Showing 78001 words to 81000 words out of 261814 words

Chapter 27 - AMEENATOU

Mamuhgee   

21 Nov 2024

9968

dagasa fa har Sai abinda mukeso ya tabbata"

Dagowa Jamaal yai ya Kalli Dad din Kai tsaye Shima yace

"Ni nafara cika nawa farkon alkawarin komai ya tafi daidai sauran alkawarin da kayi na tabbatarda ka auramun yarinyar a gobe.......

Wuta Mam ya dauke Dad Lameenu kuwa dakatawa yayi daga Kaida kawon dayakeyi cikin rudewan zuciya da Kai Daya dauki zafi ya dawo gaban Jamaal din ya tsaya ya juya ya kalli mam dayake Jin kansa Shima Yana daukan wuta kafin ya sake dawo da kallansa Kam Jamaal kafin yayi magana cikin tsananin zafi da bacin Rai daya rufe Mam idanuwansa na rufewa zaiyi magana Lameenu yayi saurin taresa da cewa

"Ba lokacin fada bane muna tsananin buqatan sanin wani abu gameda magajin Omar ko yayane Kamun gobe a daura auren Nan,

Ana daura auren Nan zai juya ya tafiyarsa yabarmu batareda mun sani sani akan abinda ya sakamu tilasta masa zuwan na,

Jinina tafasa yakeyi Kuma bazai daina tafasa ba zuciyata bazata daina bugawan tashin hankali da baqin ciki ba idan bamu samu sanin abinda mukai shekarun Nan ba muna bibiyan son sani,

Rayukan da aka kashe duka an kashesu a banza,
Har matar Omar din dana yanka cikinta aka kashe duka an kashe a banza,
Hakama su kasim da jamilu da muka kashe da hannuwanmu duk da zamansu jini da Rabin jikinmu tin farko duk anyi a banza,
Duka a banza idan har daga karshen Nan bamu samu sanin abinda Omar ya haifaba da inda yake muka hadasa da Omar din muka kawar dukiyan ta shigo hannunmu,
Duka wannan komai da komai zai tashi a banza idan dukiyar Nan Bata dawo tamu ba,

Zamu rasa komai,zamu koma Asalin zero agaban Omar....."

Maganganun cikin tsananin zafi da radadi tareda tafasar zuciyar yake fadansu idanuwansa jajir Dan kuwa an daura auren kaman yanda suka samu labari Haroon kasar zai bari Dan su BB sun kawo masa tabbacin Haroon din yakai Ameenatou anyi mata passport ba tareda saninsu ba bayan sun San ko garin Lagos Haroon Baya bari Saida izininsu.

Jin wannan maganar a bakin Lameenu ya Saka Mam Jin kansa ya qarasa daukan zafi Shima zuciyarsa wani zafi takeyi a quntace ya kalli Jamaal da idanuwansa sukai wani irin mugun jajir hannuwansa na wata irin rawa ya dunqule hannuwan sbd rawan da sukeyi tayi yawan dayake Jin zai iya raba Dad Lameenu Kamanninsa na asalin mutum Dan haka juyawa yayi kirjinsa na nauyin da Saida yayi saurin dafesa Yana dafa table din gabansa sbd wani mummunan jiran Daya dubasa kansa ma Neman kasa daukan abinda kunnuwansa suka ji masa yakeyi sbd sunayen dayaji suna ambatar sun kashe da hannuwansu,

Mutuwan granny dinsa Dayake matiqar kauna yaji a bakin Lameenu cewan Dad ne......wani irin sarewa kafafunsa sukai take ya durqushe a Gurin Yana riqe hannuwansa Dake tsananta rawa da zufa me tsananin gaske amma har lokacin Babu Wanda ya tsaya lura da yanayinsa sbd a rikice  suke Suma da tashin hankalin Dan sun tabbata Jamaal na tafe wlh.

Lameenu ne yafara tahowa gurin Jamaal din da sauri Yana cewa

"Ka tashi kaje kaman yanda ayau ka rudar dashi da kamannin Jamaal kaje ayau a matsayin Jamaal ka tabbatarda kaji wani abu gameda inda 'dansa yake...

