Showing 3001 words to 6000 words out of 197960 words

Chapter 2 - ABin Abinda Zuciya Keso

M SHAKUR   

25 Nov 2024

15010

kibari idan zamu kwanta saina baki, yanzu tashi jeki cire towel
dinan kisaka kaya babanku yahanaki zama da towel haka" dan turo baki tayi ta tashi
tafita daga dakin tana tafiya ahankali Mummy tabita da kallo harta bace mata,
dakinta tawuce ta tsallake barin shinkafan datayi tahau kan gado abinta, jakan
makarantan ta tabude taciro wayarta Samsung mai kyau ta bude data tana dube duben
message, fita tayi ta shiga game tafara bugawa, shima fita tayi ta jefar da wayan
kan gado babu abinda kemata dadi, littafan ta taciro na school ta shiga dubawa suma
babu wanda ke mata dadi hakan yasa ta watsar dasu akasa ta kifa kanta kan gadon
tana nishi sama sama kaman mai asma tana bubbuga kafafun ta akan gado kanta nawani
irin sarawa sai lashe bakinta take tana bubbude wa kaman wacce kejin kishi, bude
kofanta da akayi yasa tabude idanuwanta dasuka kankance Lubabatu ce ta tsaya daga
bakin kofa tana kallonta babu alamun wasa kan fuskarta tace "Malama kitashi kije
ankira sallan la'asar nasan ma kona azahar bakiyiba kiwuce kije kiyi, kin daisan
Abba yace mudinga kiranki idan zamuyi salla ko to kitashi" harara tawani irin watsa
mata kafin takara gyara kwanciya kan gadon kifa kanta kan gadon tace "Malama
kitashin mini agaban kofan daki tunda ba dakinki bane" daga bakin kofan Lubabatu
tace "okay bazakiyi sallan bako bari nahadaki da Mummy" tsaki Auta tayi tace "anan
dukanku kukafi auki gulmammun babbunan banza kawai" "Mummy, Mummyyy" Lubabatu ta
kwalama Maman su kira, fitowa Mummy tayi ta tsaya daga bakin kofanta tana kallon
Lubabatun, cikin tsananin jin haushi Mummy tace "wai menene matsalan ku da yarinyar
nan eh, Zeenatu tasamata yaji a abinci kekuma mai kika biyota yanzu kimata, kasheta
zakiyi?" cikin jin haushi Lubabatu tace "Mummy nifa ko dakin ta banma shigaba fa,
kiranta nayi tazo muyi sallan la'asar" cikin fushi Mummy tace "to bazatayi ba
kubarta inta gama hutawa zatayi Allahu Gafurur Raheem, wuce kibace daganan wurin
munafukan yara sun tasa yar kanwarsu agaba wlh Allah zai saka mata" kallon dakin
Luba tayi auta tamata gwalo tana kyalkyacewa da dariyan iskanci da sauri Lubabatu
tawuce tana kunkuni tace "kiyita lalata ta yarinya bata salla kona asuba da kyar
takeyi" da sauri Mummy tace "dani kike magana ciki ciki?" dakinsu ta shiga batare
datace komiba, komawa dakinta Mummy tayi ta shiga bayi alwala ta dauro sanan tai
sallan la'asar tafito dakin Autan ta leka ganin ta lumshe ido yasa tadauka bacci
take tawuce dakinsu, ahankali tabude dakin dawani irin gudu Zeenatu tai bayinsu ta
garkame kofan kwafa Mummy tayi tace "ai wlh saina rama mata, ba yanzu zamu haduba
Zeenah" ta kalli Siddiqa dake kan dadduma tana kallonta tace "harya tafi Sadiq
din?" gyadamata kai tayi, tabe baki tayi tace "shine bakizo kin fadamin ba, anyway
kutashi dukanku kuje ku daura abincin dare, Luba tashi kije dakin auta ki sharo min
shinkafan data zubar akasa kifito da komi waje" wani kallo Siddiqa tama maman nasu
kafin ahankali tace "Mummy yanzu fisabilillahi ya zaki saka taje ta sharo abincin
da kanwarta ta zubar ba dole su dingajin haushin autaba in aka kuma tabata kidinga
masifa, ita autan batada hannu ne, bata iya aiki bane? Mummy gaskiya abinda kikeyi
baida kyau wlh kina nuna sonk......." yowa kanta da Mummy tayi yasa tai shiru Mummy
ta nunata da yatsa tace "ina baki girman ki amatsayin ki na yayansu baki kama kanki
ko, wlh duk randa kika karamin magana haka I will not mind muna gaban kanninki ne
saina kikkifa miki mari wlh, kitashi kiwuce kitchen kuhada dinner babanku yakusan
dawowa" tashi Siddiqa tayi cikin bakin ciki sosai ta zare hijabin jikinta tafice
daga dakin kaman zata tashi sama fuu, itama Luba tashi tayi Mummy tabita da harara
tace "kindaiji aikin danasaki kiwuce ki dauko tsintsiya kije ki kwashe abincin daya
bare inkin gama saiki wuce kitchen kuyi girkin" sanan ta kalli bayin tace "wlh
Zeenah inna dawo dakin nan nasame ki abayi baki wuce kitchen kun daura abinci ba
saina kakkaryaki dako ubanki inya dawo bazai ganeki ba" tana maganan tawuce tafita
daga dakin.



