Showing 24001 words to 27000 words out of 197960 words
Rahima tayi takoma kwance tana
buge hannunshi cikeda masifa, tsaki yaja da sauri yadauki key motarshi daga kan
table yabude kofan ahankali gudun karyay kara asirinshi ya tonu sanan ya leko da
kanshi kadan dan duba ko akwai mutane a falon, ganin babu kowa a falon yasa da gudu
yafito yay hanyar kitchen sabida yabita backyard fence ya dirka ta baya ya arce
daidai lokacin Sameer ya shigo flat din, ganin Chris yafito daga wani daki da gudu
yayi ta kitchen yasa yabishi da gudu, daidai ya shiga kitchen wani officer NDLEA
dayaji fitowanshi ya labe abayan kofan gudun karya ganshi yafito ya tadiyeshi
yafadi timm akasa, ihu Chris yayi dan yaji zafin faduwan yace "officer I didn't do
anything naaa, we are just having birthday party fa, why u wan arrest me en? Wetin
I do naaa?" dagashi officer yayi bayan ya kulle hannayen nashi cikin tsawa yace "my
friend shut up, we we are busy having sleepless night to make sure youth like you
stop all this kind of life and be serious with your education so that u guys will
have a bright future but you guys are here busy taking what is killing you and
killing your future as well, let's go my friend" ya fincikeshi sukabi ta gefen
Sameer dayay irin tsayuwan sojojin nan yana kallonsu suka fita sanan yadaura
idanunshi akan dakin dayaga Chris yafito daga ciki kafin ahankali yadaga kafa
yafara tafiya daidai boot dinshi na making sound yakarasa wurin dakin da Chris
yafito daga ciki, yadade yana kallon kofan yanabin rubuce rubuce da Zane zanen dake
jikin kofan da kallo zanen shisha pot dasu cigarette ne a jikin kofan katakon da
akai da biro, ahankali yazare hannunshi daga bayanshi yakama handle din kofan
yabude kofan wani irin warin wiwi da sauransu ne suka dakanmai hanci hakan yasa ya
yatsine fuska kafin idanunshi su sauka kan Rahima dake kwance tana dirkan baccinta
hankalinta kwance, kallo daya yamata yagane musulma ce ita, ita kadaice musulman
dayagani tunda aka fara fito da matayen dake wurin, wani officer ne ya shigo dakin
yana tahowa wajen Sameer yace "da saura ne Lieutenant?" gyadamai kai Sameer yayi
kafin ya nunamai cikin dakin dayake tsaye a gabanshi da sauri officer ya shiga
cikin dakin yay inda Rahima ke kwance, hannu daya yasa ya fincikota hakan yasa ta
tashi tsaye luu kaman zata fadi, turo baki tayi sosai idanunta arufe cikin fushi da
shagwaba in a very slow way tace "leave me aloneeeeeeee Chris" tai baya luuu takoma
zata fada kan kujeran a mugun buge, sake fincikota officer yayi yana kokarin kama
hannun ta tabaya ta fizge kaman zatai fada dashi tana layi, cikin slow tsiwa irin
na wanda ya bugun nan tace "leave me kona dalla maka mari, I want to shower, uhmmmm
wanka nake kadena damuna, kawomin ruwa in sirka ruwan zafin Ya Siddiqa" tawani irin
zube akasa wurin kafin ta daura kanta kan table din dasu shisha pot kekai tacigaba
da bacci, officer zai kara kamota akaro na Uku Sameer yace "wait!" tsayawa chak
officer yayi ya kalli Sameer din dahar lokacin bai shigo dakinba, takowa yayi ya
shigo cikin dakin, babban bottle water Swan daya gani kan side drawer gadon dakin
yadauka ya shiga budewa yana tahowa inda take kwance gaban kujera ta daura kanta
kan table tana bacci tana surutai kasa kasa, matsamai Officer yayi yakoma baya,