Mam Dayake kasa kallansa sbd baqin cikin halayen Haroon din wasu lokutan yace

"Alaqarsa da Babbah nakeson fara sani komai rintsi a Daren Nan kafin daurin auren gobe sbd kada mu daura aure da Wanda bamusan me muka Saka kanmu a ciki ba Dan Omar din Shima zai iya komai Dan ganinmu a qasa Dan haka a yau ka tabbatarda kasan alaqar Babbah da Omar idan ba haka ba wlh bazan daura Maka auren Nan gobe ba"
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
50

https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl

Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen



**********
Jamaal take yaji Yana Neman samun attack na zuciya sbd bugawan datakeyi Daya wuce kaida da sauri ya miqe sbd iska datai masa karanci
Saiga BB ya shigo office din Yana kallan Mam yace

"Ranka ya Dade P.A din Chris Jeremy ne ya iso karban Sako gurin Barr" ya qarasa fada Yana kallan Jamaal Dake kokari da yaqin Neman iskan Data kasa wucewa cikinsa.

Cikin zafi da bacin ran dayake cinsu ya fizgo takardun Daya zubar a table dazu ya miqawa Jamaal Kai tsaye yace

"Yi signing ka miqa masa ya basa"

Siddeeq Daya shigo office din Shima a lokacin shine ya karbi takardun cikeda girmamawa daga hannun Dad din ya kawo gaban Jamaal Wanda dakyar ya iya riqe pen din da aka basa yayi signing ya fice daga office din.

Miqawa BB file din takardun yayi yace yayi yace yayi scanning nasu a tura masa copy din ta email dinsa ko na Lameenu.

Karba BB yayi Shima ya fice daga office din ya Satan kallan jamaal Daya fice zuciyarsa na shiga shakku Dan kuwa shidai yau JAMAAL idanuwansa suka nuna masa ayau din ba Haroon ba Dan haka ya shiga shakka da tsinkewan zuciya Dan wancan Karan a abinda Bai wuce daqiqa nawa ba ya kakasu prison din da aka gana masu azabar da take tayi kusan sanadin rayukan yaransa biyu.

Bayan ficewansu Dad Lameenu da sauri ya dauki wayarsa Yana sake hada gumi ya kira likitansa Dan Jin yakeyi kaman hawan jini zai sake kama sa.

Mam kuwa zaunawa yayi Babu abinda yake tafasa zuciyarsa da sake cike ta da baqin ciki da zafi sai murmushi da nutsuwan dayake cikeda rayuwan Omar tareda Kwanciyar hankali Dan sun tabbatarda ko crisis na business Baya samu idanma ya samu a take Ahmed ke handling nasu batareda da Omar y samu ciwon Kai ko damuwa ba a wuce gurin.

Amma su gasunan gaba Daya rayuwarsu kullum cikin tashin hankali da fargaba suke da shakka da baqin ciki duk da suna cikin arzikin Amma kwata kwata basuda nutsuwan zuciya Dana fili Dana boye musamman shi Baya tareda 'dansa dayake cikin zuciyarsa fiyeda komai.


***Jamaal na fitowa siddeeq ne ya taimaka masa ya Isa mota yana shiga ya rufe masa ya zagaya da sauri yaja motar suka fice daga Mansion din cikin mugun speed siddeeq na saukan masa da dukkanin glss din motar sbd ganin yanda idanuwansa da sukai wani mugun ja ya rintse su numfashinsa na fita ba adaidaiba.

Suna isa Haroon da tinda Dad ya kira hankalinsa ya kasa Kwanciya Yana ganin Jamaal yaji gaba Daya gashin jikinsa ya tashi da tsananin tashin hankali sedai Jamaal kwata kwata Baya son komai face shiga dakinsa ya fasa abinda yakejin ya tsaya masa a kirji sbd yau yaji abinda ya jijjiga jarumtarsa da karfin halinsa.

Rufe kansa yayi a daki Wanda ya Saka Haroon juyowa da Sauri ya Kalli siddeeq kafin yayi magana siddeeq din ya girgiza masa Kai Kai tsaye alaman baisan komaiba tukuna.

Sake tashi hankalin Haroon yayi ya Isa kofan da Jamaal din yake ciki yayi knocking Yana Kiran sunansa cikin tsananin kulawa da fargaba.

Ganin ba alaman sauki ya Saka Haroon din karban key dinsa motarsa hannun siddeeq ya fito Kai tsaye gida ya ko zai fahimci wani abin.