Agaban dakin Autan ta tsaya tana kallon yanda Lubabatu ke tattare shinkafan Auta
kuma na wasa da wayanta tana shishila kafa ko lura ma da Mummy batayiba. "Auta na"
jin muryan Mummy yasa da sauri ta dago kanta, murmushi tayi ta sauko daga gadon da
sauri tana gyara daurin towel din jikinta ashagwabe tace "Mummy na nazo yanzu?"
Tsaki Lubabatu dake shara tayi ta cigaba da aikinta, ahankali Mummy tace "a'a
anjima, me zakici yanzu dan bakici komiba, su dafa miki Indomie ne?" yatsine fuska
tayi tareda girgiza kai dan batada apatite ahankali tace "a'a, banajin yunwa yanzu
Mummy" murmushi Mummy tamata tace "to kwanta kicigaba da hutawa abinki" gyadama
Mummy kai tayi tana murmushi tai kwanciyan ta tana hararan Lubabatu da gefen ido
tana murguda mata baki, kallon Luba Mummy tayi tace "dau sharan kifita me kuma
kikeyi?" daukan pakan tayi tafita daga dakin Mummy tarufo kofan tawuce tai dakinta.
[6/3, 9:40 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_* 💫

_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always 💔


M Shakur



3️⃣4️⃣ 3️⃣ & 4️⃣



Ahankali Zeenatu ta lallabo tafito daga bayin tafito tana leke leke ganin babu kowa
yasa da gudu ta kwasa tai kitchen dinsu, babban kitchen ne sosai irin family
kitchen dinan dake dauke da komi irin na yan gayun nan, Siddiqa da Lubabatu tagani
suna aiki, Siddiqa dake wanke kayan miyane agaban tap ta kalleta ganin ta shigo
tace "zogashi kiyi blending kayan miyan nan nariga na wanke miki, stew zanyi" da
sauri takaraso ta karba ahankali itakuma Siddiqa takoma gaban gas, blender ta dauka
ta zuba komi ta nika saida tagama blending din tass sanan ta juye a bowl tazo wajen
ta mikama Siddiqa dake zuba rice a pot bowl din, karba tayi ta ijiye agefe tana
kallon fuskarta ganin duk tayi wani iri hakan yasa tace "menene Mummy tamiki
fadane?" girgiza kai tayi hakan yasa Lubabatu dake yanka su carrot itama ta tsaya
tana kallon Zeenah tace "to menene duk kikai wani iri?" hawayen dake kokarin zubo
mata tasa hannu ta share cikin wani irin yanayi na bakin ciki tace "Ya Siddiqa wai
mesa Mummy batason mu tafison Rahima, kuma muyakamata ta......" hannu Siddiqa
tadaga mata tareda girgiza kai tace "Zeenah karma kifadi abinda kikeso kifadi nasan
me kikeso kifada, konima nasan banson rashin kunyan Rahima but sometimes nafi
putting blame din akan Mummy, Mummy ko kadan bata barinmu mu nunama Auta the
difference between right and wrong kuma itama bata nuna matan, sometimes ba iskanci
zalla takemana ba she really feels is very okay abinda take mana dan haka Mummy
take nunamata, Mummy kullum kallon yarinya take mata, yarinyar da aka haifa jiya
batasan ta girma ba yanzu, Allah dai ya shiryata, she will change eventually I know
that komujima komu dade, now muci gaba da aiki kar Dady yadawo bamu gamaba" cigaba
da aikin sukeyi su uku gwanin ban sha'awa sunadan taba hira.