tsayawa Sameer yay akanta ya cillar da marfin goran gefe, daga goran sama yay da
hannu daya ya shiga kwararo mata ruwa kaman ana mata fitsari akai yana sauka saman
dankwalinta, dudda she was damn high amma saukan ruwa dataji akanta yana sauka kan
fuskarta wasu na shiga kunnuwanta, wasu na gangarawa wuyan ta zuwa cikin riganta
yasa ta mugun zabura kaman wacce ta zare ta mike tsaye tana shashare fuska tana
wanan nishin da mutum keyi in ruwan sanyi na tabashi tana sauke ajiyan zuciya tana
share fuska tana kokarin ta bude idanu takasa sabida yanda ruwan ke saukowa, dudda
ta tsaya agabanshi tana shashafa fuska trying to open her eyes baisa yadena kwara
mata ruwan ba harsaida ya juyemata ruwan goran tass sanan ya tsaya, wani irin
ajiyan zuciya ta sauke tasa hannayenta duka biyu ta share fuskanta ruwa na diddiga
harta cikin riganta, ahankali ta janye hannunta daga kan fuskar nata cikeda bala'i
tace "uban wayace kazubamin ruwan sanyi ajikinta eh?" sanan tabude idanun nata tass
ta saukesu kan fararen kafafun ta dasuka jiku da ruwa tana kallon wani boot army
green dake gab da kafafun nata ga dilli dillin ruwa akan boot din shima, tundaga
kan takalmin shi take binshi da kallo har zuwa kan cikinshi zuwa kirjinshi da a iya
nan tsawonta ya tsaya kafin ta daga kanta da fararen idanunta dat look moist
tsabagen ruwan dasuka sha ta daura dara daran idanunta akan fuskarshi kaman yanda
shima yake kallonta fuskarshi babu alamun Rahama balle dariya, wani irin faduwa
gabanta yayi ganin wani babban soja a gabanta gashi da tsayi bakin mutum, kasa
motsi tayi balle ma tasake yunkurin magana batare daya janye idanunshi daga kanta
ba yawani irin cillar da goran ruwan dayagama juyemata cikin kakkausar murya yace
"take her away Officer" da sauri officer yakaraso wajen yana kama hannunta ta baya
yana handcufff nata Sameer kuma yajuya yana takun nan kaman wani bijimin zaki
yafita daga dakin, saida yafita daga dakin kaman anbude mata baki ta shiga kokawa
da officer tace "me haka kakesamin a hannu ina zaku kaini? Su waye ku mena muku?
Ina zaku kaini eh? Chris" ta kwalama Chris kira.
_Zan baku another page anjima koda bayawa, ina bimuku book din daki daki ne VIPs,
I've been busy yau wlh, sababbin kajina nata mutuwa, guda goma shadaya sun mutu
yau, cuta takamasu, nakira Dr wai sanyine, sauran ma don't look good at all, wlh
kaman zanyi kuka, dan Allah kumusu addu'a banso nai asara, gobe fa zamasu cika sati
daya da sayosu😭 innalillahi wa innailaihi raji'un_[6/3, 9:41 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN
ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣6️⃣
6️⃣
1️⃣ 1️⃣6️⃣
Janta officer yayi suka fito daga dakin yace "Chris can't save you lady, u are
arrested sabida ankamaki kina shaye shayen miyagun kwayoyi da gwamnati tahana sha
sabida cutar da halakar, da wulakantar da rayuwar dan adam datakeyi, headquarter mu
zamu kaiki yanzu haka" wani irin uban ihu ta kurma tace "wlh kasakeni ni baza ka
kaini ko inaba Mummy" tafashe da kuka sosai tana kokarin fizge kanta tana turje
turje tana kiran Mummy. "wlh kasakeni nibabu abinda namuku, leave me alone,
Mummyyyy" tasake kwalama Mummy kira tana kuka sosai, janta yayi da karfi da yaji
yafito da ita compound din tana kuka tunda aka haifeta bata taba shiga tashin
hankali irin wanan ba, bama tasan cewa akwai tashin hankali hakaba aduniyan nan