Koda ya Isa gidan duka a hargitse da Yan biki da hayaniya sbd evening event din da zaayi a ranar mutane sun halarto manyan motoci Tako ina da securities Dan haka baima yi cikin gidan ba da Ayeesha ya Hadu ta sanar masa Dad Baya Nan duka matane cikeda da gidan anata Shirin tafiya event din wadda aka kashewa kudi bana wasa ba dan ita kanta amaryan kayan da zata Saka a ranar daga Dubai mum Atee Tayo odansa da duk abinda zaka Saka a event din hakama masu makeup dinma professionals aka aika na musamman Dan shirinta.


******Dad Baya gidan ya fita Dad Lameenu kuwa Yana samansa Yana hutawa sbd jininsa daya Dan hau likita ya basa shawaran hutawa jinin ya daidaita.

Hakan ya Saka Haroon komawa side dinsa Yana sakawa da warwara cikin matsuwa da kaguwan dawowan Dad ga mum dinsa ma ta kirasa Bata samu s
Jirgi ba aranar sai washe gari zata iso kusan ma ba zata samu aurenba Dan Koda zata iso kilama amaryan ta tare.

Bangaren Jamaal dayafi na Haroon din girma sosai aka gyara tareda zuba komai na Jin dadin rayuwa masu kudi sabo a cikinsa Nan amarya zata tare su umman fadila ne suka taho suka sake gyara komai tareda Saka abinda suka kawo na turarukan wuta da duka abubuwan da aka Siyawa Ameenatou din suna gamawa suka koma Dan nasu Shirin na tafiya bikin ranar.

Har lokacin event yayi Dad Bai dawo ba Dan haka dole Haroon ya fita yabar gidan Dan zuwa dubo Ameenatou wadda tana can ana shirinta Kuma ladies event ne kawai Dan haka tace saiyazo yaga kwalliyanta kafin kowa ya Gani.

Yana barin gidan Dad na dawowa lokacin duka an tafi bikin Babu kowa a gidan sai masu aiki Dan haka abinci kawai yaci a dining din palonsa ya huta sosai kafin ya fito ya nufi office dinsu Dan Kiran duba sakon da Chris Jeremy yace ya turo ta email ayi gaggawan dubawa.

Yana shiga office din BB ya shigo ya sanar masa tin jiya suke bibiyan Omar Kuma tabbas sungano alaman magana yakeson yi da Babbah sbd a masallacin anguwan babban yayi sallan magrib Dan ishai jiyan hakama yau acan yayi azahar da laasar yanzu ma daga can suke.

Mam na Jin hakan ya dago idanuwansa ya zubawa BB din Yana Jin kansa na shiga tinani.

Wayarsa ya dauka ya Saka Kiran Lameenu Wanda Shima ya gama hutawan zaune yake Yan amsa wayoyi saiga kiran Mam din ya dauka Yana Jin Abinda Mam yace ya kashe wayar tareda miqewa tsaye ya fito sanyeda jallabiya fara qal da wayarsa a hannunsa sai farin glass dinsa Dake fuskansa.

Mam na shigowa kafin yace komai Kiran Chris Jeremy ya sake shigowa wayar Mam Dan haka iPad dinsa ya dauka Dake kan table ya kunna Ya shiga duba sakon.

Abinda yagani je ya sakashi ajiye iPad din gefe ya miqawa BB hannu ya dauko masa glass dinsa na qara Gani dakyau ya miqa masa ya karba ya goge da tissue da kyau kafin ya Saka ya sake daukan iPad din ya sake dubawa dakyau.

Numfashi ya sauke ahankali tareda rintse idanuwansa ya Bude fes akan iPad din hannunsa zufa na tsatsafowa daga goshinsa Wanda Hakan ya Saka Lameenu daga Kai sama ya shaqi iska me zafi sbd ganin abinda ya Saka Mam zufa daga gashi to ba qaramin balbalin balai bane Dan haka hannuwansa suka jiqewa da zufa Yana zuba dukkanin idanuwansa da Kunnuwansa akan Mam din Yana jiran Jin Abinda zai fada.

Mam dago jajayen idanuwansa dasukai jajir din a take ya Kalli BB yace bani copies na takardun file din Chris Jeremy.

Da sauri BB ya juya ya nufi locker dinsu ta takardun sirri ya Saka pin ya Budeta cikin sauri ya Nemo takardun Daman sune a sama Dan shine ya ajiyesu bayan yayi scanning da photocopy dinsu.

