya fice Yabi bayan babban Dan suyi magana.

Mum Nur ce itama tazo tana shiga farin Cikin zancen itama Dan tsaf hakan yayi mata Dan haka rarrashinsu da kwantar musu da hankali itama tafara yi tana Jin duka ta Dena Jin laifinsu saima kaunarsu.


Haka aka wuni a gidan ana zuba bori karshe dai Koda zancen ya isa kunnen su Dad Omar take ya amince ba musu uncle Ahmed ma kusan farin Cikin da Didi tayi shi yayi Yana sakawa babbah albarka da qarin Nisan kwana.

Dr Aleena ma hakan ya mata Dadi Dan haka a bakinta su Jamaal suka samu zancen.

Kallan siddeeq Jamaal yayi zaiyi magana siddeeq din ya katsesa Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da cewa

"Am 100 percent happy and okay with it"

Rungumesa Jamaal yayi Yana cewa

"Congratulations to us tohm,and luv you my personal person, Siddeeq and Jeey for life bro"

"Thank you hero"
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
148
Kwana biyu shiru su Jamaal sukai a nasu bangaren sbd nasu Shirin Wanda ya Saka Mum Aleena dawowa dole.

Dad Omar ma Suna dawowa ba Bata lokaci Aka buga katin dauren aure bayan an gama zaman Neman auren an amince da komai da kowa.

Lafiyayyan gida a maqale da mansion din aka fara ginawa Hafiz Wanda dole sukai shiru suka zubawa sarautar Allah Ido akan auren da ko zasu mutu sunsan Babu fashinsa.

Fatmah ma data Hana kanta zaman lafiya ganin Babu abinda zai Hana auren dole ta dangana.

Ashley hadda kwanciya rashin lafiya tayi kwana biyun Amma haka ta gama ciwon ta miqe Babu alamar fasa komai itama dole ta dangana gashi daga ranar Bata sake daga wayar siddeeq dinba sai dai yayi text ta kalla ta share jiki a sanyaye.

Su Mum Nur Wani gyaran gaske aka fara yiwa amaren harma da Ameenatou da Mum Nur keson ta tare itama Dan tasan Jamaal bazai taba barinta ba kaman yanda Taga shirunsa tasan komai zai iya yiyuwa.

Dole bikin daman an sakasa wata daya me zuwa ne sbd Shirin komai Cikin nutsuwa.

Gabaki daya familyn mata Paris suka tafi sukai shirye shiryensu acan kafin daga Nan suka wuce Dubai acan Akai gyaran amaren da Babu wacce Bata sauyaba hatta mum Nur da Didi gyaran sukai take suka koma kaman wasu Yan mata amaren sbd Suna sunada kyan jiki.

Ameenatou kuwa kasancewan akwai Ciki a jikinta sai ta fisu yin haske sosai sai Ashley wadda itama take fara sosai Fatmah kuwa daman chocolate beauty ce,skin dinta brown ne me shegen kyau da lafiya ga Hutu dayake Ciki tin haihuwa haryanzu.

Duk wata siyayyar da zasu sunyi,

Hafiz da kansa ya bada mahaukatan kudin da zaa hadowa Fatmah din lefen alfarma Wanda yaji sarkokin gwal bama guda daya ba da tsadaddun komai.

Satinsu uku suka dawo Nigeria Dan haka Suna dawowa aka fara bikini da zai hada duka wasu shegun qasa da manyan mutane Tako Ina.

Kwanansu hudu da dawo aka kawo lefen Ashley Dana Ameenatou Wanda ya girgixa mutane aka ringa yawo da bikini kawo lefen kawai da Akai Wanda shi kansa bikin kudin da aka kashe masa zai Gina gida da furnitures din cikinsa.

Babu abinda ya banbanta lafiyayyan lefen Jamaal Dana siddeeq Wanda Mum ce ta dauki manyan Nigerian designers na Hausa da sukasan al'adun Hausan da maman fadeela da Ayesha ta fita dasu waje sukaiwa dukiya zubarwan da kusa su kansu masu siyayyar duk budewan idonsu da kudin da suke cikinsu Basu taba hado kayan lefen irin wannan ba.

Sarkokin gold Dana diamonds kadai dasuke Ciki Saida aka ringa yawo da hotinansu.

Ta bangaren sauran surutar sakawa kuwa da sauran kayan baa magana.

Acan gidan Jamaal din kuwa Suna barin qasar aka daga gidan aka sake budesa sosai da Wani irin girma aka Gina part biyu iri daya masu girman gaske da walwala Cikin qanqanin lokaci Suma aka kammala gyaran sedai komai dayake gidan uncle Ahmed ne yayi SA sbd komai iri daya aka siyawa su ukun wanda kowannensu har Fatmah gidanta yake dauke da palours guda kusan uku uku da bedrooms da zasu Kai hudu hudu Dan haka luxuries ne kawai ta ko Ina sbd ba qananun kudi aka zubarba aka zuba musu luxuries din.

Dad Omar daya rasa abinda zai musu sbd angama komai motoci ya siyawa kowannensu har Jamaal da Siddeeq din
Angwayen mota iri daya ya Siya musu Rolls-Royce phantom fullsize luxury car sai Matan su uku ya Siya musu Bentley continental gt farare tas.

Babbah da baisan duk wannan hidimar ana yinta ne da yarsa ba sbd ganin ma Cikinta harya Dan fito ana ganinsa ya barshi akan sunayi ne duka Dan shawo kansa ya sauko shiyasa Akai su lefe da sauransu duk da Abu daya ya sani Babu wanda zai dauki yarsa ya bawa Wani idan ba shi yaso hakan ba.

Ba sosai ma Ameenatou ta sake a bikin ba sbd Cikinta dayake a dan bayyane Dan qarami dashi da Kuma boyon da sukewa angwayen Dan ko Ashley taqi bawa siddeeq daman ganinta hakama sisters dinta sunxo bikin sedai haka suka koma kaman Yan kallo sbd ita Kanta Ashley din tayi musu Nisan da sedai kallo da fatan qarin daukaka su da ita Danma tana Basu kudi sosai.

Sunga Siddeeq Shima Wanda suka buqaci ganin mijin yar uwarsu ko yayane kafin su wuce Dan haka Yana ganinsu Shima kudin gaske ya Basu tareda Saka driver ya maidasu har Abeokuta.

Dad Omar ma yayi musu alkhairi hakama babbah ya musu alkhairi Dan haka da farin Ciki suka koma batareda sun tsaya har a gama bikinba sbd basuga irin tasu jamaar ba agurin manyane masu abin duniyar gaske Tako Ina a zagaye da shaanin.

Ranar daurin auren da farin Ciki tareda hidima families din suka tashi musamman dayake haddata maauratan sun dangana sun Dan sake.

Karfe 12 na rana dubban

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login