daga zuwanta birthday yan sanda ne koyan menene sunwani kamata, Sameer dawasu
officer guda biyune kawai a compound din yana musu magana, sauran suna waje wurin
mota tsare da yaran dasuka kama, yanda Rahima ke kuka sosai tana kurma uban ihu
tana kwalama Mummy kira yasa yadago kanshi ya kallesu, ko'ina na jikinta bari yake
har lokacin dan kwalin kanta da riganta duk ajike ne sabida ruwan daya kwaramata
tana kuka, babu abinda take tunawa sai maganganun Mummy karta sake tai abinda zaisa
aganosu kokuma tai abinda zai tonamusu asiri idan Dady yaji ankamata ai saiya luma
mata wuka aciki tamutu dama bayasonta yafison su Siddiqa. "dan Allah kasakeni
natafi wurin Mummy na, ni wlh banmuku komiba, please please karku tafi dani kaji
Abba na zai kasheni ne" zufa officer ya share da hannu daya tsabagen yanda take
bashi wahala yasa yake zufa yace "ashe kinsan abinda kikeyi baida kyau, muje" janta
yayi ya fitar da ita daga gidan zuwa inda sukai parking yay mota da ita, jefata yay
cikin motan ganin irin mutanen dake cikin motan da aka kakkama sai warin shaye
shaye suke yasa ta kifa kanta akan cinyarta tahau kuka sosai kaman za'a kasheta,
Chris da batama lurada shi bane yanachan gaba tsaye yakutso kai yazo ya tsaya
akanta yana kallonta tabashi tausayi dan yasan tadamu duk ta tsure, ahankali yace
"Hey Beautiful a......." "don't call me beautiful I hate you Chris" tafada tana
tashi tsaye daga kan kujeran cikeda masifa tana kuka sosai, tace "just thank God my
hands aren't free da wlh saina waska maka mari mai gishiri, a dog like you" cikeda
masifa dan shima he feels furious and frustrated as well yace "I love and respect
you beautiful but I won't have you calling me names, I am not gonna tolerate that
am 25 nasan nabaki nothing less than 5yrs so pay some Goddamn respect u lousy hausa
spoilt brat" cikin kuka sosai da shegen muryan ta mai bala'in zaki da dadi tace "u
are the lousy one hypocrite kawai and I said it you are a dog" azuciye yawani irin
bugamata kanshi a goshi da karfi sabida yanda hannunshi suke a daure, baya luuu
tayi tafadi a daidai baki bakin motar kaman wacce iska ya diva tai wani irin tumble
kafanta ya malkwade tafado daga motar zuwa kasa daidai lokacin Sameer da all the
eight NDLEA officers sun karaso wajen akan idanunsu ya bugamata kai a goshi, daidai
kafan Sameer tafado tai wani irin kara goshinta na jini bayanta ya mugun bugu
tafashe da kuka idanunta na juyawa, daya daga cikin officers ne ya shiga cikin
motar, finciko Chris waje yayi ya zubamai Mari yace "how dare you hit a woman?"
cikin fushi dajin haushin yanda officer ya marai agaban all his friends yace "Sir
is personal issues besides she's my girlfriend you don't have to interfere" daya
daga cikin officer ne yace "ahhh yaro kaidan iskane naga alama kanka na hayaki,
kafasama yarinya goshi sanan kama fadamana we don't have to interfere" kulkin dake
jikinshi ya zaro shima dayan haka suka shiga dukanshi yana ihu saida sukamai lilis
yana ihu duk Sameer na kallonsu baice musu uppan ba sanan sukazo inda Rahima take
agaban Sameer tana zaune tana kuka sosai, tana taba goshinta dake jini tana kallon
jinin a hannunta tana kara kecewa da kuka kaman zata shida, daya daga cikin
officers dinne yace "ke tashi ki shiga mota mukakai head quarter za'a dubaki?"