Babansu bala'in mai kudine amma irin mutanen nanne da bai yarda ya shagalar da
iyalinshi ba, dudda Mummy ta dameshi asamo musu mai aiki ki yayi acewarshi gashi da
yara mata dasuka tasa tadinga koyamusu komi sunayi da kansu, saisa breakfast kawai
Mummy keyi kullum shima dan suna zuwa makaranta da safene but weekend suke hadawa
dakansu, gyaran gida ma haka sukeyi, dudda kudinshi bai irin ginin mansion dinan
ba, gidanshi daidai daidai na rufin asiri ne 6 bedroom flat ne dakeda babban
compound daya wadatu da fulawowi.



5:38pm
Horn akayi mai gadi yafito da gudu yabude gate danko a bacci yasan horn din motar
Alhaji, shigowa wata babbar mota jeep tayi tai parking awurin da aka tanada dan
parking, da sauri Mai gadi yarufe gate yadawo wajen parking din daidai wani
magidancin mutum dake sanye da bakaken suit da neck tie ga wasu manyan littafai
guda biyu masu kama da textbook a hannunshi idanunshi sanye da fararen glass kana
ganinshi zaka gane daga aiki yake sabida yanayin shigan dake jikinshi, akalla
mutumin zaiyi 64-65yrs, da sauri Mai gadi yadan russuna yace "barka da dawowa
Alhaji ya kotu?" Mai gadi yay maganan yana mikamai hannu danya tayashi karban yan
littafan hannun nashi dan murmushi yayi yabashi yace "Sani, barka da warhaka, ya
aiki?" murmushi Mai gadi yayi yace "Alhamdulillah Alhaji" "to, to barkan mu"
mutumin yay magana yanabin gidan da kallo wanda dabi'an shine kullu yaumin idan
yadawo daga aiki saiyabi tsakar gidan da kallo yay inspecting gidanshi tsaf,
idanunshine suka sauka kan kayan da aka shanyasu kan flowers yace "menake gani
haka? Ban hana adena shanya a tsakar gidaba ga backyard nan inda akwai igiyan
shanya kala kala, waye da wanan aikin?" Alhajin yay magana azafafe ayanda yay
maganan zaka gane irin iyayen nanne masu fada da masifa sosai, cikeda girmamawa Mai
gadi yace "Allah huci zuciyan Alhaji laifinane wlh, kayan Auta ce kuma tariga
tafadimani idan suka bushe na shigan mata dasu na shafa'a ne, a yakuri bari na
kwashe su yanzu nakaima ta su ciki" da sauri Mai gadi yajuya zaije wurin kayan
cikin fada Alhajin yace "zonan, dawonan Sani" da sauri Sani yadawo, yace "this
should be the last time da Rahima zata saka aiki irin wanan kayi kanajina ko?"
gyadamai kai Mai gadin yayi Alhaji yajuya yay hanyar flat dinsu Mai gadi biye
dashi, da sallama mai kara as usual yayi yabude kofa ya shiga ciki yana kallon
ko'ina jin sallaman Abban su yasa da gudu har suna yar rige rigen fitowa su Siddiqa
suka fito daga kitchen din sukai wurin Mahaifin nasu cikeda murna. "Abba oyoyo,
Abba sannu da zuwa, Abba Sannu dazuwa" sosai ya shigo da masifa amma ganin yaranshi
duk sun fito daga kitchen da gudu suna mai oyoyo da sannu da zuwa cike da farin