Yana kawowa Mam da sauri ya karba hannuwansa na rawa ya budesu zufansa na karuwa ya jefa idanuwansa a inda signature din Jamaal take wadda tabbas tabbas da gangan Daman Jamaal yake Saka signature dinsa a duka aiyukan masu mahimmanci sbd signature din Haroon daban tasa daban Dan haka aiki bazai taba yiyuwaba Saida Wanda Saka hannunsa yake ciki shikuma Baya Nan Dan haka sunaji suna Gani zasu ringa rugejewa Daya bayan Daya.

Sakin file din Mam yayi da sauri Yana miqewa ya nufi locker din da kansa ya fizgo dukkanin files dinsu dake ciki na aikin miliyoyin da biliyoyin kudin da zaayi bayan auren dansa
Hannuwansa na wata irin rawa da jijjiga ya ringa budesu Daya bayan Daya Yana duba signing din dayake cikinsu duk na Jamaal Seelah ne ba Haroon seelah ba........

Kasa tsayuwa yayi ya zube a kujeran datake gurin zufansa na tsiyaya kaman ya hadiye kunama da ranta.

Lameenu dayake tsaye Yana kallan Mam zufansa Tama Fi ta Mam din Dan kaman ana gobara a cikin jikinsa haka yakeji dakyar ya iya tattara yawu ya hadiyewa makoshinsa Daya Bushe yace

"Jamaal ne ko??
Jamaal ne ba Haroon ba,
Signatures din duka na JAMAAL ne ko??
Shine yake tareda mu duk tsawon lokacin Nan?
Shine yake tsaye a gabanmu da bakinmu mum sanar dashi har abinda Haroon Bai saniba ayau din sbd Haroon baisan dukkanin wainnan da na lissafo ayau mune da hannuwanmu muka kashesu ba.......

JAMAAL me mukai Maka??
Wane balai da masifa ne wannan?
Wace masifa Haroon ya sakamu bayan tarin wadda take gabanmu...


BB ma da tini zufan ta katse masa cikin fargaba da shakkar abinda zai iya biyowa Baya kallan Mam yai Wanda zuciyarsa ke Neman bugawa sbd zufa yakeyi sosai hakama zuciyarsa Bata bugawa daidai.,

Lameenu kujeran datake kusa dashi yayi saurin zaunawa Yana cewa

"BB yi sauri kirawo likita ya dawo bana Gani zuciyata Bugawa zatai jinina ya mummunan hawan da baa so yi sauri kirawosa"

Daga Mam din har Lameenu jininsu mummunan Hawa yayi dole Akai gaggawan Kiran Dr Koda yazo Lameenu yafi Dad shiga Mummunan hali Dan haka shi aka fara dubawa kafin Dad Wanda shi zuciyarsa bugawa take Neman yi kawai.

Dr na fita Haroon da BB ya sanar da Dad na Nemansa Yana shigowa BB ya rufe kofar.

Haroon dayake kallan Dad Lameenu dayake numfashi ahankali ahankali alaman ba cikakkiyar lafiya mayar da kallansa yayi gurin Dad dinsa Wanda ya dago jajayen idanuwansa yayi masa kallo Daya na tsaftan gaske ya tabbatarda Haroon ne a gabansa take ya daga hannu ya sauke masa wani mahaukacin Marin Daya Saka gefen bakin Haroon din fashewa da jini.

Dagowa yayi bakinsa na jinin ya Kalli Dad din sedai wani Marin Dad ya sake saukar masa Mai zafin dayafi na farko.
#MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
51
Radadin Marin Kai tsaye a zuciyarsa yake sauka wadda take tarwatsewa aduk lokacinda mahaifinsa ya Saka masa hannu duk shekarun dayake dasu Wanda da yayi auren wuri da tini ya Tara Yara biyu ko uku.

Jajir idanuwansa sukai a karo na farkon dayaji zuciyansa na tabbatar masa da shidin ba komai bane a Gurin Dad Kuma har abada bazai taba zama komai ba a gurinsu,

A zero yake gabansu Kuma a haka zaici gaba da zama..


Yanda zuciyarsa ke radadi da qunan dayake tafasa jininsa haka ta Dad dinsa ke tafasa ya kallesa da jajayen idanuwansa yace

"Ayau nayi baqin kasancewa Wanda ya haifeka,
Nayi baqin ciki da Dana sanin barinka a qarqashin inuwata sbd har abada bazaka taba zama me amfani ba,
A yanda Aleena ta haifeka ba komai cikin kanka haka ka girma Babu komai a cikin kan naka dayekeda amfani ko buga Maka lissafi Mai amfani........