makemusu kafada tayi tana kuka tace "ni yanzu zakuyi treating dina I can't feel my
leg at all, am bleeding I don't want to die now pls" bushewa da dariya all the 8
officers sukayi daya daga cikinsu yace "you don't want to die shine kike shaye
shaye kina shan su shisha da codeine that kills faster than anything you could
think of, my friend stand up" yay maganan yana mikar da ita tsaye, wani irin ihu
jin yanda kafarta yamata mugun ciwo tai tangal tangal zata fadi akasa ta daga
kafarta daya sama tai baya hakan yasa Sameer dake bayanta yatare ta tafado in his
arms, atsorace ta juyo dakai ta kallai tana kuka hawaye na bulbulowa ta gefen
idanunta gabanta nafaduwa kaman zata mutu, dauke idanunshi yayi daga kallon
datakemai kaman wacce keson karanta abu ahankali yadauketa kaman yadau paper da
sauri tai wrapping hanuwanta around his neck, yana kallon gabanshi yake tafiya
daidai harya karasa da ita wurin motar dasuke ciki, da ido daya yama wayanda aka
kaman alamun su matsa, matsawa sukayi ya ijiyeta akan dan kujeran bencin wajen tana
kuka ciki ciki hawaye na bulbulowa kaman famfo, kafarta na dama ya kama, hannu yasa
yazare White takalmin dake kafarta dakeda dan tsini ya ijiye agefe yana kallon
yanda ankle looks so reddish gawani leg chain data daura a kafar daya zubama ido
for a while sai kyalli take abinku da farar fata, kafan harya kumbura kashin gefen
ankle din yadawo tagaban kafan, wani irin fashewa da kuka tayi tana kallon kafar
tace "innalillahi kululun kafana yadawo gaba shikenan zan mutu yau" ta fashe da
kuka sosai, dariya officers din suka shigayi suna mata dariya, daga kafar yayi
yarike kowa na cikin motar na kallonsu barinma Chris dayasan aikinshi ne, wrist din
kafan yarike gam kafin yakama foot dinta yay wani irin twisting dayasa ta kwala
mahaukacin ihu kaman ta sume tafado daga kan kujeran tana dukan hannun Sameer din
tace "kabari dan Allah, wayyo Allah na Mummy na" sakin kafar yayi ahankali batare
daya kalletaba yajuya ya kalli officers din yace "Dr should check the leg when u
get to the headquarter, see you guys next time" yajuya yawuce ya shiga motarshi,
shiga motocin su suma officers din sukayi, Officer biyu suka tsaya abaya tareda yan
shaye shayen gudun karsuyi jumping su shiga titi in attempt to excape sukai
headquarter dasu shikuma Sameer yay gida dan ya mugun gaji.
Parking yayi a compound dinsu yana kallon motar Nuru alamun yazo gida kenan baiyi
mamaki ba dan yasan dukansu daga Nuru har Muhammad kullum da yamma insun taso daga
aiki saisun biyo sun gaida Ummi dan da safe basa iya zuwa sabida zuwa aiki, bayan
sunyi magrib saisuma Ummi Sallama su tafi gidajen su, motar Nuru dayagani yasa
yagane Muhammad bai riga yataso daga wajen aikinshiba, flat dinshi yawuce dan he
wants to shower kafin yaje wurin Ummi, wurin fridge dinshi yayi dake falon budewa
yayi yadauko bottle water yabude yakafa abaki, bude kofanshi da akayi yasa yadan
juyo while drinking the water ganin Nuru ne yasa yacigaba da shan ruwan, zare goran
yayi daga baki hakan yasa Nuru daya karaso wajen yace "sannu da dawowa yayan mu ya
aiki?" "Alhamdulillah fine, Muhammad bai dawoba?" gyadamai kai Nuru yayi yace "eh
baidawo ba, wurinka nazo Ya Sameer amma naga you want to shower yanzu ka shigo bari
na jiraka" dan murmushi yamai yace "alright give me just 5min okay" gyadamai kai
Nuru yayi hakan yasa yawuce yay bedroom dinshi Nuru yabishi da kallo yana mugun son
wanshi Sameer saidai bakajin cikinshi tun yana gani kaman kawai Ya Sameer baiso yay
aurene har wakan Ummi shima yasoma zama a kunnenshi to the extend yanzu yasoma
believing maybe wani matsala yakedashi saisa baya sha'awan auren according to Ummi.
Bude fridge din yayi yadauko vita milk yasa opener ya bude yamaida fridge din
yarufe yadawo kan kujera yazauna yanasha yana kallon news.