ciki yasa yasakin musu murmushin dabai shirya yiba ya tsaya yace "yaran Abban su"
karban littafan shi Siddiqa tayi daga hannun mai gadi, itakuma Zeenah tace "Abba
nizan cirema neck tie" murmushi yayi yace "to yar albarka gashinan zoki ciremin"
itakuma Lubabatu da saurinta ta zaremai jacket din suit din jikinshi har rige rige
suke, murmushi mahaifin nasu yayi sosai ganin sun gama cirewa yasa yazauna kan
kujera yana sauke ajiyan zuciya yace "to nagode, Allah yamuku albarka yabaku mazaje
nagari" duk zama sukai kusada shi sukace Ameen Abba, Siddiqa tace "Abba yaya aiki
ya kotu? Mutane nawa kasa akai kai gidan yari yau?" dariya dukansu sukayi harda
Abban nasu dan Judge ne shi a federal High Court din Abuja kullum inya dawo sai
sunmai wanan tambayan, murmushi yayi sosai yace "yau babu kodaya, case akayi za'a
sake zama sanan za'a yanke hukunci, me kukeyi a kitchen dukanku gidan ya dumame da
kamshin girkin yan matan Abban su" da sauri Lubabatu dake kusada Abban tace "girki
mukeyi Abba mai dadi" waigawa yayi kafin ya kallesu duka, babu alamun wasa kan
fuskarshi yace "ina Rahima?" da sauri Zeenah kaman jira take tace "Abba tana daki,
Abba kagani Ya Luba saida taje takirata tazo muyi salla taki, tun sallan asuba
batayiba, Abba kagayau dazu data dawo daga school tama Ya Siddiqa da Ya Sadiq
rashin kunya harda cema Ya Siddiqa mayya, tacema Yaya Sadiq dansa ido, sanan muma
tamana rashin kunya, kuma kaga Abba mukadai keta girki bata tayamu komiba wlh Mummy
wai mubarta tahuta tagaji tana kwance adaki" shiru Abba yayi yana sauraron ta duk
cikin yaran nan nashi hudu baiga wacce take bashi matsala marajin magana irin
Rahima ba, gashi harga Allah kusan yafi sonta kan dukansu wanan natural haka Allah
yadauramai but bataji saisa ko kadan baya wasa da ita, basa shiri, duk gidan shi
kadai take tsoro, horata yake da kyau, sabida Rahima ne yanzu yake kokarin yasan
yanda zaiyi yadena tafiye tafiyen nan, babu randa baya mata addu'a kan Allah ya
shiryar da ita, koya zaneta taci kukan ta koshi baya hana anjima takara laifin
dayadaketa akai saisa yanzu yarage dukanta sosai danta girma baiso yamata illa
koyaji mata rauni tana mace, ajiyan zuciya yayi ya kalli Siddiqa babban yarshi ta
farko dan dukta fisu hankali ga fadan gaskiya, ahankali yace "hakane Mamana?"
gyadamai kai tayi tace "hakane Abba" kwala mata kira yashiga yi. "Rahima! Rahima,
Rahima!!!"




A mugun zabure Auta ta tashi daga kan gadon jin muryan Abban su na kiranta, tsoron
Abba take sosai bana wasaba, bakinta har rawa yake tsabagen firgita tace
"na.....Na'am Abba, ganinan zuwa" gyara daurin towel dinta tayi tsabagen rudewa
tama manta yahanata yawo agida da towel tafita daga dakin da sauri sauri gudu gudu
tai falon.