Tsananin 'dacin maganganun ya Saka Haroon rintse idanuwansa dasuke tsananin radadi sbd Jan da suke qarawa hannuwansa na rawa kansa na sarawa ahankali ahankali Yana qara qarfi.

Dad Lameenu da ayau tsaban shock baida karfi ko kadan a zaune yake Yana Jan numfashin wahala da 'dacin zuciya Bude Baki yayi yace

"Ban taba daukan karshenmu a hannunka zai faro ba Haroon sai ayau din,
Ban taba sanin jinin kafiran dayake yawo a jininku na mahaifiyarku zai taba aiki a kanku ba wataran sai yau,
Haroon Ashe bakada Imani bakada ha nkali???
Tin yaushe ne Jamaal yake acikinmu batareda mun saniba???
Tin tsawon yaushe muke kirari muna dabawa kanmu wuqa a gabansa batareda mun saniba??
Jamaal da yayi alkawarin saiya mayar damu mabarata kafin ya San sirrinmu kenan yanzu Daya San hatta yanda muke kalan numfashinmu kana tinanin a mabaratan zai barmu yanzu???
Wlh Jamaal Saiya tabbatarda ko Baran idan munyi bazaa bamu sadakar ba..... innalillahi wainna ilaihirrajiun,. innalillahi wainna ilaihirrajiun,

Kallan Mam yayi jininsa na sake hayewa a rikice yace

"Wlh mamman Jamaal bazai rasa hada kwararan shedu akanmuba,
Bazai rasa recording na wasu maganganunmu ba......

Kirjinsa ne ke Neman rikewa Dan haka BB Dake tsaye Yana jiquwa da zufan Shima yowa kan Lameenu Yana masa fifita duk da sanyin AC Daya cike office din tsaf Amma dukkaninsu a jiqe suke da zufa.

Mam dayakeji zuciyarsa na tinkudo masa baqin cikin duniya da bacin Rai kallan Haroon yayi Wanda jikinsa keta tsananin rawan Dayake nuna da ciwonsa yafara tasowa Daman gashi tinda ya dawo mum Atee ta Dora daga inda ta tsaya.

"Haroon kaman yanda ka ha'ince ni kabi shawaran Dan uwanka da mahaifiyarsa kuka sakani wannan baqin cikin wlh saina nin ka masa Wanda yafisa Dan bazaka auri wannan yarinyarba wallahi indai nine na haifeka,
Bazaka samu farin cikin dakake tinanin zaka samu ba idan ma ka gujeni ka komawa mahaifuyarka,

Kaman yanda kuka rusamu wlh dakai zamu dawwama acikin wannan baqin cikin da rashin Dan kuwa idan baka sani ba ka sani wannan ciwon haukan Daya kwakwalwanka Babu inda zan zaka Daya wuce na tattara ka na aikaka asibitin mahaukata Koda kanka zai Bude,

Idan har lissafina ya buga daidai Dan uwanka yanda yake kwararren likita na tabbata ya karanci yanayinka Kuma bazai rasa bincike akan abinda ya fahimta tareda Kai ba Dan haka zuwa yanzu yasan mummunan Nisan da qwaqwalwanka yayiba a Juyewa Dan haka ka Saka aranka Babu maganar aurenka gobe wlh....

Dad Lameenu dayake cikin mawuyacin hali har lokacin dagowa yayi yace

"Yanda Babbah ke son 'yarsa har abada bazai tabawa me tabin kwakwalwa auren yarsa ba kome zaayi kuwa Dan Haka takardun asibitinka kawai zamu basa a Daren ba sai gobe ba,
Maza ma ka fice ni ko ganinka Haroon a yanzu banason yi qaramin hawan jini yakeyi,
Ka cucemu Kaci amanar mu Kaci amanar kaunar da mahaifinka yake Maka.

Zuwa lokacin Haroon ba iya hannuwansa kadai ne suke rawa ba dukkanin jikinsa jijjiga yakeyi sosai hakama kansa tini yayi wani irin mugun nauyi Yana Neman inda zai fara bugasa bakinsa yakeson budewa Yayi magana Amma Dad Shima ko ganinsa bayason yi a lokacin sbd zai iya masa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login