Almost 10min Sameer yabata sanan yafito falon sanye da bathrobe fari ya zauna
kusada Nuru yace "je kitchen ka hadamin coffee Noor" tashi Nuru yayi da sauri yace
"to yayan mu" kitchen dinshi ya shiga that is so clean kana ganin kitchen din kasan
ba'a cika amfani dashiba, cikin 5min yahada mai coffee yazubamai a mug yasa spoon
da sugar yafito yakawo mai, karba yayi yace "thank you" ya ijiye dan yasan da zafi,
kafin yadauka sipping kadan yayi ya ijiye yadan daga gira daya sama yace "not bad"
fashewa da dariya Nuru yayi yace "kai Ya Sameer nai kokari fa sosai" shima dan
murmushi yayi yace "yeah was just kidding, its actually taste good thumbs up"
murmushi dukasu sukayi sanan yace "alright, let's talk, what is the matter?" dan
shiru Nuru yayi kafin ahankali yace "Yaya Sameer yesterday I was busy inata nazarin
abubuwa da dama" gyadamai kai Sameer yayi yana sake kai Coffee bakinshi giving him
his fool attention, ganin haka yasa Nuru yace "uhmm Ya Sameer why don't you marry
Asiya? Naga tana sonka"
Wani irin kallo Sameer yamai saida gabanshi yafadi da sauri yace "I mean bawai tana
sonka ba but naga kuna shiri taku tazo daya please understand me kaji yayan mu, she
is our cousin and tanada natsuwa, tana 300 level a school ga ilimin islamiyya what
else?" "get out!" yadakama Nuru tsawan da saida yasa ya firgita, cikin fushi yace
"u think sabida kai aure kanada gut din tunkarana kamin maganan aure harda fadamin
wanda zan aura my sister Asiya, yaushe aka haifi Asiya? Is Asiya even ripe for
marriage, you know me you know what I hate banson raini Noor, watch your tongue,
now get out" tashi Nuru yayi ahankali dukyay wani iri he feel awful duk laifin Ummi
ne saida ya gayamata yafi so tamai maganan da kanta bata aikoshi in disguise ba,
ahankali yace "I'm sorry Yaya Sameer kayakuri" da yatsa Sameer yanunamai kofa babu
alamun wasa kan idanunshi hakan yasa yajuya yafita da sauri, jingina yayi da kujera
ya lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya ranshi yabaci sosai. Karan da wayanshi yayi
na shigowan sako yasa yadau wayar NDLEA ne yaga sunmai message.
" _Lieutenant Chairman asked us to call you, something come up u have to come to
the headquarter please_ ".
[6/3, 9:42 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣7️⃣
7️⃣
1️⃣ 1️⃣7️⃣
Tashi yayi yawuce bedroom dinshi ranshi abace wasu kananun kaya ya dauko, Black
jean yasaka sai wata Ash color riga short sleeve mai gajeren hannu yasaka, rigan
nada V neck daya bayyanar da kwantaccen gashin kirjinshi, rigan ta kamashi sosai,
kaman rigan zata barke ajikinshi sabida yanda ta bayyanar da kiranshi na full packs
man, Black jacket yadauka yadaura kan rigan yasaka wani boot baki yadau car key
dinshi, kana ganinshi kaga soja yafito daga flat dinshi yaso ya shiga wajen Ummi
but no Inya dawo yaje, he don't want to waste anytime, motarshi ya shige yaja
tareda danna horn mai gadi ya budemai gate yabar gidan.
Tashi Ummi tayi daga jikin window bayan taga taga fitanshi jikinta ya mugun yin
sanyi takoma kan gado ta zauna ta buga uban tagumi cikeda damuwa ta daga hannayenta
sama tace "wanan wani irin jarabawa ne Ya Allah meke damun Sameer ne dako kadan
mace bata gabanshi?" tai dan shiru tasa hannu tai maza ta goge hawayen dake shirin
zubomata, tasowa Nuru yayi yazo kusada ita yabata side hug cikeda damuwa yace "Ummi
kidena damuwa okay, kidinga mai addu'a in sha Allahu har jikokin shi zaki gani nan
bada jimawa ba kuwan" fuskar Nuru ta kalla tace "anya? Kaduba pa am sure sabida
maganin dana gayamishi Baffa shi yakawomai ne yau da safe yasa yaki shigowa dan
baisoma yasha, Noor ya zanyi da raina eh? Yayanku fa Noor duk ya girmeku nesa ba
kusa ba, yabaka almost 8yrs but look at you now da Nabila batai having miscarriage
ba da kanada yara biyu aduniya, I tot yanda na kawo maganan Asiya he will accept da
gudu sabida cousin dinshi ce kuma naga suna shiri yarinyar na sonshi sosai, bazai
wani sha wuyan neman aure ba dan da gudu Baffa zai bashi ita amma kalli abinda
yama" ahankali Nuru yace "Ummi kibar maganan Asiyan nan, it won't work, ai dama tun
kafin kiturani na gayamiki kice Yaya Sameer ya auri Asiya ai kaman kin kara
koranshi daga zancen auren ne, Yaya Sameer dason girma tsiya inya auri