Shigowa falon tayi harta karaso gaban Abba jikinta bari yake, sosa keya tayi arude
tawani kwantar da murya looking so innocent kaman ta Allah, ahankali tace "sannu da
dawowa Abba" tundaga kafa Abba kebinta da kallo daga ita saidan mustard towel din
dake daure a kirjinta data daura tun dazu bayan tafito daga wanka ya tsaya mata
acinya kanta babu dan kwali tai zuru zuru tana kallonshi, ko jiya saida yamata fada
kan wanan daurin towel din gashi yauma same thing still saida ta daura, Zeenah Abba
yataba batare daya janye idanunshi daka kan Auta datai zuru zuru tana kallonshi ba
yace "je dakina ki dauko min dorinar nan mai baki hudu Zeenatu" dorina dataji Abba
ya ambata yasa tafashe da kuka sosai jikinta narawa kaman mazari tace "Abba dan
Allah ka yakuri menayi eh? Dan Allah karka dakeni banison dorinar nan please, Ya
Siddiqa please kar Abba yadakeni" taja hannun Siddiqa takama tarike tana kuka sosai
tana yarfe dayan hannun tana kallon Abba dahar lokacin kallonta yake irin kallon
nan dake saka hanjin cikin yara kadawa in fear.




Ganin Zeenatu tadawo rikeda dorinar yasa tawani irin kurma ihu ta kwalama Mummy
kira. "Mummy, Mummy kizo, Mummyna wayyo Allah na zan mutu" tawani fada jikin
Siddiqa ta chukwikwiyeta tana kuka kaman za'a nikata a injin, Zeenatu da Lubabatu
sai gimtse dariyan su suke dadi kaman ya kashesu ganin yanda mara kunyan ta rude
haka, har Allah Allah take Abba yafara lallasata, all this haukan kukan tanayi
kaman zata koma cikin Siddiqa ko tashi Abba baiyiba yanadai rike da dorinar a hannu
yana kallonta cikeda takaici, ganin towel din jikin nata na neman kwancewa yace
"saki Siddiqa kitashi kizonan" sakin Siddiqa tayi tana kuka sosai ta sauko daga
jikinta tana rike da hannunta tana gyadama Abba kai kaman kadangaruwa, gabanshi
Abba yanuna mata da dorinar yace "kneel down here kuma nace kisaki yayan ki ko,
saken mata hannu" arude tasaki Siddiqa tana kuka sosai tana yarfe hannu tace "Abba
dan Allah karka dakeni kaji dan Allah" tana maganan tana kneeling a gabanshi inda
yanuna mata tana gyara daurin towel din jikinta tana kuka sosai, daidai lokacin
Mummy tafito arude. "wayatabamin Aut......" kasa karashe maganan tayi sabida mugun
kallon da Alhaji yamata ta tsaya chak agaban corridor, Rahima na ganin Mummy takara
karfin kukan ta tanama Mummy alamu da hannu datazo ta ceceta tana kallon Abban nasu
tana kuka, ajiyan zuciya Abba ya sauke anatse yace "Rahima!" cikin kuka tace "na'am
Abba, Abba dan Allah ka yakuri, wlh wlh bazan karaba, Abba in kanawa binta
Rasulullahi in kanawa iyayen ka kayakuri Abba, Mummy dan Allah, Mummy kizo" tai
maganan tana kuka sosai tana mikama Mummy hannunta kaman mahaukaciya, ahankali
Mummy takarasa shigowa cikin falon cikeda damuwa ranta duk abace, takaraso gaban
Abba zatamai magana ya daga mata hannu ganin babu alamun wasa akan fuskarshi yasa
tai shiru, cikin kakkausar murya yace "Rahima nahanaki yima yayyunki rashin kunya
koban hanaki ba?" cikin kuka sosai tace "wlh kahanani Abba" gyadakai Abba yayi yace
"bance miki kidinga kifitowa kuna aikin gida tareba" cikin kuka tace "kacemini haka
Abba" ahankali Abba yace "good, ban hanaki yawo agida da towel ba?" fashewa dawani
irin kuka tayi sosai tace "e....e..h kahanani Abba" "bance kidinga fitowa kuna
salla tare da yan uwanki kullum ba?" gyadamai kai tayi hawaye kaman anbude dam tace
"kacemini Abba" cikin kakkausar murya Abba yace "laifin ki nawa kenan?" cikin kuka
tana kara mikama Mummy dake tsaye gefen Abba hannu tanaso tariketa tace "laifina
hudu Abba" shiru Abba yayi ayanda yakejin haushinta inyace yamata hukunci da fushin
nan zai iya yimata illa, he is just trying to calm himself down, ajiyan zuciya
zuciya yasauke yace "jeki dauro alwala kizo nan kiyi salla agabana inkinga dama ki
kara dawomin nan da towel, tashi daga nan, will you get out of my sight ko saina
saba miki!" ya daka mata tsawa da gudu ta tashi tai ciki tana kuka sosai, cike da
kunan rai Mummy tace "Alhaji dan Allah kadinga yimata ahankali...." "don't tell me
rubbish Maryam!" Abba yadaka mata tsawan da saida yasa tai shiru da sauri, cikin
fushi yace "I said don't tell me rubbish Maryam! while kullum ina fita nema dan na
wadataku keda yayan mu, nabarmiki duka yaran nan namu amana, ke kina nan kina
lalata Rahima, babu wanda Rahima ke gani da daraja aduniyan nan, bata ganin kowa da
gashi, could you imagine saidai mai gadine zai kwaso mata kayan data shanya which
am sure bama ita ta wanke suba, kina gidan nan tareda dukansu kin kasa sata tai
salla me amfanin kito eh amatsayin ki na mahaifiyarta? An gayamiki Rahima yarinya
ce har yanzu? Allah zai tambayeni dagani harke kan yanda muka bama wayan nan yaran
tarbiyah" yanuna mata duka su Siddiqa da kansu ke kasa ganin ran Abba yau yabaci
yanama Mummy fada which of course sunsan she deserves it, Abba yacigaba yace "yaran
nan matane, idan bamuba Rahima tarbiyah ba intai aure me zata bama nata yayan iyye?
Wani irin hali kikeso taje tana nunawa agidan mijinta, angayamiki zata dawwama tana
rayuwa damune? Dazu da rana awurin aiki Aminina yasamen da magana dayamin zafi
yamin ciwo amma nasan alkhairi yake nufi dani da bazaizo yamin maganan ba" yadanyi
shiru yana sauke ajiyan zuciya sanan yace "yau zai taho aiki yabiya ta school dan
ijiye su Aisha da Hafsat a school yaga driver ya sauke Rahima tana sanye da Jean fa
da t-shirt sai dan ficicin gyale akanta rabin gashinta awaje agabanki yarinyar nan
tai shiga kaman yarinyar arna ta tafi makaranta haka baki hanata ba, idan kinsan
bazaki iya bama yarana tarbiyah ba zanje na auro wacce zata basu, this children are
my life, gift din da Allah yabani ne inhar zan fita nema nabarki dazu bazaki
koyamusu abinda yakamata ba wlh zan iyasaka konawane na auro wata matan inhar ta
yarda tai na'am zata bama yarana tarbiyah nagayamiki" faduwa gaban Mummy ya shiga
yi, tasan halin mijinta tsaf kaifi dayane wlh kuma zai iya aikata hakan, babu
abinda ta tana aduniyan nan kaman kishiya, ahankali ta tsugunna tareda kama
hannunshi tashi Siddiqa tayi daga wurin hakan yasa sauran yaran ma duk suka tashi
sukai dakinsu, cikin damuwa sosai Mummy ta damke hannun Abba ahankali tana kallon
fuskarshi tace "nai kuskure baban Siddiqa, amma kayakuri, ka gafarce ni zan gyara,
ka gafarce ni dan girman Allah karkace zaka karo aure sabida tarbiyah yara, bagasu
Siddiqa ba banine nabasu tarbiyah ba duk nice ko, to kayakuri dan Allah" tai shiru
tana kallonshi ganin yaki kallonta har lokacin bala'ine bayyane karara akan
fuskarshi yasa ta fashe da kuka mara kara sosai ta yanda yaran bazasu jisuba irin
kukan nan mai karya zuciyan miji, cikin kuka tace "nayi kuskure, na yarda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login